Showing 3001 words to 6000 words out of 132090 words
Chapter 2 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
suka dinga yi Amma ta sake zabga uban tagumi tana duban yaran nata ‘daya a zuciyarta tana godewa Allah da ya raya mata har suka zama wani abu a duniya kamar ba su bane a lokutan baya ta dinga wahala da su, abubuwa da dama suka dinga rincab’e mata. Da sauri ta runtse idanunta ba ta son tuna wancan bak’ar rayuwar don muninta ya girgimama. Dijah ce ta fara kawar da tunanin ta hanyar cewa “Mu mata addu’a Amma, ina tunanin lamarin Ayra sai addu’a Khairan In sha Allah ubangiji zai kawo wani da duk k’iyayyarta da aure sai ta aureshi in dai mijinta ne.”
Gaba ‘d’aya suka jinjina kai Amman ta fara korarsu ta hanyar cewa sai su tashi su tafi gidajensu tunda sun birkita mata y’a “Don sanda kuka sake zuwa kuma harzik’a min auta wallahi zaku sani.” Murmushi suke kawai suna mik’ewa ‘daya bayan ‘daya don dama yammaci ya kawo kai.
Takaicin Uba…..
Na
Nazeefah Sabo Nashe
08033748387.
3…
Littafin Takaicin Uba.. paid book ne, 500 ne kacal ga masu buk’atar karanta shi za su iya biyan ku’din su ta wannan account ‘din a saka su a paid group..2118666253 U B A.
Akwai kuma special people masu son a bisu har gida a tura musu privately ba ruwansu da hanyaniyar group, ko turo min inda aka wuce ni a kullum aka yi posting zan tura musu privately. Ku biya 1k kacal.
Sai masu turawa groups ‘din su ku kuma ku biyo ni gida mu yi ciniki. Kada ku manta littafin mai zafi ne fiye da ME ZAN YI DA ITA? Da YA ABIN YAKE?
Sai na jiku pages 12 ne kacal free pages.
—————————
Ko a wajen rakiyar da Amman ta musu, kashedin da Amman ta sake musu mai tsauri ne, don yau kam Ayra ta gigita tunaninta gani take a condition d’in da ta tarar da ita tsaf zata kashe kan nata. Ta sake jaddada kashedinta ga Zainab musamman kasancewar ta fi su tsaurara lamarin.
Zainab ajiyar zuciya kawai take saki don dai ita da za’a bi ta tata da Tuni Ayra ta dad’e a d’akin miji gani take duka zancen kisan da take rainin hankaline don ta ga suna biye mata ne. A tunaninta wancan kuskuren mahaifin nasu bai zama dalilin da zai rinjayi zuciyarta ta gicciyar da lamarin aure lokaci guda ba. Ta d’auke kanta bayan ta tabbatar wa da mahaifiyarsu ba zata sake tsoma baki game da lamarin Ayran ba sai dai tana rok’on Ubangiji ya ganar da su abinda ita tuni ta dad’e da ganewa. Bata wani jima a wajen ba ta ja tawagar yaranta ta bar gidan ranta a matuk’ar b’ace don idan ta zauna tabbas duk wanda ya takaleta zata iya sauke takaicinta a kansa.
Ko a mota mitar da take kenan sai da Babbar y’arta ta dinga tausar zuciyarta kafin ta samu ta lafa daga b’acin ran da take ciki.
___________
Da wani irin farin ciki ta tashi da safiyar kashegarin ranar da abin ya faru. Zuciyarta wasai ta tabbata a yanzu ko da ganganci babu mai sake mata maganar aure tunda Amma ta Riga ta gindaya sharad’i mai zafi game da lamarin auren. Ta sani sarai suna shakkar mahaifiyarsu ba sa son bijirowar b’acin ranta ko misk’ala zarratin.
A tsaye take a gaban mudubi tana sake cancad’awa fuskarta kyakykyawan make up. Da ya sake bayyana wani irin sihirtaccen kyanta ko ba ta yi kwalliya ba dama mai kyau ce balle ita ma’abociyar son kwalliya ce da duk wani k’yalek’yale. Eyelashes d’inta ta sake bi da mascara ta tusa musamman kasancewar su zara-zara kamar na kanti sai dai nata ne daga Indallahi (naturally). Kyakykyawan lips d’inta ta gogawa pink lipstick sai ya sake bayyana tsananin kyanta ta d’aura d’ankwalin black material da yake jikinta sai dai bai b’oye zara-Zaran gashin da suke kwance luf-luf a gaban goshinta ba. Ta d’an fesa turarenta mai matuk’ar k’amshi da tsada na kamfanin lulu. Sannan ta d’au gogaggen hijabinta bak’i sid’ik wanda ya zame mata gado ta ratayashi da nik’ab da hand bag d’inta ta fice Falon gidan.
Kamar kowace safiya gidan an gyarashi tsaf da taimakonta da na mai aikinsu sai baza k’amshin turaren sandal wood yake mai asalin k’amshi. Saman Dinning ta zauna tana had’a coffee ga al’adarta duk safiya sai ta sha coffee kafin ta ci komai, musamman kasancewrta ma’abociyar k’in abinci tsakaninta da abinci akwai gaba mai girman gaske. Ta zari salted biscuit guda biyu ta fara sha da coffee d’in.
Amma ta bi hannunta da kallo “Yau ba zaki ci ko chips d’in ba, sarkin k’in cin abinci.” Girgiza kai ta yi tana cuno bakinta “Wallahi Ammaty yau Abincin nan ba zai samu shiga ba, wannan ma is okey idan na ci abincin ba zan iya hassala komai a office ba, kuma ina da aiki mai tarin yawa.” Amma ta girgiza kai “Madalla da Agogo sarkin aiki shi yasa ga ki nan kullum jiya I yau.” Mik’ewa ta yi tana tuntsira dariya cikin farin ciki ta rungumi Amman kafin ta zura hijab d’inta da nik’ab ta kuma zurmuk’a hannayenta a aljihu ta sake rungumar Amman murya k’asa ta ce “Amma yau may be zan iya kaiwa past 4:00 saboda muna da meeting.” Amma ta matsa hannayenta tana murzasu kad’an-kad’an cikin kulawa ta ce “Allah ya yiwa nemanki albarka Auta. Ya tabbatar min da ke kan tafarkin sirad’il mustak’eema.” Feck ta bata a kumatu ta fice da d’an hanzari ganin 7;30 tuni ta wuce Amma ta sake Binta da wasu addu’oin a zuciyarta “Ubangiji ya yaye miki wancan tunanin a zuciyarki, ya kawo miki mijin aure na gari da zaki goge tabon k’iyayyar maza a zuciyarki, har ki furta da kanki wata rana MAZAN SUNA SUKA TARA.” Irin Addu’oin da Amman take Bin ta da su kullum kenan a cikin sallolinta guda biyar. Ta tabbatar kuma Allah yana jinta abubuwan duka za su wuce da ikon Rabbi sai dai jinkiri. Kowanene Mijin Ayra? Shine tambayar da kullum takewa kanta take kuma burin ganin Mijin Ayran kafin a kaita kushewa.
________________________
A zaune akan dakalin k’ofar gidan nasa ya zuba hannayensa a k’unci cikin zuzzurfan tunani. Kana ganinsa ka ga wanda talauci ya yiwa dabaibayi. Ba shi da sukuni ko kad’an kullum kuma a cikin halin da yake kasancewa kenan.
Amininsa na kullum ya iso wajen hannunsa rik’e da ledar da take d’auke da k’osai da kunu. Kamar kowace safiya nan yake biyo wa su ci da abokin nasa. Ya zauna daf da shi yana kai hannu kan kafad’arsa kasancewar duk sallamar da ya masa bai ji ba dalilin zuzzurfan tunanin da ya afka. A razane ya d’an jiyo duk da ya san shine don shi kad’ai ne mutumin da yake mu’amalantarsa dalilin rashi da ya fad’a kowa ya daina kula shi, sab’anin sanda ya ke da ku’di kuwa shine na kowa har fadanci ake masa. Malam Hadi ya ja tsaki yana kallo cikin idanun abokin nasa kafin ya ce “Wallahi idan ba kayi wasa ba Tunani zai bugar maka da zuciya. Kullum fa a yanayin da kake kenan, kana da hanyar yayewa kanka duk matsalolinka amma ka zauna talauci ya maka dabaibayi bayan a y’ay’anka har da matar Minister matar d’an majalisa matar gwamanan banki ka zauna talauci zai kasheka.” Alh. Kabiru ya girgiza kai kafin ya ja wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya cire hularsa furfurar kansa gaba d’aya ta bayyana alamar yana cikin wahala “Wallahi Hadi ba zan iya ba, ba zan iya ido hud’u da talatu ba shin da wani ido kake son na kalli su kansu yaran nawa balle Talatu na tabbata a duniya a yanzu ba wanda suka tsana sama da ni.” Mai. Hadi ya ja tsaki kafin ya bud’e takardar k’osan da za su ci shima ba don komai yake wannan hak’ilon da Amininsa ba yake ciyar da shi kullum sai don ya san tabbas nan gaba kad’an zai fanshe wahalarsa a duk lokacin da Amininsa ya daidaita da y’ay’annasa duk da ya san abin da kamar wuya, don tab’argazar da Amininnasa ya aikata girmanta ya yi shaharar da ba za su yafe masa nan kwana kusa ba, idan ma za su yafe masa ‘din kenan, bai k’i ba ko idan suka gan shi a gadon sharafa yana shirin tafiya kushewa amma ai bai bari sun gwada ko sau d’aya su ga ko za’a dace ba.Don haka yana cilla k’osai a bakinsa ya ce “Ka bari mu gwada ni zan je da wani a cikin danginka a gaya musu halin da kake ciki ai ba kai zaka je ba.” Alh. Kabiru ya ja ajiyar zuciya kafin ya ce “Ina jiye muku tsoron sauke muku kwandon wulak’ancin da suka yi niyyar sauke min.” “Sai me? Daga wulak’ancin in dai za su amince su dinga baka Naira waye bai san arzikin da suka yi ba? Amma su ko tunaninka ba sa yi kamar ba kai ka haifesu ba.” Ya girgiza kai “Na yi musu abinda ban cancanci afuwa ba, a haka ma gode musu nake da lamarin bai kai mu ga kotu ba, tunda ka nace sai ka je shikkenan na baka dama ka gwada zuwa amma fa duk abinda ya biyo baya kada ka yi kuka da ni ka yi kuka da kanka.” Mal. Hadi ya girgiza kai cikin farin ciki ya ce “Ko kai fa ba mamaki ma kai kake abinka su tuni sun manta wallahi.”
Alh. Kabiru ya zaro ido cike da tabbatarwa ya ce “Wallahi ba su manta ba ai abin ba abin a manta ba ne.” Malam Hadi ya girgiza kai “Ai shikkenan kada su manta d’in ka bar ni da su, idan an bi da su ta ruwan sanyi suka k’i ba da had’in kai dole a bi da su ta yarda shari’a ta ce, yara dai naka ne ko jikinku a ka tsaga tilas a ga jininku d’aya da su don haka tilas ba’a canjawa tuwo suna a cikin satin nan zan je har gidan ayi wacce za’a yi.” Alh. Kabiru shiru ya yi idanunsa a k’asa tunani ya rinjayar da hasken annurin da yake fuskarsa, fuskar tuni ta bak’unci wani irin yanayi da tarin dana sani da nadama gami da kaico su suka wanzu a fuskarsa. Hawayen da ya saba zubar wa suka shiga ambaliya a fuskarsa. Da gaske lamarin yana masa ciwo yana ji da yana da iko da ya dawo da rayuwar baya ya gyara tarin kuskurensa, shi da kansa ya Riga ya san ya dasa tsanarsa a zuciyar yaransa da ma duk wani da yake kusa da shi. Ashe da gaske lokacin zai zo da zai yi bak’in cikin wancan fentin da ya goga wa kansa tamkar yarda mahaifinsa ya gaya masa tun yana raye. Cikin wata karyayyiyar murya da take rawa ya ce “KAICONA NI KABIRU ni da kaina na yi Allah wadarai da halayena da suka gabata Astagfirullah Ya Allah.” Ya saka hannu ya d’auke k’wallar da take idanunsa yana dafa hannayen amininsa murya cike da sanyi ya ce “Ka taimaka min Hadi don girman Allah ka shawo min kan su, ko da ba za su dinga min komai ba ni ba wannan bane burina, burina su yafe min su kuma amince su karb’eni a matsayin mahaifi ina tabbatar maka yarda nake jin yarda zuciyata ke ciwo tabbas ta kusa bugawa na mutu. Dukiyarsu bata gabana amincinsu kawai nake nema.” Wani kallo Hadi yake masa a zuciyarsa yana tunanin rashin hankalin abokin nasa, bai San wace irin dukiya ce da yaran nasa ba shi yasa yake fad’in haka. Kamfani ne da su Guda na kayan gine-gine da duk Nigeria da mak’waftanta ba wanda bai san kamfanin ba saboda bunk’asar sa (Talatu furnitures and construction company) Amma ji zancen da yake wai shi ba don arzikin su zai shirya su ba, ai kuwa shi ba za’a yi wannan k’aryar da shi ba shi don arzikinsu zai daidaita su don ya san tabbas shima zai dandali arzikin. Amma don kada ya nuna zalamarsa sai kawai ya girgiza kai yana tabbatar masa zai yi iya bakin k’ok’arin sa.
______
Tunda Ayran ta tafi aiki. Amma Talatu ta mik’e alwalarta tayi don gabatar da sallolinta na walaha kamar yarda ta saba. Tana idar wa ta kishingi’da tunani ta fara yi game da Ayran da yarda take so ta yakice aure daga rayuwar ta, tabbas ba taga laifinta ba don idan ka ji tarihinsu na baya hakan da Ayran ta yi shine daidai dole ta tsani maza ta kuma jinginasu ga ma’auni ‘daya ba kowa kuma ya janyo hakan ba sai mahaifinta, da ya cusa mata k’iyayyar maza tun tana y’ar ficilarta da hakan ta tashi a ranta. Talatu ta runtse idanunta sai ga wasu irin tarin hawaye suna kwaranya daga idanunta masu k’una da zafin gaske..
Ta dinga cizar lab’banta tana fa’din Namiji ! Namiji!! Allah dai ya kyauta amma tun farkon rayuwarta ita kanta uwar Ayran da Takaicin ‘da namiji ta tashi Ya ilahi take ta furtawa a ranta saboda yarda zuciyarta take zuba luguden daka…
TAKAICIN UBA…
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
https://arewabooks.com/book?id=6455383e1c910f5cf9785c27
(Kada fa ki bari a yi tafiyar nan ba ke! Takaicin Uba yanzu aka fara wani irin mur’dadden labari ne mai sanya tausayi takaici ga uwa ba tsantsar k’iyayyar da take juyewa ta koma makauniyar soyayya. Kun sani sarai bana kawo muku labaran banza.
Za’a sha dariya, Za’a goge hawaye duka a cikin labarin.
Zai zo muku Akan 500 kacal.
Sai special people manyan matan nan masu aji da ba sa son hayaniyar group, suna kan kujerar su za’a tura musu har cikin wayarsu ba ruwansu da an tsere min turo min. Za su biya 1k kacal duk da Naga Akwai Hajiyoyin gimbiyoyin mazajensu da suke tura min yafi haka. Tabbas gaisuwar ku daban ce.. samba’do ku’dinki ta wannan account ‘din 2118666253 U BA..
Y’ar mutan makwarari ke cewa Marhababikum Lale Lale ana uhibbukum billah 😊😊😊❤️
4_____________
Da walwala sosai a fuskarta take duban sakatariyar tata duk da bata ganin fuskarta amma a muryar shugabar tata ta fahimci tarin farin cikin labarin da ta zo mata da shi, na zuwan bak’uwar da ta dad’e tana tsimayin zuwanta. Aminiyartace sosai da karatu ya farrak’a su shekarun da suka wuce ita ta koma rayuwar egypt saboda admission da ta samu a can, yanzu ma hutu ta zo don ta samu aikin koyarwa a can egypt d’in.
Tunda ta mata waya zata zo take cikin murna da zakwad’i da son ganin aminyar tata Saboda tsawon lokacin da ta d’auka bata ganta ba.
Saleemah Sa’ad ta shigo cikin wata irin k’Saitacciyar shiga, fuskarta d’auke da matsanancin murmushi tana bin office d’in AYRA GAYA da kallo. Shigar da take jikin Ayran ce ta sa ta ware ido tana kallonta so take ta ga fuskar Ayran da nik’abi ya mata shamaki. Da hanzari Ayran ta tuje nik’abin fuskarta ganin sakatariyar ta ta ta fita cikin farin ciki da murna ta isa wajen Saleema ta kai mata kyakykyawar runguma. Salima ma murmushi take tana sake duban Ayran da ta k’ara wani irin fitinannen kyau fatarta sai kace glass don taushi da sulb’i. Sai dai yanayin shigarta ya bawa Salima mamaki. Ayra dai Ayra da ta sani y’ar gayu mai yawan saka English wears sanda suna secondary school ita ce sanye da wannan shigar me ya faru? Me ya mayar mata da Ayra haka? Bata yarda ta zauna ba har sai da ta cillawa Ayran tambaya “Malama yaushe kika yi aure ban sani ba? Kuma wani rik’akken Malamin kika aura da ya mayar da ke haka?”
Ayra ta saki murmushi tana jan hannun Salima,suka zauna a kan katafariyar kujerar mai taushin gaske da take can gefen office d’in. “Questioneer Allah ya dawo min da ke, ban yi aure ba Allah Kuma Kada ya k’addara min aure a rayuwata, ba na fatansa ko misk’ala zarratin daga yau kuma bana son naji kin sake danganta ni da kalmar matar aure please and please.” Ta fad’a tana had’e hannayenta waje d’aya alamar rok’o. Wani irin kallo galala Saliman take mata na tsananin mamaki da takaicin Ayran, ashe har yanzu wancan bahagon tunanin yana nan a zuciyarta babu abinda ya canja sai ma dad’a bun k’asa da lamarin ya yi. Tun suna yara ta sha fad’ar haka sai dai sam suna d’aukan abin shirme a
Kullum kuma suka tambayeta dalili sai dai ta yi murmushi ta runtse ido tana rawar murya zata ce “Dalilina mai k’arfi ne kuma gamsashshe amma babu buk’atar ku ji shi.” Daga haka zata goge k’wallar idanunta a kuma tsayin ranar ba zaka sake
Ganin walwala tattare da ita ba, wannan dalili ya saka Saliman sam bata cika damunta da tambayar son sanin mak’asudin k’iyayyarta da aure ba.
Yanzun ma jan ajiyar zuciya ta yi kafin ta ce “Allah ya kyauta, ni kuwa yanzu shirin auren ne ya dawo da ni Nigeria na ga kuma ba wacce ya kamata ta shige min hidimar bikina idan ba ke ba. Tunda duk k’awayen namu sun yi aure daga ni sai ke ne dama mu ka yi jinkiri.”
Tuni duk wata walwala da take fuskar Ayra ta Kau, murya a shak’e ta hau girgiza kai had’e da fad’in “Idan kin amince mai zumbulelen hijabi da nik’abi ta ja ragamar bikin ki sai na ce you are welcome.” Kallon cikin ido Salima take mata kafin ta ce “As how Malama? Kada dai ki ce min duk in da za ki da wannan shigar ki ke zuwa?” Ta girgiza kai cike da tabbatar mata “Bayan ku na kusa da ni da muka yi secondary tare ba wanda ya san kamannin Ayra Gaya ko mutanen da muka yi jami’a tare tsirari ne suka sanni, bari na sanar miki k’arshe mutanen companyn nan ba su san zahirin kamanni na ba, da wannan shigar suka sanni na ci sa’a companyn na mu ne ba wanda zai takura min akan shigata. Ko yanzu ba ki ga sai da ta fita sannan na bud’e miki fuskata ba?” Saliman ta sake dubanta tana mamaki da al’ajabi da wani ne da kyan Ayra cike da fariya zai dinga nuna shi amma ita kyan ne ma bata son a dinga gani ta ‘dan jijjiga kai kafin ta ce “Kada dai ki ce min duk don kada ki samu miji ki ke aikata haka?” Ayra ta d’aga kai tana sakin murmushi “Ko