Showing 6001 words to 9000 words out of 119425 words

Chapter 3 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

iya kulu suka ja yaransu suka fita tareda yiwa junansu sai da
safe.

Bayan fitarsu Dada ta sauke izzatu ta lallab'a ta kwantar da ita, tareda tofeta da addu'o'i,
sannan ta rab'a agefenta ta d'an gincira, aiko ba shiri bacci mai nauyi ya d'auketa.

Asubar farin izzatu ta tada Dada daga barcinta mai dad'i da takeyi, ta hanyar kwantsama kukan
da tayi tayi, dole Dada ta farka ba shiri.

Da dubara ta samu tayi sallah, sannan ta
dawo hidimarta, akayi dai dai malam ya shigo domin ganin meke faruwa, saboda yaji kukan
izzatu,haka kawai yakejin son yarinyar tamkar shine ya haifeta, da sallamarshi ya shigo idonshi
akan izzatu yana yiwa Dada barka da safiya.

Bayan sun gaisa ne Dada tace dashi:

"atatso nono aba izzatu tasha saboda yunwa ce ta tada ita daga bacci"

Malam jikin shi yana rawa ya fito, bai ko bi takan iya kulu ba yaje ya tatso nonon da zafinshi
yakai aka bata, sai da tasha ta koshi sannan ta koma bacci, hankalinsu ya kwanta.

Malam yana shirin fitowa d'akin ya had'u da iya kulu ta fito tana kiciniyar had'a wuta, domin ta
aza ruwan zafin da za'a yiwa izzatu wanka, malam yace da ita:

"Na tatso nono anbaiwa izzatu tasha"

Iya kulu tayi saurin d'agowa daga hurin wutar da takeyi da bakinta tace:

"To ai kuma ba'a bada kud'in ba ko anbiyo ne?"

Malam ya kalleta sororo sannan yace:

"Na jiya da na baki asusu nace ki saka su halan?, yanzu ke don Allah tun da sassafe zaki saka
mutane d'aga jijiyoyin wuya, to daga yau ma ta daina shan nonon sai ki dinga kasa shi a
kasuwa kina saidawa idan kinso, amma nikam babu ni aciki"

Yana k'are maganar ya wuce abinshi zai shige d'akinsa, iya kulu ta bishi da kallo tareda
murgud'a baki ta fara gungunin cewa:

"Mutum da abunsa bazaiyi tambaya ba?, waya saya mun akuyoyin?, ai da kud'in adashe na ne
da nikeyi na sayi kayana, don haka bazan tab'a lamunta aci da hak'k'ina ba, ko don kai ke bani
kud'in zubin adashen, shiyasa zakayiman gadara, to ai kyauta ka bani ba ranko aciki"

Bayan ta k'are 'yan surutanta sannan tayi saurin biyar shi abaya tana bashi hak'uri, saboda ta
fahimci ransa ya b'aci akan hakan, baija zancen da tsauri ba yace da ita: "taje bakomi".

Sannan ta fito ta nufi d'akin Dada domin ta dubo ya suka kwana.

Bayan sun gaisa ne taje ta juye ruwan zafin ta kawo akayiwa izzatu wanka, sannan Dada ta
shafeta da man kad'e tas sai k'yalli takeyi, ta k'ara shiryata ta goyeta.

Saiga Garzali ya shigo kamar an jefoshi, yana mutsu mutsun idanuwa, sai rabasu yakeyi domin
ya hango izzatu, amman bai ganta ba, acikin tashin hankali yace :

"Dada ina izzatu yanzu shikenan ank'waceta ta tafiyarta bazamu sake ganin ta ba?"

Acikin mamaki Dada da iya kulu suka bishi da kallo, ganin yanayin kallon da suke yimasa yasa
ya gasgata mafalkin shi ya fara kuka yana sanbatun cewa:
"Yanzu shikenan sun karb'eta don mugunta"

Da dai Dada ta fahimci inda ya dosa, tayi saurin cire lullub'in zanenta da ta rufa wanda shi ya
hana shi yaganta a goye, aiko yana ganinta kafin Dada tace wani abu yayi saurin washe bakin
shi yace:

"Laa ashe basu tafi da itan ba"

Dada da iya kulu suka tuntsure da dariya, Abu dake bayanshi, saboda ya biyoshi yaji me ya
firgitashi acikin bacci, jin abunda yake fad'a ayanzu shiyasa yaji haushin sa, don shi sam
yarinyar batayi masa ba, ba shiri ya buga tsaki yabar d'akin, Dada ta gallawa k'ofar da ya fita
harara tace:

"Kai kam duk wanda yaga girmanka sai yaga fad'in rai, bak'in hali k'arara tun kana d'an k'aramin
ka to ina ya ka girma?, Allah dai ya shiryeka amman kam akwai aiki"

Iya kulu ta b'ata fuska tace:

"Zai daina ne ai"

Dada ta kalleta tareda yimata wani kallon reni tace:

"Daman aike baki so aga laifin d'anki, kuma dole ne a nuna masa kuskurensa ko don gobe ya
gyara, don in har aka barshi da tarbiyar ki, kece zaki kwana aciki inya girma, donmu alokacin
ma bamu araye bale muga kayan takaici"

Iya kulu ta zunb'uro baki ta fitowarta, Dada tace:

"Ai komi da Abu yakeyi gado yayi awurinki, bai yar ak'as ba, don haka daga ke har shi Ubangiji
Allah ya shirye ku"

Bayan sun karya ne suka fara shirin zuwa gidan mai unguwa domin ahad'a su wad'anda zasuyi
masu jagora zuwa birnin, aiko daga zuwan su ba wani tsaiko daman su kawai ake jira suka lula
sai asibitin birni.

Bayan duk wasu gwaje gwaje da akayiwa izzatu an tabbatar batada matsalar komi, amman sun
rubuto mata magungunan da za'a rik'a bata tanasha, masu inganta jiki, sannan an fad'a masu
madarar da zasu dinga bata wacce take d'auke da wasu sinadaran da nono yake d'auke dashi.

Malam ya nemi alfarmar wata nurse da ta rakashi yaje yayi ma izzatu siyayyar abubuwan da
zata buk'ata, aiko ba musu ta d'auki excuse suka garzaya sai wani babban shago, nurse
d'innan ta zage damtse tayita lodowa izzatu kaya, tun daga b'angaren sutura da pampas, da
madara hatta kayan wasa idan ta k'ara girma duk saida ta d'auko, malam dai iyakacin shi ido,
duk da yana da 'yar wayewarsh dai dai gwargwado, amman kam wasu kayan ko ganinsu bai
tab'a yi ba balle yasan me akeyi dasu.

Bayan sun gama siyayyar ne, nurse d'in tayi masa bayanin duk wani abu da ya shige masa a
duhu, malam yaji dad'i sosai yayi mata godiya, sannan suka dawo inda su Dada suke jiransu,
ganin uwar siyayya ledaodi manya manya ya saka Dada tambayar malam akan cewa "duk me
ya siyo har haka?".
Malam yace: "Ta jira idan sunje gida zai yimata bayani"

Nurse d'innan tayi masu sallama zata tafi, Dada tace da ita:

"Dawo 'yar nan, kigayamuna sunanki, ko don mu k'ara yimaki godiyar irin wannan hidima hk"

Ta dawo tana murmushi tace:

"Suna na Aisha"

Dada tayi murmushi ta fara yiwa nurse Aisha wak'a tace:

"Sannunki shatu shatulle, indo A'i farar d'iya, baki aure k'auye kisha wuya, daga birni sai
babban gari, sai ko wani babban malami, koko wani babban attajiri"



Indo an wasu🤣🤣🤣



Akafta�





D/Auta ce👌🏻

مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*

*⛈RUWA DA KANKARA�*


*NA HADIZA D/AUTA*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*PAGE EIGHT*

********************

Aiko BA shiri nurse Aisha ta washe baki har kunne, saboda taji dad'in wak'ar da Dada tayi mata,
aiko ta samu wuri ta zauna sai fira ta b'alle atsakaninta da Dada,har zuwa lokacin da izzatu ta
fara kukan neman abinci, Dada ta kalli Aisha tace:

"Na shigesu ni mairo, ko ina zan sami nonon akuya inbaiwa wannan yarinya?"

Aisha ta zaro ido awaje tace:

"Nonon meye?"

Dada acikin tabbatarw tace da ita:

"Nonon Akuyoyi"

Aisha tayi murmushi tace:

"Jirani minti biyu inzo"

Aiko saigata ta dawo da Flack's na ruwan zafi da cup da spoon ta ajiye agaban Dada, sannan
ta bud'a ledodin siyayyar ta fiddo da gwangwanin madara d'aya don guda uku aka siye, saboda
tazarar dake tsakanin k'auyen SU da garin.

Sannan ta fiddo fida babba taje ta wanko ta tas, sannan ta zuba madarar akofi ta tsiyaya ruwan
zafi dai dai madarar ta jujjuya,har saida ta hade gaba d'aya, sannan ta juye madarar afida ta
rufe.

Dada dai da sauran wad'anda ke wurin, sai binta da kallo sukeyi, acikin mamaki dada tace:

"Yanzu shikenan za'a iya bata tasha ahaka ba sai in dafa awuta ba?"

Aisha tayi 'yar dariya tace:

"Haka akeyi akullum idan za'a bata yanzu ad'an jira ta rage zafi sai abata"

Aiko farin ciki ya wadatu afuskokin su gaba d'aya, musamman Dada da malam da suka if kowa
shiga damuwa akan kukan da izzatun takeyi, suna tunanin yanda zasuyi, saiga mafita
asauk'ak'e Allah ya kawo masu.

Aiko saboda kukan da izzatun takeyi, Aishar ta d'ebo ruwan sanyi akofi ta jefa fidar madarar

tana juyawa, minti k'alilan madarar ta huce aka bata sai zuk'a takeyi, kamar ta saba sha, kafin
kace me har ta shanye fidar gaba d'aya, sannan tayi gyatsa sai bacci.

dukansu sunyi mamakin madarar da tasha, shiyasa aka sake kad'a mata wata madarar, koda
zata falko kafin suje gida.

Sukayiwa Aishar godiya sosai sannan suka mik'e zasu koma k'auyen su, anan ne Aishar take
tambayar a'ina suke, dada tayi mata bayanin sunan k'auyen da suke zaune, nurse Aisha tayi
mata alk'awali duk lokacin da ta sami dama zataje har k'auyen ta dubo izzatu, saboda yarinyar
ta shiga ranta sosai ta burgeta.
Dada taji dad'i sosai tayi ta yimata adduar gamawa lafiya,aiko da ita Aishar aka sakawa su
Dada kayan su amota, daga nan sukayi sallama, akan sai watarana, suka rabu acikin kewar
juna.

Tafiyar da bata gaza minti arba'in ba itace ta kawo su d'an k'aramin k'auyen su, kai tsaye aka
wuce dasu Dada har gidan mai unguwa, bayan sun k'are yimasa bayani abunda ya wakana
acen asibiti, suka nuna masa siyayyar da akayowa izzatu, ya jinjina masu sosai tareda saka
albarka acikin duk wani nufi nasu na alkhairi akan jinjira marainiyar Allah izzatu.
Bayan sun k'are ne mai unguwa ya saka aka jidi kayan nik'i nik'i aka kai masu gida tun kafin su
K'arasa agidan.

Suna shiga suka iske Iya kulu tayi fillah fillah da kayan ak'ofar d'akinta sai kallo takeyi, inta duba
wannan at ajiye ta d'auko wani har takai kan gwangwayen madarar da aka siyowa izzatu, ta
d'aga gwangwanin tana kallo sai jujjuyashi takeyi, saboda tana son ta k'ara tantance shin miye
aciki, ta girgiza taji k'arar garin madarar dake aciki yana sukuf sukuf, batareda tunanin komi ba
ta saka hannu ta b'alle murfin, saiga wannan 'yar silbar takarda dake rufe da bakin gwangwanin.

Ba shiri ta b'urmama farcen ta atsakiya aiko sutuf ya fad'a kasancewar akaifarta da take da
itace tayi saurin walshe takardar, aiko bata tsaya wata wata ba ta yage takardar gaba d'aya ta
jefar, ta saka hannu ta kwaso madarar ta kai abaki zata afka saiga sallamar Dada da Malam
sun shigo, aiko ba shiri ta guma madarar, sannan ta jawo murfin gwangwanin ta rufe tana
k'ok'arin maida kayan acikin ledodin.

Baki asake Dada ta bi iya kulu da kallo, saboda gaskiyar ma taxi mata yawa, malam kam
k'arasowa yayi ya dinga tama ta suna maida kayan, Dada saboda haushi kasa magana tayi ta
shigewarta d'akinta.

Malam yana ganin shigewar Dada, iya kulu ta kawo hannu zata d'auki wani tissue ta mayar
leda, da sauri ya bangaje ta, ba shiri ta fad'i ak'asa warwas, aiko madarar dake bakinta ta
dunk'ule mata mak'oshi ta sark'e, ta fara tari ido suka gwalalo awaje sai nuni takeyi da hannu
akan ya taimaka mata da ruwa.

Malam kam yana k'are maida kayan, ya nufi d'akin Dada yabarta anan tana neman agajin abata
ruwa, ya fahimceta kar amma yayi banza da ita ya tafiyarsh, acikin zuciyarshi yana cewa:

"Indai hak'k'i ne to kad'an kika gani"

Da rarrafe taje wurin tukunyar ruwanta, ta kandamo tayi masu muguwar zuk'a aiko saigata da
k'walla k'ara tace:

"Wayyo wuyana!"

Saboda yanda ta had'a ruwan sukayi muk'ut suka fad'a da k'arfi tareda dunk'ululun madarar da
ya tsaya mata amak'oshi, saiga su Garzali sun dawo inda ta aikesu.

Da sauri Garzali ya k'araso idonshi akanta yace:

"Iya lafiya idanunki sukayi ja haka?"

Iya kulu ta had'iye miyau tace:

"Bari kaidai d'an nan, kwad'ayi da dad'i amman akwai wahala idan rana ta b'ace aka rutsa da
mutum"

Sai jin muryar Dada tayi tana fad'in cewa:

"Ai dama ance duk wanda ya hau motar kwad'ayi, to ba inda zata saukeshi sai tashar
wulak'anci, duniya dai ce ta ishi kowa riga da wando, wanda bai zo bama jiranshi takeyi"

Iya kulu tayi sum sum ta fad'a d'akinta, saboda ita kanta bata ji dad'in riskarta da akayi ba,
amman dai kam taji dad'in madarar ba kad'an ba, shiyasa afili ta furta cewa:

"Anji kunya ansha dad'i"





Tofa😹😹



Akafta�

D/Auta ce👌🏻

[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*PAGE NINE*


**********************

Dada ta k'walla mata kira, sai ga iya kulu ta fito jiki ba kuzari, don tasan yau kam ta jawo wa
kanta jangwam, Dada ta galla mata harara tace:

"Duk da kinga kayan tun kafin a nuna maki, amman kizo ki k'ara gani saboda bayanin da ayuba
yake yimani akan yanda za'ayi amfani da kayan ne ya rikice ni, nace bari in kiraki kizo kiji kema
don k'ila ke kifini ganewa, don nikam ba duka na fahimta ba"

Garzali yana k'yalla ido yaga Dada, aiko sai gashi da jin wani farin ciki ya mamaye sa bakinshi
yana rawa yace:

"Laa ashe kun dawo Dada?, ina izzatun?"

Dada tayi masa nuni da hannunta, sannan tafara tafiya domin ta koma d'akinta, wanda kafin ta
isa har Garzali ya rigata kaiwa a d'akin.

Iya kulu tana biye dasu a baya ranta fess, don atsamaninta Dada ta mance da abunda ta aikata.

Tana shiga ganin izzatu ahannun malam yana bata madara, ga Garzali da ya kasa ya tsare
yana rik'e da hannunta, yana kallon yanda take zuk'ar madara a lokaci d'aya taji wani b'acin rai
ya ziyarceta, batasan lokacin da tayi tsaki azuci ba, saboda jin takaicin wannan rawar k'afar da
sukeyi da jaririyar, sai kace malam shine yayi silar kawota a duniyar.
Dada ta dinga nuna mata, malam sai bayani yakeyi dallah dallah kamar yanda nurse Aisha tayi
masa bayani, iya kulu sai gyad'a kai takeyi, tamkar wata k'adangaruwa.

Bayan malam ya k'are bayanin ne iya kulu ta kalli tulin kayan ta kalli izzatu, sannan tace:

"Yanzu duk wad'annan tulin kayan na wannan jinjirar yarinyar ne?"

Dada ta harare ta sannan tace:

"To ai kud'in ta ne ba ko k'wandalar mu aciki, saboda haka idan kina da kud'in kema ki kawo,
sai gobe aje ayo maki siyayyar da tafi ta jinjirar"

Iya kulu tab'ata fuska tace :

"To ai abun bai kai cen ba, ki gafarceni"

Dada tace:

"Madarar fa itama bazaki siye irinta ba?, ki dinga cika hannu kina afkawa abaki, tunda nasan
kinji dad'in ta"

Aiko iya kulu sai ido suka rena fata, don tasan Dada tsaf da bugun gorar ta, shiyasa ta fita
d'akin salun alun batared ta koma cewa k'anzil ba.

Amman fa abun nasu ya fara b'ata mata rai gaskiya, saiga sallamar kande mak'ociyar ta, ta
karad'e gidan gaba d'aya, saboda kande mace ce mai d'aga murya idan zatayi magana,
batasan ta sassafta halshenta ba yayin magana, duk inda take muryarta ce zata sanar da
zuwanta.
Tana zuwa tayiwa kanta mazauni, ta hanyar janyo kujera 'yar tsugunno ta zauna, idanunta
akan iya kulu acikin mamakin ganin yanayinta tace:

"Kefa lafiya?, ko keda Dadar taki ne, yau ma kuka hau sama?"

Iya kulu tayi mere tace:

"Ke ko wata tsintacciyar mage ce aka tsinto aka kawo muna acikin gida"

Kande ta dafe baki tace:

"Ashe dai zancen da nakeji yana ta yamad'd'i agari gaskiya ne?"

Iya kulu tayi mata wani kallo tace:

"To yanzu kinji dimun ai jiya aka tsinto ta anata zuba ruwa da k'ank'ara, yanzu haka an saka
mata sunan izzatuna"

Kande tace:

"Lalle wagga 'ya ta zama 'yar gaban goshin, a'i da anbarta da sunan ta na yanka RUWA DA
KANKARA, don shine yafi dacewa da d'iyan shegun da ake haifa ana yardawa"

Iya kulu ta zaro ido awaje tace:

"Rufawa kanki asiri kar Dada ta jiyoki, ance fa ba shegiya bace da ubanta"

Acikin mamaki kande tace:

"To ku taya kukasan ba shegiya bace ba?, to kenan kunsan iyayenta ko?"

Iya kulu tace:

"Acikin takardar da aka tsince ta atare da ita ne aka rubuta, cewa ba shegiyabace"

Kande ta mere baki tace:

"Kuma ku har kun amince?, cab da sauran ku wallahi, yanzu harda shi malam yanzu ya gasgata
wannan shirmen?, to bari kiji koda shegiyar ce da gaske baza'a fad'a arubuce ace itace ba, don
idan ba hakan ba me zaisa a jefar da ita haka kawai?"

Iya kulu tayi tagumi, tareda zurfafawa azurfin tunani, musamman da ta tuno da kud'in da aka
sako acikin kwalin, aiko anan take zuciyar ta ta gasgata zancen kande, wani sabon b'acin rai ya
ziyarceta, fuska ahad'e tace:

"Indai da gaske shegiyar ce, to wallahi ban yafewa hidimta mata da nayi ba, kuma da sannu sai
nayi sanadin da zata bar gidan nan, tunda ba da kud'in ubanta ne aka ginashi ba"

Kwatsam sukaji maganar Dada asaman kansu tana cewa:

Inajin ai kema da kike zaune agidan bada kud'in naki uban aka ginashi ba, balle kiyi ik'irarin fitar
da wata a gidan"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login