Showing 33001 words to 36000 words out of 132090 words
Chapter 12 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
bo’ddon ta dawo k’ark’ashin kulawarta, sai dai sam Moddibo Ya k’ek’ashe idonsa Ya hana tunda Innawuro ta masa wani kallo. Da ky’ar ya amince ta dinga zuwa tana yini ta dawo da yammanci. Lokacin ta samu d’an sassauci a gidan su Hameeda take cin abinci ta sha ta yi wanka Hameeda kuma ta koya mata karatun boko. Suka shak’u sosai da Hameeda duk inda za su je tare suke zuwa Hameeda ta zame mata garkuwa tunda ita macece mai zafi ba kuma ba ta ‘daukan raini. Bo’ddo hankalinta ya fara kwanciya duk gari suka fara rubibin neman aurenta a shekarunta goma kacal. Hakan ya sake tunzira su Inna wuro haushi kamar ya huda k’irjinsu. Suka canja mata suna daga Bo’ddo zuwa Talatu don suna bak’in cikin su kirata da sunan da kai tsaye yake nufin kyau a fillanci.
Kabiru wani hatsabibin mutum ne da ya gagari jama’ar k’auyen, kowa kuma yake jin shakkarsa don idan ka bari ka shiga gonarsa mai rabaka da shi sai Allah. Tunda ya k’yallara ya ga Talatu ya saka ‘dambar samun aurenta ko ta wane hali. Ya uzzira wa Talatu da neman Soyayyarta ko da ta dole ne. Babu kuma wanda ya isa ya kulata idan kuwa ya ji labarin kana neman aurenta har gida yake zuwa Ya baka garga’di mai kyau. Talatu bata kulashi domin bata ma shirya soyayyar ba a k’ank’antar shekarunta balle ta karb’a, me ma ta sani? Shi yake ki’dansa yake rawar sa. Sau tari ya sha rutsata Amma sai Hameeda ta janye ta tana masa masifa.
Mahaifiyar Hameeda ita taso tsaya mata akan maganar Kabiru sai dai kana taka Allah na tasa cikin dare ciwon ciki ya kama mahaifin Hameeda Ya rasu, hankalunsu suka tashi.
Wannan shi ya jawo Su Hameeda barin k’asar don takanas iyayenta suka aiko aka tafi da ita da yaranta gaba ‘daya. Hameeda Kuka Talatu kuka don ba sa son rabuwa da juna Amma suna ji suna gani aka rabasu suka tafi don Moddi yace ba zai bada Talatu ba a barta aure zai mata.
Wannan shine mafarin shiga duk wani hali da Talatun ta tsinci kanta, tabbas mummunar k’addararta tana ‘danfare ne da auren Kabiru.
Kuka da ihu ba irin Wanda ba tayi wa mahaifinta ba, a lokacin da Ya k’udiri aniyar aura mata Kabiru. Su Inna wuro kuwa gefe suka koma suna shek’e mata dariya da tunanin hak’ansu ya
Cimma ruwa, burinsu Ya cika Talatu zata yi k’ask’antacciyar rayuwa a gidan Auren Kabiru.
Shekarunta sha uku cif sanda aka ‘daura mata aure da Kabiru aka kuma kai ta ‘dakinsa ba tare da shagalin bikin da aka sabawa duk wata budurwa a garin ba. Matar k’anin Babanta Innayo ita ce mai ‘dan kulawa da lamarinta tun bayan tafiyarsu Hameeda, sai dai su Inna wuro Sun fi k’arfinta komai za tayi sai dai a bayan fage. Ita ta bata buta da langa tuwo da miya da tray na langan sai cup, sauran tarkace kuwa wanda ya ga Allah ne ya bata mai kofi mai faranti mahaifinta kuma ya siya mata katifa shikkenan aka sadata da ‘dakin mijinta. Gidan mijin da kai tsaye zata iya kiransa kurkuku saboda bala’in da tarar a cikinsa. Gidan mijin da da aurensa gwara babu, gidan Mijin da Ya rusa mata farin cikinta da na y’ay’anta gaba ‘daya…. Gidan mijin da da da da ‘din da yawa ita kanta ba zata iya lissafo rashin alherin Auren Kabiru ba da bakinta, sai dai ta San duk wata jarrabawa da Mace take fuskanta a gidan aure ta tata ta zarce ta tata.
Takaicin Uba….
16
Nazeefah Nashe
💔💔💔
Daren farko a gidan mijinta, dare ne da ba zata iya mantawa da shi ba, dare ne da kai tsaye zata iya kiransa Rabin mutuwarta don a yarda Kabiru ya kusanceta cikin k’ask’anci da rashin tausayi shi ya fara firgitata da lamarin aure, gaba ‘d’aya duk wata buk’ata tasa ya jirkice ta akan k’aramar yarinya, ba tausayi ba tunanin k’ank’antar shekarunta, ta dinga jin wani irin ra’dadi da azaba, kai kace gabanta ne zai zazzago. Yana gamawa kuma ya tsallake gefenta Ya kwanta ya barta tana kuka mai tsima zuciya. Ji take da da hali da ta bi mahaifiyarta inda ta tafi da ta huta da wannan azabar duniyar. Kukan ma da take madadin rarrashi Kabiru tsaki ya yi ya hau mata masifa “Malama ki min shiru, bana son shashasha cin banza menene amfaninku dama ku mata? idan banda wannan ‘din ba don haka dama ai aka ce mu aureku, kuma sadaki na ne nake gurza son raina kin san da wahalar da na samo ku’din da na biya sadakin ki? yanzu ma hutawa zan yi na k’ara.” Wani irin kuka ta sake saki duk da tana k’ok’arin kawar da kukan, Amma ta razana k’warai da jin furucinsa. Haka nan tana ji tana gani ya sake haik’e mata cikin daren nan, wannan karan Talatu sai da ta shi’de ta rasa inda zata saka kanta, bai damu da suman nata ba ya ja filo Ya mayar da kansa yana sakin murmushin jin da’di. Sai da ya ga alamu Sun nuna kamar ta mutu sai ya mik’e ya samo ruwa Ya watsa mata sannan ta kawo gauron numfashi, ta dinga jin haushin da addu’ar da ta yi bata karb’u ba, ta shek’a barzahu kamar yarda Innanta ta tafi.
Har rana ta ‘daga Talatu ta kasa tashi, don ba k’aramin illa Kabiru Ya mata ba a gabanta, ciwo take ji sosai ga jikinta ya mata tsami, kwanciya kawai ta yi kan katifa tana zubar da hawaye rashin sanin abinda zata yi, bata da kowa a garin da zai zo ya duba halin da take ciki kamar yarda ake wa Amare a duk darensu na farko a garin. Tana kallo Kabiru ya yi wanka Ya zira kayansa ya tsallake ya fice yana fa’din “Gwara ma ki k’warara jikinki da azahar zan dawo na sake…” Yana shirin fita ya wurgo mata ku’di “Idan kin gama rakin ki saka yaro ya siyo miki koko da k’osai, ko ba komai ai kin samu cigaba don na tabbata a gidan tsoho ‘dumame ake ci.”
Wannan karan runtse ido ta yi tana fatan mutuwarta kafin azahar ‘din don ta tabbata idan Kabiru ya sake kusantarta a halin da take ciki mutuwa zata yi Har lahira, gabanta kamar ana zazzaga borkono saboda ra’dadin tashin hankali.
Kamar daga sama ta juyo muryar matar k’anin Babanta Innayo tana sallama ita da ‘danta Jabiru da Ya rik’o mata roba da wata leda mai ‘dauke da langa da ta yiyo mata farfesun ganda. Farin ciki ya shiga zuciyarta ka’dan, musamman da ta ‘daga labilai ta shigo tana zabga salati “Me zan gani haka ni Tarasulu?” Ta fa’da tana kai idonta kan Talatu da jini ya b’ata jikinta. Ta k’arasa da sauri tana nunawa Jabiru waje “Maza Jabiru ta fi wasa, ba wajen zamanka bane nan.” ta kamata tana fa’din “Tashi Talatu mu gani Amma Kabiru an yi matsiyaci Allah yasa bai illata ki ba.” Da k’yar ta mik’e amma zama ya gagara sai kuka da ta saka ta rungume Innayo tana furucin mutuwa zata yi.” Salati kawai Innayo take ganin yarda Kabiru ya mata illa ba y’ar ka’dan ba.ta mayar da ita ta kwantar da ita ha’de da fita sararIn gidan da sauri ta ha’da wuta.
Ruwa mai zafi ta zuba a roba ta kai cikin ‘dakin da ko dab’en siminti Babu k’asa jajir zube a k’asan ‘dakin. Ihu kawai Talatu take da ta shiga cikin ruwan nan da aka zuba gishiri da lalle da bagaruwa ka’dan, sai dai ta ‘d’an samu sauk’i.
Sai yamma Innayo ta tafi ta bar Talatun tana tsinewa Kabiru a ranta. Bayan dawowarsa a yammacin ranar ma sai da ya sake kusantarta yana fa’din sadakin sa ya mora.
💔💔💔💔
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya a wajen Talatu cikin wani irin mugun yanayi, tun farkon rayuwarta bata huta ba har zuwa sanda ta haifi y’arta ta farko. Lokacin ne ta fara samun abokiyar hira. Duk da Majeederh irin yaran nan ne miskilaye amma tana Jin da’din zama da ita. Kabiru Sam bai damu da yarinyar ba ba ruwansu da ita, sanda aka haifeta ma da k’yar ya yanka mata abin yanka shi ‘din ma sai da yaga idon y’an gari Sun masa caaa aka sannan ya yanka ‘dan bunsuru, riga kuwa guda ‘daya jal ya siya mata shikkenan sai ya matse bakin aljihunsa, a cewarsa shi bai shirya haihuwa ba, koma ya shirya ma ba mace yaso a Haifa masa a farko ba, shi da yake son Magaji da zai taya shi noma, me zai yi da mace da bata San komai ba sai dai a taimaka mata haka rayuwarta zata k’are kullum sai dai ya wahalta mata. Hakan yasa Talatu ta zage ta dinga aikatau itace wankau itace surfau duk don ta kula da rayuwarta da ta ‘yarta. Majeederh na da wata uku cur wani cikin ya sake bayyana a jikinta, wannan karan ma Kabiru bai so bayyanar cikin ba, ba don komai ba sai don cikin yana hanashi rawar gaban hantsi ya fi so a koda yaushe ya kusanceta ba safiya ba dare ba rana, ba kuma wata kulawa yana shigowa zai fara gyaran murya sai kuma ya ce “Gyara” daga gyara ‘din nan sai dai ta ji mutum ya shigeta. Hakan ya sanya mata rashin son auren ta dinga tunanin bakomai a cikin rayuwar aure sai wahala. Abinci kuwa tsaba yake ajiye mata ita zata nemi na mai da na Maggi, ba abinda ya dame shi, tunda shi zai fita ya samu mai kyau ya ci. Haka ya sata a gaba da fa’din sai ta zubar da cikin, ita kuwa ta kafe ba zata zubar ba. Ido a raunane ta kalleshi kafin ta ce “Haba Kabiru ka yi hak’uri mana, tunda cikin ya riga ya shiga kuma Baka San me za mu Haifa ba, wata k’ila nan gaba sune za su ji k’anmu.” Ya zuba mata harara “Ni dai na gaya Miki idan kuwa kika sake kika haife cikin nan sai dai ki nemi uban da zai Miki hidimar sa, haka kawai mace da zarar an tab’a ki sai ciki kamar ke
Kika kawo haihuwa duniya.” Kuka take sosai kafin ta ‘daga Kai ta ce “Na yarda zan yi wahalar tasa, in dai zaka amince na haifeshi.” Bai sake magana ba ya zabga tsaki ya fice daga gidan. Yana ayyana idan kin san wata ba ki San wata ba. Daga wannan furucin sai ya samu dama, San da ta tashi haihuwa nak’udar ta zo mata da matuk’ar wahala ga Innayo ba lafiya dama ita ce mai taimaka mata, haka ta yi ta murk’ususu a ‘d’aki tana addu’a ga Majeedah ta yi yarinta balle ta aiketa mak’ota a samo mai taimaka mata, cikin hukuncin Ubangiji ta haife y’arta jajur da ita. Sanda Kabiru ya dawo daga yawon Daren sa idanu ya zuba mata ita da jaririyar, cikin b’acin rai ya ce “Me kika haifa?” Ta sunkuyar da Kai tana taraddadin amsar da zata ba shi. Murya a raunane ta ce “Macece.” Wani uban ashar ya k’unduma kafin ya ce “Ina fatan baki manta yanda mu kayi da ke ba, to har yanzu ina nan Akan Baka na, k’wandala ta ba zata yi ciwon Kai a kan lamarin yarinyar nan ba, tunda ke ba abinda kika iya sai haihuwar y’ay’a mata.” Ya zabga tsaki ya fice ba tare da ya ko kalli y’ar ba, balle ya mata hu’duba. Wa’danda suka dubi Allah ne suka dinga zuwa mata barka a k’auyen, Innayo tana fama da kanta ba dama ta zo gidanta sai aike ta mata da gaisuwarta saboda itama tsohon ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe zata haifi k’anin ‘danta Jabiru.
Haka ta yi jegonta ga Majeedah y’ar shekara ‘daya da Rabi ga Zainabu jaririya. Ta sha matuk’ar wahala don Zainabu kam ko bunsurun ma bata samu ya
yanka mata ba, ita da kanta kuma ta ra’da mata suna Zainab.
Bayan sati guda da haihuwar Zainabu Innayo ta amsa kiran mahallicinta bayan doguwar nak’udar da tasha bata haife abinda yake cikinta ba. Sanda Talatu ta je dubata ta ja hannun Talatu ta ‘dora Akan na Jabiru ‘danta da Talatun ta ba shi shekaru biyu. “Na baki amanarsa Talatu, na San idan na mutu babu Mai kula da shi tunda kinga ubansa ba mazauni bane ba, Ki kula da shi don Allah Talatu.” Wani irin kuka ne ya kecewa Talatu, kukan da ake kira kuka mai tsananin cin rai ta dinga Jin duniyar tana juyi da ita, sanda ta tabbatar Itama Innayo ta amsa kiran mahaliccinta.
Bayan sadakar Uku kowa ya ce ba zai rik’e Jabiru ba tunda Akan idonsu Innayo ta bada amanarsa ga Talatu bata San da su ba, to Talatu ta je ta rik’e Jabiru sun bar mata. Haka Talatu ta ha’de Kayan Jabiru kaf ta tafi da shi gidanta. Tashin hankali ba Wanda ba su yi da Kabiru ba Akan Jabiru, ya ce sai ya bar masa gidansa. Ita kuwa bu’dar bakinta ta ce “In dai zaka kori Jabiru sai dai ka ha’da da ni.” Sak ya yi yana kallonta don duk bala’insa yana son Talatu don yana samun gamsuwa a wajenta fiye da kowace Mace da zai kusanta don haka ganin da gaske take sai ya ce “Shikkenan ki yi ta rik’e shi Amma ki tabbata kwabo na ba zai yi ciwon Kai a Kansa ba.” Talatu ta bi shi da kallo kamar ta ce masa dama mai kake tsinanawa yaranka ma balle Wanda ba naka ba? Sai dai ta ja bakinta ta yi shiru. Haka ta hak’ura ta ja Jabiru ta rik’e shi suke ta gwagwarmayar rayuwar tare.
Bayan wata uku da haihuwar Zainabu Kabiru ya tattara ya tafi ci rani birni, don a cewarsa ya gaji da zaman noma ya tafi Neman arzikinsa. Sai bayan tafiyarsa sannan Talatu ta fahimci tana da ciki.. hankalinta ya tashi sosai don ita kanta a wannan gab’ar bata so haihuwar ba, saboda kula da su Zainabu ma aiki ne ja a wajenta balle ga Kabiru ya tsallake ya tafi ya barta da kula da yara. Cikin ya zo mata da wani irin laulayi mai wahalar gaske. A wannan tsukun kuma Mahaifinta ya fa’di ya mutu duk y’an uwanta suka juya mata baya. Ta rasa gata ta kowane fanni sai Gatan Allah. Ga yara ga ciki da k’yar suke samun su ci abinci sau ‘d’aya a rana sau tari tuwo ne take tuk’a musu shi su kwana biyu suna cin sa kafin ta sake musu wani, sai kuwa koko da suke sha da safe shima don Jabiru yana zuwa taya aikin noma ne to idan za’a sallameshi sai ya ce ya fison a ba shi tsabar masarar da geron sai ya kawowa Talatu su ‘d’an kwana biyu suna ci. Ta gefe guda rik’on Jabiru sai ya zame mata alheri don ko bakomai yana taimaka mata kuma yana tayata wasu daga aiyukan gidanta, musamman sanda cikinta ya tsufa har a lokacin Kabiru bai waiwayi gida ba tsawon wata shidda har ta haifi y’arta ta uku da ta sakawa Aishatu bai waiwayesu ba sai da ta kusan arba’in sai ga shi yazo, abinda ya bata mamaki yarda ya zama Alhaji Kabiru lokaci guda ba kamar yarda ya tafi ba. Sakar baki ta yi tana kallonsa da tsananin mamakin canjawar tasa lokaci guda.
Ko ha’diyar yawu ya gagareta illa wani irin fa’duwar gaba da
Ya risketa lokaci guda.. tunaninta ‘daya wace Sana’a Kabirun yake da ya samu wannan sauyi lokaci guda… Fashi..?Yankan kai..?
Sune abubuwan da suka zo mata k’wak’walwa ta runtse idanunta tana fa’din Allah a’a Ubangiji kada ka k’addara masa Uban y’ay’ana ne ba zan so ya kasance daga cikin wa’dannan halayen ko ‘daya ba.
Cikin takaici Kabiru ya dinga harararta ganin yarda duk ta yagune ga wata y’ar a cinyarta da alamar wata haihuwar ta sake yi, shikkenan haihuwa zata kassara masa
Jikinta, jikin da yake samun Hutu a cikinsa, ji yarda Nonuwanta suka tamushe. Kasa b’oye furucin ya yi a cikin ransa ya fito da shi a fili yana yagune fuska ya ce “Wai yagwalgwal kenan haka kika dawo nonuwa a shafale kamar silifas.. ina ai lokacin k’ara aure na ya zo.” Idanunta kamar su zubar da hawaye ta ‘dago ta zubesu cikin nasa “Yanzu irin kallon da zaka min kenan Kabiru duk da da’dewar da muka yi bamu ha’duba?” “Wani kallo kike son na miki banda wannan ‘din? Kin saki jiki kina ta zuba haihuwa uwa tunkiya ‘dan kyan da kike da shi ma duk yara Sun tsotse ina ai mata suna birni Alaji ka gansu a cike fam suna juyi da k’yar ke kam ai kin tashi daga aiki kin dawo kamar tsohuwar mota rik’onki sai mai hak’uri.” Ya fa’da yana fa’dawa cikin ‘daki “Ki kawo min abinci kizo kuma ki gyara duk da sai na rufe ido na ina hango wa’dancan tsalatsalan y’an matan sannan zan iya biyan buk’ata ta dake.”
Wani abu mai ‘daci ne yazo ya tokare mata wuya da mak’oshinta, jikinta a salub’e ta shiga kitchen ragowar ‘dumame ta zubo masa da ruwan sha a kwanon sha. Yana cikin ‘dakin ya baje kan katifa gefe guda ga ki’dan garaya ya ware a radio yana rausayar da kai, daga shi sai gajeran wando ya nuna mata katifa fuska a murtuke ya ce “Gyara, kuma ki ‘daure wa’dannnan abubuwan naki masu kama da silifas bana son ganinsu, na Saba ganin tula-tula.”
Takaicin Uba….
Na Nazeefa Nashe
Pg 17
💔💔💔💔
Runtse idanunta ta yi cikin Jin zafin furucinsa da take ganinsa kamar cin fuska ne a wajenta, cin fuska mana idan ma ragwab’ewar tayi waye y’a janyo mata? Aikin wahala take yi don ta Tsira da mutuncin ta da na y’ay’anta babu cima mai kyau da zai gyara mata jikinta da fatarta, ba dole ta yamushe ba.. ta ma godewa Allah da ta Kai har haka bata yak’une ba. Ta ha’diye wani Abu mai ‘daci tana shirin juyawa ta fice, ya fincikota ya afka mata kamar yarda ya Saba.
Bayan ya gama gurzarta son ransa ya mik’e yana zabga tsaki har da tsartar da miyau ransa a b’ace ya ce “Aradu mata na birni, ya aka yi gabanki ya bu’de kamar k’ofar gari..” wannan