Showing 15001 words to 18000 words out of 132090 words

Chapter 6 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

yi tana warwarewa hankalinta ya kwanta ta mik’e tana ka’de jikinta….




________________


Magriba sakaliya ya shiga gidan nasa. Alh.Sulaiman turaki ya yi parking a bakin harabar gidansa. Kana ganinsa ka ga usulin fulani kuma ingarman namiji mai tsayi da fa’di fari tas da shi, farin nasa har wani ratsawa yake yellow. Ba walwala a fuskarsa ko ka’dan don bai kasance daga cikin mutane masu walwala ba. Ya dinga amsawa masu gadinsa sannu da zuwan da suke masa fuska a ha’de.
Ta k’ofar baya ya shiga gidan nasa, k’ofar da direct zata sada shi da stair case ‘din da zai hau zuwa part ‘dinsa.

Ta ga shigowar tasa ta ji kuma takunsa don haka ta mik’e tsam ta sake bulbulawa kanta turare sannan ta bi bayansa, ta cikin sashen da take da zai sadata itama da stair case ‘din nasa. Ta yi kyau sosai cikin shadda light brown da ta sha ‘dinkin y’an senegal, jelar gashinta sai reto take a gadon bayanta. Farin ciki fal fuskarta da zata yi arba da shi a yau bayan shafewar wasu watanni tunda ya dawo wajen amaryarsa bai sake waiwayarsu ba don haka ta shirya taran sa tana son kuma ta nuna masa tana nan a Hameedarta mai tsananin kishi wanda dama dalilin hakan ya sa ya barta a can k’asarsu ya kuma hanata zuwa Nigeria. Sai yanzu da ya tabbatar girma yazo mata hankali ya samu ya san da wuya ta zo ta aiwatar da haukan kishi zata ji kunyar hakan. Tsawon shekaru sha biyar da aurensa da amaryarsa tun a lokacin ta so dawowa mahaifarta cikin dangin babanta amma S.Turaki ya kafe sam bai amince da hakan ba kuma ko hutu bai amince ta zo ta yi ba. Yanzun ma an kai ruwa rana kafin ya amince da zuwan nata, kuma zuciyarsa tana d’ar-d’ar sai dai ko a waya bai nuna mata ba, dalilin yayan Babanta ne ya sanar da shi ya kamata ta zo ta ga dangi yaranta kuma su san dangin kakansu tunda Amin da y’ar uwarsa ne kawai suka tab’a zuwa. A can ya ha’du da ita wajen business ‘d’insa soyayya mai k’arfin gaske ta shiga tsakaninsu, duk da ra’ayinsu ya sha banban shi mai kafaffiyar zuciya ne yayin da ita kuma ta kasance mai sassauk’an hali. Ko a wajen tarbiyyar yara sai da suka sha artabu don sosai ya nuna mata ya fi son yaransa su tashi da harshen hausa a bakinsu ba harshen su na labanawa ba, don dole ta amince take musu magana da duka harsunan biyu shi yasa suka iya hausa kamar me? Tunda itama bahaushiyar ce mahaifinta haifaffen cikin garin kano ne kuma asalin bahaushe, mahaifiyarta ce kawai ta kasance daga jinsin larabawan labanon. Tun lokaci da ta rigime da son zuwa Nigeria shi kuma ya tattara ya mata yaji tsawon wata bakwai sai da ya ga abin nata ba na k’are bane sannan ya ce su tattara su taho ya gama musu gini.


A hankali ta tura k’ofar idanunsu suka gamayya da juna. Fuskarsa ta ‘dan saki ka’dan yayin da tata ta washe da fara’a gaba ‘daya ta dinga jifansa da k’awataccen murmushi.
Hannu kawai ya mik’a ya janyota kusa da shi ba tare da ya yi magana ba. Ta shige jikinsa sosai tana k’ok’arin kawar da kishin da yake k’asan ranta. Sosai ta shiga nuna masa yarda ta yi kewarsa tana gaya masa yayinda shi kuma ya shiga sarrafata ba bakin magana a tunaninsa hakan ne kawai Zai nuna mata ya yi kewarta ba ‘dan ka’dan ba…..



Zazzafan coffee ‘din ta shiga jujjuya masa tana k’ok’arin mik’a masa murya a sauk’ak’e ta ce “Na samarwa Turaki mata…” gaba ‘daya cup ‘din ya sub’uce a hannunsa yana dubanta ya ce “Ba dani ba, na gama yiwa Turaki aure yana zubar min da mutunci ta hanyar sakin yaran mutane..”
Takaicin Uba….

Na

Nazeefah Sabo Nashe..


08033748387.


9_________



Da k’imata da mutuncina kika saka ya dinga zubar min da mutunci a idanun jama’ar da nake jin kunyarsu matuk’a dattijan mutane masu fa’da aji a
K’asar nan haka kawai yake sako musu yaran ba laifin tsaye ba na zaune, wannan karan kam ba dani ba ki bari ya nemawa kansa da kansa matar da ya ji yana so kuma zai iya zama da ita kamar matarsa ta farko.”

Shiru Hameeda ta yi ta zuba hannayenta a k’unci don sarai ta san mijin nata kaifi ‘daya ne
Baya magana biyu ta san kafin ta shawo kansa aiki ne ja. Murya can k’asa ta yi magana tana goge masa jiki da handkerchief in da ya b’aci da coffee “Ka yi hak’uri Yallab’ai hannunka fa baya rub’ewa ka yar idan ba mu nema masa aure ba ba ta yarda za’a yi Turaki ya nemawa kansa mata, kuma ba k’ima da mutuncin mu bane a ce Turaki yana zaune ba matar aure…” Da sauri ya ‘d’aga mata hannu “Sau nawa na siya masa mutuncin ni ya zubar min da nawa mutuncin? Sau nawa na bashi k’imar ni ya kawar min da tawa k’imar? Ba ruwana kema kuma ki fita daga sabgar rashin aurensa idan ya gaji da zama ba auren da kansa zai nemawa kansa aure..” Fuskarta ta ‘daure sosai don ta san idan ba hakan ta masa ba ba zai yarda da abinda zata ce ba “Ka gwada wannan karan ina tabbatar maka za’a dace In sha Allah don matar da na zab’ar masa ina tabbatar maka itace matar da ta dace da irinsu Turaki wanda duk taurin kansa ba zai iya ‘dauke idanunsa daga kanta ba, na yarda da Talatu na san ba zata bar yaranta kara zube ba dole zata samar da nagartacciyar tarbiyya ga yaranta wacce za su yi zarra a cikin mutane.. In sha Allah wannan karan ba zai samu mafakar rabuwa da wannan matar ba, tunda waccan dai ya ce saboda rashin budurcinsu yake rabuwa da su, to wannan karan kam an yi dace In sha Allah an samu gidan mutunci..” Tsawon mintuna ya ‘dauka idanunsa cikin nata kafin ya jijjiga kai ya ce “Saboda nacinki na amince zan nema masa aure a karo na hu’du bayan rasuwar matarsa, sai dai on a
Condition Wallahi idan ya sake ya rabu da wannan matar sai dai ya nemi uban da zai masa walittarka aure next time.” Cikin murna Hameeda ta dinga jijjiga kai alamar ta amince ta kama hannunsa tana godiya, a tunaninta matsalar Ameen Turaki tazo k’arshe don ta amince da nagarta da tarbiyyar yarinyar… Shima yana murmushin ya ce “Wanene Uban yarinyar? A ina za’a same shi a yi maganar auren?” Ya fa’da yana kallon k’asan k’uncinta da yake lob’awa saboda dariyar farin ciki da take ya sani Amin shine mafi soyuwa a cikin zuciyarsu fiye da duk wani ‘da da suke da shi dole farin cikinsa suke nema ta ko ina. Hameeda ta fara bashi labarin Kabiru da Talatu na lokutan baya sannan ta tabbatar masa zata tambayi Talatun sanda za’a samu Kabirun a je masa da maganar auren duk da ta b’oye bata sanar da shi basa tare ba. Ya ‘daga kai ya ce “Sai ki gaya min gobe don ina son in yi kyakykyawan bincike a kansu kafin maganar aure ta kankama don yanzu ba kowane b’aragurbi kake so ya shigo maka cikin zuri’a ba.” Cike da gamsuwa Hameeda ta hau ‘daga kai, don ita sam bata hango aibu game da Amma Talatu da zuri’arta ba.





___________________________


Da zazzafan zazzab’i ta tashi mai ha’de da sarawar kai da mutuwar jiki gaba ‘daya. Ta da’de a kwance a saman gadon ta kasa katab’us sai juyi take tana jin yarda gab’obinta suke ciwo matuk’a da gaske. Hawayen idanunta tuni suka k’afe k’af bak’in cikin da take ciki ya fi gaban ta zubar da hawaye sai dai gum da baki kawai. Ta dinga murza goshinta tana jin yarda jijiyar kan take sake d’aure mata. Tabbas a
Lokacin ji take rabuwarta da numfashinta shine abu mafi soyuwa a wajenta fiye da fushin da Amma take yi da ita akan sai ta amince da maganar aurennan.

Har sha biyun rana bata fito ba, balle ta yi aiyukan da ta saba yi a duk safiyar ranar, Amma kuma bata nemeta ba duk da hankalinta kacokam yana kanta sai dai bata son ta nuna mata karaya da sauri.


Sallamar Dijah ne yasa Amma ta saki ajiyar zuciya don ta San dole Dijan zata tambayi Ayran ko don kasancewar lahadi ce ta san bata gari. Dija da yaranta gaba ‘d’aya suka zo gidan maza biyu mata biyu. Yanayin da taga Amman ya tsorata don haka a ki’dime ta dinga tambayar Amman ko lafiya? Amma tana murmushi da son kawar da cunkushashshiyar damuwar da take ranta ta ce “Lafiya lau Dijah kune tafe da tsakar ranar nan, wannan satin nan aka yi yo kenan.” Ba don Dijah ta yarda ba ta ‘dagawa Amman kai ha’de da cewa “Allah Amma baki da lafiya ko baki fa’da ba idanunki sun nuna, don Allah me ya sameki?” Amma ta saki ajiyar zuciya tana amsa gaisuwar jikokin nata kafin ta ce “Maza ku tafi sashenku ku yi wasa” suka mik’e kuwa suka yi hanyar sashensu don musamman Amma ta Ware wajen saboda jikokinta. Suna tafiya ta mayar da kallonta kan Dijah ta fara bata labarin halin da suke ciki da Ayra tun maganar auren da aka zo da ita.

Wani farin ciki ya ziyarci Dijah ta saki murmushi tana fa’din “Alhamdulillah Allah Alhakamu nesa ta zo kusa, Allah Amma wannan karan ki cire tausayin Ayra a ranki ki sadata da ‘dakin mijinta ganin kina nuna kina tausaya mata ne yasa take sake tab’arewa ki zubar da tausayinta a gefe a mata auren shi angon ya ladabtar da ita ta hanyar da dole zata yi zaman auren.” Amma tana jijjiga kai shawarar Dijah ta zauna daram a ranta ta ce “Haka za’a yi Dijah, amma ba anan matsalar take ba, shima fa mijin ba son auren yake ba, don kuwa mijin matacciya ne ance bayan mutuwar matarsa sau uku ana masa aure yana sakin matan, to tsoron da nake ji kada ya mayar da Ayra bazawara itama ya saketa..” Dijah dariya ta saki ta ce “K’arya yake Amma, ai ba irin su Ayra maza ke saki da wuri ba, sannan kuma irin wannan auren Ai yafi da’dewa zaki sha mamaki nan gaba yarda za su zo suna son juna, balle Ayra tana da duk wata sura da zata tafi da hankalin namiji….” Karaf zancen nan ya shiga kunnen Ayra da take shirin fitowa falo. Cikin b’acin rai ta juya jikin mudubin console ‘din da yake falon ta dinga k’arewa kanta kallo tana jin takaicin zamowarta a jinsin kyawawa, ai kuwa in dai don kyan zai sota tabbas zata je ta siyo muni da ku’dinta zata jirkita halittarta da artificial ta hanyar da ba zai tab’a ganin kyanta ba sai zallar muninta ta yarda zai saketa da sauri, ta ma ji da’di data samu wannan labarin na ba ya iya rik’e aure sabida matacciyar matarsa, ashe ma aure ne zata yi na wuncin gadi ta dinga sakin murmushi farin ciki ya cika zuciyarta ta zubar da wancan tarin bak’in cikin ciwon kan ma nemansa ta yi ta rasa da sauri ta k’arasa falon cikin karsashi ta fa’da jikin Dijah tana fa’din “Oyoyo da Yayar Amarya.” Ba Dijah ba Harta Amma sai da ta dinga kallonta da mamaki ita kuwa sai dariya take ta kama hannun Amma tana murzawa cikin dakiya ta ce “Amma ki yafe min na amince zan yi auren tunda shine farin cikin ki..” wata irin runguma Amma ta kai mata tana shafa bayanta farin ciki yasa fa’di take “Alhamdulillah, Allah nagode maka daka bani yara masu biyayya Ubangiji yasa ya zame miki farin ciki a rayuwa yasa mutuwa ce zata raba ku..” yarda k’irjinta ya buga da Amma ta saurara da kyau zata fahimci zallar yaudara ce cikin zuciya ta dinga furta ba Ameen ba Ya Allah, Allah kasa kada na yi ko sati a gidansa Ubangiji ka sanya masa tsanata kasa abinda na nufi yi ya yi aiki.” Dijah tuni ta ‘dai waya ta dinga kiran sauran Yayyansu tana sanar musu kyakykyawan albishir ‘din. Kowa ya ji sai ya ce “Dijah bana son zancen banza da wasan banza.” Sai Dijan ta musu rantsuwa sai su saki ihu tare da fa’din “Alhamdulillah! Ma sha Allah” wa’danda suke gari tuni suke cewa yanzu za su zo wa’danda suke Abuja kuwa sai ki ji suna muna nan zuwa ranar Friday. Tausayinsu ya kama Ayra ganin yarda suke ‘daukan lamarin da girma basu San auren jeka na yika za ta yi ba. Sai dai ba zata nuna musu ba, ta fi son a jingina duka laifin a kansa tunda an masa tambarin auri saki. Da wannan tunanin Ayra ta saki zuciyarta ta daina damuwa da zancen auren sai ma shiri da ta fara yi da zuciyarta na yarda zata samu artificial abubuwa ta sauya halittun fuskarta ta yarda ba zai tab’a son ta ba.





_____________________


Cikin asibitin murtala specialist hospital b’angaren emergency nan aka kwantar da Alh.Kabiru. Tun bayan fa’duwarsa da mutane suka taimaka suka kawo shi asibitin yake kwance a wajen, da kyar aka samu k’aninsa yake jinyarsa. Yaransa maza kuwa babu wanda ya sake zuwa tun bayan da suka yi zuwa bibbiyu. Matarsa ce dai kullum tana zuwa ta yi zaman awa guda ta tafi, tunda likitan ya sanar cutar mutuwar b’arin jiki ce ta kama shi don haka zai samu tsawon lokaci kafin ya warke. In dai ba waje za’a fita da shi ba.

Yau ma bata zo da wuri ba sai kusan azahar tuni likita ya basu sallama ita dama ake jira, don k’aninsa ba shi da ku’din motar da zai kinkimeshi zuwa gida.

Ranta a b’ace da jin cewa ku’din daga wajenta za su fito ba ta dinga hararar k’aninsa tana tsaki “Allah wadaran dai zumunci irin naka Kamilu ace baka da ku’din motar da zaka kai ‘dan uwanka gida.” Kamilu shima a harzuk’e ya dubeta “Kada dai ki ce zaki zageni, lokacin da yake da shi kin bar shi ya taimaka mana ne ina ce ke kika gurji arzikinsa yanzu ma sai ki fito da ku’di ki kinkimeshi ki kai shi gida, ai ni na yi na Allah don girman Allah ma na duba na zo na zauna da shi daga nan kuwa gida zan yi Allah ya bada lafiya ya sauwak’a.”

Kabiru dai bin su yake da kallo idanunsa cike da rauni hawaye yana bin fuskarsa ka’dan-ka’dan shi Kabiru shine ya zama haka tun a duniya ma kenan? Mutanen da ya kyautatawa lokacin da yake da shi su suke gudunsa a halin da yake tsananin neman taimakonsu.

Ganin da gaske Kamilun zai tafi yasa hannunsa mai ‘dan ragowar lafiyar ya kamo shi hannun yana rawa ya dinga nuna masa alamar ya taimakeshi. Tausayinsa ka’dan ya kama Kamilun ya fasa niyyarsa ta tafiya ya juya a hankali ya kinkimeshi tunda Kabirun yanzu ba wani nauyi gareshi ba don ma dai ‘daya b’arin jikin nasa ya nauyaya.

Sai da ya saka mata shi a A daidaita ta samu ta rik’eshi da k’yar sannan ya juya ha’de da cewa “Allah ya k’ara lafiya Yaya, In sha Allah zan gaya mutanen k’auye halin da kake ciki nima kuma zan dawo duba ka idan an kwana biyu.” Daga haka ya juya ya wuce Kabiru ya bi shi da kallo gani yake kamar sallamar kenan kamar ya rabu da ‘dan uwansa kenan. Hawaye ya ‘dan zubo masa wanda yasa Larai sakin tsaki ta ce “Ko na kira shi ya tafi da kai ne? Nima an rage min wahala Haba ka bi shi da kallo kamar me?”

Da sauri ya ‘dan kawar da kansa da k’yar daga kallon Kamilun shi kuma ‘dan adaidaitansu ya ja yana mamakin halin wasu matan irin na Larai mijinki ba lafiya Amma kina masa irin wannan ‘dabi’a?





_________________


Idanu Turaki ya sake zubawa wayar tasa, yayin da kiran Hayateey wato Ummeey bai fasa shigowa cikin wayar ba.

Ya dinga murza goshinsa yana jin tsoron ‘dagawa don ya san zancen da zata masa kenan zancen Aure! Bata San shi mata gaba ‘daya haushi suke ba shi ba gani yake duk halinsu ‘daya Sun zubar da k’ima da mutuncinsu a titi.


Da k’yar ya ‘d’aga wayar cikin rashin da’din murya ya ce “Hayateey! Barka da yamma.” Hamida ta ja tsaki kafin ta ce “Yanzu Turaki kana ganin kira na sai da kaga dama sannan zaka ‘daga? To ya yi kyau hakan da ka yi ba shine zai saka na fasa waccan maganar ba, idan kaga ban ‘daura maka aure nan da wata guda ba kace an kai ni kushewata…” K’irjinsa ya dinga duka sosai kamar zuciyarsa zata b’alla k’irjin ta fito murya a dashe ya ce “Please! Ummeey ki janye wancan zancen, wallahi tunda kika sanar da ni hankalina ya kasa kwanciya..” “Ai kuwa sai dai kada ya kwanta don aure babu Fashi, har na gayawa Abbanku, kuma ya amince akan cewa za’a yi nan da sati biyar kafin azimi da sati biyu kenan, sai ka fara mata processing visa, ka kuma fara shirin zuwa biki ka tafi da matarka ka ji na gaya maka.”

Turaki kasa amsa mata ya yi illa jan huci da ya dinga yi, gaba ‘daya tun kafin ya ga yarinyar ya ji ya tsaneta a zuciyarsa don bai tab’a ganin auren da Ummeey ta so kamar na tan ba, ya kasa kashe wayar yayinda Ummeey ta dinga jin hucinsa Har cikin ranta ta kashe wayar ba tare da ta tausaya masa ba, don ita tabbas ta San gata ta yi masa ta yarda ta gwangwajeshi da zuk’ekiyar mata wanke hannu ka tab’a.
Ya dinga bin wayar da kallo bayan jin Ummeey ta katse wayar, wato ma ta daina tausaya masa da da ne idan ta ji a wannan yanayin lallashinsa zata dinga yi tana lallab’ashi akan ya amince Amma wannan karan Sam ba ma amincewarsa take nema ba dole za’a masa ya ciji leb’ensa a hankali kafin ya mik’e yana zagaye ‘dakin AUREN DOLE kenan Ya furta a nutse yana murmushi kafin ya ce “Koma wacece ina baki shawara kada ki yi ganganci shigowa cikin rayuwar Turaki tabbas zaki nadama don zaki zaman aure ne kamar zaman kurkuku!” Haka ya dinga fa’da yana murzar hannnayensa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login