Showing 18001 words to 21000 words out of 119425 words

Chapter 7 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

hassatu ba riba bane a wurinta.

Sau biyu hassatu tana gaidata, amma batasan tana yi ba, har sai da malam ya kira sunanta da
k'arfi, sannan ta zabura a cikin d'imaucewa tace:

"Itace ko, wallahi itace!"

Malam da hassatu suka bita da kallo, a cikin mamaki, kallon da taga suna biyart da shine yasa
hankalinta da ya b'ace na wuccin gadi, ya dawo ya shigeta, ta gyara zama ta natsu da kyau
fara kumbure kumbure tana shan k'amshi.

Malam yace:

"Bakiji amarya tana gaidaki ba?"

Iya kulu b'acin ranta da tsantsar kishinta,ya k'ara hauhawa acikin fushi tace:

"Banji ba, daman akan in saurari gaisuwarta ne, kace inzo zamuyi magana, to bani buk'ata ta
adana gaisuwarta wa mai so"

Malam ya gyara zaman shi da kyau,acikin jarumta irinta mazajen k'warai yace:

"A jiye wannan zance naki, muyi maganar da ta taramu a nan, daman ba komi bane yasa na
had'a ku, saboda ina son ku had'a kanku kuyi zamanku lafiya, ku tsara yanda zamanku zai
kasance, insha Allahu zan kasance mai adalci a tsakaninku"

Iya kulu tayi wani mere sannan ta mik'e a tsaye ta rik'e kunkuru, sanna ta k'are masu kallon uku
saura kwata tace:

"Kwaji da munafuccinku dai daga kai har ita, kuje ku fad'awa 'yan kaji, wad'anga 'yan zabbi ne,
a dalci wane kala kake kira?, kana adalci kayi mata d'aki biyu ka had'e mata ni ka barni da d'aki
d'aya k'wallin k'wal, sannan ka dawo ka dinga karanta man karatun bayan littafi"

Malam kam wata damuwa ta ziyarceshi, saboda yaji zafin kiranshi da iya kulu tayi munafuki,
amman ya share don kar ta b'ata masa daren farin cikinsa, yace:

"Ita ta bada kud'inta aka gina mata wani d'akin, kema idan kinaso ko yanzu bata b'aci ba, sai ki
kawo naki kud'in gobe a fara yimaki aikin"

Iya kulu ta d'age d'ankwali ta juya baya tace:

"Fad'awa k'eya"

Ran malam yayi k'ololuwar b'aci, hassatu tana ganin yanayin da ya shiga, a cikin wayancewa
taje ta fad'a a jikinshi ta fara yimasa tafiyar tsutsa da hannunta, ba shiri ya dawo da hankalinshi
akanta,ta sunbace shi, sannan ta kirashi da wata murya, mai d'auke da aika sak'on abunda
akeso a wurin wanda ake yiwa ita, sannan tace dashi:
"Nifa Alhajina bacci nikeji"

Aiko malam ya rud'e gaba d'aya, ya d'imauce suka fara musayar kalamai tareda aikawa juna
sak'onni, sun manta shaf da iya kulu tana d'akin, sukam sai b'arje gumin soyayyarsu sukeyi.

Iya kulu tajira taji bala'in da malam zaiyi, don tasan ta kunno shi da yawa, amman taji shiru,
juyawar da zatayi idanunta sukayi mata mugun gani, domin kuwa sun fita hayyacinsu, sai
neman hanyar da zasu gamsar da juna sukeyi, da sauri iya kulu ta dafe kunnuwa ta kurma
kuwwa, ba shiri suka dawo hayyacinsu, aiko iya kulu ta kasa juyawa a million ta fara gudu zata
fito a d'akin, malam ya d'aga murya yace:

"Idan kin fita ki rufo muna d'akin"




Wayyo Allah iya kulu nidai kar ki fad'i kiji ciyo garin gudun�

Akafta





D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*

*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*COMMENT'S DINKU YANA SANI FARIN CIKI BA KADAN BAKUCI GABA
DA RUWAN COMMENT'S MUTANE NA ONE LOVE❤*

*PAGE SAVENTEEN*

**********************

Ba shiri takai zaune, zuciyarta sai bugawa takeyi da sauri da sauri, amman duk da hakanan
tana jin sallamarsu a k'ofar d'akinta, sai da tayi k'arfin halin d'age kai sama tana hurar hanci, ta
amsa sallamar da cewa:

"Ku shigo d'akin ne ai kun kawo, lafiya?, me kukazo nema?"

Aiko suna jin lafazin bakinta, ba shiri suka ja birki a k'ofar d'akin, d'aya daga cikinsu tace:

"Barmu kawai muyi abunda ya kawo mu, ba sai mun shigo ba makullin d'akinmu zaki bamu"

Iya kulu ta taso tazo bakin k'ofar d'akin, tana k'are masu kallo sama da k'asa, sannan tace:

"Ku da d'akinku kuma ace ku kasa makullin shi, to kuje gida ku d'auko tunda har kun manta shi
acen"

Tana k'are maganar ta saki labulenta, ta komawarta d'aki, ta barsu anan tsaye, kowace mamaki
fal ranta, sai ga inna hure tazo tana fad'a masu cewa d'akin fa abud'e yake, suzo suje har
sauran 'yan uwansu, sun fara aikin, sannan sukaja k'afafunsu suka isa d'akin, amma zukatansu
kowace da abunda take saka masu.
Suna ta hada hadar jerensu har marece, sai firarsu da dariya sukeyi, inna hure kam bayan ta
kawo masu abincin, ta shige a cikinsu anata aikin, sai shewa sukeyi suna gud'a idan firar tayi
dad'i.

Bayan ank'are jeren ne, wasu suka tafi wasu suka tsaya anan har sai ankawo amarya, inna
hure ta k'ara aza masu wata sabuwar sanwa, wasu 'yan unguwa da abokan arzik'in inna huren
suka taimaka aka dafe abincin bikin ras, sannan suka fara kaiwa dangin amaryar, sannan aka
baiwa 'yan biki masu shigowa, don kuwa abun kamar had'in baki, duk da iya kulu bata gayyaci
kowa ba, amma mutane sai tud'ud'uwar shigowa sukeyi, suna sanyawa auren albarka, inna
hure ta baje abunta sai karb'ar bak'in takeyi tareda sakin fuska, don a d'akin Dada wanda ya
zama nasu Garzali a yanzu, acen ta koma abinta tana hada hada da bak'i masu shigowa.

Iya kulu tana d'aki bak'in cikinta yana cinta, don kuwa duk wadda tsautsayi ya sakata shiga
d'akinta, wai yimata Allah sanya alkhairi, to cin mutunci ne ke rabasu, saboda ta tub'ure sai
zabga hauka take yiwa, 'yan unguwa da dangin babanta masu shiga d'akinta.

Ana yin magriba sai ga 'yan kawo amarya sunzo, gida ya runtume sai murna ake tayi da zuwan
amarya, Amarya ta danno kai sai wani k'amshi ne na jiyo yana tashi ajikinta.

Abun mamaki koda aka shigo da amaryar, ko kallon d'akin iya kulu ba'ayi ba aka shige da
amarya a cikin d'akinta, sai shewa danginta sukeyi suna ta rafka gud'a.

Nidai nayi k'ok'arin kutsawa na fad'a d'akin, ina shiga na k'yalla idanuna na hango, wata
hamshak'iya k'irar matan masu kud'i, mace ce mai jiki, fara,mai kyau, wayayya taci ado irin na
'yan birni, sai shan k'amshi takeyi, na k'ara gwalalo idanuna domin in tabbatar shin itace
amaryar malam, koko matar wani hamshak'i ce a birni,don kuwa naga da tayi murmushi harda
k'yallin hauren makka na hango a bakinta, don wannan kam batayi kama da mutanen k'auyen
ba, sam ma babu mahad'i, to shin nikam taya aka haihu a ragaya??????.

Na kasa samun wanda zai bani wannan amsar☹.

Mutane sai turuwar shiga d'akin sukeyi domin suga wacece amaryar malam, nidai na samu na
fito dak'yar, domin kawai inyi nad'iyar rahoton, abunda ke gudaana a wajen.

Cen naga wasu mata su biyu sun fito daga d'akin amaryar, fuskokinsu d'auke da mamaki fal,
d'aya ta jawo hannun d'ayar da sauri suka fito gidan, suka yada zango a kofar gidan, ni kuma
ina ganin haka, nasan lalle da magana abakin wannan mata mai suffar tsegumi, ba shiri na biyo
bayansu, na samu na mak'ale ajikin k'ofar gidan nasha jinin jikina domin in d'auko maku rahoton
abunda zasu fad'a.

Aiko sai naji mai siffar tsegumin tana cewa:

"Ke wai kinko gane wacece malam ya aura?"

D'ayar tace : "A'a nikam taya zansan wannan zuk'ek'iyar 'yar birnin "

Mai tambayar tace:

"Yanzu kina nufin baki gane hassatun gidan idi mai icce ba?"

Wadda ake ba labarin ta zaro ido bakinta yana rawa tace:

"Ki bari don manzo yanzu kina nufin itace wannan mai siffar hajiyoyin?"

Mai bada labarin tayi wata shewa sannan tace:

"Ai ni inbaki labari daman cen, abunda ya kawoni kenan, don in ganar wa idona da gaske
hassatu ce malam ya auro?, lalle soyayya gaskiya ce, tunda har hassatu ta bar 'yan birnin dake
sonta, ta dawo k'auye ta zauna, saboda son Ayuba da takeyi, kinsan fa ita yaso ya aura tun
farko, sai gashi Dada ta lik'a masa 'yar kuluwa, saboda yawon ta zubar d'in da ta tab'a zuwa yi a
birni"

Wadda ake baiwa labarin a cikin jimami tace:

"Yanzu kina nufin 'yan birni sunyi sonta, shine ta yankawa kanta kazar wahala ta dawo a nan
garin ta zauna saboda soyayya?"

Mai bada labarin tace:

"Tabbas ko, don abokan Alhajin da ta aura, sunyi ta zuwa a garinnan da zunduma zunduman
motocinsu, suna neman aurenta, amma tak'i kowa saboda son malam Ayuba da takeyi, to
yanzu dai k'urunk'us kan b'era ta auri Ayuban, gata ga 'yar kuluwa nan sai suyita fafatawa"

Wadda ake ba labarin ta rik'e baki a cikin jin haushin amaryar malam tace:

"Ita yanzu ita ko makkar da akace Alhajin, ya kaita kafin ya rasu bata dubawa, taje taci gaba da
auren alhazawa taci arzik'inta, tafiso ta dawo a nan tashin hankalin 'yar kuluwa ma bazai barta
tayi wani kumari ba, 'yar k'ibar da tayo a birnin ma sai ta zube ta ai, ta koma zubin muciya,
saboda dambacewar da zasu dinga yi a kullum, oni ige arzik'i yana biyarka kana gudu"
Abokiyar firar tayi wani mere tace:

"Zo muje abunmu, tunda tace zata iya had'iye gatari, ai sai arik'e mata b'ota, mu meye namu
aciki?"

Ina lab'e abayan k'ofar gidan, ba shiri wata dariya tazo man nace:

"Nace naku a ciki shine tsegumi"

Bayan tafiyarsu ina k'ok'arin fitowa mab'oyata ne, langa langar dake k'ofar gidan, ya kartoni da
sauri nace wash, na samu na fito zan wuce ya rik'e mani gefen hijabi,ba shiri nace wayyo ni
dije, saboda naji tsoron ya b'arka man shi, jin tsegumi ya jaza man shiga uku, saboda hijabina
ne na sallah da ogana ya saiman ko wankinshi ban tab'a yi ba saboda sonshi da nikeyi, da
dubara na cire hijabin, nayi hamdala da naga baiyi komi ba, sannan na koma cikin gidan domin
inji, shi kuma me zan samu, inga wace wainar ce ake toyawa.



Ashe Malam fashi yayyi




Akafta




D/Auta ce
[8/22, 1:56 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*

*�RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*ALHMDLLH RUWA DA KANKARA YAYI MASOYA YAKAI HAR INDA KO NI BAN TABA
TUNANIN ZAN KAI WAJEN BA SAI GASHI A SANADIYYAR BUK DIN SUNANA YAJE
ALHMDLLH ALLAH ABUN GODIYA NAGODE SOSAI MASOYANA ALLAH YA BAR KAUNA
DUKANKU I LOVE YOU ALL*

*PAGE NINETEEN*

**********************

A sukwane iya kulu ta fad'a d'akinta, idanunta a rufe taci tuntub'e da kwanon k'anzon da ta
karkare a jikin tukunyar abincin da su inna hure suka dafa, tana ganin mutane sun watse ta fito
da sand'a ta karkare k'anzon tayi saurin shigewa d'aki don kar wani ya ganta, amma tana shiga
d'akin loma d'aya da tayi dak'yar ta samu ta had'iye, ta tasa abincin a gaba tana kallo, saboda
halin da take a ciki ma yasa taji bata iya cin abinci, yunwar ma ta tafiyarta ta dangware abincin
nan a tsakiyar d'aki saboda haushin kowa da takeji.

Aiko shigowarta a d'akin ido a rufe, at mance shaf da kwanon abincin dake tsakiyar d'akin, ta
shura shi da k'arfi kwanon har sai da yayi sama,sannan ya dawo, bai tashi fad'awa a ko'ina ba
sai a saman goshinta, yace: "k'wall!!".

Ba shiri ta dafe goshin tace:

"Wayyo ni 'yarkuluwa karuwa zata sa in halaka"

Ta samu gefen gadonta ta zauna, tana murza goshin, zafi biyu da biyu ga na zuciya gana fili,
kafin kace me goshi ya haye, har ya kumbure, aiko bak'in ciki ya k'ara shigarta, musamman da
ta tuno abunda idanunta suka gano, wanda majigin photonsu sai yawo yake a idanunta, ba shiri
ta k'walla kuwwar kiran sunan Dada tace:

"Wayyo Dada, ki dawo kiga cin kashin da Ayuba yake yimani, daman ashe ganin idanunki ne
yake mutumin kirki, Wayyo Dada zan ari bakinki in tsine masu gaba d'ai shida tsohuwar karuwar
shi, subi dare su b'ace b'at a shafe labarinsu, na tsane su na tsani kowa na duniya tunda babu
mai sona sai ke, gashi ke kuma k'asa ta shafe idanunki, wayyo ni kaina zuciyata zata buga idan
ban d'auki matakin gaggawa ba, wallahi duk hanyar da zanbi sai na bita, ko don insami salama
a zuciyata, idan ba haka ba wallahi ina gaf da haukacewa inbi duniya"

Aiko 'yar kuluwa ta fara kuka kashirb'in, har da su gurje gurje, ita kad'ai a cikin d'aki ba wanda
yasan abunda takeyi, har sai da ta gaji don kanta sannan tayi shiru.

Zuciyarta ta kitsa mata ta d'auki matakin kashe izzatu kawai, ko don ta rama cin zarafin da
malam yayi mata, na auro tsohuwar kilaki ya kawo a cikin gidan aurenta.

Aiko a cikin zafin nama ta zabura, taje ta lalabo sharb'eb'iyar wuk'a ta nufi d'akin Dada, inda
dasu Garzali suke kwana akayi dace basu rufe d'akin ba.

Tana zuwa ta baza idanuwa ko'ina bata ga izzatu ba, a cikin jin haushi ta kaiwa Garzali wani
shuri da k'afa, a zabure ya falka, ya fara waige waige, bai tantance ba yaji saukar wani bahagon
mari a kan fuskarshi, da sauri ya mik'e tsaye yana kallonta a cikin mamaki, kafin yace wani abu
ta rigashi, ta hanyar tambayarsa ina izzatu, a cikin tsoro da fargaba, yana in ina yace:
"Tana d'akin Mama"

Iya kulu saboda son ta aiwatar da nufinta, bata bi ta kan Garzali ba, da ya kira hassatu mama
ba, ta fita fuu kamar wata bajimar zakanya, jikinta har rawa yakeyi ta kai d'akin.

Garzali yana ganin fitarta, yazo da sauri ya rufe k'ofar d'akinsu, dafe da k'irjin shi, don idan har
ba idanunshi bane ba, ya hango kamar wuk'a a bayanta ta b'oye.




����Ku kawo agaji iya kulu zatayi kisan kai





Kuyi manage wlh banida caji wanga ma dakyar na kukuta nayi maku typing‍♀

Akafta☹





D/Auta ce�


[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈️*


*NA HADIZA D/AUTA*


*MY FANS BANDA BAKIN DA ZAN GODE MAKU AMMA KUSANI COMMENT'S DINKU YANA
SANI FARIN CIKI BA KADAN BA INA JIN DADIN ADDU'O'INKU A GARENI NAGODE SOSAI
ALLAH YA BAR ZUMUNCI*


*PAGE TWENTY*

**********************

Koda iya takai k'ofar d'akin hassatu, ba shiri taja burki, ganin k'ofar rufe ruf, abun mamaki harda
su guzurin saka kwad'd'o, dole taja baya tana huci.

Garzali dake jikin k'ofar d'akinsu, ya fad'a tunanin ya fita ko ya k'ara mak'alewa, wata ziciyar
tace dashi:

"wυĸa ғa ce a нannυnтa ĸυмa тana тaмвayar ιna ιzzaтυ wayyo allaн вa d'aι ĸaѕнeтa zaтa yι вa
мυ ѕнιga υĸυ"

Aiko ba shiri ya bud'e k'ofar da k'arfi, har sai da Abu dake bacci ya zabura, saboda tsoron da
yaji, aiko ganin Garzali ya fita shima ya biyo sa a baya, domin yaga me Garzali zaiyi a waje a
cikin wannan dare, saboda sun saba idan zasu fito fitsari, a tare suke fitowa, d'aya ya rako
d'aya, aranshi yace kodai kashi ne ya kora shi, shiyasa ya biyo bayanshi.
Iya kulu dake a tsaye bakin k'ofar hassatu tana huci, sai kace wata kububuwa, tana jin motsi a
bayanta ta juya da k'arfi takai suka da wuk'ar.

Garzali dake bayanta yayi sauri yayi tsalle, har ya ture Abu dake bayanshi shima suka fad'i

k'asa a tare, amman a cikin rashin sa'a sai da wuk'ar ta yanki gefen cikin Abu, aiko ba shiri ya
k'walla k'ara, don yaji zafin yankan har a cikin k'wak'walwarshi, da sauri ya dafe inda iya kulu ta
yankesa, aiko saiga jini yana ta b'ub'b'ugowa, kamar an kunna famfo.

Garzali ko k'arar da yaji Abu yayi, ta kid'imesa ya tashi ya zuba da gudu sai k'ofar gida, yana
kuwwa a kawo masu d'auki iya ta kashe Abu.

Iya kulu kam tana k'yall ido taga aika aikar da tayi, ba shiri ta jefar da wuk'ar ta aza hannu a kai
ta fara kuwwar kiran sunan Abu, a d'ari ta nufi wajen shi, ta rungume tana wani marayan kuka,
da taga jinin yaki tsayawa, jikinta yana rawa ta fisge d'ankwalinta, ta d'aure gefen cikin, Abu ya
k'ara kurma kuka, ganin haka itama iya kulu ta k'ara sautin kukanta tana sambatun kiran sunan
Abu, wai yayi hak'uri bata zaci shi bane.

Malam da hassatu kam suna tsaka da farantawa juna rai, suka jiyo kuwwa da kuka yana tashi
a tsakar gidan, ba shiri malam ya zura rigarshi ya bud'e d'aki ya fito, Hassatu ma ta kimtsa ta
biyo bayanshi.

Malam yana fitowa, yayi arba da iya kulu rungume da Abu tana kuka, a cikin mamaki ya k'arasa
wajen da suke, kafin yayi magana sai ga zugar mutanen k'auyen sun shigo gidan, Garzali yana
gaba suna bayanshi, kowa da abun bugunshi a hannu, mamaki ya k'ara kama malam, idon shi
akan Garzali yace:
"Wai meke faruwa ne?"

Garzali ya kalli Abu dake murd'e murd'en zafi, ya kalli iya kulu dake kuka na tashin hankali, ba
shiri wani kuka yazo masa bakinshi yana rawa yace:

"Aljannun iya ne suka tashi, suka d'auko wuk'a sukace sai sun kasheta, to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login