Showing 72001 words to 75000 words out of 119425 words

Chapter 25 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

gidan Abbaah, koda suka je har ya ajiye motar ya shige gida, dak'yar mai gadin gidan
ya barshi ya shiga harabar gidan bayan ya nuna masa kud'in,yace dashi ya jira anan get d'in sai
Alhaji yace ya shigo.

Aiko minti biyar a tsakani sai ga maigadin ya dawo tareda Abbaah, yana hango ledar a hannun
baban Dr ya tuna lokacin da take a hannunshi bakin shagon, ba shiri yace da baban Dr ya
karaso cikin gidan har babban falonshi ya saukeshi, bayan sun gaisa ya mik'a masa kud'insa zai
tashi Abbaah ya dakatar dashi, sannan yayi masa godiya ya zaro d'auri biyu na kud'in ya mik'a
masa, sannan yace dashi wace sana'a yakeyi?, baban Dr a lokacin buga buga ce kawai yake yi
shiyasa da yay masa bayani, Abbaah yace dashi yazo zai bashi aiki a d'aya daga cikin
shagunanshi.

Tun daga lokacin ya bashi aiki ya rik'i kanshi da iyalinshi, Dr ma karatun shi shine ya d'auki
nauyi tun secondary har ya zama Dr a yanzu, ta hanyar wannan zumuncin ne har shu'aib yasan
Dr suka k'ulla abota.

***

Izzatu a garden ita da su fahat da ammar sai guje gujen wasar 'yar b'uya suke yi, tana sanye da
wasu riga da wando yan kanti sun kama ta sosai, ta rufe fuskarta da k'yalle tana neman inda
zata lalabo su ammar caraf taci karo da mutum tayi tagataga zata fad'i, shu'aib yayi sauri ya
rungumota a jikinshi.
Ammi dake tsaye a window'n sama tana kallon abunda yake faruwa, da sauri ta runtse idanuwa

saboda ganin rungumar da shu'aib yayiwa izzatu, sabida daman ta dad'e tsaye a tagar tana
kallon yanda izzatu ta saki jiki ta biye su Ammar suna ta wasa kala kala, tana jin dad'in wannan
k'auna dake tsakanin izzatu da 'yan k'annenta, domin tunda tazo gidan a kullum suna manne da
ita tana koya masu karatu, idan sun k'are a koma wasa har da labarai take basu kala kala da
tarihin annabawa, shiyasa shak'uwar tayi yawa saboda suna jin dad'in zama da ita, haka itama
tana bala'in tsintar kanta a cikin farinciki musamman in ta tuna k'annenta ne fa uwa d'aya uba
daya, shiyasa take zage damtse tana koya masu abubuwan da zasu amfana.

Izzatu tana jinta a jikin mutum da sauri ta cire k'ullin k'yallen da ta rufe fuskarta da shi, caraf
idanunta suka sauka akan fuskar shu'aib, da yake ta feshe ta da wani shu'umin murmushi
tareda d'age mata gira d'aya, a cikin zafin nama ta saka hannu biyu ta ture shi yayi baya, ta
nuna shi da d'an yatsa a cikin fushi tace, "this is the first and last da zaka saka kazamin
hannunka ka tab'a ni, idan ba haka ba wallahi sai na nuna maka kuskurenka don ni ba 'yar iska
bace da zaka wani had'a jikina da kai, kana yiman wani kallo da jajayen idanuwa tamkar wani
tsohon maye, to bari kaji mayun ma na gaskiya sun ganni sun barni ballantana kai k'aramin
k'waro."

Sai ga su Ammar sun gaji da b'oyon da sukeyi a k'ark'ashin kujerun dake wajen, sun ji shiru ga
bata zo kamasu ba shine suka fito, fahat ya kalleta ya kalli shu'aib a cikin rad'a yace da ita,
"Kema yaya shu'aib yayi maki muguntar da yake yimuna halan aunty?."

Izzatu ta ri'ko hannun fahat tace, "Ku zo muje don wasar bazatayi dad'i ba tunda jemagu
sun sauka a wurin."

Ta k'are maganar tareda dallawa shu'aib wata harara, ta duk'a ammar ya haye bayanta ta
goyashi suka bar wajen, a cikin takunta na kasaita mai cike da motsa uku suna sittin saba'in.

Shu'aib yana yi mata wani kallo ya sosa gemunshi, tareda lashe lab'b'anshi tamkar wani wanda
ya samu alawa, yana murmushi yace,

"Allah ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi birgima."

Ammi dake kallonsu ta sauke wata k'atuwar ajiyar zuciya, saboda taji dad'in abunda taga izzatu
tayiwa shu'aib, duk da bata jin me suke fad'a amman hakan ya burgeta, ta k'ara tabbatarw
zuciyarta lalle izzatu ta sami tarbiyya mai kyau a wurin iyayen rik'onta.



Shin Ammi kema baki son shu'aib d'in ‍♀️‍♀️wanga Black blood fateam shu'aib ku fito muyi
zanga zanga‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️

Akafta‍♀️







D/Auta ce⛹‍♀️
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈️*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*PAGE FIFTY ONE*

**********************

IZZATU tayi shirin zuwa k'auyensu domin taje ta gano aikin ginin da ta bada kwangila, waton
gidan mai unguwa da gidan malam da yanzu haka ba kowa a ciki da ta k'ara siyen filin da ke a
bayan gidan aka k'ara fad'ad'a shi, sai gidan su inna hure da shima tasa aka rushe aka sake
gina masu wani sabo dal, ank'are ginin ne take so taje ta gano sannan ta kai gaisuwarta ga
d'aukacin mutanen k'auyen gaba d'aya.

Taci kwalliyarta son kowa k'in wanda ya rasa, ammaah sai kod'a ta takeyi saboda tsantsar
halittun kyaunta da suka bayyana, Ammi kanta a ranar da izzatu taje yi mata sallama sai da ta
cire kawaici tace da ita, "Anya 'yar Ammaah zaki bari azauna lafiya kuwa?, irin wannan
kwalliya da kika zuba ai sai ki firgice mutanen k'auyen naku."
Izzatu tana murmushi tace, "Ammi to ni har wani kyau ma nayi nida ba kwalliyar kirki ma na
iya ba, ke dai kiyi man addu'a kawai ALLAH ya dawo damu lafiya."

Ammi tana murmushin jin dad'in ganin 'yarta masha ALLAH tace, "Duk wadda Ammaah tayi

bata isa ba ni har sai na k'ara?, to matso inyi maki irin addu'ar da nike yiwa su Ammar idan kina
so."

Izzatu tana dariyar jin dad'i tace, "Ko ta jarirai ce yiman kawai Amminah! ina so."

Ta k'are maganar tareda duk'awa a gaban Ammi tana dariya, Ammi ta saka hannu ta dafa kanta
tayi ta zuba mata addu'o'i tana tofa mata, bayan ta k'are ne tayi murmushi tace da ita,
"ALLAH ya tsare hanya, amman dai zaki biya gidanku mamarki ta ganki kafin ki wuce ko?."

Izzatu ta mik'e tsaye tace da Ammi, "Eh sai naje cen kafin in wuce, domin tare da Amina
zamu je."

Ammi tayi murmushi tace, "to a dawo lafiya ki gayar man da su duka."

Izzatu ta fara tafiya zata bar d'akin tareda cewa, "Zasu ji sai mun dawo."

Ammi ta bita da kallo a cikin farinciki tareda k'ara yiwa ALLAH godiya da ya bayyana mata 'yarta
a cikin aminci, shiyasa a kullum su malam suke da girma a wurinta, musanman mama hassatu
da a yanzu ta d'auke ta tamkar wata 'yar uwarta, saboda tana amfanuwa da shawarwarin da
take bata idan tabi, don itace ma ta bata shawarar tayi kawaici wajen nuna tsantsar soyayyarta
a fili ga IZZATU, saboda yanda ammaah take k'aunar izzatu da sauran 'ya'yanta kaf da ta haifa,
hakan zaisa damuwar rashin 'ya'yan da ta rasa ya rage ta d'auka cewa tamkar itace ta haifi
izzatun, domin da gaske take son izzatu tamkar itace ta kawota duniya saboda kyakkyawar
zuciyar da ALLAH ya azurta da samu.

Koda izzatu ta fito sashen Ammi, Amma dake tsaye tana jiran fitowarta, saboda tana son taga
tafiyarta domin ta koma wurin su fahat da tayiwa wayo don kar suce sai sunbi izzatun, shiyasa
tana hangota ba shiri tayi murmushi wanda ya k'ara kawata kamilallar fuskarta.

A tare suka rankaya har gindin wata arniyar motar da aka tanada musamman saboda wannan
tafiyar, wadda baba kallah ne zai jata saboda shi kad'ai ne Ammaah ta amince da yaja izzatu.

Bayan motocin da zasu take mata baya tareda escort din da zasu je a tare, sai motar sojoji biyu
da zata yi masu rakiya saboda tsaro.

Izzatu ta bud'a motar ta shiga tana yiwa Ammaah bye bye, ammaah tace da baba KALLAH, ga
amanar 'yarta nan ta bashi yana murmushi yaja motar, sauran motocin da zasuyi masu rakiyar
biyo shi, wasu a gaba wasu a baya aka saka motar baba kallah a tsakiya har gidansu su
malam.
Izzatu direct sashen iya kulu ta shiga a gurguje ta gayar da ita ta fito, mari ta biyo bayanta sai
kirari take zuba mata har sai da izzatu ta taka mata burki sannan tayi gum,izzatu ta fad'a
sashen mama da gudu tana k'wallawa ilham kira, mamar ma jin muryar izzatun a fujajan ta fito

suka had'u a hanya suka rungume juna a cikin farinciki, mama ta kalli izzatu tun daga sama har
k'asa tace, "wai dai nikam ko musayar 'ya aka yiman ne?, tubarakallah masha ALLAH
wannan kyau haka 'yata?."

Izzatu tana dariya yace, "Mama ina ilham?."

Mama tace, "Bacci take kinsan ta ko kasa bata fita bacci ba, sai dai in bata ji cikinta da nauyi
ba."

Kafin izzatu tayi magana sai ga Amina ta fito a cikin shirinta, itama tayi kyau gwanin burgewa
sai kace ba ita ba, tayi kyau ta murje bazaka tab'a cewa iya kacinta primary ba, duk da yake
yanzu an jefata secondary ss1 da taimakon lesson d'in da mama tasa aka yi mata a gida.

Izzatu ta kalleta tace, "dallah malama muje kin wani mak'ale kina so ki b'ata muna lokaci."

Amina ta harareta tace, "Lalle ma yarinya yanzu duk lokacin da kika b'ata kafin kizo baki gani
ba sai nawa."

Izzatu tayi dariya tareda shigewa d'akin mama inda ilham take bacci, ta duk'a tayi mata kiss
tace, "Rimammata."

Sannan ta fito tana yiwa mama sai sun dawo, mama tayi masu addu'ar a dawo lafiya sannan ta
rakaso su suka fito, abin mamaki sai ga iya kulu ta zama kalar tausayi a gaban baba kallah.

Ba wanda ya bi takanta suka fice suka shiga mota suka kama hanya, amma zuciyar izzatu sai
mamakin ganin fuskar iya kulu da tayi kamar harda guntun hawaye,tana ta sak'e sak'e a ranta
har suka fara tafiya zasu bar garin, izzatu tace da baba kallah, "Don ALLAH baba wani gida
nike so muje kafin mu wuce."
Baba kalla ya juya akalar motarshi sauran motocin ma suka biyo su, izzatu ta kalli Amina da ta
cika da mamakin ina zasu je tace da ita, "Gidansu Dr hashim nike so muje zaki iya gane
gidan.?"

Amina ta fad'ad'a fuskarta da murmushi tace, "keda gidanku ace har sai na nuna maki?, to
nima bazan iya gane gidan ba gaskiya a yanzu."

Baba kalla yace dasu, "Dr Hashim d'in da na sani abokin shu'aib kuke nufi?"

Izzatu tayi saurin fad'in, "shi fa baba kasan gidan su ne halan.?"

Baba kallah yana murmushi yace, "nasan shi sosai kuma nasan gidansu saboda ai
mahaifinshi, a d'aya daga cikin shagunan maigida yake aiki"

Dukansu suka zaro ido, Amina tace,

"To acen gidan zamuje."

Izzatu kam tuno cin zarafin da mamar Dr taje tayi masu a k'auye, ya k'ara fad'o mata a zuciya
ba shiri tayi murmushi amma har a lokacin tana jin zafin lafuzzan da ta yab'awa mamarta akan
rashin sanin asalinta, ashe ma a karkashin abbaah suke bata da labari, aiko ta k'ara samun
kuzarin zuwanta gidan ko don ta nuna mata ita d'iyar sunnah ce ba shegiya ba, haka zalika
matsayinta yayi wa nasu fintinkau.




Manage plss‍♀️



Akafta




D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈️*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*PAGE FIFTY ONE*

**********************

Baba kallah bai zame a ko'ina ba sai unguwar su Dr, yana gaba sauran motocin suna bayan
shi har k'ofar gidansu Dr sannan yayi parking, wanda shigowar su ya jawo hankalin mutane da
yawa, yayin da wasu suke ji tsoron ganin wad'annan kosassun sojojin suka fara gudu, 'yan gani

kashe kuma suka tsaya kallo zuciyoyinsu a cike da mamakin, me su Dr sukayi suka tsokano
fushin masu hannu da shuni ganin rantsatsun motocin sababbi k'al sai d'aukar ido sukeyi.

Ita kanta maman Dr ta lek'o neman yaron da zata aika ne ta hango motocin suna doso k'ofar
gidansu, har ta so ta tsaya kallo amma tana hango motar sojojin ba shiri hantar cikinta ta kad'a,
musamman da taga sun tsaya a k'ofar gidan suna dirowa daga cikin motocinsu, abun mamaki
kuma sai taga wasu security's sun tsaya a gefe da gefen wata rantsatsiyar mota, waton motar
da SU izzatu suka shigo, suka tsaya gefe da gefen motar wani ya saka hannu ya bud'e murfin
motar, sannan wanda ke gefen guda ma ya bud'e d'ayan murfin idanuwan maman Dr a waje
tana so taga wad'anni shafaffu da mai ne?, aiko tana nan k'urin da idanuwa ta hango k'afar
izzatu d'aya da ta sauko a k'asa kafin ta fito gaba d'aya, ba shiri maman Dr ta k'ara zaro
idanuwa aranta tace,

"Bak'in turawa mukayi a unguwar tamu.?""

Kafin ta baiwa kanta amsa sai ga izzatu ta fito gaba d'ayanta ai kuwa ba shiri maman Dr ta
k'ara gwalalo idanuwa baki a bud'e tace, "tsalki ya tabbata ga mak'agin wannan halitta."

Ta gano da gaske gidan zasu shigo ne saboda ganin izzatu da Amina sun doso gidan, sannan
ga wasu security's mata sun take masu baya a guje har tana tuntub'e ta shige gidan, bata tsaya
a ko'ina ba sai a k'uryar d'akinta tayi likimo tana sauraren shigowarsu, domin zuciyarta ta bata
tabbas ba lafiya don ita a rayuwarta KAF bata tab'a ganin wad'annan halittun ba.
Aikuwa tana jin shigowarsu tareda takun takalmansu dake k'wask'wa, a d'ari ta bazama toilet ta
zubarda zawon da taji yana barazanar fito mata ko ba shiri, tana jin sallamar su izzatu amma ta
kasa amsawa sabida zawon da take fesawa, bayan ta k'are ne ta fito jiki a sake tana amsa
sallamar a cikin raunanniyar muryarta, tana fitowa a tsakar gidan ta k'ara yin tozali da
fuskokinsu izzatu, ba shiri cikinta ya k'ara kad'awa duba da yanda taga security's d'in matannan
suna ta muzurai, a haka ta daure dai ta k'ara tsuke k'ofar zawon don kada yayi mata tonon silili
a gaban mutane, a cikin dakiya ta fara yi masu sannu da zuwa kamar haka,

"Sannunku da zuwa hajiya anzo lafiya?ku shigo daga ciki mana."

Tana gaba su izzatu suka bita a baya har cikin falonta, bayan sun zauna suka k'ara gaisawa
fuskar izzatu ba yabo ba fallasa tace da ita,

"Dr fa?"

Mamar tayi k'ara tsurewa ido suka rena fata bakinta yana rawa tace, "Yanzu zaki ganshi ya
shigo domin fitar shi kenan yaje yiwa wani abokin babansu allura."

Izzatu tayi warai da idanuwa tareda wani munafukin murmushi tace, "Sai naga kamar baki
waye mu ba mama."

Mamar Dr tayi saurin zaro idanuwa domin ta k'ara tantance su saboda jin da tayi izzatu ta kira ta
da sunan mama, kafin mamar Dr tace wani abu izzatu tayi wa wata security magana da turanci
akan ta bata jakarta dake a hannunta, a gaban mamar security tazo ta rusuna ta mik'awa izzatu
jakar ta saka hannu ta karb'a tareda yin murmushi tace, "Thanks."
Sannan ta soka hannu a jakar ta ciro check tareda rubutu dubu d'ari biyu a jiki ta b'allo paper'r
ta mik'awa mamar, a cikin mamaki mama ta zura hannu ta karb'a tana jiran taji ba'asin check
d'in menene, izzatu ta mik'e a tsaye ta feshe ta da wani shu'umin murmushi tace,

"Idan Dr yazo kice masa izzatu d'iyar Gwamna yahaya badawi tazo."

Tana k'are maganar ta fito falon Amina ta take mata baya, mama kuwa tana jin wannan suna ta
dafe gaba saboda dakan luguden da kirjinta yayi ba shiri, tareda zaro idanuwanta duka a waje
kamar zasu fad'o a guje ta biyo bayan izzatu har taci tuntub'e zata fad'i, izzatu tayi saurin rik'ota
tace,
"Subhanallah mama."

Ido cikin ido mama take kallon izzatu a cikin mamakin da yake barazanar kaita lahira bata
tantance ba, tareda kallon tuhumar da mamar take biyarta dashi, izzatu ta lumshe idanuwa
tareda bud'esu taras akan fuskar mama saboda karantar abinda ke cikin zuciyarta da tayi, a
hankali ta d'aga kai tace, "Kada kiyi mamaki mama nid'in dai ce 'yar k'auyen nan da kuka
hanawa Dr ya aura, haka zalika nice yarinyar da kikaje har k'auye kika gorantawa asali, kada ki
damu nasan rashin sani ne ya jawo hakan, kada kiji komi ni na yafe maki saboda a tsakaninmu
da Dr har gobe akwai mutunci domin yayi muna alkhairin da bazamu iya manta shi ba."

Izzatu tana k'are maganar ta feshe mama da wani murmushin mai cike da ma'anoni ta fito gidan
security's suna take mata baya, mama baki a bud'e tayi zaman 'yan bori a tsakiyar gida
hannunta aka ta kurma wata bajimar kuwwa, me ta tuna kuma tayi saurin dafe baki tareda
bazawa a guje kamar wata k'aramar yarinya tayi toilet tana kwararo zawo.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login