Showing 63001 words to 66000 words out of 119425 words
Chapter 22 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
misalta farin cikin da na shiga ba a daliin samun wannan yarinya da nayi, nayi
mata hud'uba da sunan mahaifiyata waton NANA AISHA.
'Yan uwa da abokan arzik'i sai murna suke taya ni, akan wannan haihuwar da hadizatou tayi
man, kwana hud'u da haihuwa muka shiga a cikin tashin hankalin da a rayuwa ta kaf inbanda
rashin iyaye da nayi, ban tab'a shiga irin shi ba, wannan tashin hankalin ba komi bane illah,
b'acewar da jaririyar 'yata tayi, yarinyar da nike jin a lokacin babu wani abun halitta da nike so
sama da ita.
Gidan Radio gidan television jaridu babu inda bamu je ba wajen cigiyar wannan yarinya amma
shiru kamar an shuka dusa,na saka malammai sunyi ta addu'o'i akan Allah ya bayyana muna
kuma ya tsare muna ita aduk inda take, tun muna sa ran zamu ganta har muka cire, amma a
kullum muna tunanin 'yarmu a cikin zuciyoyinmu.
A lokacin ganin damuwar da bintu ta shiga sosai a sanadiyyar b'atan wannan 'ya, yasa na nemo
d'aya daga cikin yaran wannan babban yayanmu wato ALHAJI SANI BADAWI mai suna
SHU'AIB akan ya dawo hannun bintu da zama koda zai rage mata wannan damuwa da saka
aranta, a lokacin yana da shekara takwas zuwa tara, sannan na bata hak'uri akan ta yafe man
duk abunda nayi mata, saboda ina zargin hak'k'in ta ne ya bibiyeni yasa na rasa 'yata da na
kwallafa rai akanta, daga nan na tattaro ta gaba d'aya na kawota wannan sabon gidan na had'e
ta ita da hadizatou, kasanceawar bintu mai sanyin hali hadizatou ma mace ce mai dad'in zama
ga biyayya, sai suka hada kansu a wuri d'aya suka yi zamansu lafiya, a cikin wannan lokacin
ne ko shekara ba'a rufa ba hadizatou ta sake samun wani cikin, daga NI har bintu muka dinga
tattalin ta da yaron cikinta har ubangiji yasa ta haifo 'yanbiyu duk maza, aka saka masu sunan
SUDEIS DA SADIS, wannan haifuwar da muka samu itace ta d'an rage muna zafin rad'ad'in
rashin 'yarmu ta farko da mukayi.
Wanda a lokacin ne itama bintu ta sami nata cikin amma watan shi uku ya zube, ta k'ara samun
wani har ta haifu amman abun baizo da rai ba,daga nan ciki hud'u tana samu yana zubewa, har
daga karshe ma haihuwar tazo ta tsaya cak!,
Hadizatou ko bayan haifuwar sudeis da sadis, ta kara haifo fahat daga nan sai Ammar.
Hadizatou haifuwar ce kawai takeyi amma duk wani hidima da renon yaran bintu ce take yi, da
zuciya d'aya take k'aunar wad'annan yara, domin kulawar da take basu ita kanta hadizatoun da
ta haifesu bata basu, hidimarsu gabaki daya bintu ce takeyi ba gajiyawa, a yanzu haka sudes
da sadis a hannunta suke tun suna kanana har izuwa yanzu da suka girma suna Sudan suna
karatun secondary.
To kunji tarihin abunda na sani dangane da rayuwar zamantakewa ta nida matana, amman
bansan su waye suka sace muna 'ya ba, sai dai ga dukkan alamu bintu tana da wata
b'oyayyiyen sirrin da take boye muna, tawon shekara da shekaru, wannda nike zargin bazai
rasa nasaba da b'atan wannan yarinya ba, bintu ki fito fii kiyi muna bayanin abunda ke damun
zuciyarki tsawon wanda yake saka ki shiga damuwa, asanadin shi har kinsa lafiyarki tayi
karanci, don Allah ki fad'a muna ko don ki saukewa kanki nauyin da kika d'orawa kanki, nayi
maki alk'awali ko ma minene a shirye nike da inyafe maki shi, duk ko iya girman laifin da kike
ganin kinyi mani, domin nasan sharri ba halinki bane sai dai in sharrin shed'an da bawa baya
iya tsallake shi, matuk'ar ba ubangiji ne ya tseratar dashi ba, domin jikina yana bani kina da
hannu a b'atan 'yata NANA AISHA (izzatu)."
Tofa hajiya fatima gareki
Akafta
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE FORTY SIX*
**********************
Ba shiri izzatu ta zaro ido a waje tana k'ok'arin yin magana ne, caraf idanuwanta suka had'u da
na Ammi, ta gano gargad'iin da Ammin take yimata da idanuwa ba shiri tayi gum, amman fa
gabanta sai dakan lugude yakeyi, sai k'iyasta kalar wulak'ancin da zata yiwa shu'aib takeyi a
cikin zuciyarta.
Garzali ma jin wannan furuci na yayan Gwamna ya saka shi shiga tashin hankali ba kad'an ba,
a lokaci d'aya yaji wani zazzab'i yana so ya rufe shi, jiki ba kuzari ya tashi tsam ya bar falon,
wanda fitar da yayi ya k'ara jefa mama da malam a cikin sabuwar damuwa, bayan ta wannan
d'anyan hukuncin da wannan dattijon ya yanke.
Iya kulu kam daman tasa a ranta yanzu izzatu tafi k'arfin Garzali, shiyasa bata ji haushi ba don
tasan ko giyar wake Gwamna yasha ba zai aurawa Garzali 'yar shi ba.
Shu'aib kuwa shi kanshi k'irjin shi sai da ya buga, saboda jin wannan hukunci da Abbanshi ya
yanke, domin shi yasan dalilin da yasa Abban yayi wannan azarb'ab'in, amman shi da za'a bar
wannan had'in da yaji dad'i, saboda shi har a lokacin baya jin yarinyar tana wani burgeshi,
saboda kallon 'yar k'auyen da yake YI mata har lokacin.
Mai girma Gwamna a zahiri ya nuna farin cikin shi, amman a zuciyarshi bai so yayan shi ya
yanke wannan hukuncin ba, musamman fuskokin su malam da ya gani jamar suma basu in
dad'i ba, yaso ace har sai izzatun ta zauna dasu na d'an lokaci koda ALLAH zai sa su fahimci
junansu da shu'aib din, amman tunda yayan ya riga da ya tanke hukuncin ba yanda zaiyi sai
hak'uri kawai, don baya son yayi abunda yayan zai ga kamar don shine ya haifeta.
Daga nan dukansu suka k'ara yiwa su malam godiya akan d'awainiyar da suka yi da izzatu,
bayan sun k'are godiyar ne izzatu ta kira sunan da taji, hajiya fatima ta kira mai girma Gwamna
dashi wato Abbaah tace, "Don ALLAH ina neman wata alfarma."
A cikin sakin fuska Abbaah'n yace, "Ina jinki 'yata fad'i koma menene matuk'ar bai first karfina
ba insha Allah NI mai biya maki da duk bukatocin da kika nema a fad'in duniyar nan gaba daya
matuk'ar ba sab'on ALLAH bane."
Izzatu taji dad'in wannan furuci na Abbaah, bakinta yana rawa tace, "Alk'awalin makarantar da
kayi man, ina son yaya Garza ya maye gurbi na yaje a madadina."
Abbaah yana murmushi yace, "Kinyi tunani mai kyau kuma naji dad'i sosai insha Allahu zuwa
k'arshen shekarar nan za'a fara yimasa process d'in zuwa makarantar UNIVERSITY LONDON,
fatar mu kawai Allah ya bada abunda za'a je nema."
Izzatu tana jin wani tsantsar farin ciki yana ratsa ta, ganin gata ga mahaifanta tana fira dasu, a
cikin murmushi mai sauti tace, "Kujerar makkah'r ma da kace ka biyaman itama na baiwa
malam yaje a madadina."
Abbaah yayi murmushi mai sauti yace, "Ba malam kad'ai ba duk wanda kike so a biyawa,
za'a biya masa acikin dukiyarki saboda ki sami ladar kema, don haka ki zab'i duk wanda kike so
wannan ba matsala bane, sannan dangane da zamansu a cen k'auyen idan ba damuwa za'a
siya masu gida a nan garin, sai suci gaba da zamansu a kusa damu."
Gaba ki d'aya falon ya runtume da kabbarar su malam, iya kulu harda mintsinin kanta domin
tana so ta tabbatar, shin mafalkin da ta saba YI ne na tayi kud'i ko kuwa a falke ne da gaske?,
tana jin zafi ta yardarwa zuciyarta ba mafalki bane, jikinta yana b'ari ta tashi ta fara dannawa
Abbaah kirari, gaba d'aya falon ita ake saurare har sai da mama ta jawo zanenta, da taxi zai
sunb'ule ne ba shiri ta zauna amman bakinta bai fasa zubawa Abbaah da su hajiya fatima kirari
ba, har sai da Abbaah ya dakatar da ita sannan tayi shiru.
Sabda jin haushin da yayan Abbaah yayi a tsaitsaye yayi sallama dasu ya fito, fuskarshi a
cunkushe ya fita yana d'agawa direbansa hannu akan yazo su tafi ne ya hango Garzali a zaune
yana latsar waya, a fusace tayi tattaki zuwa wurin shi a cikin sassafta murya tamkar munafuki
yace dashi, "D'an samari a fahimtar ka da nayi kaima son auren izzatu kake yi ko?, to bari in
sanar dakai izzatu tafi k'arfin d'an k'auye irinka talaka fak'iri me zatayi dakai, idan ba kana son
ka yaudari kanka ba sawunka a likkafa ka cire wannan tunani a ranka, in kuma dukiyar da kaji
ance an bata ne kake kwad'ayi, to shafawa kanka ruwan sanyi tun kafin inyi sanadin da zaka
k'are rayuwarka a gidan yari, dubara ta rage taka ka shafawa kanka lafiya ko ka jefa rayuwarka
a cikin had'ari."
Yana k'are maganganunsa masu busar sarewa a kunnuwan Garzali, ya juya fara taku zai bar
wajen, Garzali ya d'aga muryarsa a sama yace, "Samu da rashi duk na ALLAH ne, haka
rabon kwad'o baya fad'uwa k'asa banza, haka zalika duk nisan dare tabbas gari zai waye, haka
ma dogara ga ALLAH jari ce, nayi imani duk abunda ya sameni daman cen an rubuta bazan
tsallake ba, son izzatu kuma ko shafin farko ban bud'a ba, kaje duk abunda kaji zaka iya kayi
kawai amma kar ka manta cewa, karya fure take bata 'ya'ya, ni murucin kan dutse ne ban fito ba
sai da na shirya, don haka sara da sassak'a sam baya hana Gamji toho."
Ba shiri dattijon ya waigo saboda kalaman bazatan da yaji, suna fitowa a bakin d'an k'auyen da
ya rena, a cikin kad'uwa da maganganun da Garzali yayi masa yace, "Da ni da kai sai anga
wanda zai yin nasara."
Yana k'are fad'ar haka ya juya ya shige mota yana huci, direban shi ya ja motar suka bar gidan,
garzali yabi motar da kallo a cikin mamaki, tareda furzar da wani iska mai zafi a bakinshi,
sannan ya kaiwa iska naushi yace, "Ni da ku shege kan fasa."
A cen falon kuwa an yanke shawarar mai unguwa ne kawai zai koma k'auyen, saboda nauyin
mutanen gari da yake kanshi, su ko su malam zasu kwana anan sai da safe su koma k'auyen
su tattara abunda suke so kafin a tanadar masu da muhallin da zasu zauna, daga nan taron ya
watse su mama da iya kulu suka koma masaukinsu, izzatu ma tabi hajiya fatima zuwa
sashenta.
Koda malam ya fito yiwa su mai unguwa sallama, yaci karo d'a Garzali fuskarshi a cunkushe, a
cikin sakin fuska ya nuna masa yazo su yiwa mai unguwa sallama, mai unguwa ya tafi tareda
direbanshi da rakiyar wasu security's har k'auyen, bayan uban alkhairin da mai girma Gwamna
yayi masa, suka rabu kowa yana farinciki.
Daga nan malam yaja Garzali suka koma masaukinsu, yana ta bashi hak'uri akan hukuncin da
aka yanke, Garzali kam sauraren malam kawai yakeyi amman zuciyar shi a k'ek'yashe take,
domin shi yasa a ranshi ruwa da iska ba wanda ya isa ya hanashi auren izzatu, matuk'ar ba
itace tace bata yin auren dashi ba, shiyasa yayi shiru bai fad'awa malam komi ba, don baya son
ya d'aga mashi hankali, domin yasan muddin malam yaji zai tilasta shi ne akan ya hak'ura da
izzatun, a haka ya biye malam suna ta firar su, kamar ba wani abu dake damunshi.
Izzatu kam tana a part d'in hajiya fatima tana kwance akan kujera, hajiya fatima tazo ta zauna
tareda d'ora kan izzatu, a saman cinyarta tana k'ara rok'arta da ta yafe mata rabata da iyayenta
da tayi, izzatu tace, "Haba Ammah ni wallahi tuni na yafe maki, don ke kanki ba da son ranki
kika aikata ba, tunzuraki ne akayi kika rama abund aka YI maki, ni wallahi ko kad'an bana jin
komi a zuciyata sai farinciki da Allah ya had'a NI daku a matsayin iyayena na gaskiya,duk da ko
da baku ni nasan bazanyi maraicin iyaye ba, don malam da mama sun yimani rik'on gaskiya da
amana, haka ma yaya garzanah!."
Ammah tayi saurin zaro idanuwa tana murmushi tace, "Anya 'yar Ammah ko ba wani abu a
tsakaninta da yayan nan?."
Izzatu tayi saurin rufe fuska tana murmushi, shigowar shu'aib shine ya hana ta fad'in abunda
tayi niyya, ba shiri ta tashi a zaune tareda galla masa wata gwarzuwar harara a fakaice, shi kam
yana ganin suna wannan annushuwa da Ammah, yaji wani bak'in ciki ya tokare masa zuciya,
ba shiri ya juya zai bar wurin amma ta kirashi ya dawo fuska ba walwala, amma ta kalkeshi a
cikin mamakin wannan fushi da yakeyi tace, "Ba zaka tsaya ka karb'i sak'on ba?."
Sannan ya sosa kai yace, "shi nazo karb'a bani na wuce sauri nikeyi inje in dawo akwai inda
zanje."
Amma ta tashi ta shige da nufin d'auko masa sak'on, ya gallawa izzatu wata harara, izzatu ta
tashi tsaye tayi wani taku biyu zuwa uku ta k'araso a gabanshi a hankali tace, "Ya kaga 'yar
k'auye a gidan Gwamna?."
Akafta ♀️
D/Auta ce⛹♀️
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Yawan comment's yawan typing*
*PAGE FORTY EIGHT*
*********************
IZZATU tayi kyau abinta gwanin sha'awa, kyaunta ya k'ara fitowa komi dake bayyana a jikin
cikakkiyar budurwa, to yaji a jikinta masha Allah, gata da faffad'an kunkuru mai d'aukar hankalin
duk wani lafiyayyen d'a namiji, ga na shanunta b'ul b'ul cike da k'irjinta, gashinta acike kaf da
kanta bak'i k'irin sai shek'i yakeyi saboda sulb'in shi, tsawonshi kuwa idan ta sake shi har
tsakiyar bayanta, gata fara tas har da surkin jajaja, ga da hanci tamkar bir tsawonshi, yayi
daidai da 'yar faffad'ar fuskarta, ga d'an karami baki daidai kiss, ga manyan idanuwa farare tas
tamkar madara, izzatu ta had'u ta inda duk mace ake so takai.
musanmman yanzu da kyawon ya had'u da hutu da gyara abun sai wanda ya gani, ruwan
k'auye sun fara bacewa a jikinta, saboda hajiya fatima tayi tsaye tsayin daka wajen maida ta
mace ta kowane FANNI.
Wanka ma sau hud'u take yinshi a wuni kuma ko wane wankan da kalar dress d'in da ake yi
masa, izzatu ta zama 'yar gayu ta bugawa a jarida ayi talla, wadda idan ka ganta a yanzu
bazaka tab'a cewa ta tab'a rayuwa a k'auye ba, kasanceawar daman cen ita ba rayuwa irinta
'yan k'auyen take yi ba, saboda mama hassatu tayi tsayin daka sosai , wajen maida ta daban
da sauran 'yanmatan dake cikin k'auyen.
Rayuwa mai cike da jin dad'i malam yake shinfid'awa da matanshi, musamman mama hassatu
da ta goge ta zama wata babbar hajiya acikin wata d'ayan da suka dawo a birni, idan ta cab'a
kwalliya bazaka ce itace hassatun da ka sani ba, sabida daman cen mama hassatu 'yar gayu ce
lokacin da tayi zama a birni, ilham ma gyara take sha sosai tamkar d'iyar wasu hamshak'ai,
saboda siyayyar da izzatu tayi mata kaya ne naji da fad'i.
Iya kulu ma anfara murjewa sai wani jiji da kai akeyi, kasancewar itama ba baya ba wajen son
taga tayi abunda zata burge mutane, domin kuwa idan tayi wanka dole ne ta shiga motar da
izzatu ta siya saboda zirga zirgar hidimar gidan idan ta kama, aiko da ita take sa ana fita da ita
ayitaa zagayen gari tana kalle kalle, wani wajen ma idan ta gani sai an tsaya ta fita taje ta d'ebe
k'eyar idanuwa, iya kulu a yanzu bata da wata damuwa sai ta Abu, da ya riga ya fand'are ta
b'angaren shaye shaye da neman mata, musamman yanzu da suka dawo birni abun nashi sai
gaba gaba yakeyi, malam yaso ya taka masa burki amma ina Abu kam ya riga yayi nisa, domin
kuwa baya jin shayin yiwa malam bak'ar magana, iya kulu kam har kamar ya doke ta yakeyi
idan tayi masa fad'a, 'yan kud'inta idan ta ajiye yabi ya sace kuma bata da ikon yin magana.
Izzatu ta saya wa malam tashi mota daban, sannan ta kawo mak'udan kud'i tace dashi yaja
jari, kasancewar malam mutum ne mai zafin nema, shiyasa kasuwanci a birni yayi masa dad'i,
domin kuwa a kullum kanshi k'ara wayewa yakeyi akan maida kwabo ya koma sisi, ya jawo Abu
a harkar kasuwancin domin ya shiga su dinga fafatawa a tare, saboda ya rage biye abokan
banzan da ya k'ara samu a birnin, amma ko sati baiyi da fara zuwa ba ya janyo wa malam,
rigimar da tasa ya dakatar dashi da zuwa kasuwar, saboda wani shagon dake mak'otaka da
shagon malam d'in ne yaje, ya fakaici idanuwan mai tsaron shagon ya kwashi kud'i masu
yawa, ashe wani ya ganshi aiko rikici ya tashi, da akayi bincike aka gano tsawon kwana uku
yana d'aukar kud'in batareda an gano shi ba, aiko da akayi lissafin abunda babu dole malam ne
ya biya kud'in, to tun daga ranar yace dashi kada ya koma ganin k'afar shi a cikin kasuwar.
Mama hassatu taje har k'auyensu ta rok'i alfarma a wurin mijin inna hure, akan ya bata Amina
tazo da ita birnin koda Allah zaisa mijinta anan yake, saboda har lokacin Aminar bata yi aure ba,
domin duk mijin da ya fito sai tace bata sonshi, har baban yayi zuciya yace