Showing 51001 words to 54000 words out of 119425 words

Chapter 18 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

ta zare jikinta daga kwanan da takeyi tareda
ilham, ta d'aga labule ta fito,karaf idanunta sukaci karo da wad'annan gogaggin yan gayu, da
sauri ta fito idanunta a kansu tana yimasu sannu da zuwa.

A cikin hayagaga mahaifiyar Dr tace,

Nazo ne inyi maku gargad'i akan 'yat tsintuwa da kuke so ku lik'awa d'ana, idan ba mugunta ba
yarinyar da ba'asan asalinta ba, zaku cusawa wani ya aura?, muna fa da labarin izzatu shegiya
ce, wadda aka haifa ta hanyar banza aka jefar a daji kuka tsinto, ina kuka tab'a ganin aure a
tsakanin mai asali d'an babban gida da d'iyar shegu d'iyar tsintuwa a cikin kwali a tsakiyar dokar
daji"


Izzatu dake tsaye a bayansu rataye da jakar makarantar ta ba shiri ta k'walla k'ara tareda
zubewa a k'asa sumammiya.








Kuyo agaji lik'i ya b'allewayyo Allah‍♀️‍♀️





Akafta

D/Auta ce�


[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈️*



*NA HADIZA D/AUTA*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*I LOVE YOU ALL MU FAN'S *

*PAGE THIRTY EIGHT*


**********************

A million Mama tayo kan izzatu ta rungumeta, tarea kiran sunan ta amma ina izzatu ko gezau
bata yi ba, da sauri ta tashi ta ciko wani jug da ruwan tukunya mai sanyi ta watsa mata, ba shiri
izzatu ta falko a firgice tareda kurma wata irin k'ara iya k'arfinta, Mama ta rungumota a jiki itama
tana kuka, izzatu ta ture hannun mama ta tashi da gudu zata bar gidan mama ta cafko ta, aiko
sai tayi tsalle ta fad'i a k'asa tana ta tumurmusa a cikin k'asa tana wani kuka na tashin hankali.

Kande dake a saman katanga itada yaranta suna lek'e, jikinta har b'ari yakeyi akan taga ya
wannan rigimar zata k'are, don bata son rigimar ta tsaya iya nan, shiyasa tace da wani d'anta
ya tafi gidan mai unguwa da sauri ya sanar da shi abunda ke faruwa, aiko yaro ya balbala
agujensa duk wanda ya had'u dashi sai ya fad'a masa cewa
"Gidan malam Ayuba 'yan birni suna cen sunzo zasu kashe izzatu"

Kafin kace me sai ga dandazon mutanen sun cika k'ofar gidan kowa da abun bugun shi, sai
muzurai sukeyi wasu suka ce a shiga a fito dasu, yayin da wasu suka ce a jira sai sun fito,
amma fa daga nan cikin gidan suna jin duk hayagagar da akeyi.

Mahaifiyar Dr da muk'arrabanta dake a tsaye, suna yiwa izzatu da mama wani kallon hadarin
kaji, suna jin sautin ruwan bala'in da mutane suke yi a waje, ga wasu 'yan ganin k'wak'waf har
sun fara shigowa, aiko cikin su ya d'uri ruwa tsoro ya shige su sai kallon juna sukeyi, suna
tambayar juna miye mafita?, wata daga cikin su ta kalli katangar dake zagaye da gidan, tana
neman ta wani gefe zata dira, sai gashi ta hango katangar gefen bayin su ta ruguzo tsawonta
ya rage, a d'ari ta nufi katangar kamar wata mai gasar tsallake katangu ta kama ta dire, sauran
suna ganin wannan hanyar itace mafi sauk'i da zasu tsira, aiko suma suka kama suka diddire,
kande da d'iyanta da sai kururuwa sukeyi suna fad'in,

"Gasu cen sun dire, ga su nan zasu tsere, abisu kar su sha banza."

Aiko mutanen dake k'ofar gida suna jin ana kuwwar sun dire, suma suka raka su a guje suka
bisu suna kururuwar a tare a tare.

Suko suna ganin sunci nasarar fita daga gidan,suka fara gudun fanfalak'i, Allah yaso su duk ba
wani jiki ne dasu ba dak'yar suka kai bakin titi suna haki, sai ga wata mota zata wuce ta kwaso
yashi, a d'ari suka tareta suka fad'a cikin yashi suna ta hakin wahala, koda 'yan k'auyen suka
k'araso sai dai suka hango su sun shige mota, suka bita aguje har saida suka ga bazasu
cimmata ba sannan suka hak'ura da biyar su.


A cen gidan malam ko izzatu ta haukacewa mama akan sai ta fad'a mata asalinta, zuwan mai
unguwa da kanshi a cikin gidan, shi ya ladaftar da izzatu daga tashin hankalin da take yi, da
kanshi ya saka ta a gaba ya tafi da ita gidanshi, bayan ya bada sallahun aje a d'auko masa
malam kasuwa.
Malam tunda yaji sak'on neman da mai unguwa yake yimasa, jikinshi yayi sanyi k'alau don
yasan ba lafiya ba, a cikin tashin hankali ya isa gidan mai unguwa.
Bayan malam yazo ne mai unguwa da wasu mutum biyu da sukayi saura, wad'anda a gabansu
Dada da malam suka zo da izzatu tana jaririya, aka saka izzatu da ke ta sharb'ar kuka kashirb'in
a tsakiya, mai unguwa yayi gyaran murya yace,

"Nasan tabbas dole ne ki shiga tashin hankalin da yafi wannan, saboda kunnuwanki sunji
abunda ya rikita tunanin ki, izzatu kiyi hak'uri da duk abunda kikaji, saboda ita k'arya fure take
bata 'ya'ya, tunda gashi yau sirrin da ake ta rufe maki shekara da shekaru ya bayyana, to dole
ne muyi maki bayanin komi, amma ki tsaya da kyau ki yiwa maganganun mu kyakkyawar
fahimta, don mu dukanmu farin ciki muke nema ba abunda zai sak ki a matsala ba, tabbas ke
d'iyar tsintuwa ce da gaske malam ayuba shi ya tsinto ki, don haka yanzu zakiji yanda akayi ya
tsinto ki har kika tashi a hannun shi, yayi maki rik'o irin na amana tareda mahaifiyar shi Dada
'yar tsohuwa Allah ya jikanta"

Gaba d'aya fadar akace "Ameen"

Malam a cikin d'inbin damuwa ya fayyacewa izzatu komi, tun daga ranar da ya tsinceta, har
izuwa gata da tattalin da Dada tayi mata, da wasiyyar da ta bari akan a rik'e mata izzatun
Amana da rasuwar ta, har zuwa auren Hassatu da yayi itama ta rik'eta tamkar itace ta haifeta.

Daga nan d'aya bayan d'aya kowa yana yimata bayanin abunda ya sani akanta, jikin izzatu yayi
sanyi hankalinta ya kwanta, musamman da taji ance ita ba shegiya bace, sannan da zargin da
sukeyi akan Baba kallah ko shine mahaifinta.

Daga nan sukayi ta kwantar mata da hankali, akan tayi hak'uri iyayenta sun kusa bayyana tunda
har kallah yasan inda take, ko ba shine mahaifinta ba to tabbas yasan wacece ita, daga nan
itama ta tuno d'awainiyar da yakeyi da ita, wadda a tsakani da Allah yake yimata hidima ba
gajiyawa, sannan ta tuno lokacin da tayi masa tambayar me yake zuwa yi a garinsu kullum, irin
yanayin da ya shiga har yaso ya jawo masu accident a titi, lokacin da ya d'auko ta daga
makaranta, haka kawai taji hankalinta ya kwanta, amman zuciyarta sai tunanin takeyi su waye
ne iyayen nata?, a wani gari suke?, me yasa suka zab'i rabuwa da ita fiye da su barta ta rayu da
su?, tana fatar taji wad'annan amsoshin a bakunan su ko bakunan wad'anda suka san asalinta.

A cikin sanyin murya izzatu ta fara yimasu godiyar irin d'awainiyar da sukayi da ita, musamman
malam da ya rik'eta tamkar d'iyar cikinshi, ya nuna mata so fiye da d'iyan da ya haifa, ta k'are
maganar tana kuka tuno irin soyayyar da akace Dada tayi mata, gashi bata raye balle tayi mata
godiya, amman tayi alk'awalin duk ta kai goshinta a k'asa tayi sallah sai ta rok'arwa Dada
rahmar ubangiji ta k'ara ninkuwa a cikin k'abarinta.

Daga nan malam da izzatu suka rankayo gida, duk inda ta wuce izzatu kallonta akeyi ana nunin
ta, ashe daman cen mai unguwa ne yayi jan kunne akan duk wanda yayi sanadin izzatu ta
gano wacece ita, to tabbas hukuncin shi d'aurin rai da rai a gidan yari, shiyasa kowa yake ta
taka tsantsan don jin tsoron wannan hukunci, amma in banda haka da izzatu ko k'ofar gida bata
isa ta fito ba, aikuwa nan take taji ta tsargu tana sunne sunne har suka kai gida ita da malam.


Koda suka shiga sun iske mama sai kuka takeyi, idanunta sunyi jawur saboda irin masifar
kukan da tasha, na tausayin 'yarta izzatu ganin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki wanda
ba zato bale tsammani, duk tasan komi daren dad'ewa wannan ranar zata ZO, amma ba a haka
taso zuwan ranar ba.
Ganin yanayin da izzatun ta shigo ne ya d'an kwantar mata da hankali, izzatu tana zuwa ta
fad'a, a jikin mama ta fashe da wani marayan kuka tace,

"Mama nagode da irin k'aunar da kika nuna man, alhali kinsan ba kece kika haifeni ba, amman
da rana d'aya baki tab'a barina nayi kukan rashin uwa ba, nagode nagode mama, yanzu na
gano dalilin da yasa kike hana ni bin ba'asin gugar zanar da iya take man, ashe kina hana ni
zurfin tunanin da zan gano inda maganganunta suka dosa ne, Allah sarki mamata kin toshe
kowace k'ofar da kikasan idan naji asalina zan shiga damuwa, Allah ya saka maki da alkhairi,

kin bani kulawarki da aljihunki da kuma gangar jikinki sannu mamata, wallahi ko a aljanna ke
taki ta k'ololuwa ce, malam da ke mamata da masoyiyata Dada da yaya Garza na, ina sanar
maku da duk abunda na zama a fad'in duniya bazan tab'a manta ku ba a tarihin rayuwa ta,
saboda kune k'ashin bayana a doron k'asa, wanda idan ba d'aya daga cikin ku bazan tab'a jin
kaina dai dai ba, ya ALLAH ka barni tareda wad'annan bayi, ka bani abunda zan kyautata maku
koda rabin rabin abunda kuka yiman ne."

Izzatu ta tashi da gudu ta rik'e k'afafun malam tace,

"A gaida baya goya marayu sannu jarumi a cikin JARUMAI, kaine babana na har abada wanda
idan na rasa shi rayuwata ta tawaya, Allah ya yi maka fiye da yanda kayiwa rayuwata gata,
nagode nagode babana!."
Mama da malam da ita kanta izzatu sai kuka sukeyi gwanin ban tausayi.



Har ga Allah nima na tausayawa wannan ahali .





Akafta �





D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈️*



*NA HADIZA D/AUTA*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*PAGE THIRTY NINE*

**********************

Iya kulu dake tsaye tana kallon su jiki a sanyaye ta shige d'aki, amma a cikin zuciyarta taji dad'in
wannan asiri da ya tonu, ko don abarta yanzu ta sakata ta wala yanda takeso.


Washe garin ranar Dr yazo k'auyen, saboda ya sami labarin fitar kutsun da mahaifiyar shi suka
yi a garin, tun a jiyan yaso yazo amman jin abunda ya faru ya sage masa gwiwowi, don jikinshi
yana bashi ba abun alkhairi suka zo suka shuko a garin ba, shiyasa aka ymasu wannan bajimin
wulak'ancin, domin kuwa mahaifiyar shi duk ta gurje jikinta asanadiyyar tsallakar katangar da
suka yi, sannan k'afafuwanta duk k'ayoyi sun shige mata aciki, don ko kafin ya fito sai da yayi
mata dressing d'in ciwukan yayi mata allurori, saboda tana komawa gida zazzab'in mai zafi ya
rufeta, jiki asanyaye yayi parking d'in motar shi ya fito, a k'ofar gidan ya tsaya ya tura wani yaro
yace ya kira masa izzatu, aiko madadin izzatu ta fito sai ga malam shi ya fito, saboda abunda
ya faru ya hanashi jin walwalar da zai fita kasuwar da ya saba.

A cikin ladabi Dr ya gaida malam, amma malam fuskar shi tamau yake amsa gaisuwar, ba
alamun zai iya yiwa Dr sassauci a wannan karon, bayan sun gaisa kafin Dr yace wani abu
malam ya riga shi da fad'ar cewa,

"Naga sak'on da ka turo iyayenka akan su ZO su kawo, to sun zo kam sunyi abunda suke so
kuma sun janyo abunda muke b'oyewa tsawon shekaru ya tonu, to Alhmdllh da ban riga na aura
maka izzatu ba, don haka ina son ka sani daga yau kada in sake ganin k'afar ka anan k'ofar
gidan, na raba alak'ar ka da izzatu har abada, koda ko ku biyu ne kawai kuka rage a cikin
duniya izzatu bazata aureka ba, abunda kayi muna na alkhairi mun gode bamu rena ba Allah ya
saka da alkhairi."

Malam yana k'are fad'ar maganar ya fara taku zai shige gida, da sauri Dr yasha gabanshi ya
dyurk'usa gwiwa bibbiyu yana cewa,

"Don Allah kayi hak'uri ka yafeman malam, wallahi ban ma san sunzo ba bale in aiko su da
sak'on cin zarafi a gare ku, kai kasani bazan tab'a yin abunda zai cutar da izzatu ba, naji na
amince zan daina zuwa insha Allahu amma bazan daina son izzatu ba, don Allah kayiman
alfarma ta k'arshe ka amince mani da inga izzatu a yanzu, domin in rok'eta yafiyar abunda aka
yi mata don Allah malam"

Ba tareda malam yace k'anzil ba ya shige cikin gidan, minti biyu a tsakani sai ga izzatu ta fito
fuskarta da busashen hawaye, saboda tun jiya hawayen dake idanuwanta sun kasa tsayuwa.

A hankali ta tako har inda Dr ya ke a durk'ushe, don k'afafuwan shi sunyi sanyi k'alau, jin yakeyi
bazasu iya d'aukar nauyin shi ba, ya d'aga kai yakai dubanshi a kan fuskar izzatu, da ta kunburo
saboda tsananin kukan da tasha, a cikin raunanniyar murya ya fara magana yace,

"Izzatu duk wata kalma da zanyi amfani da ita wajen baki hak'uri, ganin nikeyi tayi k'aranci,
amman duk da haka ina baki hak'urin don Allah kiyi hak'uri ki yafe man, wallahi bada sanina
suka zo ba har sai bayan sun dawo ne na sami labari"

Izzatu da idanunta k'yar akanshi tana yimasa wani kallon da ita kad'ai tasan ma'anar shi, a cikin
dusashiyar murya tace,

"Ai ni taimako na ma sukayi, don sun fitar dani a cikin duhun da a kullum ya kamata ace na fito
acikin shi izuwa haske, Alhmdllh duk ta hanyar da aka sameni nayi imani da Allah akan cewa
shine k'addarata, kuma na rungumeta da hannu bibbiyu, abu d'aya ya hana in nuna maka kalar
'ya'yan tsintuwa saboda naji an fad'a ma asalina kuma kaji ka gani a hakan kake sona baka
k'yamace ni ba, asanadiyyar hakan kaje na yafe maka itama mahaifiyarka na yafe mata tashin
hankalin da ta sakani, ALLAH ubangiji ya had'a fuskokin mu a aljannah nida kai,na gode da
d'awainiyar da kayi tayi dani, ina maka fatar ALLAH ubangiji ya baka mace ta gari yar asali
wadda zakayi alfakhari da samunta, na barka lafiya sai watarana"

Tana k'are maganar ta zo da gudu zata shige gida, a sanadiyyar wani kuka da yazo mata, ya
d'aga murya ya kira sunanta, ta tsaya cak ba tareda ta waigo ba, a cikin wata murya at ban
tausayi mai had'e da kuka tace,

Zuciyar Dr hashim ki sani har abada bazata iya daina k'aunar ki ba, son ki a cikin jinina yake
bazan iya cire shi ba har sai ranar mutuwa ta, I love you too my izzah! i love you up to end of
my life, never mine izzatu, ina yi maki fatar alkhairi a rayuwarki."

Wani kuka yazo mata ba shiri da gudu ta fad'a gidan sai gunjin kuka takeyi, jin kukan da takeyi
ya k'ara dagula wa su malam zukata, gaba d'aya ta k'ara famo masu damuwar dake damunsu.

A cen k'ofar gida kuwa, izzatu tana shiga gida Dr yaji kamar an zare masa duk wata laka dake
a jikinshi, ba shiri yakai jikin motar shi ya jingina, tareda dafe zuciyar shi dake barazanar fitowa,
saboda bugun da takeyi da sauri da sauri, yana nan a tsaye sai kawai ga d'aya daga cikin
'yanmatan kande, tana wani kwarkwasa tana fari da ido, mamaki ya kama Dr na ganin wannan
rashin hankali da takeyi, ba shiri ya maida idanuwanshi ya runtse saboda tsabar takaicin da ta
bashi, mariya d'iyar kande ganin hakan yasa ta zaci tarkon da ta d'ana masa yayi kamu, aiko ta
fara zuba tamkar kanya tana cewa,

"Sunana mariya amma anan garin anfi sanina da mari, a duk garinnan idan ka zagaya kaf babu
wata mace da ta kamo k'afata, tunda ita wannan 'yar tsintuwar bata da rabo, to me zai hana ni
ka dawo a kaina?, nayi alk'awali zan baka farin ciki fiye da wanda kayi kwad'ayin samu a
wurinta, ka soni ka turo iyayenka ni kaga gidanmu a nan, uwa da uba na duk 'yan garinnan ne
kowa yasan asalinmu, don haka idan ka amince ni a shirye niko ko a gobe ne kazo a d'aura
muna aure ni da kai"

Dr ba shiri ya bud'e idanuwanshi ya kalleta tun daga sama har k'asanta, ita ko ganin haka sai
wani juye juye takeyi tana murmushin nasara, bai san lokacin da wata dariya ta sub'uce masa
ba, sannan ya had'e fuska kamar ba shi ba yace,

Ke wai a zatonki ke mace?, cab to bari in fad'a maki gaskiya a baki d'aya yanayin ki kaf ba na
mata, don farkon ganin da nayi maki nama zaci namiji ce, har sai da naji muryarki na gano ashe
mace ce ke, to nikam taya zan kwashi mai siffar maza in kai gidana?, idan anzo a kasa gano
waye mijin wacece matar.?
Kafin ta tantance ya shige motar shi ya bata wuta, aiko ganin da gaske tafiya zaiyi tayi saurin
zuwa ta tsaya a gabanshi, ya zuro kanshi yace,

"Kauce daga nan ko in nuna maki k'arshen rashin kunya."

Mari tayi tsaye tana yimasa gwatsine gwatsinen ido da hanci, aiko Dr da k'arfi yayo cikinta ba
shiri ta kauce tana yimasa Allah ya isa.




Kwanaki sun ja a kullum malam da mama sai k'ara kwantar mata da hankali sukeyi akan tayi
hak'uri insha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login