Showing 102001 words to 105000 words out of 132090 words
Chapter 35 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
shigowa da dare su gyara gidan. Sannnan ya mayar da kansa ya runtse yana fatan barci ya ‘dauke sa, sai dai ya kasa moment ‘dinsu na daren jiya ya tsaya masa a rai ji yake kamar ya janyota ta k’arfi ya k’ara kusantarta sai dai ya daure kawai ya hak’ura a ransa yana raya da kan ki za ki kawo k’afarki Ayra.
Sai 6:45 ya farka daga barcin da ya ‘dauke shi, Ayra kuwa har a lokacin barcinta take peacefully da alama ta samu sauk’in jikinta sai da ya lek’a fuskarta yana kallonta kafin ya saki ajiyar zuciya yana mik’ewa. Bai san wani irin so yake ma yarinyar ba da ya tsaya masa a rai har haka, ko barci yake tunaninta ne ‘danfare a ransa. Ya shige toilet yana k’ok’arin sakarwa kansa ruwa don shi da kansa ya san wanka ya kama shi tilas. A gaggauce ya fito da tunanin kada lokacin sallah ya wuceshi. Sai da ya idar da sallah sannan ya shige toilet ya tara ruwa mai zafi a Cikin bathtub ya saka duk abinda ake buk’ata sannan ya fito. Idanunsa suka fa’da kan Ayra da take kwance ta k’udundune abin rufar ma ya zame can gefe daban gaba d’aya santala-santalan cinyoyinta a waje. Turaki ya k’arasa wajen yana k’ok’arin danne abinda yake ransa kafin ya ‘daga ta cak. Da sauri Ayra ta bu’de ido “Me ye haka ajiye ni bana so.” “Ni kuma ina so.” Ya fa’da yana kaiwa bakinta sumbata “Ki tsaya ki min shiru ko na sakeki a k’asan wajen nan, don kin ga ma ina tattalinki.” Ta bu’de idonta sosai a kansa sai dai da azama ta runtse don ba zata iya jurewa narkakken kallon da yake mata ba. “Ni nace ka yi tattalina?” Ta fa’da tana cuno bakinta. Murmushi Turaki ya yi yana kissing lips ‘dinta da suke da taushin tsiya kamar ana jik’asu kullum “Mara kunya, sai rakin tsiya bayan ba ki da juriya ko ka’dan. Idan ba ki wasa ba mata uku zan aura na ha’da ku da su.” Ta ‘dauke kanta kafin ta ce “Ka auri goma ma ina ruwana ba sai ka ganni ba.” Dai dai lokacin ya saka ta a bathtub ‘din yana k’ok’arin cire rigar da take jikinta ta yi saurin rik’e hannun. “Bari ba na so.” “Ni kuma ina so, bari ma ki ga sunnar annabi za mu bi tare za mu yi wankan.” Ayra ta runtse idonta ganin da gaske Turaki yake ta hau watsa masa ruwa tana fa’din bata so. Da sauri na juya don idanuna ba za su jure ganin wannan sirrrin nasu ba, na san dai yau Ayra ta gane Turakin mu first class ne a wannan fannin don luf ta yi a jikinsa tana amsar wasu irin sak’onni masu shiga rai a zuciyarta mamakin maza take da basu da kunya ko ka’dan, idanunsa rufewa yake idan an zo wajen nan.
Duk abinda yake kallonsa kawai take don ta sakawa zuciyatta dole ya rabu da ita, tana kallo ya tattara duk wasu kaya da suka cire kafin ya k’araso wajenta hannunsa ‘dauke da black abayanta ya mik’a mata. “Oya maza saka mu tafi.” Tsayawa ta yi tana kallonsa kafin ta furzar da numfashi ka’dan ta ce “Ina?” “Our House mana, na saka an gyara tun ‘dazu, mu je ki ga gidanki.” Ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya kafin ta mik’e tana tsayen ya zura mata rigar. Ya bata hug sosai yana fa’din “Ki saki fuskar mana Hayateey.” Ta ‘dauke kanta ha’de da fa’din “Sunana Ayra.” Murmushi ya saki yana tallafar hab’arta ya fata lalubar k’wayar idonta so yake su ha’da ido sai dai ta k’i ba shi dama sai runtse idon take. Ya shafi lab’banta da suke fusgar hankalinsa ya ce “Ana so ana kaiwa kasuwa, mhmn?” Ya jata suka fice daga ‘dakin.
Sai da ta jira shi a reception ya yi signing sannan ya k’araso wajenta suka fita wajen mai Cab ‘din da yake jiransu.
Tun daga waje yanayin tsarin gidan da ya kasance duk glass ya yiwa Ayra kallon gidan kawai take tana jin yana sake burgeta tun kafin ma ta shiga ciki. Ga wata iska da take ka’dawa a hankali gefe guda k’aramin garden mai ‘dauke da nauikan tsuntsaye iri-iri, kowa dai ya san tsari da yanayin zubin gidajen turawa. Sanyin da ake ne yasa Ayra ta fara takurewa saboda har snow ne yake zuba ka’dan-kadan a nahiyar garin. Shigarsu parlourn ya sa ta sake jin wani uban sanyi musamman a.c ‘din parlourn a kunne take. Da sauri ta takure a kan kujera tana jin yarda sanyin yake neman kassara gab’obin jikinta. Kula da hakan yasa Turaki ya yi saurin kashe air condition ‘din ya kunna heater yana kallonta ya ce Kumama” ta ‘dauke kanta tana kallon yanayin falon da komai na cikinsa ya zama golden brown. Sai da ya kai kayan ‘d’aki sannan ya dawo ya tsaya a gefenta yana mik’a mata hannu. “Taso mu je in nuna miki bedroom.” Ta mik’e bata musa masa ba don ta gaji sosai akwai kuma tazara tsakanin hotel ‘din da anguwar da suka zo. Har tsakiyar babban bedroom ‘dinsa ya kaita da yake fitar da wani irin ni’imtaccen k’amshi ‘dakin ga shi ya ‘d’au ’dumi sai ya dace da yanayin sanyin da ake kwararawa a garin. Ayra ta tsaya tana kallon cikin ‘dakin kafin idonta ya kai kan hoton ta da yake jikin bango sai dai kamar zanawa a ka yi. Da sauri ta k’arasa jikin bangon tana k’arewa hoton kallo kafin ta juyo da niyyar yi masa magana, sai kawai jin ta tayi a jikin mutum ya rungumeta tsam a jikinsa a kunne ya ra’da mata “Kin san hoton nan?” Tana k’ok’arin zame jikinta ta girgiza masa kai “Ban san sa ba, a ina ka samu?” Ya juya bayan pic ‘din yana sakin murmushi kafin ya jata bakin gadon suka zauna jikinsa a jikinta ya ce “Na same shi 8yrs back, the same date da yake jikin hoton. A airport na ‘dauke ki a pic ‘din. Kin tuna wata rana da muka yi clashing aairport ina kallonki har kika yi tsaki kika yi saurin jan nik’ab ‘din ki.” Ayra ta yi shiru tana nazari duk da an da’de Amma sai yanzu abin yake dawo mata kamar majigi, tabbas sanda ta gan sa sai take imagining ta tab’a ganin sa Amma ta rasa a ina ne. “So ki daina cewa na rabu da ke, daman kece buri na you are in my dream all these years. Baki tab’a bari na na huta ba, kullum addu’a na Allah ya ha’da ni da ke, don haka dole na
Ji ba da’di sanda na ha’du da ke aka kuma zo min da maganar wai kin tab’a yawo…” ya ciji leb’ensa “shine abinda yasa ki kaga hankalina ya tashi na ji ba da’di har nake miki abinda na miki, but am sorry please.” Zuciyar Ayra ta ‘dan rusuna sai dai ba wai don ta hak’ura ba, ta tab’a baki tana fa’din “Wallahi ba zan hak’ura ba, sai na je na fa’da a gida, kuma ni abinda yasa na yarda da kai don ka tabbatar bana hul’da da maza, amma ni ban tab’a son ka ba.” Turaki ya runtse idonsa cikin jin zafin abinda ta ce “Wai shine mace yau take cewa ba ta so, ransa ya ji yana b’aci kafin ya mik’e a hankali ya zameta daga jikinsa. “Na ji ba kya so na, nagode,but do me a favour, kada ki kai maganar nan gida ki yi zaman ki ni kuma ba zan sake kulaki da sunan mu’amalar aure ba har sai kin amince da ni da kan ki, amma don Allah kada ki kai maganar nan gida.” Ya durk’ushe a gabanta yana jan tattausan hannunta yana matsawa a hankali. Ayra ta yi shiru tana runtse idonta “Kada ki kai please! Ni kuma zan yi k’ok’arin koya miki so na.” “Never for ever!” Ta fa’da a zafafe tana zame hannunta “Na amince ba zan kai maganar gida ba, amma a kan shara’di guda kada ka sake kusanta ta kamar yarda ka ce har sai na amince da kaina, sannan ba zan dinga maka girki ba, ba abinda zai ha’da mu ko magana.” Turaki ya tsaya yana kallonta cikin tashin hankali ya ce “all these? Ya yi min tsauri ki na dai ba ni abinci kuma zan dinga mi ki magana, ai musulunci ya hana gaba.” “And Musulunci ya hana ka tozarta ‘dan uwanka musulmi ba. Hakan shi nake so idan fa ka amince idan ba haka ba kuma I should park my things and leave.” Murmushi ya ‘dan saki ya ce “Na ji na yarda amma idan kin yarda zan yi aure ko?” Ta bu’de idanunta tana kallonsa ta ce “Na yarda ka yi uku ma.” Turaki ya ciji leb’ensa yana tunanin da gaske yarinyar bata son sa, dole ya nemi mafita, kafin soyayyarta ta kassara shi. “Nextweek zan yi aure.” Ayra ta ‘dauke kanta tana fa’din Allah ya kai mu.” Turaki ya ciji leb’ensa yana kallonta ya ce “Ga can ‘dakin ki, ki ja kayanki ki fita, kuma duk abinda ya biyo baya ba ruwana don’t blame me okey?” Ta ‘dauke kai tana fitar da k’aramin tsaki ta ce “Oho, ni ina ruwana.” Turaki ya ja trolleynta yana fa’din “Na ji zo ki tafi.” Ta bi shi a baya kuwa suka fice daga ‘dakin sai da ya nuna mata har kitchen da komai na gidan sannan ya saki hannunta yana fa’din “Na amince ki shiga ko ina, ban da can part ‘din anan zan saka amaryata.” Ta tab’e baki tana shiga ‘dakinta…
Takaicin Uba…
52.
Turaki ya bita da kallo yana mamakin kafiya da taurin kai irin nata? Ya saki ajiyar zuciya don idearrsa ta k’are bai san me zai mata ba kuma ta hak’ura, don ba ya jin zai iya cika alk’awarin da ya ‘daukar mata. Ya da’de a wajen yana folding hannayensa yana sakewa. Kafin ya ja k’afafunsa a hankali ya koma kan three seater ya kwanta idanunsa a runtse yana tunanin haka dama soyayyar take don shi ko Hibba bai wa son da yakewa Ayra ba, Hibba kyawawan halayenta ya ja shi gareta ita kuwa Ayra gaba ‘dayanta yake son ta ba shi kuma da wani k’wakkwaran dalili.
Ita kuwa Ayra tana shiga bedroom kifewa ta yi a kan gado zuciyarta ta yi rauni sosai da tunanin da Turaki ba a budurwa ya sameta ba wani irin wulak’anci ne zai biyo baya. Ta saki ajiyar zuciya tunani ya shigeta sosai ta fara tuno wancan halin da ta shiga Allah ne ya ceceta duk da a lokacin bata ga zahirin fuskar mahaifin ta ba, sai bayan da k’addara ta Riga fata a hankali komai ya dinga dawo mata kamar majigi kamar ma yanzu aka yi abin.
________________
Sanda Hadi ya ce Kabiru ya ‘dauketa Ayra runtse ido kawai ta yi, don bata san me zai aikata mata ba, tunda k’wak’walwarta har a lokacin ba ta san akwai wata mu’amala da take tsakanin namiji da mace ba. Sai da suka shiga ‘dakin idanunta ya raina fata ganin yarda a gaggauce ya cire mata kayan jikinta shima ta ga ya zare wandon sa ya kwantar da ita rigingine yana shirin aikata abinda ya yi niyya ganinsa a hakan yasa ta runtse idanunta ta kuma k’walla k’ara hakan yasa Kabiru saurin kashe fitilarsa da waya ya toshe mata baki. Daidai lokacin suka ga Ya. Majeeda ta rufta cikin ‘dakin da sauri hankalinta a tashe ta janye Kabirun a zafafe tana fa’din “Kada ka cutar da ita, ta yi k’ank’anta ni na amince ka min abinda zaka mata.” Ba wani shakka Kabiru da ya tuna a maganar bokansa dama Ayra ko Majeeda ya ce sai kawai ya jawo Majeedan ya haik’e mata. Ihun Majeeda shi ya gigita Ayra bata san lokacin da ta suma ba cikin wani irin gigitaccen k’ara Majeeda take jin azabar da take fisgarta bata san lokacin da ta tuge bak’ar fuskar da mahaifin ta ya sa a fuskarsa a kuma lokacin ne cikin hukuncin Allah wutar nepa ta dawo hakan yasa Majeeda ta yi ido hu’du da mahaifinta da razana da tashin hankali suka saka ya mik’e da sauri yana kallonta kafin ya yi aune Majeeda wani k’arfi yazo mata ta janyo katako ta buga masa tana ihu tuni ya zube a wajen ya suma banda buguwar da ya yi tashin hankali ma ya isa ya saka shi ya k’ara suma. Majeeda ta fita falon da gudu duk da azabar da take ji a zuciyarta bai hanata isa wajen Amma ta rungumeta ba cikin kuka ta ce “Amma Abba ne, Abbanmu ne a ciki.” Jin haka Hadi da sauri ya fice a guje jin an gane Kabiru ne a ciki ba ya son shima su gane shi. Amma jikinta na rawa ta kama Majeeda ta na fa’din “Majeedah mai kunnuwa na suke jiye min? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna.” Kafin ta yi aune Majeeda ta zube a jikinta ta sume cikin wata irin mak’yark’yata Talatu ta ja k’afarta ta isa ‘dakin ido biyu kuwa ta yi da Kabiru kwance a wajen a sume. Amma ta runtse ido jikinta na rawa ta zube a wajen tana kukan tashin hankali kafin itama numfashinta ya fara sama ta zube a wajen a sume. Zainab hankalinta a tashe ta fice daga gidan ta hau buga gidan Kamilu tana kuka tana kiran Kamilu. Da sauri Kamilu da Jummai suka farka a ‘dimauce suka yi bakin gate jin muryar Zainab ya ‘daga hankalinsu. Kamilu ya bu’de gate ‘din hankali tashe yake duban Zainab “Ke nutsu Zainab yi min bayani Waye ya mutu?” Zainab da take aikin mayar da numfashi don k’irjinta ya yi nauyi ji take itama kamar ta suman ta ja hannun Kamilu kawai a fisge suka shiga cikin gidan. Ta kai su har cikin ‘dakin tana nuna musu Kabiru “Shi ya yiwa Ya. Majeeda da Ayra fyad’e.” Saura k’iris Kamilu ya zube a wajen banda Jummai ta yi saurin rik’e shi tana fa’din “Nutsu Maigida idan ka zube ni Kuma ya zan yi? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna. Yanzu menene abin yi?” Kamilu ya ce “Y’an sanda zan kira Jummai, wannan lamarin Ai ya fi k’arfin a yi shiru.” Jummai ta girgiza kai tana jan hannunsa suka zauna a kan kujera “Kada Ka fara Kamilu, kiran y’an sanda ba shine mafita ba, illa tonawa kan mu asiri.” “To me kike so a yi Jummai? Kin ga fa abinda Kabiru ya yi kamar wani mahaukaci, y’arsa fa ya cikinsa Jummai sai ka ce ya sha k’waya.” Ya fa’da idanunsa yana zubar da hawaye. Jummai ta saki ajiyar zuciya itama kukan take sai dai bata son a kai maganar wajen y’an sanda gudun fallasuwar sirrinsu, hakan yasa ta dafa Kamilu murya a raunane ta ce “Ka yi hak’uri mu yi aiki da hankali Kamilu, yanzu dai zuba musu ruwa mu samu su farfa’do.” Kamilu ya kasa mik’ewa don ji yake idan ya mik’e zai iya fa’duwa saboda jirin da yake ‘dibansa. Jummai ce ta ‘debo ruwan ta shek’a musu. Sai ga Ayra ta farka a firgice tana ihu “Amma ya cire min kaya na shiga uku Amma ya hau kai na me zai yi min?” Surutai kawai take kafin Jummai ta kamata ta rungume cikin raunin zuciya tana dubata ta ga ita Kabiru bai tab’a ta ba. Sai Majeeda da ya Riga ya shigeta, tausayin Majeeda ya kama Jummai ta kamata da k’yar suka shiga toilet sannan ta tara ruwa mai zafi ta saka ta a ciki Majeeda na ihu tana fa’din “Ya Allah ka ‘d’au raina rayuwata bata da amfani.” Jummai ma kuka take. Can falo kuwa Amma ko motsi ta kasa yi shi kuwa Kabiru ya mik’e da k’yar yana jin wani irin nadama da ciwon kai mai tsananin gaske fata yake mutuwarsa ta riskesa a wannan lokacin da wannan abin kunyar da ya aikata. Ya runtse idanunsa bayan Kamilu ya zuba masa uban mari a duka kumatunsa guda biyu, sannan ya mik’e yana jan hannunsa daidai lokacin da aka yi Assalatu yana fa’din “Mik’e tsaye Kabiru, tafiya za mu yi da kai wajen y’an sanda yanzun nan su maka hukuncin da ya dace da kai, mahaukaci dabba, jahili ‘dan akuya. Wallahi ina tur da zamowarka ‘dan uwana Kabiru na tsaneka tsana mafi muni. In sha Allah tun a duniya sai Allah ya saka musu. Daidai lokacin da yake jan sa Jummai ta shigo hannunta rik’e da Majeedah da ta ke ta k’yarma idanunta na sake cin karo da mahaifinta ta sake zunduma ihu tana fa’din “Allah ya isa Baba Allah ya bi min hakkkina.” Kabiru ya runtse idanunsa yana jin duniyar na masa wani irin walagigi. Jummai ta kalli Kamilu tana fa’din “Wai ina za ku je ne? Na ce maka fa ka bar maganar zuwa wajen y’an sanda ka bari yanzu su gama shiryawa mu ‘dunguma a tafi Shagogo duk abinda magabata suka ce da shi za’a yi aiki, tunda dai cuta ya Riga ya cucesu ya gama da su.” Kamilu ba don ransa ya so ba ya saka Kabirun a wani ‘daki ya kullesa don kada ma ya gudu. Sannan ya fita samo musu shatar mota don su tafi Shagogo.
Haka suka rankaya suka tafi Shagogo rayukansu a cunkushe da b’acin rai, musamman Amma da sam bata gane abinda ake yi kawai bin su take da idanu, ta ma kasa magana tsabar takaici da zuciyarta take ciki. Ayra kuwa ba a awa guda bata razana ta firgice ba, Majeeda zazzafan zazzab’i ya rufeta kafin isar su Shagogo.
________
Gaba ‘d’aya labari ya kara’de garin Shagogo, kowa ya samu labarin irin badak’alar da Kabiru ya yi ba ta yarda za’a iya b’oye irin wannan magana mai girma. Sai dai Maigari ya rok’i mutanen garin a kan su dubi girman Allah kada su k’etara da maganar wani gari duk da ya san hakan ba lallai ya yiyu ba. Mutanen gari suka taru suka dinga tsinewa Kabiru suna kuma rok’ar Talatu afuwa don a yanzu halin Kabiru ya fito muraran kowa ya yi tur da Allah wadarai da shi, aka kuma ce ba shi ba garin. Sai a sannan Talatu ta yi magana tana kallon Mai gari “Ka gaya masa ba shi ba