Showing 63001 words to 66000 words out of 132090 words
Chapter 22 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
ce “Na yi dana sanin ha’duwata da ke a yau, na yi kuma Takaicin da ya zamo ke ce Matar da aka aura min, ban da umarnin Mahaifiya a yau Zan sake ki saki uku.”
Da sauri Ayra ta ware idanunta a kansa, idanun nasu suka gamu a lokaci guda ba tare da sun shirya ba, ji ta yi ba zata iya k’yale kalamansa ba ba tare da ita ma ta tofa nata ba, ita fa dama ta sani Maza duka halinsu ‘d’aya ga shi nan tun a ranar farko daga ‘daura aurensu zai bayyana mata halin y’an maza ai kuwa daidai take da shi. “Da igiyar a hannuna take da ko minti biyu aurenka bai cika a
Kaina ba, kamar yarda Biyayya ka yi nima ina tabbatar maka biyayyar na yi, Biyayya Mai cike da taken ‘daukan fansa, ban shirya aure ba ban kuma ‘dau kowane namiji a bakin komai ba banda Karen farauta na, da ina da iko duk mazan duniya sai na mayar da su bayin Mata, tunda kun zubar da darajar da Allah ya baku, abu na k’arshe da zan gaya maka ba kowacce banzar magana Ayra Gaya take ‘d’auka ba….” Ta fa’da tana zabga masa kallo mai cike da tsana da Takaici iri-iri, da gaske ji take kamar ta tashi ta rufe shi da duka. Yarda ta ta zuciyar take haka shima ta sa take zafi da tafasa fiye ma da tata, takaicinsa na farko yarda yake fatan ganin Angel nitsatstsiyar
mace ba haka ya sameta ba tunaninsa a yarda ya ganta da shigar kamala da hijabi har k’asa bai yi zaton zai samu tambarin karuwanci a kanta ba. Kullum addu’arsa Allah ya ha’da shi da Angel su yi aure ta haifa masa yara masu suffarta da kamalarta ku san duk wanda ya san shi da Aljanarsa har Aman da yake k’arami ya san burin Dadansa na ganin Angel har idan yana so ya masa abu yaron ya kance Allah ya baka Angel Dada, sai ga Angel ta zo masa a yanayin da yake k’yamatar duk wata Mace. B’acin ransa ya cigaba da hauhawa da ya gano itama ba son sa take ba sab’anin wa’dancan Matan da suke masa masifar So. Ya mik’e cike da izza yana sake bin ta da kallo kafin cikin cunkushewar murya ya furta “Barkanki, Allah ya taimakeke da ba kya son auren, dama duk wasu tamba’daddu Ai ba su fiye son a aurar da su a killacesu ba, dalili saboda ba za su samu damar huld’a da kowane karabitin namiji ba, ki k’addara gidan Turaki kamar Prison ne. Gwara ma tun farko ki san yarda kika yi kika bijirewa auren nan cikin sauk’i don ni ban shirya zama da Karuwar da mutane suka santa a kan Karuwanci ba…”
Cak numfashin Ayra ya daina tafiya yarda take so, wani abu ya zo ya tokare mata zuciya Karuwa! Yau ita ake kira da Kalmar Karuwa ta bud’e baki zata yi magana sai dai kafin ta furta komai ta hango shi ya fice a zafafe har yana bugo mata k’ofa da k’arfin gaske. Da sauri ta mik’e tana shirin bin sa ta ci masa mutunci Majeeda ta shigo ‘d’akin nata tana ‘dan sakin murmushi. “Amarsu ta ango!” A zafafe Ayra ta ‘dago tana kallonta kafin wasu hawayen bak’in ciki su shiga suntiri a idanunta murya a k’untace ta ce “Yaya Majja bana so please!” Daga haka ta koma
Kan gado ta kwanta tana tunanin a yanayin da zata shiga gidan wancan mutumin mai amsa sunan MIJINTA! Abu ‘daya da ta yi farin ciki da shi ta san ba zai wahalar sakinta ba tunda ta hango bahagowar tsanarta a idanunsa mai caku’de da jin matsanancin haushi ba tare da ta san laifinta garesa ba, illa son zuciya da ya bi wajen saka mata sunan Karuwa! Kalmar da take fita bisa gaskiyarsa har k’asan zuciyarsa, ya zama wa jibi ta nuna masa ita ‘din Karuwa ce kamar yarda aka fa’da ya ji ya kuma yarda. Sai a lokacin ta ji k’amshin turaren da ya bar mata a ‘d’akin ya addabi hancinta ta dinga jin rashin da’din turaren har k’asan ranta. A zafafe kamar kuma yana ‘dakin ta mik’e da azama tana hararar in da ya zauna, kafin ta ‘d’auko nata turaren ta fara feshe ‘d’akin da shi, da niyyar nata k’amshin ya rinjayi nasa ko hancinta ya huta da shak’ar k’amshin nasa mai saka ta dinga tuna mummunar fuskarsa. Ga mamakinta kamar turi ta yiwa na sa turaren don ba abinda ya ragu sai ma k’ara k’amshin da ya yi a ‘dakin. Majeedah dai na tsaye tana bin ta da murmushi k’asa-k’asa don sarai ta fahimci abinda take nufi. Wannan zarka’de’den mijin ta san lokaci ka’dan zai sace zuciyar Ayra, yanayinsa na kamun kai da nutsuwa Uwa uba kwalliya da fasali mai kyau irin na cikakkun maza ya isa ya fisgo hankalinta garesa. A zuciyarta ta ce “Dama kin daina wahalar da kan ki yarinya, k’arewar shak’ar k’amshin turarensa nan da sati guda za ku zama k’ark’ashin inuwa guda zan ga kuma ga uban da zai hana shi kusantarki. A zahiri kuwa murmushi ta saki ta ce “Sai ki tashi ki fita a gaisa da mutane tunda Dodon naki ya tafi.” Ayra ta yi burus da ita kamar bata fahimci mai take cewa ba.
Tunda ya samu ya fice daga gidan ya saki jin yanayin zuciyarsa ya cigaba da zafafa, Ina ma duk abinda ya gani mafarki ne, ba Angel ‘dinsa bace, da k’yar ya samu ya isa inda motarsa take abokinsa Kamal yana jiransa. Bai bi ta kan kallon da Kamal ‘din yake masa ba, ya fa’da motarsa da sauri ya zauna a mazaunin Driver yana kallon Kamal a zafafe ya ce “Zaka shiga ko na yi gaba?” Kamal ya saki ‘dan murmushi kafin ya bu’de motar ya shiga yana fa’din “Su kuma sauran mutanen da ka bari a tsaye suna jiranka su maka Allah ya sanya alheri fa?” “Su nemi Uban da ya gayyato, look Kamal bana son magana please and please!” Kamal ya saki murmushi yana fa’din “Mhnm, ba ni na kar zomon ba…” a guje ya finciki motar bai tsaya ko ina ba sai a gidansa da yake Riba’do Road. Bai saurari Kamal da yake masa magana ba illa cilla masa key ‘din motar da ya yi ya fad’a cikin gida yana fa’din “See you later.” Kamal ya bi shi da kallo sam bai damu ba, saboda a karo da dama irin halin da abokinsa yake kasancewa kenan, a duk sanda aka ce an masa aure tun bayan mutuwar matarsa, sai dai na yau ya fi na kullum don daga ganinsa a harzik’e yake harzik’in da ya bayyana har a saman k’wayar idanunsa.
Kasa kai kansa ‘d’aki ya yi, ya ci burki a falonsa. Kwanciya ya yi kan carpet idanunsa runtse yana tunano a sanda ya fara ganinta sanye da dogon Hijabin da ya mata kyau, ha’da idon da suka yi da saurin turo bakinta alamar k’unk’uni tana jan nik’ab ‘d’inta duk ba su b’ace daga kansa ba, suna nan zaune ra’dam a zuciyarsa kamar yanzu abubuwan suke faruwa. Ya sha mafarkinta a matsayin matar da yake so, ya sha mafarkin shine mijin da zai amshi budurcinta ashe wasu banza ye can sun amshe, bai san da maza nawa ta yi mu’amala ba abinda yake assasa bak’in cikin zuciyarsa kenan. Ya sake bu’de pic ‘d’inta a wayarsa samun kansa ya yi da zabga tsaki da cilli da wayar ya tura hannunsa cikin gashin kansa a hankali yana jin kamar ya saki kuka ko ya samu sauk’in zuciyarsa…
💔💔💔💔
Kabiru ya dinga bin Kamilu da kallo da goro da alawar hannunsa, muryarsa a raunane ya ce “Kamilu an ‘daura ko?” Kamilu ya ‘daga kai yana washe baki ya ce “Ai Auta ta yi goshi, manyan mutane ne suka aureta don baka ga cikar da aka yi ba, a idanuna dai na ga manyan gwamnati masu rik’e da manyan mak’amai duk sun halarta.” Kabiru ya sunkuyar da kansa yana jin k’wallar da take shirin zubo masa ta fara zuba ba k’akk’autawa, takaicin kansa da dana sanin abubuwan da suka faru a baya suka dinga bijiro masa, ji yake da yana da iko da ya mayar da bara bana, tabbas da ya dawo da rayuwarsu ta baya ya nunawa Talatu tsananin Soyayya ya kuma so abinda za ta haifa ko da za su kasance Mata ‘dari ne. Fitowar Karima daga ‘d’aki cikin zafin rai ne yasa Kamilu fasa fa’dar abinda ya yi niyya. Kabiru ya dinga dubanta cike da takaicin yarda take masa abubuwa kamar ba Mijint
aurenta ba, yaranta mazan da yake tunk’ahon ta haifa masa sun zama sam ba su da amfani tunda ba sa tausaya masa sun kuma raina shi matuk’ar raini musamman suka bi turbar da nahaifiyarsu ta ‘dora su na shi ‘din ba Uba bane na gari kuma kaf ‘dawainiyar gidan ita take yi. Ya dinga tunanin irin gatan da ya dinga musu a lokutan baya ya mayar da y’ay’an Talatu ba komai ba don kasancewarsu Mata sai ga shi yanzu sune suka zama wani abu, sune suka zama y’ay’an da za’a kalla a yi alfahari da su ba wa’dannan da ba su da tarbiyyar arziki ba. “Auren wa aka ‘daura? na ji ana ta kambama Mijin a baki kamar wani shugaban k’asa.” Kamilu ya bita da kallon banza, kamar yarda ya saba a duk sanda za su ha’du, bai bata amsa ba illa mayar da kansa kan Kabiru da yayi ya ce “Kana ji ko Yaya? Idan an kwana biyu In sha Allah daga can Gayan za mu yi gangamin zuwa kaf ahalinmu mu bawa Talatu hak’uri, duk da mu ma mun yi kuskure mun cutar da ita da yawa a rayuwa haka za mu toshe kunnenmu daga dukkan abinda zata ce mana….” “Ahayye cas! Kace dai kawai shegen kwa’dayinku za ku je ku nunawa Talatu, saboda rashin zuciya In sha Allahu sai ta muku korar kare… arzikin nata na karuwanci da ba’a san asalin ungulu bane sai a ce daga masar take.” Kamilu ya tab’e baki yana kallonta “Don uban mutum ya ce Ungulun ba fara bace mana, kin ga Karima idan kina jin y’an rashin mutuncinki ki daina tsunduma Kamilu a ciki, don ni ba k’aramin aikina bane na b’atar da mace Wallahi shima Yayan shi ya ga zai iya kayan rashin mutuncinki. Kuma zuwa gurin Talatu kamar mun je idan ma Maular ne za mu je a hakan tana da abinda za mu Maulatan ne, gayyar tsiya arna a idi.” Ya mik’e a zafafe yana fa’din “Yaya Allah ya k’ara sauk’i na bar bak’i a waje suna jirana.” Kabiru ya ‘d’aga kai yana sakin murmushi mai bayyana k’uncin da yake ciki “Nagode Kamilu, kace musu nagode da ziyarar da suka kawo min.” Kamilu ya saka takalminsa yana fa’din “Sai mun zo In sha Allah.”
______________
Tsaf Yayyen Amarya suka shirya gidan Amaryar da yake Riba’do Road sun kashe ku’di har da na mamaki kaya ne y’an turkey masu tsanar gaske aka zuba mata, gida ya yi ras da shi sai jiran amaryar da zata tare a ranar da daddare. Ayra kallonsu kawai take, tana tausaya musu yarda suke rawar jikin auren nan, Auren da ya sakawa suna Jeka na yi ka.
Magribar Fari Amma ta shiga ‘dakinta ita da mai gyaran jikin da zata mata na tafiya gidan miji, bata yi musu ba aka gyareta tsaf sai tashin k’amshi take tamkar wacce aka b’arar da kwalaban turare a jikinta, ita kanta k’amshin har tsaya mata yake a mak’ogaro, haka aka na’deta cikin tsumammiyar laffaya fara tas da ita. Cike da sanyin jiki Amma ta zauna a gefen gadon cikin rawar murya da son kawar da kukan da yake son kufce mata ta ce “Ayra! Alhamdulillah Nagode Allah da ya nuna min aurenki, ba zan ce miki komai ba game da zaman aure na san kin san komai tunda ke ba jahila bace, sai dai ina neman alfarma‘d’aya a wajenki wacce itace cikamakin duka buri na da farin cikina Ki yi Min alk’awarin za Ki yiwa mijinki biyayya, biyayya da ake da suna biyayya kwatankwacin wacce na yiwa Babanki, kada ki ba ni kunya Ayra please kada ki yi abinda Mijin zai dinga kiranki da sunan y’ar Mace ki min wannan alfarmar Ayra don Allah.” Ta fa’da kuka na kufce mata kukan da take yi ba don komai ba sai don ta saka Ayra rauni a zuciya ta saka ta ta amince da alk’awarin ko da bata shirya ba. “Wannan ce kawai sakayyar da nake so ki yi min a matsayina na mahaifiyar da ta raineki ita ka’dai ba tare da Uba ba, cin ki da shan ki iliminki suturarki duk ni ce, ki tina irin k’alubalen da na sha a kan ku a rayuwa wannan ne kawai abinda nake so ki yi min…” Kuka ne ya kufce wa Ayra fiye da kukan da take yi, ya zata yi ? Ya zata yi da Umarnin Mahaifiyarta da take jin kamar ta k’ullla mata dabaibayi ne, kamar Amman ta shiga zuciyarta ta ga mai take k’ulla wa waccen mutumin da aka kira da sunan Mijinta. Jin tsananta kukan Amman tana fa’din “Na san ba zaki min wannan alfarmar ba Ayra….” Da sauri ta fa’da jikinta tana furta “Na miki Amma, na miki alk’awari ko da hakan yana nufin rusawa nawa farin cikin ne ko da hakan ya na nufin ajalina ne, zan masa biyayya irin biyayyar da kike so Ammatyyyyy….”
Ta fa’da cikin wani irin gunjin kuka mai nuni da zallar zafafar zuciya….
Jikarnashe✍🏽
Takaicin Uba….
*Nazeefahnashe* ✍🏽
32.
💔💔💔💔
*INGANTACCEN ZANCE*.
*Ina da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*.
*Haka uwargida ma ban barta a baya ba da irin nata tagomashin*
*Kaya ne masu kyua ba garabiti ba*
*SAIWOWIN itatuwane da basu da illah*
*Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.*
*Akwai hadaddun turaren wuta, da zai kawar Miki da karni da bashin damina*.
*Kawai ki tuntu'bi wannan lambar dan samun gamshasshen bayani*
*Nation wide delivery*
*08032773332.*
✍️.
Zan masa biyayya irin biyayyar da kike so Ammaty, zan masa girki da duk wani abu da ya danganci matar aure na gari,amma please kada alk’awarin da zan miki ya shafi gangar jikina don Allah Amma ba zan iya ba, ba zan iya ba!!” Amma tana murmushi ha’de da matsa hannunta ta ce “Za ki iya In sha Allahu zaki iya Ayra, idan har ya kusantoki ki amince masa shine amfanin auren, ba ki da ikon haramta masa jikinki Alhali ubangiji ne ya halasta masa ki yi hak’uri ki kuma dinga karanta Hasbunallah a zuciyarki, komai zai wuce da izinin Allah, ki kuma saka a zuciyarki ba duka maza bane halinsu ‘daya da yawa daga cikin maza halayensu sun farrak’a da na mahaifinki, ina ji a jikina biyayyar da kika mana ba zata tafi a banza ba, In sha Allah kin dace da mijin k’warai Ayra, kamar yarda na dinga rok’on Ubangiji na san kuma ya amsa In sha Allah ba za kuyi Boranci a gidajenku ba, za ku zama ababan So a wajen Mazajenku ababan tattali da nuna kulawa a kowane hali, ina ji a jikina kuma addu’ata ta amsu ki saka a zuciyar ki biyayya kika je gidan Mijinki, biyayyar da zata kai ki dukkan Matakin nasara Allah ya miki albarka ya sadaki da dukkan alhaiiran da suke cikin gidan aure, ya nisanta ki da sharrin da yake cikinsa.” Zuwa lokacin fa’dar yanayin da Ayra take ciki abin ba zai kwatantu ba, ta dai san k’irjinta ya yi nauyi, nauyin da bai tab’a yi mata ba ta dinga kokawa da numfashinta da yake fitar da k’yar. Kukan ma ya ‘d’auke tsam daga idanunta ba mamaki tashin hankalin ya zarce na fitar hawaye sai dai a dinga furzar da shi ta hanyar numfashi mara da’di, Da gaske ba zata iya ba ba zata iya ha’da makonci da wancan mutumin da ya kirata kai tsaye da sunan Karuwa ba!
Tana ji tana gani a karo na farko a ka b’anb’are jikinta daga na mahaifiyarta Majeeda ta maye mata gurbin Amma ta tabbata dai ita Ayra yau zata yi sallama da Amma zuwa gidan Aure, abinda hasashenta ko mafarkinta bai tab’a kwatanto mata ba. Amma ta damk’i hannunta ta rakata har mota tana tofa mata addu’oi masu mahimmanci daga bakin Uwa wacce ta amsa sunanta UWA TA GARI. Sai da ta saka a cikin mota sannan ta juyo karo na farko tana sakin nata murmushin mai tafe da ajiyar zuciya da hawaye masu ‘dimin gaske, tana murna da auren Ayra a wani b’angaren kuma tana takaicin rabuwa da Ayra mafi soyuwa a cikin y’ay’anta. Ta saka hannu tana share hawayen ha’de da fa’din “Khairan In sha Allah” Jikinta a salub’e ta koma cikin gidan zuciyarta cike fam da tunanin ko wane irin zama Ayra zata gudanar a gidan Mijinta duk da dai ta yiwa abin riga kafi ta hanyar saka ta yi mata alk’awarin da ta tabbatar ko da Ayran zata wahala sai ta cika mata shi saboda yarda ta san yake darajata fiye da kowa a duniya haka take girmama zancenta fiye da na kowa a duniya.
***
Tas suka sake gyare gidan suka ba’deshi da turarukan wuta. Kafin Majeeda ta ciro kwalbar Humra tana murmushi ta ‘dorata a kan mudubinta, ita ka’dai ta san tarkon wannan Humran mai gigita maza kenan da zarar mace ta yi amfani da ita to fa namiji bai isa ya tsallake tarkonta a wannan daren ba, Sirrin mutanen Chadi kenan daga wajen Anty na Surayya dee marubuciyar Halin yau, gida ya ba’de da K’amshi musamman sun san Ayra ma’abociyar son k’amshi ce kada ma na bare bari ya ji labari da na turarukan OUD. Suka sake mata nasiha duk da sun san bai zama lallai ta amshi irin wannan nasihar ba sai dai nan gaba zata yi mata amfani lokacin da za su daidaita da Mijin.
Gida fa ya yi tsit, an bar Ayra daga ita sai halinta. Ranta a b’ace ta janye lullub’in abayar da yake jikinta ta fara bin ‘d’akin da kallo da ya ji set ‘din fararen furnitures farare k’al da su, sai ratsin ash (ruwan toka ka’dan) ta mik’e a hankali tana zagaye ‘d’akin kamar mai son