Showing 78001 words to 81000 words out of 132090 words

Chapter 27 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

samu wanda ya santa dubi dai yarda wancan yake kallon Ki da alama ya tab’a mu’amalantarki.” Da sauri Ayra ta ‘dago tana kallonsa ha’de da kallon mutumin da yace yana kallonta sai kuwa mutumin ya saki murmushi ha’de da ‘d’aga mata hannu ya ce “Ayra Gaya kwana biyu?” Wata hautsinawa cikin Ayra ya yi ganin Kallon da Turaki yake mata cikin wani irin razanannen kallo fuskar nan tasa kamar an masa albishir da mutuwar Ummeey, murya a sark’afe ya ce “Ta shi ki koma wajensa wa ya sani ma ko ke kika sanar da shi tafiyar da za mu yi ya biyoki idan yaso ku je can ku cigaba da abinda kuka saba……
Takaicin Uba…..

Nazeefah Nashe

38.


💔💔💔💔


A tsorace Ayra ta zuba masa manyan idanunta masu kama da an ‘diga zaiba a ciki, wani irin hucin b’acin rai yana fitowa tun daga zuciyarta har zuwa mak’ogaronta tana furzar da shi ta k’ofofin hancinta, shi ‘din ma idanun nasa wanda ake kira da sexy eyes ya zuba mata yana jin kamar ya shak’eta ya daina ganinta ya huta da takaicinta da yake cin ransa. “Bar tsareni da ido ko sharri na miki? Kina ji dai Ai ya ambaci sunanki, ki mik’e ki koma wajensa kafin na aiwatar da abinda raina yake gaya min.” Ya fa’da yana sake nutsar da idanunsa cikin nata. Ga mamakinsa sai ya ga Ayran ta saki ajiyar numfashi tana sakin murmushi lokaci guda ha’de da mik’ewa “Shi wancan ‘din da kake gani ya fiye min kai sau dubu, kuma yanzu zan k’arasa wajen nasa.” Ta ‘d’au jakarta tana shirin ficewa daga inda take a zaune. Ganin da gaske take bai san sanda ya saka k’afa ya kwarfo ta ta fa’do cinyarsa yasa hannu ya rik’e mata hab’a “Ni zaki rainawa hankali? Tafiyar da kike shirin yi?” Ya fa’da yana jefa mata wani irin kallo da yasa tsigar jikinta ta tashi, shi kansa zuciyarsa harbawa take da sauri dalilin kusancin da suka samu sosai a tsakaninsu. Bai ‘dauke idon ba ya dai san ya samu galaba a kanta ganin yarda ta lumshe ido zuciyarta na harbawa sosai “Tashi ki je, na ce ki tashi ki je gurin wanda ya fi ni muhimmanci.” Kasa mik’ewar ta yi illa zamewa da ta yi ta koma mazauninta tana mayar da numfashi a hankali, idanunta a lumshe Turaki kuwa ya sake tsare gira ganin yarda mutumin ya mik’e ya iso inda suke. A Karon farko ya mik’awa Turakin hannu, kamar ba zai ba shi ba kuma sai ya ba shi fuskarsa a ha’de, shi kuwa mutumin sai ya sake mayar da kallonsa kan Ayra Gaya yana sakin murmushi ya ce “Ba ki gane ni ba ko? Brother mijin Yayarki Majeeda ne, sau ‘daya nima na tab’a ganinki a gidanta a nan na shaidaki, so ya gida?” Ayra ta saki ajiyar zuciya tana kallon Turaki ta saki murmushi ha’de da cewa “Gida Alhamdulillah, nagode sosai.” “Bakomai nima tare da iyalina nake, yanzu za su shigo sai ku gaisa.” Ayra ta ‘d’aga kai shi kuma mutumin ya shige. Sai sannan Ayra ta sake mayar da kallonta kan Turaki ta saki murmushi ha’de da fa’din “Zato zunubi…. Allah ya yi mana sakayyar k’azafin da ka yi mana.”
Daga haka ta mayar da kai tana lumshe ido da k’ok’arin mayar da k’wallar da take son zubo mata. Shiru cikin jirgin ya ‘dauka dalilin sanarwa fara tashi da jirgin zai yi kowa yana addu’a a cikin zuciyarsa. Shi kuwa Turaki turaren Ayra ne duk ya bi ya takura masa kamar a jikinsa aka saka. “Kada ki sake saka turare idan za ki fita ba na so.” Ya samu kansa da fa’da cikin isashshiyar murya ba tare da ya kalleta ba. Ayra ta gefen ido ta kallesa tana ‘dan turo baki kafin ta ce “Kafin ka san haramcin hakan na fika sani.” “A saboda kin girmeni kin kuma rigani shiga islamiyya ba, ki rufe min wannan bakin naki kafin na yi maganinsa ta tilas, Sai tsiwar tsiya kawai.” Ya fa’da yana jan tsinin hancinta. Ayra ta kautar da kai ha’de da jan bargon cikin jirgin ta k’udunduna saboda barcin da ya fara fisgarta. Turaki murya k’asa k’asa ya ce “Ai ba ki ma fara jin sanyi ba yarinya sai mun je Moscow zan ga uban da zai baki Aron rigar sanyi da kika taho haka wai ke y’ar gayu.” Gaban Ayra ya yi wani irin duka don sosai ta san kanta bata son sanyi ko ka’dan don tana da cutar pneumonia mai k’arfin gaske. Ta ware ido tana kallonsa “Amma baka fa’da min ba tun a gida.” “Ba zan fa’da ba, ke duk bincikenki ba ki tab’a binkito Moscow garin sanyi ba ne, ai dai kin san Rasha ba sauk’i a wajen sanyi to Moscow da ya zama babban birninta sai ki ke tunanin zai zama garin zafi… mhmn za ki gane baki da wayo.” Ayra ganin da biyu yake mata mugunta sai ta maze ta masa banza ta nuna masa ba damuwa.



_____________________

*Moscow*

Sheremetyevo Alexander S. Pushkin
International Airport.

Bayan wahalce wahalcen tafiya, da Transit Allah ya isar da su babban filin tashin jirgi na Moscow. Tun daga yanayin da Ayra ta gani ta window na dusar k’ank’ara da take zuba a garin Ayra ta tabbatar da maganar Turaki na zuga sanyin da ake a garin. Hankalinta ya tashi musamman ganin yarda kowa yake aikin saka rigar sanyinsa da hula har da safa, ta dubi yaloluwar rigar da take jikinta sai ta ji k’irjinta ya buga. Duk abinda take Turaki na kallonta yana sakin murmushi k’asa-k’asa kafin ya ja trolley ‘dinsa yana kallonta ya ce “Shall we?” Ayra ta ‘d’aga masa kai jikinta a mace ta bi bayansa tunda ita tata akwatin aunata aka yi sabida girmanta. Haka suka fice daga cikin jirgin suna zura k’afarsu a step ‘din jirgin Ayra ta ji wani huci mai kama da k’ank’ara ya buso fukskarta da sauri ta k’ank’ame hannayenta a k’irji ta fara jin hak’oranta na ka’dawa da gaske ake sanyi ba na wasa ba, ba kuma irin sanyin mu na Nigeria ba. Tana hango masu sanye da jibga jibgan rigunan sanyin ma suna aikin k’udundune jikinsu masu mata kuma suna shigar da su jikinsu. Sai ta zama abin kallo a wajen mutane ganin yarda take sanye da y’ar shafal ‘din After dress. Sosai jikinta yake rawa hak’oranta na ka’dawa da k’arfin gaske kamar za su datse harshenta. Turaki yana gaba bai san abinda ake ba, tun Ayra na k’ok’ari har ta gagara don nunfahshinta ya fara fita sama sama kamar Athmatic tuni ta samu waje ta zauna tana mayar da numfashi. Maganganun mutane ne suka ankarar da Turaki ya juya don ganin me ke faruwa yana janye wayar da yake yi daga kunnensa. Da sauri ya ware ido ganin Ayra zube a k’asa ta k’udundune ga mutane turawa sun yi cincirindo a kanta. Bai san sanda ya saki akwatin hannunsa ba da sauri a ‘dimauce ya k’arasa in da take, hankalinsa a tashe ya ‘dagata ya mannata da k’irjinsa sai dai tuni numfashinta ya fara season. Da azama ya janye rigar Sanyin da take jikinsa ya shiga kiciniyar saka mata yana jero duk addu’ar da tazo bakinsa don da gaske gani yake kamar zai rasa Ayra a gab’ar da yake jin sonta yana neman kassara masa rayuwa. Bata numfashi don numfashin ya tsaya cak hakan yasa mutane suka nemi kawo masa ‘dauki ta hanyar kiran ma’aiktan da ke cikin airport ‘din aka zo da ambulance aka ‘dauketa da gaggawa bayan an manna mata oxygen a hancinta. Tuni Turaki ya gigice ta lafiyar Ayra kawai yake don haka yana zaune gaban gadon akan idonsa ake komai duk da k’ok’arin doctors ‘din gani yake kamar ba sa aikata komai kamar ya amshe su yake ji, sun kuma rok’esa ya fita ya k’i don baya jin ko taku ‘d’aya zai iya k’arawa daga inda yake. Da k’yar suka samu nasarar janyo numfashin nata ta fara fisgar sa da sauri kafin a hankali ta bu’de idonta tana sauke su kan Turaki da ya kafeta da nasa idon hannayensa damk’e da nata hannayen yana murzasu cikin wani salo. A hankali ta sake janye idonta tana lumshe su kafin k’ak’karfan nunfashin ya biyo bayan barcin da ya ‘dauketa mai bayyana tsananin galabaitar da take ciki. Turaki ya saki ajiyar zuciya yana kaiwa lab’banta gamsashshiyar sunbata ba tare da jin kunyar likitocin ba duk da suma ba su da kunyar ya da’de yana tsotsar bakin nata abinda ya da’de yana mafarki kafin ya janye yana mayar da nasa nunfashin da yake fita da wata irin nauyayyiyar soyayyar Ayra mai shirin b’alla k’irjinsa cikin wata irin murya ya ce “Ya Rabb save my wife you know she is my everything.” Ya fa’da yana lunshe ido sai ga wata siririyar k’walla tana zuba daga idanun nasa. Da gaske ainun ya tsorata sosai gani yake kamar zai rasa Ayra a gab’ar da ya shirya mallaka mata rayuwarsa gaba ‘d’aya tunda ya kasa jumurin jurewa idan ba so yake ya samu matsala a gab’ban jikinsa ba da gaske wahalar da soyayyarta take ba shi ta kai mak’ura kullum barcinsa a wahale yake yinsa, shi yasa ya ji ya amince zai karb’eta a duk yarda ya sameta tunda ba budurcinta yake yiwa ba zallar so mara algus yake mata. Tafin da likitocin suka masa ne ya ankarar da shi abinda ya yi ‘din, sai kawai ya sakar musu murmushi yana murza hab’arsa mai cike da kwantaccen gashin da ya k’arawa kyansa kyawu mai ban k’aye.

Har tsakiyar dare yana tare da ita sallah ce kawai take tashinsa daga wajen. Ta da’de tana barcin kafin ta samu ta farka sai sannan ta tuna a inda take ta dinga bin ‘d’akin da kallo kafin ta sauke kallonta a kan Turaki da ya zuba mata nasa Sexy Eyes ‘din ya kamo hannunta yana matsawa A hankali “Ya jikin?” Muryar da ya mata magana ce ta saka ta k’ara dubansa da kyau tana tantama idan daga bakinsa furucin ya fito. Ya ‘d’aga gira yana sake murza hannun a tausashe ya lumshe ido kafin ya ware su a kanta “Am sorry! Me kike so yanzu?” “Gida” ta fa’da cikin karyayyiyar murya Ha’de da k’ok’arin zare hannunta yana murmushi ya ce “Wane gidan?” “Gidan Amma.” Ta fa’da hawaye na zubo mata kamar an kunna famfo wannan karan hawayen ya kalla sosai kafin ya ‘dauke kai cikin kasalalliyar murya ya ce “Kukan mace shine abu mafi munin saurare a wajena Don Allah ki bari” kukan ta sake fashewa da shi sosai ya ware ido yana kallonta kafin ya kai bakinsa daidai kunnenta yana fa’din “Kina son na saka ki shirun dole ne?” Yanayin kallon da yake mata ne yasa ta runtse ido da k’arfin gaske, ta caku’de fuska kafin ta ce “Please ka min booking flight na koma gida sanyin garin nan zai hallakani.” “Zan miki maganin sanyin, za ki daina ji in dai kin bani dama bari mu isa masauki.” “Da me zaka min maganin sanyin?” “Da jikina.” Ya fa’da yana k’ank’antar da idanunsa cikin nata…. A razane ta dinga kallonsa tana son gano abinda furucinsa yake nufi….



A yi hak’uri uzuri ne yau ya tsareni shi yasa za ku ga typing ‘din ka’dan. Nagode…😊
Takaicin Uba…..

Nazeefah Nashe.

39.



❤️♥️❤️♥️


Kokawa ta fara yi da yawun bakinta da k’yar ta samu ta ha’diye Wanda ya tsaya mata a wuya. Ba ka’dan ba furucinsa ya razanata me take shirin ji? Me yasa yanzu yake son kusanta kansa gareta? Bayan a da ba shi da ra’ayin hakan asalima k’yama muraran yake nuna mata, me ya canja zuciyarsa shin ya daina mata kallon fasik’ar ne? Karuwa? Kamar yarda a lokuta da dama yake kiranta. Tabbas kuwa an zo gab’ar da zata ba shi mamaki zata nuna masa Jikin Ayra Gaya mai tsada ne ba kuma za’a same shi karabiti ba tana da ajin da zata ja zarensa har sai ya raina kansa, kuma bata fatan gamayya da wani ‘da namiji da sunan auratayya duka ta tattarasu ta jefa su a mahalli ‘daya, sunansu ‘daya halayensu ‘daya ba su da wani banbanci sai ta fuskar kamanni. Tunanin da take yi kenan a ba’dini yayin da shi kuma ya zuba mata masifaffun idanunsa masu nuni da zallar soyayyarsa da buk’atuwarsa zuwa gareta. “Kin yi shiru?” Ta jiyo sautin fitar furucin nasa kamar ba nasa ba kamar aro muryar ya yi yake mata magana da ita, ina waccan Kausashshiyar muryar mai fitar da sauti cikin isa da gadara wato yanzu sak’on yaudararsa yake son isar mata tunda ya kwa’daita da jikinta ashe kuwa za su kwashi y’an kallo. Ta ja siririn tsaki da ya fita ta iya tsakanin lab’banta “Na gaya maka ba abu mafi soyuwa gareni a yanzu irin na ganni a Nigeria….” Mhmnm ya saki ajiyar zuciya yana matsawa da jikinsa sosai kusa da ita fuskarsa tana neman gugar tata don har tsinin hancinsu yana gugar juna ga numfashinsu da yake sauka lokaci guda yana dukan junansu, numfashin da yake sake hargitso masa da kwantacciyar sha’awarsa ta shekara hu’du, ita ‘din ma hakan ce ya kasance a tare da ita kusancin nasu ya saka ta a wani yanayi da ya matuk’ar gigita tunaninta. Da sauri ta ja jikinta har tana ha’da k’irjinta da nasa abinda ya saka shi saurin runtse ido yana fitar da wani sauti na ‘Ahhhh’ a hankali ya runtse idonsa yana mayar da gangar jikinsa jikin kujera hannayensa cushe cikin gashin kansa yana fisgarsa a hankali cikin zuciyarsa yake furta yarinyar nan nema take ta k’ureni. Shiru ya bak’unci ‘d’akin kowa ya afka cikin wani yanayi da shirun shine yafi amfani a lokacin don dai magana ta furucin baki ba zata iya fita ba, idanunta a runtse suke yayinda shi kuma ya kafa mata ido yana kewaye jikinta da kallo ba inda bai yiwa kallon k’urilla ba a ranar fatansa kawai Allah ya kai damo ga harawa ya zubar da abinda yake cikin jikinsa yake wahalar da shi tsawon shekara hu’du. Bata bu’de idon ba shima kuma baya fatan ta bu’de yafi son ya morewa kallonta yana tunanin ta sigar da zai bi ya mallaki zuciya da gangar jikinta. Idanunta a runtse amma ta san idanunsa a kanta suke yawo. “Na gaya maka gida nake son zuwa.” “Na ‘daure ki ne?” Ya fa’da da yanayin fara gajiya da maganar gida da take masa. Ta ware ido tana kallonsa shima ‘din kallonta yake kafin ya furta “Ki k’addara ke da gida sai nan da shekara cif idan muna da yawon rai.” “Wasa kake amma?” Ta furta cike da mamakin kalamansa “Time will tell bari mu ba ko wasan nake.” Shima amsa ya bata yana ‘dauke kansa don ya lura kamar laushin da ya fara masa ne yake nema yasa ta rainashi bata son har yanzu daurewa yake ba idan ya tuna shashashun mazan da ta yi hul’da da su, don haka kafin komai ma ya shiga tsakaninsu sai sun je an musu gwajin HIV da STD don ba zai je ya samu cuta a banza ba. “Kin tab’a test ‘din HIV da STD?” Ya samu kansa da jefo mata tambayar da shi kansa bai shirya yinta ba illa sub’utar harshe. A gigice ta ‘dago tana masa kallo kafin ta ce “Whatttt???” Ya kafe ta da ido duk da kunyar ta na neman kama shi sai ya ga kamar tambayar bata dace ba, amma kafaffiyar zuciyarsa ta hana hakan yi masa tasiri fuska a ha’de shima yana ‘dan ware ido ya ce “Yess! Kin san duk wanda yake yawon banza ya kamata time to time ya dinga test ‘din nan.” Numfashinta ne ya fisga da k’arfi da b’acin rai ta sauke idanunta k’asa don yak’i da k’wallar da take son zubo mata sam bai dace ta yi masa kuka ba tunda shi bai san mutunci ba “Ina son rayuwar aure da ke, amma on One condition dole ki je asibiti a miki wannan gwajin.” “Idan kuma na k’i fa?” Ta fa’da tana tsareshi da idanu da yake hango matsanancin b’acin rai a cikinsu “Fine and good sai na bar ki da y’an iskan ki, ni kuma na auro Kamila.” “Shine abinda ya fi maka sauk’i don wallahi da na ha’da gangar jiki da kai gwara na mutu..” Da sauri ya ‘dago yana kallonta da gaske ya hango matsananciyar tsanarsa a idanunta cikin b’acin rai ya ce “Kin gwammaci ha’da jiki da y’an iska a kan ni Mijinki na sunnah.” Tana girgiza kai alamar tabbatarwa ta ce “Sun fiye min kai sau dubu, su cikakkun maza ne da suka amsa sunansu Maza idan nace cika ina nufin cika ta zahiri da ba’dini kai kuwa fa na tabbatar yarda kake da hasken fatar nan baka da k’warin da zaka iya gamsar da Mace rago ne kai tabbas!” Bata san sanda ya mik’e ba ita dai kawai ta gansa a gabanta yana huci kamar zakanya “Ni kike kira ragon namiji?” Ya ciji lab’bansa “Lokaci ya zo da ya kamata na ankarar da ke menene ma’anar ragon namiji tabbas a yau ba sai gobe ba zan nuna miki ragontaka ta…” “Me zai saka ka kusanci sauran wasu?” “Rashin kunyar da kika min ne zai saka na banbance miki tsakanin aya da tsakuwa wallahi sai kin raina kan ki ki tanadi duk wani magani da kika san zai samar miki da sukuni a irin gurzar da zan miki tunda ke ba ki da kunya duk dai na san hanyar a bu’de take warwar Amma yau zaki banbance tsakanina da sokwayen mutanen da kike kira sun fi ni.” Sosai ta tsorata da furucinsa sai dai ko ka’dan bata nuna masa a fuska ba, don k’arfin hali sai cewa ta yi “Sai mu zuba mu gani.” Ya runtse ido yana jin amsa kuwwar furucinta ba ka’dan ba ransa ya b’aci ji yake kamar tun a yanzu ya fara fatali da duk wata sutura ta jikinta ya je mata a Jaruminsa kamar yarda Hibba Uwargidansa ta sha Kambama shi da sarautar jarumtaka ya shafi sajensa yana futar da murmushin takaici.


Sai da drip ‘din da aka saka mata ya k’are tsaf sannan suka tafi don samun motar da Zata kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login