Showing 75001 words to 78000 words out of 119425 words
Chapter 26 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
Izzatu kuwa suna fitowa a k'ofar gidan sai ga motar Dr tayi parking kasancewar k'ofar gidan mai
fad'i ne, amman fa fuskarsa a cike take fam da mamakin ganin wad'annan motoci a k'ofar
gidansu, mamakin shi ya saitu ne a lokacin da ya hango izzatu da Amina suna fitowa daga
gidansu, jikinshi yana rawa ya k'araso tareda fad'ad'a fuskarshi da wani yalwataccen murmushi,
izzatu da Amina ma suka mayar masa da murmushinsa, Dr hannunshi a baki yake k'are masu
kallo a cikin jin dad'in ganinsu musamman ita izzatun, da yake raba dare a kullum saboda
tunaninta, domin yayi iya yinshi akan ya kawar da sonta a gefe amma ina yana nan tsayenshi
k'yam a tsakiyar zuciyarshi, yana murmushi mai sauti yace, "'yanmata adon gari yau ziyara
aka kawo muna.?"
Dukansu sukayi murmushi Amina tayi caraf tace, "Tunda ku ba kwa nemanmu ai mu sai
muzo mu kwashe ladar."
Dr yayi dariya idonshi akan izzatu yace, "sannu hajjaju kunyi k'ok'arin gane gidanmu."
Izzatu a cikin nauyi tace masa, "Baba kallah ne ya kawo mu ai."
Da sauri Dr yakai dubanshi inda motar farko dake kallonshi, yana dariyar jin dad'i ya nufi motar
baba kallah ya fito sukayi musabaha, sannan suka gaisa su izzatu suka k'araso jikin motar,
sanna izzatu ta kalleshi tayi wani tsadadden murmushi tace, "Mu zamu wuce sai kuma wani
jik'on idan ALLAH ya nufa."
Dr yana murmushin yace da ita, "okay na fa gode sosai da wannan ziyara ALLAH ya biya ku da
gidan aljannah, idan kunje ku gayar man da su malam."
Izzatu da Amina Suka had'a baki wajen fad'in, " zasuji"
Sannan suka shiga motar baba kallah ya tada motar da sauri Dr ya lek'o saiti da mazaunin
izzatu yace,
"Ranki ya dad'e ko za'a taimakan da number?, saboda akwai maganar da nike so muyi."
Izzatu tayi dariya har saida fararen hakoranta suka bayyana tace, "me zai hana ko? tsaf zaka
samu."
Daga nan ta dinga fad'o masa number'r yana sakawa a wayarshi, sannan ya janye tareda d'ago
masu hannu alamar bye bye suna maida masa, karaf idanuwan Dr suka sark'e a cikin na
Amina ba shiri ta feshe shi da wani murmushin da ita kanta batsan ko na minene ba.
Baba kallah ya mik'a hanya aka saka shi a tsakiya, motar sojojin d'aya a gaban jerin motocin
yayinda d'aya take a bayan su, suka kama hanyar zuwa k'auyen a guje izzatu tayi wani
murmushi tace da baba kalla, "Mun gode fa baba."
Yayi murmyshi yace, "Kinfi k'arfin komi a wurina 'yata."
Izzatu tayi dariyar jin dad'i tace, "Yawwa baba wai d'azun me ya had'aka da iya kulu ne?, naga
kamar tana 'yan guntayen hawaye."
Ta k'are maganar tareda dariya, baba kalla shima dariyar yayi yace da ita,
"Wata dirama ce mukayi da ita bayan kin shige sashen mamarki, shine tana hangoni lokacin da
ta rako ki, jikinta yana b'ari tazo wurina tana gaidani na amsa mata ba sakin fuska, to shine tace
dani wai da gaske nasan duk matsin lambar da tayi ta yimaki?, nace mata eh hadda tallar da
tayi ta d'ora maki ina yimaki juye duk na sani, aiko shine hankalinta ya tashi ta durk'usa har
kasa tana rok'ona wai don ALLAH in rufa mata asiri, kada in fad'i irin abubuwan da tayi maki na
zalinci a wurin kowa, don tun ranar da akayi wannan taron tayi ta nemana ta rok'eni sai na b'ace
mata, nace mata bazan fad'i ba amma da sharad'in ta gyara tarayyarta da unbangiji, sannan ta
k'ara rokarki yafiya akan ki yafe mata to shine kika ganta a rud'e."
Izzatu da Amina suka k'yalk'yale da dariyar shirmen iya kulu, baba kalla yana tamasu yace,
"ni sai nake ganin kamar wannan mata ba kanta d'aya ba fa, don na fahimci tana da shiririta
sosai a cikin lamurranta, akwai fa ranar da na tab'a ganinta a bakin badawi plazar, sai lek'e
lek'e takeyi bansan me take nema ba a wurin, saboda a bakin k'ofar shiga wurin na ganta tana
rabon idanuwa tamkar wata zararriya, ALLAH yasa bata ganni ba."
Su izzatu ko dariya suka yi ta ci har suka kai k'auyen, sai ga mutane sai gudun tsira sukeyi
ganin sojoji da bindigoginsu, ganin sun nufi k'ofar gidan mai unguwa ne da yasha gyara tamkar
ba shi ba, sai ga wasu marasa tsoron sun garzayo domin su ganewa idanuwansu abunda zai
faruwa.
Aiko ganin izzatu da Amina sun fito tareda baba kallah sai kallo ya koma sama, saboda
dukansu ba wanda ya d'auka mutanen da suka tab'a sani ne ganin sun sha ado ba na wasa ba,
kai tsaye izzatu da Amina suka shige gidan mai unguwa wajen matanshi suka gaidasu duk da
suma basu wayesu ba, sannan aka yimasu iso suka shiga fadar mai unguwa shikam yana
ganin izzatu ya ganota, saboda farin sanin da yayi mata sannan sanin daular da ta shiga a
yanzu yasan dole ne ta canza sosai, a cikin farinciki ganin juna suka durk'usa har k'asa suka kai
gaisuwa ga mai unguwa.
Wanda shima k'ok'arin gaida izzatun yakeyi ta hana sai ya buge da yimata godiyar irin abun
alkhairin da ita da mai girma Gwamna suka yi masa, sabida yanzu haka gari biyar dake zagaye
da garin duk shine sarkinsu duka, wannan karramawa ce da Gwamna yayi masa saboda
yabawar da yayi da adalcinshi.
Bayan sun k'are gaisawa ne izzatu tayi masa bayanin akan a tara mata mutanen k'auyen duka,
domin tana so ta raba masu kyautarsu da tasa aka zo ita tun kafin su k'araso, aiko haka akaje
akayi ta shela akan kowa yazo k'ofar gidan mai unguwa ana son ganinsu, wanda kafin su had'u
duka akayi ta sauke kwali kwalin da aka ciko tireloli dasu, sai da aka cika k'ofar gidan mai
unguwa taf da kwalayen amma har wasu basu sami fili ba dole aka bar wasu kwalayen acen.
Bayan sun had'u ne mai unguwa ya fara koro masu bayanin kamar haka, "Assalamu Alaikum
nasan zakuyi mamakin abunda yasa aka taraku a yanzu, to ba wani abu bane illah 'yarku ce
wasu kuma kanwarsu, itace ta kawo maku ziyara saboda karamci irin nata da tayi gadon
mutunci gaba da bayanta, kuma 'yar halas wadda bata mance alkhairi komi k'ank'antar shi,
wato IZZATU 'yar gidan malam ayuba da hassatu, wadda a yanzu ta rikid'e ta koma 'yar Mai
girma gwamna wato ALHAJI YAHAYA BADAWI."
Gabaki d'aya wurin ya d'auki sowa da farin cikin jin wannan labari, yayinda kowa ya matsu yayi
ido biyu da 'yar Gwamna IZZATU, mai unguwa ya bada umurnin izzatu ta fito aiko sai ga izzatu
ta fito d'auke da wani murmushi akan fuskarta, gabaki d'aya wurin ya ruguntsume da kirari kowa
da jinjinar da yake yimata, saboda sunji dad'in wannan ziyara da takawo masu.
Daganan aka ce kowa yayi shiru ba shiri wurin yayi tsit saboda suna girmama mai unguwa
sosai gani irin adalcinshi a garesu, sannan mai unguwa yace da izzatu tayi magana, aiko a
hankali ta fara kai gaisuwarta ga d'aukacin wanda ke wurin daga nan tace,
"Nayi farinciki sosai da ALLAH ya sake had'ani daku, saboda komi na zama a rayuwa to bazan
tab'a mantawa da mutanen wannan gari ba, musamman babana MALAM AYUBA da mamata
hassatu da baba mai unguwa, sannan da yayana kuma maigidana insha ALLAH wato yaya
Gazanah!."
Aiko fili ya d'auki kabbara fuskokinsu a washe sai jinjina irin wannan karamci na izzatu sukeyi,
tsofaffi sai saka mata albarka sukeyi matasan garin kuwa sai fito suke suna furta kalmomin
girmamawa tareda jinjina a wurinta.
Daga nan mai unguwa ya sanar dasu kyautar da ta zo masu da ita, aka umurcesu da su layi
maza daban matan da suka zo suma daban, har sun fara ruguguwa aka tsawatar dasu, dole
suka natsu saboda bindigogin da suke hange a hannun sojoji dukansu suka shiga taitayinsu.
Aka fara rabon kwali kwali ga duk wanda ya halarci wurin, mutane sai tud'ud'uwar zuwa sukeyi
cen na hango taku kande da 'ya'yanta 'yanmata a layin mata sai rabon idanuwa suke yi, d'aya
bayan d'aya duk wanda yazo wurin sai da aka baiwa kowa, sannan sauran da suka rage akayi
ta jida ana shiga dasu gidan mai unguwa, sai da komi ya lafa sannan mutane suka watse bayan
sun shiga daga ciki izzatu ta ciro check ta rubutawa mai unguwa kud'i masu tsoka ta mik'a
masa, mai unguwa yayita godiya har da 'yar k'wallar shi sannan izzatu tayi masa sallama suka
nufi gidansu kande,mutane suka biyo su abaya suna ta saka mata albarka.
Ko da suka shiga gidan kande ta watse kwalaye anyi masu fillah fillah ana kallon abubuwan
dake ciki, saboda tun a waje da d'iyan suka hango su izzatu zasu shigowa suka arto da gudu
suna sanar da ita ga IZZATU nan zuwa gidan, ba shiri ta janyo mayafi ta yafa ta fara maida
kayan dake cikin kwalin da suka firfito dasu suna kallo.
Koda IZZATU ta shigo kande duk ta diririce wai yau 'yar Gwamna a gidansu, a tsaye suka gaisa
izzatu ta ciro kud'i rafar d'ari biyar ta mik'a mata sababbi k'al, ba shiri kande ta kai durk'ushe
wajen karb'ar kud'in saboda tsananin rud'ewar da tayi, aiko tana jin d'imin kud'in a hannunta ta
fara kuka tana cewa, "Don ALLAH izzatu ki yafe man duk abunda nayi maki."
Izzatu tayi murmushi ba tareda tace da ita k'anzil ba ta fito gidan suka nufi gidan malam.
Kande ta kalli kwalayen dake gabanta guda biyar da ta samo d'aya mijinta d'aya sai yanmatanta
biyu da idi d'aya, sannan ta k'ara kallon kud'in dake hannunta ta fashe da wani zakin kuka tace
da 'ya'yanta , "tabbas d'an hakin da ka rena ashe da gaskiyar hausawa shine yake tsone maka
idanuwa, yanzu ku duba ku gani ko buhun shinkafar nan zaici tiya biyar biyar fa, sannan ga
jarkar manja ga na mank'uli ga maggi ga sugar ga sabulai sannan a kowane kwali ga dubu biyar
a ciki sannan ga wad'annan mik'ak'k'in kud'in sababbi k'alk'al, oni kande wannan bajinta ai sai
d'an gidan girma wanda ya gadi k'ashin arzik'i a gaba da bayanshi, izzatu yau kin nuna muna
cewa tabbas ke 'yar halas ce, mun yimaki sharri kinzo har gida kin saka muna da alkhairi."
Ba shiri ta k'ara fashewa da kukan nadamar abunda tayi ta k'ullawa iya kulu akan tak'i izzatu, da
jifarta da miyagun kalamai da take tayi ita da yaranta, tana kuka tana ALLAH muntuba ka yafe
muna.
í ¾í´”í ¾í´”í ¾í´”í ¾í´”Su kande anfara shiriya?????.
Akaftaí ½í±í ¼í¿»
D/Auta ceí ½í±Œí ¼í¿»
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈ï¸*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE FIFTY TWO*
**********************
Ummaru ya bud'e 'yar k'aramar k'ofar wangalelen get d'in gidan, a cike da karsashi sannan su
izzatu suka shiga da bisimillarsu saboda gida ne na ji da gani, wanda a kafatanin k'auyen kaf
bayada na biyu, wanda ko a birni sai anyi dak'yar kafin a samo wanda ya fishi, masha ALLAH
gida ya tsaru part hud'u ne a cikin gidan kowane ka shiga sai ka d'auka cewa sashen ne kawai
a gidan saboda haduwarshi, sun shishiga lungu da sak'o na gidan sun gani tareda jagorancin
ummaru d'an inna hure, wanda shine izzatu ta wakilta a matsayin idanunta shiyasa ragamar
komi na gidan yake a hannunshi, wanda shima izuwa lokacin ya siye k'aton filin shi har ya fara
aza gini.
Bayan sun k'are dudduba gidan ne suka fito suka nufi gidansu inna hure, wanda shima d'in aka
gyara shi fesfes da gini irin na zamani gwanin burgewa, Amina ganin yanda gidansu ya koma
sai wasar bakin jin dad'i takeyi tana k'ara jin k'aunar izzatu har cikin b'argonta, domin ita har
gobe ta d'auki izzatu tamkar 'yar uwarta wadda suka fito tsatso d'aya.
Koda izzatu suka shiga gidan inna hure farin cikinta ya kasa boyuwa saboda jin dad'in
ganinsu, kafin kace me da shigarsu aka cika gabansu da kalolin abinci wanda wannan duk
hidimar ummaru ce saboda yasan da zuwansu.
Bayan sun gaggaisa ne inna ta fara yiwa izzatu godiya, babansu Amina ma ya shigo suka
gaisa tareda k'ara jaddada godiyarsu a wurinta, a gaggauce su izzatu suka ci abinci suka YI
SALLAH, sannan suka yi masu sallama bayan izzatu ta dunk'ulo kud'i masu tsoka ta baiwa inna
taja jari, shi kanshi baban Amina tayi masa kyautar bajinta ummaru ma gefe ta ja shi ta dunk'ulo
kyautar da itama batasan ko nawa bace tace dashi ya k'arasa ginin gidanshi, suka fito k'auyen a
cike da kewar juna tareda tsarabar k'auyen da aka lafto masu kala kala.
Suna tafe akan hanya Amina ta fashe da kukan farinciki saboda jin dad'in hidimar da izzatu
takeyi dasu ba gajiyawa, izzatu tayi saurin kai kallonta ga Amina a cikin mamaki tace,
"Malama me aka yimaki ne? da zaki cika muna kunnuwa da kuka."
Amina ta ri'ko hannunta duka biyu ta runtse idonta a cikin na izzatu tace, "Mun gode sosai da
ALLAH ya azurtamu da samunki a cikin ahalinmu, tabbas ke d'iya ce har da rabin d'iya a
rayuwata kaf ban tab'a ganin mai halacci irin naki ba, mun gode sosai da hidindiminki agaremu,
ALLAH ya saka maki da gidan aljannah ya nuna muna ranar aurenki da yaya Garzanki."
Izzatu tayi murmushin jin dad'in addu'ar da tayi mata musamman da ta ambato sahibil k'albinta,
bakinta a washe tace, "Nifa wallahi har yanzu ji nikeyi tamkar ku d'in jinina ne na gaske,
shiyasa bana k'yashin yin komi don ganin nikeyi ai kaina na yiwa idan nayi, naso ace
DADATAH! Itama ALLAH yayi mata tsawon rai domin kawai in rab'i jikinta inji sanyi, duk da
banyi wayon saninta ba amma ina jin sonta ba kad'an ba ALLAH ya jik'anki DADAtah!, ya k'ara
haskaka maki k'abarinki halinki na k'warai ya biki."
(ALLAH sarki nima na tuno da rasuwar masoyiyata Asama
Bawa Kaura ALLAH ya jik'anki da rahama ya k'ara haskaka makwancinki ya sawa abunda kika
bari albarka í ½í¸).
Ta k'are maganar tareda zubowar k'wallah akan fuskarta, kai tsaye aka wuce gidansu malam
aka ajiye Amina, izzatu tasa aka raba tsarabar biyu aka shigarwa da su mama rabi, sannan ta
shiga tayi masu sallama ilham ta lik'e ta ala dole sai ta bita aiko ta d'auko ta suka nufi gida.
****
Maman Dr kuwa ta fito bayin tana zaune tana maida numfarfashi sama sama, Dr ya shigo gidan
da sallamarshi a cikin wani farinciki da yake ta ratsa zuciyarshi, koda ya shigo falon yaci karo
da check d'in da izzatu ta baiwa maman yashe a bakin k'ofa, ya duk'a ya d'auki check d'in yana
dubawa ba shiri ya zaro idanuwa a waje tareda karasowa cikin falon inda mamar take a zaune,
fuskarshi a washe yace, "Wannan check d'in fa mama.?"
Sai a lokacin mamar ta tuno da shi tana yatsine yatsinen cikinta da yake ta yamutsawa tace,
"Wannan yarinyar kirkin ce ta bani."
Dr ya sami kan kujera ya zauna idonsh akan mamar yace, "Ai shikenan kuma mama kinyi
kud'i kin barmu."
Mama ta kalleshi fuskarta d'auke da kallon son Dr yayi mata k'arin bayani, Dr yana dariya yace,
"'yar k'auyen da kuka hana ni aure ce tayi maki kyautar kud'i nera na gugar nera har dubu d'ari
biyu."
Ba shiri mama ta k'walalo idanuwa tareda sakin baki tamkar wata sakarya, Dr ya tabbatar mata
da abunda yaga an rubuta a jikin check d'in, aiko sai ga mama ta tashi aguje ta koma masai
saboda tahowar wani lafiyayyen zawo da ya k'ara kawo mata ziyara, minti biyar a tsakani sai
gata ta fito tana dafa bango ta zauna idonta akan Dr tace, "Don ALLAH ka yafe mani cutar
da kai da mukayi, don tabbas wannan yarinya ba k'ashin yadawa bace, inda hali don ALLAH
kaje ka dawo da soyayyarku wallahi nayi danasanin hanaka aurenta da mukayi, kana gani dai
ko shi babanka tun ranar da yaji 'yar wace, yake sukuku tamkar wani mara lafiya saboda
takaicin wannan abun kunyar da muka tafka."
Dr yayi murmushi yace, "mama ina son ki gane da da yanzu ba d'aya ba, domin kuwa ke
kanki kinsan izzatu tafi karfina wallahi, ko ba komi zan tayata yiwa marik'anta halacci saboda
akwai D'ansu da nasan yana sonta sosai kuma itama tana sonshi, kuma shima malam yasan da
wannan soyayyar tasu, amman duk da haka yayi biris ya rufe ido yaso ya auraman izzatun ya
hanawa d'anshi, sai gashi kwatsam kunzo kun wargaza komi to kinga yanzu nima na gano
izzatu bata dace da kowa ba sai Garzali, zanyi farinciki sosai idan naga ta aureshi saboda nima
in zama d'an halas in sowa d'an uwana abunda na sowa kaina."
Mama tayi zuru tana kallonshi na d'an lokaci sannan tace,
"K'awarta fa da suka zo?"
Dr ya sosa kai yana dariya yace, "ita kuma yanzu kike so ki aura man? ina bintar anfasa da ita
kenan.?"
Mama tayi masa dak'uwa tace, "kai kanka