Showing 123001 words to 126000 words out of 132090 words
Chapter 42 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
shiga rattabowa maimartaba duk irin halin da Kabiru yake ciki ya kuma bawa Maimartaban labarin abubuwan da suka faru da. Ran mai martaba ya b’aci sosai da jin wannan labari da ya kira da bak’in labari fuskarsa a ‘daure tamau yana duban Kamilu ya ce “A haka kake son kuma su yafe masa? Bayan wannan tozarcin da ka zayyano ya musu?” Kamilu ya rausayar da kansa ya ce “Ba don halinsa ba za su yafe masa ba, sai don suma su sauke hakkinsa da yake kansu kamar yarda Ubangiji ya musu umarni idan banda haka Kabiru bai cancanci yafiya ba.” Maimartaba ya yi tsam da ransa yana jin zuciyarsa tana tafasa ya kalli Kamilu ya ce “A gobe nake son ganin Kabiru a gabana, zan nuna masa dangin Talatu zan kuma ‘daura mata aure da mutum mai nagarta mai arziki a gabansa zan nuna masa gidan da Talatu zata je ta yi aure ta huta sannan idan ma yafiyar zata biyo baya sai su yafe masa tunda a yanzu sun masa fintinkau Allah kuma ya nuna masa isahara. Ashe har yanzu Akwai masu halin dabbobi irin Kabiru? Tabbas ban da darajar yara sai na saka an kulle shi sai dai yanzu ma bai tsira ba don abinda zan masa sai ya gwammace d’aurin rai da rai. Zan bada motoci a ‘d’aukoshi da abokin nasa, a kuma ‘dauko jama’ar garin ko da su ashirin ne su gani su shaida Talatu ba matsiyaci ya bace da gatanta.”
Ba wanda ya yi magana ganin yarda ran maimartaba ya kai k’ololuwar b’aci, bai kuma sake bi ta kan Talatu ba don ya shirya aurar da ita da sonta ko babu. Burinsa yanzu ya inganta rayuwarta ta samu duk gatan da ta rasa a lokutan baya.
Nan da nan Maimartaba ya saka aka ha’da manyan motoci don tafiya k’auyen Shagogo. Waziri kuwa jin wannan labarin bai saka ya ji son auren Talatun ya fita daga ransa ba, sai ma wata tarin k’aunarta da ya ji ta sake shiga ransa don a rayuwarsa burinsa ya auri Mace mai hak’uri sab’anin nasa matan guda uku da suka zama duk marasa hak’uri. Ya sake daidaita zamansa a kan kujerar da take fuskantar Talatun a parlourn Maimartaba. Murya cike da nutsuwa da dattijantaka ya ce “Ki amince da aure na Talatu ba za ki yi nadama ba, na yi alk’awarin baki farin cikin da kika rasa a baya zan nuna miki aure suna ya tara zan ‘daga darajarki in baki kulawa ta musamman matsalolin yaranki za su zama nawa zan kuma basu kulawa kamar yarda Zan bawa yaran cikina.” Talatu ta yi shiru tana wasa da zoben hannunta haka kawai sai ta ji tana kunyar fuskantar mutumin kwarjininsa da kyawun kamalarsa yana sake rikitata ainun, ga wani irin fa’duwar gaba da take ji a duk sanda ta ji sautin muryarsa abinda bata saba ji ba idan tana tare da Kabiru “Kin amince?” Ya fa’da a hankali yana rankwafowa yana kallo fuskarsa. Talatu ta kawar da kai tana sakin murmushi a hankali ta ‘d’aga kanta. Waziri ya furta “Alhamdulillah yana sakin ajiyar zuciya, burinsa zai cika na samun kammalalliyar mace mai tarin nutsuwa da kamala kamar yarda ya da’de yana fata. “Allah ya yi albarka a aurenmu yasa ace gwara da aka yi.” Talatu ta amsa a zuciyarta sai kunyarta ta sake burgesa don ya na cikin kammaluwar mutuncin y’a mace ta zamo mai kunya. Da zai tafi sai da ya ajiye mata ku’di dollars ‘din America Talatu ta amsa hannu bibbiyu don da kunya ta ce ya bar shi. Waziri ya sake jin kansa a sama don abu ne da bai saba gani ba matansa ba sa saka hannu bibbiyu idan zai ba su abu. Ya saki murmushi kawai yana jin kamar ya janyo Talatun ya rungumeta ya fita daga parlourn a zuciyarsa yana furta “Na ji a jikina yanzu zan yi aure”
Talatu ta shiga cikin gida haka kawai sai ta samu kanta a cikin tarin farin ciki da walwala. Musamman da ta sake ganin fuskokin yaranta suma cike da walwala. Ta zauna a cikinsu Ummeey tana waya da tailor a kan ya kawo mata rantsatstsen lace da ya amsa sunansa lace kuma ready made take so. Tana kashewa ta sake janyo waya ta kira mai gyaran jiki. Da sauri Talatu ta kalleta “Haba Hameeda sai kace wasu yara?” Ummeey ta Zuba mata harara “Sai kin tashi tsaye matansa da kike gani kilallune idanunsu a bu’de yake taryau, sai an yi miki gyaran jiki na sati biyu don haka ba yanzu ma za ki tare ba sai mun gama shirin mu.” Talatu ta zuba mata harara tana nuna mata yara. Ummeey sai ta saki murmushi kawai tana fa’din “To bari za mu saka labulai.”
Lokacin Turaki ya shigo shi da Ayra da take sunnewa a bayansa. Ba wanda ya mata magana hakan yasa ta ‘dan saki jiki bayan sun gaishesu ta ‘dago tana kallon Deejah ta ce “Wai murnar me kuke ne? Na ga kuna ta dariya.” “Gobe Amma zata yi aure da wazirin Gombe.” Cak numfashin Ayra ya tsaya ta kafawa Deejah ido cikin b’acin rai ta ce “Ban gane ba, Auren lafiya? Gaskiya a’a…..”
𝔍𝖎𝖐𝖆𝖗 𝖓𝖆𝖘𝖍𝖊✍️
Takaicin Uba….
Nazeefah Nashe✍🏽
Saura k’iris☺️
Gaba ‘d’aya wajen suka zubo mata ido, cikin jin mamakin furucin da ya fito daga bakinta. Majeeda ta wurga mata harara ha’de da fa’din “Ban gane a’a ba Malama, Auren ne ba zata yi ba ko me?” Ayra ta sake zumb’ura bakinta kafin ta isa kusa da Amman ta rusuna a gabanta tana dafa cinyoyinta ta ce “Ki ce min ba haka bane Amma, don Allah kada ki yarda da wani aure a yanzu da shekarunki suka riga suka ja, ba zan jure ganin namiji na wulak’anta ki ba kamar yarda Babanmu ya wulak’anta ki.” Wannan karan Zainab ce ta fusata a zafafe ta ce “Sannu uwarta, waye ma ya gaya miki duka maza sunansu ‘daya Ai yanzu da kika yi auren kin fahimci na ki mijin sab’anin halayen Uban mu ne da shi, don haka aure fa kamar ta yi ta gama tunda har aka samu mai sonta duk da tsufan nata, ke ki ke ganin ma ta tsufa shi gal yake ganinta.” Ayra ta sake gyara zama a jikin Amman wannan karan sosai idanunta suke zubar da k’walla gaba ‘d’aya Turaki ya ji zuciyarsa ta cunkushe ganin yarda kowa ya taso mata ya dinga jifansu da wani irin kallo a zafafe sai dai su ba su san ma yana yi ba. Sai ganinsa kawai suka yi a gaban Ayra yana mik’a mata Handky murya a cunkushe ya kalli Zainab ya ce “Kowa ya fa’di ra’ayinsa Ai itama sai ku barta ta fa’di nata dalilin Ban ga dalilin wannan hayaniyar ba.” Zuba masa ido suka yi har Ummeey da ya kusan bata dariya ganin yarda ya ha’de rai kamar ba da surikansa yake magana ba. Jin Ayran ba zata yi shiru ba yasa shi jan ‘dan k’aramin tsaki ya saka kai ya fice daga parlourn. Amma murmushi ta yi wani farin ciki yana ‘darsuwa a zuciyarta ta san ko yanzu burinta ya cika Ayranta ta samu Miji irin wanda ta da’de tana mata fatan samu. Mijin da ake kira ‘d’aya tamkar da dubu. Mijin da zai kula da lamarinka ya kuma baka farin ciki ko a gaban waye. Ummeey ce ta dafa Ayran murya can k’asa ta ce “Tashi daughter tashi rabu da su mu yi magana.” Ayra ta koma jikin Ummeeyn tana cigaba da hawaye gaba ‘d’aya zuciyarta ta jagule bata son wani zancen auren Ammanta. Mu je ‘daki saboda y’an saka ido” Ummeey ta fa’da tana jan hannun Ayran suka tafi ‘dakinta. A gefen gado ta zaunar da ita murya a tausashe ta ce “Kina son damuwa da ka’dai ci su saka Amma ta samu ciwon zuciya?” Ayra ta girgiza kai “Yauwa, to ki k’yaleta ta yi aurenta, don a yanzu mai ‘debe mata kewa take nema, mai saka ta nisha’di saboda ta doshi shekaru 45 idan ba ta yi aure ba zata iya shiga damuwa kuma wancan tabon da Kabiru ya yiwa zuciyarta ba zai goge ba, Baba Waziri kuwa na tabbata zai bata dukkan kulawa ya saka mata farin ciki a zuciyarta walwalar ta zata dawo zata ji da’din da ta rasa a shekarun baya, k’warin gwiwa za ku bata ba ki sagar mata da gwiwa ba. Kin ga ba ke a kusa ba kowa damuwa zata mata yawa ga yanayin ciwonta ba’a son ta shiga damuwa auren Baba Waziri kuwa zai saka ta manta da waccan bak’ar rayuwar kin gane?” Ayra ta ‘d’aga kai tana sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya duk wani kulli da b’acin rai na zuciyarta ya silale ya bi iska, Ummeey ta bata courage da gasken gaske ta ji ta samu nutsuwa ta kuma fahimci cewa tabbas auren shine abinda ya dace da Amman yanzu. Ummeey ta saki murmushi tana jan kumatunta ta ce “Kin amince yanzu?” Ayra ta ‘d’aga kai tana murmushi “Good girl, kada ki sake nuna mata damuwa kin ji?” Ayra ta sake sakin murmushi tana fa’din “In sha Allah.” “Yauwa amaryar Turaki mu je ki cire mata shakku ta gane kin amince da auren na san zata ji da’di yanzu kuwa Kuka Ki ya saka ta samu rauni.” Suka mik’e tare hannunta cikin na Ummeey suka nufi falon fuskar Ayra ‘dauke da murmushi ta fa’da jikin Amma tana fa’din “Ammata Am happy for you, Allah yasa auren Baba Waziri ya zame mana alheri.” Amma ta saki ajiyar zuciya tana jin damuwarta ta kau, da kam zuciyarta ta ji ba da’di duk da ta yi na’am da auren sai dai idan har Ayra bata amince ba itama Zata turesa gefe yanzu kuwa sai ta ji ta samu sukunin zuciya ta rungume Ayra tana fa’din “In sha Allah Autata.” “A’a fa ki canja Auta wannan ba autar Ki ba ce ga Tayseer nan na bar miki Ayra autata tace” Ummeey ta fa’da tana dariya shikkenan aka cigaba da zancen auren Amma da y’ar walimar da za’a ha’da mata ranar da zata tare. Turaki dai tunda ya lek’o ya ga Ayra ta saki jiki sai ya ji hankalinsa ya kwanta ya fita k’arasa ragowar harkokinsa don so yake a jibi ya tafi turkey kafin ya dawo ya sake tafiya da Ayra.
______________
Lamarin Allah da girma yake kuma kowa ya ja da girman Ubangiji ya yi asara. A ranar juma’ar da za’a d’aura auren Motocin da suke d’auke da ahalin Kabiru suka iso daga garin Shagogo. Tunda suka shigo fadar gaban Kabiru yake fa’duwa bai san me Suka zo yi ba tunda Kamilun bai gaya musu ba sai dai gaba ‘daya jikin sa a sanyaye yake. Matarsa Mai da’din na gefensa sai cika take tana batsewa ‘d’aya daga cikin yaransa maza su takwas shine ya yi k’ok’arin biyosu don shine mai ‘dan dama-dama a cikinsu yake ‘dan kula da Kabirun wani Sa’in. Sai sauran ahalin gari ciki kuwa har da Maigari da shima tsufa ya kama sa da k’yar ma yake tafiya sai yayyen Talatu da suka ha’da Uba ‘daya. Jabiru ma ranar ya diro garin don Amman ta gaya masa maganar auren ta waya. Sai dai bai iso fadar ba so yake sai gaf da ‘daurin auren ya yiwa su Kabiru shigar bazata ya ga da wani idon Kabirun zai kallesa.
Fada fa ya cika mak’il da Sarki ya bada sanarwar a yi shela akwai ‘daurin auren Wazirin Gombe da za’a yi bayan sai kowa daga masallachi.
Amma suna cikin gida ta sha Ubansu lace an kuma na’deta da laffaya da ta sha gabbasa sai zabga k’amshi take. Fuskarta ta sake kyau sosai sam ba zaka ce ita ce ta zubo yaran nan mata da jikoki reras ba, ko don auren wuri aka mata sannan tana da k’aramin jiki irin na fulani. Fatarta ta sake murjewa ko don ta fara gyaran jiki ne. Su Ayra ma gaba d’aya sun sake kwalliyarsu cikin rantsatstsen lace da ya mata kyau sosai. Tun a jiya Kuma ta gujewa Turaki don ba k’aramin Gurzuwa ta yi a hannunsa ba ranar. Tun yana aikowa a kirata har ya zo da kansa Amma Ayra ta yi k’ememe da gaske har lokacin bata saba ba tsoron Turakin take ji don ta lura ba sanya a lamarin sa. Yanzu ma tsaf ya shigo cikin farin yadin filtex babbar rigar a hannunsa bai saka ba sai zabga k’amshin turare yake ya shiga parlourn Ummeeyn inda duk suke zazzaune idanunsa a kan Ayran da ta masa wani fitinannen kyau har bai san sanda ya shagala da kallonta ba sai da Ummeey ta yi gyaran murya sannan da sauri ya ‘dauke kai yana ‘dan sosa k’eya ya maze yana fa’din “Ayra zo mana 2 minutes.” Ayra ta ‘dago da sauri tana kallonsa ya ‘d’aga mata gira ‘d’aya abinda ya zame masa jiki sannan ya juya abinsa yana fa’din “Yi sauri ana jira na sak’o zan ba ki.” Ayra na jin haka ta mik’e a hankali tana sake yafa gyalenta don kayan ba k’aramin cikata suka yi ba har mamakin kayan ta yi da alama k’iba ta k’ara don sanda aka ‘dinka lace ‘din duk da fitted gown ne bai matseta haka ba. Ta bi bayansa cikin jin kunya duk da ba wanda ya lura da abinda take. Bata gansa ba a babban parlourn tana juya ta jita a jikinsa ya mata wata kyakykyawar runguma yana fa’din “Na kama mai gudun Miji.” Da sauri Ayra ta bu’de ido tana k’ok’arin janye jikinta ya sake rungumeta tsam a jikinsa “Bari mana, kin san irin wahalar da kika ba ni daga jiya zuwa yau.” Ya fa’da mata cikin ra’da a kunnenta Ayra idanu ta ware ganin yarda ya kama lips ‘dinta yana tsotsa. Tsawon lokaci kafin ta ji ya ‘dagata cak ya yi b’angarensa da ita “Ka bari kada wani ya gan mu.” “And so what? Haramun na yi?” Ya fa’da yana kaiwa karan hancinta sun bata “Mu je ki yi biyan bashin da kika ci jiya.” Ya fa’da yana tura k’ofar ‘dakinsa da k’afa sannan ya direta yana bin ta da kallo yarda rigar ta fitar da duk wata sura ta jikinta tuni wani kishi ya zo ya tsaya masa a zuciya a hankali ya ce “Bala’i, hope ba wani k’aton da ya gan ki a haka?” Ayra ta dubi jikinta a kunyace tana girgiza kai ganin yarda yake bin jikinta da kallo kafin ya saka hannunsa ya kai in da yake Tsole masa ido “Da kin cuceni idan aka ce wani banzan ya ga wa’dannan kayan nawa. Kada ki sake saka irin wannan kayan in dai ba daga ni sai ke ba.” Ya ja hannunta suka isa gaban mudubi yana fa’din “Kalli kan ki ki ga irin surar da Allah ya ba ki ba namijin da zai gan ki ya kasa raya wani abu a zuciyarsa don haka Blacks Hijabs d’in da kika saba sakawa su za ki cigaba da sakawa nik’abs and socks don zan iya aikata komai akan wanda ya yaba min surar jikin ki.” Ayra dai Shiru ta yi tana jinsa ya sake janta jikinsa yana budirinsa shi ka’dai tun tana iya jurewa har ta gaza jikinta ya soma rawa ba shiri Turaki ya ‘daga cak zuwa kan gado…….
Yana busar mata da kai bayan fitowar su daga wanka ya kalleta yana fa’din “Ma sha Allah Matata mai kyauce In and out, fa’da min menene sirrin?” Ayra ta saki murmushi har hab’arta tana lotsawa ta ce “Ba wani sirri, ka yi sauri ka tafi kada ka makara ‘daurin Aure.” Ya janye jikinsa yana fa’din “Ina zuwa.” Waya ya ‘d’auka ya kira Tayseer yana gimtse muryarsa ya ce “Ki samo wa Ayra wasu kayan, ki ha’do da Black Hijab d’inta da nik’ab.” Ayra ta Zuba masa ido “Me Zan Yi da Hijab kuma yau?” “Abinda kike yi da shi da, ai ni yanzu na san amfaninsu ban da su na tabbata da maza ba zasu barki ba idan ba su dinga bin ki suna miki fya’de ba, oh ni Aminu da an cuce ni.” Ya fa’da yana rik’e hab’a Ayra bata san sanda ta shiga tuntsira dariya ba ganin yarda yake kwaikwayar mata shima murmushin ya saki ya ce “Zan yi missing ‘din ki gobe zan wuce turkey zan dawo idan An gama tariyar Amma sai ki musu sallama ke da su kuma sai Baba ta gani ba mamaki sai kin haihu. Yanzu ni matsalata ya zan yi da tarin sha’awarki?” Ayra da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannunta ya dafa kafa’dar ta yana rankwafawa wuyanta ya ce “Am serious kin Riga kin shayar dani wata irin zuma mai da’din da ba kwatance sai dai a yi kurum kawai ga visar ki ta turkey bata kammala ba, ga shi ina da tarin ayyuka a can. Ni dai Aminu na ga ta kaina Wallahi na jangalowa kai na.” Ya fa’da yana goga kumatunsa a nata. Ayra ta lumshe ido tana jin itama tun a yanzu ta fara kewarsa ga shi zuciyarta ta kasa yarda akan cewa ba su rabu da Shaheedah ba, don haka cikin raunin zuciya ta ce “Ba ga Shaheedah ba sai ka aureta kawai.”
Ya bita da kallo yana mik’ar da ita tsaye ya ce “Shaheedo ba Shaheedah ba ba ki yarda da alk’awarin da na miki na ba ke ba kishiya ba ko? Ko kin zata duk a cikin giyar jin da’di na yi furucin to it’s true from the buttom of my heart ke ce Uwargida kuma amaryar Aminu da ga ke ba k’ari idan da wata ma ta narke.” Wani farin ciki ya kamata har bata san sanda ta kankameshi ba tana ba shi wani irin tattausan kiss leb’ensa Turaki ya lumshe ido yana jin wani farin ciki na ratsa sassan jikinsa tunda yake aurensa bai tab’a karo da mai zazzak’a tattausan lab’ba kamar Ayra y’ar mutanen Gaya ba. Ayra ta zare leb’en tana d’auke idonta ganin yarda Turakin ya lumshe ido ya rik’o hannunta murya a sark’afe ya ce “I need more….” Da sauri Ayra ta ja jikinta tana jan towel ‘don da yake son zamewa ta ce “Ana knocking.” Turaki ya kasa