Showing 27001 words to 30000 words out of 119425 words
Chapter 10 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
Shin ina iya kulu da Abu?????
Akafa
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*SORRY MY FAN'S NAYI MANTUWA BANSA NUMBER A PAGE DIN DA NAYI BA♀️PAGE 23
NE WANCEN KUYI MAN UZURI KUNSAN RAI AJIZI*
*PAGE TWENTY FOUR*
**********************
Iya kulu dai ana cen tsohon kangon gidansu, kasancewar babanta ya dad'e da rasuwa, matar
babanta ce a gidan zaune da yaranta, aiko wulakancin da take sha a gidan ba d'an kad'an ba
ne, domin kuwa k'annenta samari da masu auren ma a gidan, duk sun rena ta, saboda
haushinta da sukeji, musamman wulak'ancin da tayi masu, a lokacin da sukaje bikin mama
hassatu da malam, tayi masu rashin mutunci mai degree, 'yan uwanta mata da matan k'annenta
da sukaje, aiko suka samu dama suma d'aya bayan d'aya suke ta shikka mata rashin mutunci,
sun renata matuk'a gaya, matar babanta ma, ba wani bata raga mata, abu kad'an zaisa tayita
jifarta da gori da habaici iri iri, tun iya kulu tana dauriya bata tankawa, har ranar da ta gaji da
abunda take yimata, aiko ta fara zagewa tana ramawa, ta saki jiki ta wanke matar babanta tass
da soso da sabulu, matar baban ko ta aza hannu akai, tana ta kuka tana kwakwazon cewa,
azo a gani iya kulu ta dake ta, aiko yaranta samari da masu auren dake a gidan zaune da
matansu, sukaji haushi ba tunanin komi suka had'u sukayita jibgar iya kulu, tana ta kururuwar
neman mai ceto, amma ba wanda yazo rabo, rigima ta kacame a tsakaninsu, saboda Abu yazo
ganin iyar ne yaga ana wannan hargitsi, shima ya shiga da nufin ya ramawa iyar dukanta a
wurin wani tsarar shi a gidan, aiko shima aka had'a dashi
suka yimasu dukan kawo wuk'a, har saida sukayi tib'is gaba d'ayansu, aiko kusan rabin k'auyen
Suka taru a k'ofar gidan, sunata kallo suna tsegumin abun, wasu suna yiwa iya kulu Allah ya
k'ara, yayinda wasu kuma suka tausaya mata, rigima dai da tayi tsamari har sai da suka
garzaya, a fadar mai unguwa saboda ayi masu shari'a,.
Kafin kace me labari ya game k'auyen kaf, malam yaji dad'in faruwar hakan, koda Allah zaisa ta
gyaru, duk da yasan cewa da wuya iya kulu ta canza halinta, ita kam mama hassatu ta
tausayawa iya kulu, saboda cin zarafin da ake yimata yayi yawa, duk dai halinta ne ke jamata,
kuma tak'i ta gano inda matsalarta take sai ta daina.
Iya kulu ta fashewa mai unguwa da kuka, akan ya kira malam a bashi hak'uri ta koma gidan
mijinta, saboda tace ita da gidansu haihata haihata, har abada bazata sake zuwa gidan bama
balle taje ta zauna.
Mai unguwa yasa aka kira malam ya bashi hak'uri, tareda yi mata jan kunne kala kala, sannan
taci darajar mai unguwar malam ya maida ta gidanshi.
Bayan komawarta ne, ta fara karatun ta nutsu, ba laifi ta rage duk wasu miyagun halaye nata,
zamansu lafiya da malam, amma bata shiga sabgar mama hassatu, saboda a ganinta ita mama
hassatun ba sonta take yiba tunda tasa aka rabata da d'anta, aka kaishi wata uwa duniya, don
kawai bata son ta wayi ido ta ganshi a gidan.
Abu ma da akazo kanshi zaa kaishi secondary tayi ruwa tayi tsaki ta hurewa Abu kunne, akan
kar ya amince yaje birnin nan, kashe shi akeso aje ayi, daman cen shi ba makarantar yake so
ba, shiyasa da akace za'a kaishi karatun yak'i, yafiso ya biye d'iyan kande suje suyita shiga daji
suna sato amfanin gonar mutane, yana kawo mata tana b'oyewa, wasa wasa sai gashi ya fara
koyon shaye shaye, a wurin matasan yaran kande dasu daman cen suna sha, su k'ule daji
suyita shaye shayensu, sai sunyi tatil sannan su nufo gari suna mashalo, suje gida suna ta
hauka.
A ranar da malam ya ga wannan tashin hankali, ba k'aramin bak'in ciki ya shiga ba, ace a cikin
gidanshi a samu d'an shaye shaye, wannan abun kunyar dame yayi kama?, mama hassatu kam
da taga ya shigo gidan taganshi a buge, shigewarta d'aki takeyi ta rufe, sai dai tayita jiyo
artabunshi da iya kulu, yana ta surfa mata zagi ta uwa ta uba.
Izzatu ma da ta ganshi bata tsayawa, saboda tana gudun tasha dukan banza, duk da ba zama
take yiba a kullum tana makaranta, sai ranar asabar da lahadi shima gidan inna hure take zuwa
karatun Allo, saboda mijinta malamine sosai a garin har makaranta gareshi yana koyawa yaran
garin karatu.
Ana cikin haka ne inna hassatu ta samu ciki, murna a wurin malam sai kace ba'a tab'a yimasa
haihuwar ba, itama mama hassatu taji dad'i ba kad'an ba, suka b'oye abunsu a tsakaninsu, don
mama hassatun itace ta rok'i malam, da yayi shiru har zuwa lokacinda zai fito kowa ya ganshi,
saboda tana jin tsoron kaidin iya kulu akan d'an tayin cikinta.
***
Izzatu ce a gefen bakin titin dake garinsu, kasancewar shi babban titi, sai motoci ne kawai
suke wucewa, daman tunda Garzali ya tafi karatu, anan take fitowa ta tsaya ta samu abun hawa
ya shiga da ita birnin.
Tana nan a tsaye tana waige waigen motar da zata tare, sai kawai ga wata mota ta alfarma tazo
zata wuce, har tayi gaba saigata tana dawowa a hankali, har ta tsaya dai dai inda izzatu take a
tsaye, aka zuge glass d'in motar ganin wanda ke a cikin motar ne ya saka izzatu maye fuskarta
da murmushi, sab'anin tsoron da ya cika mata zuciya, a cikin murna irinta k'urciya tace:
"Laaa baba dama kana nan, ka daina zuwa garinmu?"
Mutumin yayi murmushi, ya kawar da tambayar da tayi masa yace:
"Ina 'yar baba zata je ne naganta da shirin zuwa makaranta?"
Izzatu washe da baki tace:
"Abin hawa nike nema zanje makaranta"
Da sauri yace:
"Shigo muje kar kiyi latti a dake ki"
Izzatu tayi shiru tana tunani, mutumin ya kalleta yayi murmushi har saida hak'oranshi suka
bayyana sannan yace:
"Ki kwantar da hankalinki 'yata ni a matsayin d'iya na d'auke ki, ko wani bazan bari ya cutar
dake ba, balle ni shigo muje in kai ki kar kije ki makara"
Izzatu ta bud'e gaban motar zata shiga, yace ta koma baya ta zauna, sun fara tafiya ne ta ya
tambayeta ina yayanta? da sauri ta kalleshi a cikin mamaki tace:
"Yaya Garza na, ya tafi makarantar jami'a ya barni, gashi yanzu in zanje makaranta a kullum
sai nasha wahala, sabida na saba shi yake kaini idan antashi ya dawo dani"
Ta k'are maganar tareda zubowar wasu k'walla akan fuskarta, sannan ta kalli mutumin tace:
"Amman Ina kasan yaya Garza na?"
Mutumin kam damuwa kwance a kan fuskarshi, yayi murmushin yak'e sannan yace:,
"Saboda me kika yiman wannan tambayar "
Izzatu tayi murmushi tace:
"Saboda naga lokacin da kake siyen tallata, baya garin ma ai a lokacin"
Mutumin ya shiru na minti biyu sannan yace :
"Ai na tab'a zuwa k'auyenku naga yana fad'a da wani da yace maki RUWA DA KANKARA, nine
ma na raba fad'an ai"
Izzatu tayi dariya tuno lokacin, sannan ta b'ata fuskarta a lokaci d'aya tace:
"Ai yaya Garza baya son yaji an kirani da wannan suna, nima haka kawai idan aka kirani da
sunan, nike jin kirjina ya buga sosai, wani b'acin rai ya ziyarci zuciyata"
Ba shiri mutumin ya kallota, shima tashi fuskar a cikin damuwa yace:
"To me ake nufi da sunan ne da bakya so?"
Izzatu ta share hawayenta tace:
"Nima ban san me yake nufi ba gaskiya, amman watak'ila shi yayan nawa yasani shiyasa
bayaso a kirani da sunan"
Daga nan firar tasu ta tsaya, har suka shigo garin, sannan ya tambayeta sunan makarantar ta
fad'a masa,jin sunan makarantar ba shiri ya kalleta yace:
"Wa ke biya maki kud'in makarantar?"
Izzatu tana dariya tace:
"Mamata da malam suna sona sosai"
Mutumin ya tamata murmushin yace:
"Allah ya biyasu da gidan aljannah"
Izzatu taji dad'in addu'ar da yayiwa iyayenta, sannan tace:
"Tareda kai, saboda kana da kirki kaima, kana taimakona a duk lokacin da nike buk'atar
taimako"
Mutumin yayi murmushi, bai ce da ita komi ba, har suka je k'ofar makarantar ya ajiyeta, ya
d'auko kud'i ya bata tak'i karb'a tayi godiya ta shige makarantarsu da gudunta.
Yabita da kallo har ya daina ganinta, sannan ya share hawayen da yake ta mak'alewa a
idanunsa, yaja motar jikinshi a sanyaye, tareda d'inbin damuwar da ta cunkushe zuciyarshi.
Koda aka tashi makaranta, izzatu tana fitowa a bakin get d'in makarantar, tayi tozali da motar da
ta kawota d'azu, amman zuciyarta ta kasa yarda da cewa shi d'inne, don tayi tunanin to me zai
dawo dashi in har shi d'in ne, koko akwai yaranshi a makarantar yazo d'aukarsu.
Har ta fara tafiya zata wuce motar, yayi mata oda tayi saurin juyowa, aiko taga yayi mata alama
da hannu da tazo, a cikin farinciki ta dawo ta gaidashi a ladafce, ya amsa a tak'aice sannan ya
fito ya bud'e mata bayan motar yace:
"Zo muje k'auyenku zanje yanzu, sai in ajiyeki"
A cikin jin dad'i izzatu ta shige mota, suka kama hanya sannu a hankali har suka kai bakin titin
dake garinsu, inda ya d'auke ta anan ya ajiyeta, zata fita ya waigo da fuskarshi akanta yace:
"Akwai wani aiki da nike zuwa yi garinku a kullum, idan kina so sai ki dinga fitowa anan tunda
safe sai in jiraki anan mu wuce in rage maki hanya, amman fa idan kin dad'e bazaki sameni ba"
Izzatu tana jin dad'i tace:
"Ai baba har sai ma na rigaka zuwa saboda sammakon da zan dinga yi"
Tana k'are maganar ta b'alle murfin ta fito, tayi masa godiya, har ta fara tafiya, sannan ya kirata
ta juyo yace da ita:
"Idan kika gayawa mamarki zata yimaki fad'a don haka kiyi shiru ba sai kin fad'a a gida ba ni
don Allah zanyi Allah ya bani lada"
Izzatu ta amince da zancenshi, tayi masa alk'awalin bazata fad'a ba, sannan suka rabu.
Tun daga ranar shi yake kaita makaranta, ya dawo da ita, hankalin su malam bai tashi ba sai
ranar da sukaje biya mata kud'in 2rd term, principal d'in makarantar tayiwa malam bayanin, an
biya mata kud'in shekara, kud'in su ma da suka bayar a farkon shigarta makarantar, dana komi
da komi ta basu tace ga abunsu nan.
Tofa jama'a wani lauje ne yayi wannan nad'inko zaku fassaraman me hakan
yake nufi???
Akafta⛹♀️
D/Auta
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*MUCH LOVE MY FANS *
*PAGE TWENTY FIVE*
**********************
Malam kam, yana jin wannan hargitsatstsen bayani, wanda ya saka shi shiga, tashin hankalin
da ba zato bale tsammani, jikinshi yana rawa bakinshi yana b'ari yace:
"Wane ne da wannan aikin?"
Principal ta nuna masa itama batasan shi ba, aiko malam ba shiri yace a kira masa izzatun,
minti biyar a tsakani sai gata anzo da ita, ba tareda wani jinkiri ba, yace tazo su tafi, acikin
mamaki izzatu ta kallesa, amman ba musu tabi bayanshi, har sun fara tafiya zasu bar office d'in
ne, principal taga da gaske Malam ya firgita, kuma da alamu d'auke 'yarsa yakeso yayi, a cikin
d'aga sautin muryarta tace :
"Malam lafiya?, me ke faruwa ne wai? Wanda hukumar makaranta batasan da zaman shi ba?"
Malam ya juyo jikinshi ya kyarma yace:
Mu muka kawo 'yarmu makaranta, to ta yaya wani zaizo ya biya mata kud'in makaranta har na
shekara ba tareda mun sani ba?, don haka daga yanzu na fiddata a makarantar, saboda
nagano akwai rashin tsaro sosai a cikinta, don haka na barku lafiya"
Yana k'are wannan zance, yaja izzatu kamar zasu tashi sama, suka bar makarantar, a cikin jin
haushin malam da abunda yayi, principal da wasu tsirarun malamai, da abun ya faru a gabansu
sai maida zancen sukeyi a tsakaninsu, saboda sunyi mamakin dalilin da yasa malam yayi
wannan haukar daga taimako?.
Kai tsaye suka zarce a kauyen su, izzatu sai faman kuka takeyi, tana tambayar malam meke
faruwa?, ita fa tana son makarantar ta, amma malam kanzil baice da itaba, har suka je gida.
Mama hassutu ko tun daga yanayin da taga shigowar malam, tasan akwai wata a k'asa,
musamman ganinshi da izzatu, tasan akwai abunda ya faru tunda lokacin tashinsu a
makarantar bai yi ba.
Mama hassatu rik'e da taguminta, izzatu ta zo ta gabanta ta wuce ranta a had'e, ta shige
d'akinsu ta b'are baki sai kuka takeyi, saboda jin haushin an rabata da makarantarta , gashi ko
littafanta a cen ta barosu.
Mama hassatu bata bi takanta ba tayi wurin malam domin taji meke faruwa?, aiko ba b'ata
lokaci malam yayi mata bayanin komi, itama kanta taji tsoron abunda taji, saboda har ga Allah
tana son izzatu, bata fatar abunda zai rabata da ita, jikinta a mace tace:
"To idan har haka ne, ai sai a canza mata wata makaranta kawai"
Malam b'acin rai kwance a kan fuskarshi yace:
"Ba wata makaranta da zata koma zuwa yi a cen, domin jikina yana bani ko wanene da wannan
aikin, to yanada alak'a da izzatu, ni kuma a yanzu duk abunda zaisa ta gano ba mune muka
haifeta ba to bana fatar zuwan shi, shiyasa kikaga duk wani rawar kai na Garzali akanta na
dakatar dashi, don bana son abunda zai d'aga mata hankali, nafi son muyita zamanmu asirinta
a rufe ruf, batareda tonuwar wannan sirrin da muke b'oyewa ba, shekara da shekaru ace ya
bayyana a gareta ta jishi ba, mafita kawai ta hak'ura da karatun, daman cen ni bai wani kwanta
man a rai ba"
Mama ta fad'a zurfin tunani na d'an lokaci, sannan ta d'ago fuskarta da damuwa shinfid'e akanta
tace;
Kayi hak'uri sai a canza mata matakarantar, sannan aja hankalin ita uzzatun da ta iya bakinta,
duka daman cen batada surutu, sannan itama shugabar makarantar, a fahimtar da ita kada
hakan ta koma faruwasu, yafi da atsayar da karatun, saboda nidai bana son karatunta ya tsaya
gaskiya, saboda shine kawai abunda zamu bata wanda zatayi alfakhari dashi a gaba, don haka
don Allah malam ka janye komi, ka bari taci gaba da karatunta insha Allahu ba abunda zai k'ara
faruwa"
Malam kam ba'a son ranshi zai k'ara barin izzatu ta koma zuwa birni karatu ba, amma tuno
wasiyyar Dada inda take cewa;
IDAN HAR IYAYENTA SUNZO KAR AYI JAYAYYA A BASU 'YAR SU.
Malam wata zufa ta karyo masa, ya saka hannu ya share, sannan yace da Mama;
"To yanzu meye abinyi?, don ke kikasan makarantun, yanzu kuma wace za'a sakata?"
Mama tayi murmushin jin dad'i tace;
"Akwai wadda za'a sakata a yanzu, hakan bazata koma faruwa ba insha Allah, saboda tana da
tsaro sosai fiye da wadda tayi;
Malam kam jinta kawai yakeyi, amman badon zuciyarshi ta amince da wannan karatu na izzatu
ba.
Iya kulu dake lab'e tana saurarensu, ba shiri tabar wajen, tana farinciki, ta shige d'akinta tana ta
shek'a dariya tace;
"Gayyar ta kusa watsewa kowa ma ya huta, ni dama ace nasan inda zanje in sami iyayen nata,
da wallahi da kaina zan kirasu suzo su kwashi kayan tsiyarsu, muga ta k'arshen iyayin masifa
da ake damun mutane dashi, ba'a aje komi ba, sai k'aton kashi ana ta cikawa mutane masai"
**
Anyi k'ok'arin canzawa izzatu makaranta, ta hanyar wata abokiyar Mama dake birnin, inda
yaranta suke yi, saboda ta tabbatar wa da Mama akwai tsaro sosai a makarantar.
A rana ta biyu ce, da zata je sabuwar makarantar da aka maidata ne, tana fitowa a bakin titin da
take taron abun hawa, sai kawai ga wata mota ta tsaya a gefenta, da sauri tasha jinin jikinta,
saboda jan kunnen da Mama tayi mata, akan kowa kada ta amince dashi, don har yaran
abokiyar tata da tayi ja gaba wajen sakata a makarantar, tace kada ta saki jiki dasu, kada tayi
sakacin da wasu zasu san sirrinta, balle ta fad'i inda take a zaune, aiko nasihar ta shiga jikinta
sosai kuma tana jin tsoron abunda zaisa asake cireta daga makarantar ta shiyasa da taga
wannan motar gabanta ya fad'i .
Sannu a hankali, mai motar ya sauke glass d'in mazaunin direba, ya fesheta da murmushi,
itama ba shiri ta mayar masa da murmushin ganin ko wanene, mutumin yana murmushin yace:
"'yata zo muje sauri nikeyi"
Izzatu ta fara waige waige, sannan tace;
"Kaje kawai Baba yanzu zan sami abun hawa insha Allah"
Mutumin ba shiri ya bud'e murfin motar ya fito, a ladafce yace da ita;
"Kiyi hak'uri ranki shi dad'e, ki shigo muje in ajiyeki sauri nikeyi, akwai sabgogin dake gabana, a
yanzu haka ma jirana akeyi"
Izzatu a cikin mamakin wannan ladabi da yayi mata, ba musu ta shiga motar suka fara tafiya,
hannunta ne izzatu takai hannunta akan tulin wasu