Showing 90001 words to 93000 words out of 132090 words
Chapter 31 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
rubuta ta kuma sanar masa idan ya tashi neman matarsa ta san inda take ya nemeta a wannan layin. Sannan ta mik’a wa Innar Kabirun ta mik’e tana fa’din “Ni zan wuce Inna Ki k’ok’arta ki ajiye masa takardar nan tana da muhimmanci sosai.” Sannan ta ajiye mata Naira dubu biyu a ku’din da Hajiya ta bata y’an d’ari bibbiyu ta fito daga ‘dakin tana yiwa matan gidan sallama da suke mata kallon k’urilla.
Suna fitowa ta ha’du da Kamilu k’anin Kabirun, ya ‘dan washe baki yana kallonta kamar ya santa hakan yasa ta ‘dan tsaya suka gaisa, kafin ya ce “wani kike nema ne Hajiya?” Jin sunan da ya kirata da shi yasa tana murmushi ta ‘daga kai “Wallahi Kabiru nazo nema sai na taki rashin sa’a baya nan.” Kamilu ya jinjina kai “Ai Kabiru ya yi b’atan dabo shekara guda muma bamu da labarin sa ba zaki gansa a garin nan ba sai tasa ta ciyoshi idan sak’o ne ki bayar a ijiye masa.” Jummai ta zage jakarta ta sake cirar takarda da biro ta rubuta numberr wayarta ta mik’a masa tana fa’din “Don Allah ka mata ajiya mai kyau, ka sanar da shi idan ya tashi neman matarsa Talatu ya kira ta wannan layin ni na san inda take, tunda Talatun ta rantse min ba zata dawo ba, to ni kuma ina jin tsoron halin rayuwa kada nan gaba ya buk’aci haka shi yasa na yiyo tattaki nazo.” Kamilu ya amsa yana fa’din kin kyauta kuwa, ni kaina da a kimtse nake Ai da naje na ga Talatun, amma idan na tashi zuwa In sha Allahu zan kira ta wannan layin sai a min kwatance nagode sosai.” Jummai ta zaro dubu uku shima ta ba shi, a zuciyarta tana fatan Kabirun ya samu sak’onta kwana kusa. Wannan shine silar sanin Kabiru inda Talatu ta koma da yaranta.
___________
Bayan shekara guda da zuwan Jummai garin su Talatu ba wani labari da ya canja don har a wancan lokacin Kabirun bai je garin ba, shi kuma Kamilu da yake son zuwa Jummai ta k’i ba shi kwatance don bata son zuwansa yanzu kada asirinta ya tonu Kabirun dai take son yazo.
Lokacin Ayra ta sake girma don shekararta biyar kenan cif har ta shiga makaranta mai tsada Hajiyan ta sakata ake kaita Intercontinental idan ka ga yarda ta sake kyau sai ka zata y’ar gidan wani hamshak’in mai ku’din ce, ta yi kyau na ban mamaki, duk Inda Hajiya zata Ayra tana manne a jikinta duk k’asar kuma da Hajiyar zata in dai ba lokacin Makaranta bane da Ayra take tafiya, duk wanda ya san Hajiya ya san Ayranta, mutane da dama zato suke jikarta ce. Tafi sabawa da Hajiya fiye da Amma mahaifiyarta da itama ta yiwa Hajiyar kara sam bata shiga sabgar Ayra. Ta rungumi sauran yaranta da suka zama y’an mata sosai.
Ahalin gidan Hajiyar suna zaune cikin kwanciyar hankali, Jummai ma tuni ta zubar da makaman yak’inta, don duk ta inda ta bi da son soke Ayran a wajen Hajiyar bata samun nasara hakan yasa ta gaji ta zuba musu ido, sai dai bata fasa tuntub’ar Kamilu ta waya ba ta ji ko Kabirun ya shigo gari kamar yarda suke fata. A wani kira da ta yiwa Kamilu ya tabbatar mata Kabirun ya shigo gari har ma ya yi arzikin da ya bawa kowa mamaki sai dai da ya masa maganar zuwa wajen Talatun basu rabu da da’di ba, ya ce ba ruwansa da Talatu da yaranta ya bu’de sabuwar rayuwa a lagos bayan Karima ma, yanzu ya k’ara mata ‘d’aya kuma sun haifa masa yara mazan da yake so, don haka Ya barwa Talatu yaranta Mata ta k’arata. Wannan labari bai yiwa Jummai da’di ba don bata so jin haka ba da kuma Kamilun ya mata maganar zuwa sai ta ce ba yanzu ba ya jirayi lokaci.
__________
Ana haka katsaham ciwo ya kama Hajiya ciwo mai zafin gaske, wanda duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata, ba kuma zaka tsammaci zata sake wayar gari ba. Ciwon ya ci k’arfinta, duk wani masoyin Hajiya yana cikin tashin hankali, kuma duk k’asar da aka je sai dai a jagwalgwalata a dawo Amma ba alamun samun sauk’i a tare da ita.
A wani dare da Talatu ba zasu tab’a mantawa da shi ba, Hajiyar ta tarasu gaba ‘dayansu da suke k’ark’ashinta. Cikin wahala da zafin ciwo ta zuba musu ido duk hankalinsu a tashe yake musamman Talatu da take ta kuka ba k’ak’kautawa ji take da tana da iko da ta sarayar da ruhinta ga Hajiyar, Hajiyar ta rayu ita ta mutu. Sai dai bata da wannan ikon rai da mutuwa duka a hannun Allah suke.
Cikin raunin murya da k’arfin hali Hajiyar ta saka aka mik’ar da ita zaune aka jinginata da filo. Muryarta k’asa sosai da sai ka saka kunnenka sannan zaka ji abinda take cewa ta ce “Ba shakka ina ji a jikina lokaci na ya yi, Alhamdulilah da Allah ya kawo ni har yanzu ba da k’arfi na ba ko dabarata ba, sai don shi yaso, yanzu kuma da yake son amsar rayuwata ban isa na hanashi ikonsa a kaina ba. Ku yi hak’uri ku yi hak’uri sannan don girman Allah ina rok’onku alfarma kada ku manta da ni a addu’oinku, ba ni da kowa ba ni da komai ba ni da mai yi min addu’a sai wanda ya dubi Allah ya tuna da ni. A tsawon zama na da ku idan na cuceku ina neman yafiya nima kuma na yafe muku. Abu na gaba na san idan na Mutu y’an uwa na dangin iyayena da suka yi saura da dama burinsu su gaji dukiyata shi yasa kuka ga da bani da lafiyar nan kullum suna tare da ni, to na san ba zaku samu komai daga kason gadona ba, ni ma kuma bana son dukiyar ta zama ta magada kawai nafi son na samu tagomashin lada ni da iyayena da y’an uwana ta sanadiyyar ta, don haka na saka aka gina masallatai aka kuma hak’a rijiyon boreholes a k’auyuka sannan aka gina majalissun ilimin addini, aka kuma damk’a kaso mafi tsoka a gidan marayu da gajiyayyu marasa gata.Abinda ya rage min shine ku da kuke k’ark’ashina kuma ku samu wani abin daga dukiyata don bana son bayan babu ni ku tagayyara na tabbata da zarar na mutu makusanta za su sallameku daga gidan nan, ina zaku? Wace Sana’a za ku yi ku dogara da kanku duk wannan ba shine a gabansu ba, don haka na gayyato lawyoyi har biyar ga su nan a zaune da nake son a yi komai a gabansu su zama shaidu. Sarkin gida Jummai Rabe, Talatu da Mai gadi akwai gidajena guda biyar a rijiyar zaki na bawa kowa ‘daya a cikinku ya zauna, da tsabar ku’di Naira miliyan biyar biyar. Sai Talatu da na bawa y’arta company bana fatan ko bayan raina wannan magana ta tashi. Akwai ku’di da na zuba masu tarin yawa a asusun companyn Ayra da nake fatan bayan babu ni a cigaba da kula da karatunta har gaba da secondary Talatu ki yi min alk’awarin Ayra Zata yi ilimi har sai ta ce ya isheta da zarar ta gama secondary kuma a kaita Jami’a a k’asar waje ta karanci business admin da shine Zata iya kula da companynta idan ta girma, ki min wannan alk’awarin.” Ta fa’da tana sauke kallonta kan Ayra da take mata wani irin so fiye da tunanin mai tunani Talatu kuwa kuka take tana fa’din “In sha Allah Hajiya zaki tashi har ki aurar da Ayranki Ai cuta ba mutuwa bace.” Murmushi ta yi tana fa’din “Mutuwa ce Talatu ina ji a jikina kuma lokaci na ya zo k’arshe addu’arku kawai nake buk’ata kada ku manta da ni bayan babu raina.” Duka gurin zuciyarsu ta karye kukan kawai suke mai bayyana tsananin tashin hankalin da zuk’atansu suke ciki. K’irazar sun raunana kamar yarda idanunsu suke ganin duffai basa gane komai ba kuma sa fahimtar komai sai sautin kukansu ne kawai yake tashi a ‘dakin. Hajiyar tana dubansu tana murmushi ta ce “Tun yau kuka fara min kuka? Ashe kada na saka rai da samun addu’oinku, don Allah idan na mutu kada ku min kuka, bana buk’atar kukanku kuka ga mamaci bala’i ne masifa ne. Ku tashi ku je ku yi sallah ku rok’a min gafara da samun sassauci zarar rai ya fiye min wannan kukan ba gata kuke min ba.” Kamar wa’danda aka zarewa laka haka suka dinga mik’ewa suna ficewa ban da Talatu da. Ayra da kuma Jummai da suka kasa matsawa daga kusa da Hajiyar da muryarta ta fara karyewa. Duk k’ank’antar shekarun Ayran bai hanata shiga tashin hankali ba, ta kwanta a jikin Hajiyar sosai tana hawaye ganin kowa ma kukan yake. Hajiya ta ‘dan shafa kanta kafin ta damk’i hannunta tana fa’din “Allah miki albarka yasa ki zama abin alfahari a rayuwar mahaifiyarki.” Ta damk’i hannunta cikin nata kafin ta kalli Talatu da ta shimfid’a sallaya tana shirin tada sallah ta ce “Amma zuba min Zam zam ki karanta min matayassara minal k’ur’an.” Da sauri Talatu ta ‘d’au robar zam zam ‘din ta tsiyaya a cup ta fara karanta suratul Mulk tana karantawa Hajiyar na binta a hankali har ta gama ta kama Hajiyar ta kafa mata a baki. Tas kuwa Hajiyar ta shanye kafin ta lumshe ido ta ce “Nagode Talatu, Allah ya saka miki da alheri ya dafa miki a rayuwarki.” Talatu ta amsa a sanyaye tana kwantar da ita kafin ta tada sallah. Itama Jumman Sallahr take duk zuciyarta ta raunana ance Sabo turken wawa musamman mutumin da yake kyautata maka dole ka ji mutuwarsa.
Ana idar da Sallahr Asuba Itama Hajiyar ta yi bayan Jummai ta mata alwala daga sallah ta kishingi’da ta lumshe idonta sai suka ji shiru a zatonsu barci ta yi sai dai ina Hajiya ta yi barcin da ba zata tashi ba sai ranar alk’iyama. Suma da suka idar da sallahr barci ne mai nauyi ya ‘daukesu barcin da Talatu ta kira barci asara don dai sanda suka tashi farkawa tuni ta bayyana k’arara Hajiyar ta amsa kiran mahaliccinta ta hanyar ganin idanunta da suka yi sama fuskarta kuma da alamar murmushi. A razane Talatu ta dinga jijjigata tana kiran sunanta, sai dai ba alamun Hajiyar zata amsa, Talatu ta shiga tashin Jummai tana fa’din “Tashi Jummai Tashi hukuncin Allah ya sauka a kanmu.” A razane Jummai ta farka don dama barci ne yake yinsa mai wahalar gaske cike da munanan mafarkai. Koke-kokensu ne yasa Itama Ayra ta farka a razane tana lalubar Hajiyar tana kallon Ammanta ta ce “Amma menene?” Cikin kuka Amma ta ce “Ayra kin yi rashi, Ayra kin yi rashin uwa mai son ki.” Tuni Ayra ta fara kururuwa da k’arfin gaske…. Hakan ya ja hankalin duk wanda yake gidan, suka ji suka kuma shaida mutuniyar kirki Hajiya Kari ta amsa kiran mahallincinta.
(Ba zan iya cigaba da typing ba, nima na tuna tawa mutuwar mahaifin shi da ‘dan uwana don Allah ku musu addu’a da ahalin musulmi gaba ‘d’aya da suka rasa rayuwarsu. Allah ya ji k’an su idan ta mu tazo Allah Yasa mu cika da kyau da Imani.)
😭😭😭
Takaicin Uba….
46.
💔💔💔💔
Kafin kace meye wannan? Labarin rasuwar Hajiya Kari ya kara’de duniya, nan da nan dandazon jama’a suka cika k’ofar gidanta dama harabar gidanta dank’am da jama’a, tabbas Hajiyar ta dace don kowa alherinta yake fa’da da taimakon da takewa talakawa da miskinai. Almajirai kuwa da iyayen marayu suma kuka suke kamar wani nasu ne ya mutu. Haka nan k’usoshin gwamnati masu rik’e da manyan mak’amai suma sun halarci jana’izar. Gwamna da tawagarsa da ma sarakuna suma sun zo don jana’izar wannan baiwar Allah tabbas baka sanin waliyi bawan Allah sai a yayin da mutuwarsa ta riskeshi. Hajiya kam ta samu kyakykyawar shaidar da kowa yake kyautata mata zato, sai dai fatan Allah yasa ta mu muma ta yi kyau kamar yarda ta magabata suka yi kyau.
___________
Kwana bakwai rus a kai ana zaman makokinta ana ci ana sha, sai gidan mutuwa ya fara riki’dewa yana komawa kamar gidan biki. Kowa budirinsa
Yake yi idan ka cire Talatu da Jummai da har rama suka yi saboda alhinin mutuwar Hajiyar. Abinci wannan Talatu bata iya shansa sai dai ta surka farau-farau ta sha ya tsaya mata a madadin abincin.
A daren bakwai ne suna zaune da Jummai jugum-jugum. Tuni suka fara ha’da kayansu don daga yanayin kallon da dangin Hajiyar suke musu sun san ba za su barsu su ‘dara daga gobe ba. Don tun ranar kwana biyar suka sanar da su su ha’da kayansu su wuce don kashegarin bakwai za’a gark’ame gidan Hajiyar tunda ya zama na magada. Jummai ta saki ajiyar zuciya bayan dogon tunanin da ta fa’da gaba ‘d’aya ta sare da lamarin duniya tana kuma nadamar abubuwan da ta aikata wa Talatu don haka tana kallon Talatun ta ce “Talatu, zan rok’i alfarma wajenki, ki yafe min abubuwan da suka faru, komai ya faru ne bisa ingizar shai’dan.” Talatu tana kawar da k’wallar idonta ta ce “Dama ban rik’e ki da komai ba Jummai, na yafe miki tun tuni Allah ya yafe mana.” Jummai ta mata godiya kafin ta ce “Yanzu kenan gobe sai mu koma can inda Hajiya ta bamu, tunda da takardu da komai kuma shaidu sun tabbatar. Allah sarki Hajiya tabbas na ji mutuwarta sosai da sosai shekararmu ashirin fa tare.” Talatu ta sake share k’wallarta ta ce “Bana tunanin a duniya za’a samu mai karamci da mutunci irin Hajiya, zuciyarta daban take da ta mutanenmu na yanzu, da ba abinda suka sani sai taka Talaka da ci masa mutunci, amma dubi yarda Hajiya ta maye min gurbin Iyaye miji har ma da y’an uwa na tabbata har abada ba zan daina kukan rashin Hajiya ba.” Jummai ta saka hannu ta zaro wayarta da take cikin k’aramar jaka tana k’ara ta kara a kunnenta. Kamilu daga can b’angaren ya ce “Salamu Alaikum Hajiya, ai na kwana biyu ina neman ki baki ‘daga ba.” Jummai ta saki ajiyar zuciya ha’de da cewa “Lokacin zuwanka ya zo, zan turo maka da Adreshin da zaka same mu zuwa gobe da safe, don za mu bar gidan da muke ma sabida matar gidan ta rasu.” Kamilu ya saka salati yana fa’din “Ashsha, Allah ya ji k’anta da rahama ban sani ba Ai da nazo.” Jummai ta ce “Ai gaisuwa bata rib’a yanzu dai ka samu dama kazo kaga muhallinsu tunda ba zaku barta da kula da yara mata ita ka’dai ba.” Kamilu ya ce “K’warai kuwa, tunda dai shi Kabiru ya kafe Ai shikkenan rayuwa ce, Zan shigo In sha Allah na duba su.” “To sai ka ji ni.” Ta fa’da tana zare wayar daga kunnenta idanunta a kan Talatu data zuba uban tagumi, hankalinta sam baya kanta balle ta fahimci wayar da take. “Talatu, da k’anin Mijinki Kamilu muke waya, na gaya masa zai zo In sha Allah..” Da sauri Talatun ta ‘dago tana kallonta kafin cikin rawar murya ta ce “Haba Jummai ya zaki min haka? Na tabbata idan Kamilu ya san inda nake kamar Kabiru ya sani ya gama.” “Kabiru ya ce baya buk’atarku, ya ma sake aure yana can lagos da matansa da yaransa maza da yake so a haifa masa ke kuma ya ce Matan ya bar miki, Kamilu kuwa abinda yasa na shigo da shi cikin rayuwarki don ya zamewa yaranki garkuwa, bai kyautu ace ke Mace ke za ki yi tarbiyyar yara mata har biyar ba, babu mai saka muku ido, daga haka za’a k’ulla muku wani babban sharrin da zai ya bibiyarku a rayuwarku, don haka zan sadaukar da kaina na auri Kamilu tunda gidan mu a jikin na juna yake na tabbata zai saka ido sosai a kan yaranki. Ban kuma yi da mugun nufi ba, na yi ne don Allah da son nima na fara koyi da wasu ‘dabi’un Hajiya na son taimakawa wanda yake neman taimako.” Talatu idanu kawai ta zubawa Jummai tana mamakin k’udirar Ubangiji wato kowane mutum da ranarsa ashe ha’duwarta da Jummai shima alheri ne, tunda take bata tab’a hasashen haka ba sai yanzu da Jummai ta yi mata haka. Godiya ta shiga mata sosai kafin ta saka kuka. Jummai ta dafata ta ce “Kada ki damu Talatu, ki ‘dauke ni kamar y’ar uwarki ni kaina yanzu ina jin ki kamar wani sashe na jiki na, Allah ya ‘dora mu a kan Kamilun ya amince da buk’atar mu.” Talatu ta ce “Ameen, amma bana tunanin zai k’i tunda a zahiri taimakonsa kika yi da zaki auresa.” Jummai ta ‘d’aga kai kawai tana jin wani nauyi da ya da’de cunkushe a zuciyarta yana bajewa a hankali ko bakomai yau ‘d’aya ta farantawa Talatu tana kuma Allah ya duba hakan ya yafe mata kuskurenta. Talatu ta muskuta tana gyara zamanta sabida yanzu ta ‘dan yi k’iba ta murje ta ce “Amma Jummai ya aka yi kika san Kamilu?” Jummai ta saki malalacin murmushi mai bayyana tsantsar nadamarta ta fara bata labarin duk wasu abubuwan data aikata don ganin ta tunku’deta daga jikin Hajiya, ciki kuwa har da zuwan ta Shagogo. Sai data gama sannan ta ce “Amma don Allah Talatu ki yafe min, wallahi na yi nadama sosai.” Talatu ta saki murmushi ta ce “Wallahi na yafe miki Jummai. Amma yanzu ya zaki yi da yaranki da suka nuna basa son ki yi aure.” Jummai ta saki dariya “Yanzu kuwa ai dole su so, Ina ce su matan a ‘d’akin mazajensu suke kamar yarda su ma mazan suke da nasu Matayen, shikkenan ni sai su haramta min aure bayan da sauran jini na a jika.” Talatu ta saki murmushi kawai ta ce “Allah ya tabbatar mana da alheri, amma ni ko sha’awar aure ba nayi a raina, jira nake ma na maka Kabiru a kotu ya sahhale min ragowar igiyarsa da ta yi saura, don ko yana mutuwa yana dawowa ba zan amince na koma gidansa ba wallahi, gwara ko hul’i a yi mana na biyasa sadakinsa ya sakar min mara na yi fitsari don wallahi sai ya sake ni.” Jummai ta ce “Ina bayanki Wallahi