Showing 39001 words to 42000 words out of 119425 words

Chapter 14 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

yace;

"Ba komi yiwa kai ne"

Mama hassatu ma da a lokacin ta farfad'o, daga kwancen tayi masa godiya, acikin muryarta ta

da ta dusashe, sai kace wadda taja lokaci tana jinya, saboda ciyon ya bugeta sosai, a fakaice
Dr yakai kallonshi akan izzatu, yayinda ita kuma a lokacin suna magana k'asa k'asa itada
Garzali, inna hure da hankalinta yakai kansu tana dariya tace;

"Yaya da kanwa gulmar wa akeyi ne a cikin asibiti?, ku a ko'ina ma sai kun nuna halinku?, to
tashi dai ka koma makaranta, mun gode da ziyarar hakanan"

Izzatu tayi saurin yin magana tace;

"Haba inna hure, don Allah ki bar man yayana, nidai bangaji da ganinsa ba gaskiya"

Ta k'are maganar tareda b'ata fuska, wasu sababbin hawaye suka zubo mata.
Inna hure tana dariya tace;

"Ah lalle akwai aiki ja a gabanku"

Mama daga kwancen ta rik'o hannun izzatu, tareda yimata alama da ido, akan tayi shiru, izzatu
kam daman cen kukan a kusa yake, shiyas hawayen suka dinga sirnano mata akan fuska,
Garzali ya rik'o hannunta yace;

"Taso muje waje kiji k'anwata"

Aiko tayi tsam tabi bayanshi, inna hure sai tsarguwa take yimasu, malam duk da zuciyarshi a
cunkushe take da damuwa, sai da ya dara, yace da inna hure;

"Mudai iyakacin mu kallo, amman ke hure yaushe suka zamo jikokin ki?"

Inna hure tana dariya tace;

"Na ari bakin Dada yau"

Daga nan suka k'ara yiwa Dr godiya, yayinda Dr ya fito malam ya biyo bayanshi, Dr tafiya
yakeyi zuwa office d'inshi, amman idanuwanshi suna kan Garzali da izzatu da suke zaune yana
lallashinta.

Bayan sunje office d'inne Dr yayiwa malam bayanin komi akan ciyon mama hassatu, malam yaji
dad'i akan taimakon da yayi masu, ya tambayi Dr abunda aka kashe sai ya biya, amman Dr ya
nuna yayi komi don Allah badon a biyashi ba, malam yaji dad'in wannan karamci na dr tareda
jaddada godiyarshi a gareshi.
Inna hure da wata k'anwar mama hassatu sai izzatu da Garzali, sune sukayi jinyar mama
hassatu har taji sauk'i, Dr ma sai fad'i tashi yakeyi dasu, ta b'angaren jikinshi da aljihun shi, su
inna hure sai jinjina kirkin Dr sukeyi, duk da zuciyarsu ta basu da biyu a cikin wannan hidima da

yake yimasu, amman saboda bai furta abund ke zuciyarshi ba, shiyasa suma suka share, sai
kwasar ganimar su sukeyi, har saida malam yace dashi d'awainiyar tayi yawa, amman bai fasa
ba, saboda shima malam a kullum nan yake yini, sai da yamma ya koma k'auyensu.

Mama hassatu taji sauk'i sosai aka sallamesu, tareda gindaya mata dokoki masu yawa, saboda
kare lafiyarta data abunda ke cikin, dukansu sunji dad'in ganin mama hassatu ta sami sauk'i,
musamman Dr da ya matsu su koma gida ya fara kafa gwamnatinshi a wurin masoyiyarshi
izzatu, duk da ganin shekarunta a lokacin basu kai ba, amma ya k'uduri aniyar zaiyi ta rik'o har
zuwa lokacinda zata san minene so.

Ranar da aka sallamaesu, Dr da kanshi ya d'auki malam, da mama da inna hure, da sauran
dangin mamar ya kaisu k'auyen, yace da Garzali da izzatu da d'iyar inna hure Amina su jira ya
kaisu malam ya dawo ya kaisu suma, aiko haka akayi yana ajiye su malam ya dawo ya
d'aukesu, har sun fara tafiya yace dasu, don Allah suyi masa uzuri ya karb'o wani sak'o a wani
wuri, sukace;

" Ba duwawa"

Dr kai tsaye ya wuce wani katafaren shago, wanda a saman shi aka rubuta ;

BADAWI SHOPPING COMPLEX.

Izzatu tana d'aga kai tayi arba da sunan, a nan take poster'r YAHAYA BADAWI ta fad'o mata a
rai, jiki a sanyaye tace da Dr ;

"Don Allah inzo in raka ka?"

Garzali ya maka mata harara,
Dr yayi murmushi yace;

"Bismillah zo muje"

Izzatu ta kawar da kanta kamar bata ga hararar da yayant yake yimata ba, tabi dr jiki a
sanyaye.
A k'ofar shagon ne, izzatu taji kirjinta ya buga, amma ta daure sai kalle kallenta takeyi, ba shiri
taci karo da wata mata har tana k'ok'arin fad'uwa,matar ta saka hannu zata d'agota, izzatu kuwa
idonta akan matar, gabanta sai dakan lugude yakeyi, bakinta yana rawa zata baiwa matar
hak'uri ne, aiko matar tayi saurin juyawa da sauri, saboda kiran da wani yaro dake cikin wata
had'ad'd'iyar mota yayi mata yace;

"Ammi kizo Ammar ya yanke hannunsa da clipper"

����



Akafta🤾🏻â€â™€ï¸





D/Auta ceí ¾í´í ¼í¿»
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*


*NA HADIZA D/AUTA*


*NAJI DADIN COMMENT'S DINKU MASOYA NA DA MASOYA BUK DIN RUWA DA KANKARA
KUNA SANI NISHADI BA KADAN BA KUSANI KUNA CIKIN ZUCIYAR D/AUTA DUKANKU I
LUV YOU ALL MY GAY'S 💋*

*KUZO MUSHA RUWA DA KANKARA⛹🏻â€â™€ï¸í ½í²ƒí ¼í¿»*


*PAGE THIRTY TWO*


**********************

Har ta shige motar, taja ta da k'arfi ta bar harabar shopping complex d'in, izzatu bata daina
kallonta ba,baki a sake tana mamakin wannan fuska da ke yimata gizo, idan ba k'arya tayi ba
tabbas ko tantama babu, fuskarta ce sak ajikin fuskar wannan mata, banbancinta da ita shine
shekaru, amma tabbas ba makawa wannan mata da aka kira da suna AMMI suna
kamanceceniya da juna, to tayaya?, shin miye had'inta da ita da suke kama?, izzatu ta kasa
baiwa kanta wannan amsar, wata zuciyar tace da ita ;

"Kama ce kawai, amma taya zaki had'a kanki da wannan mata irin hutu, wadda a duba d'aya
zaki gano hutun da ya ratsa fatar jikinta, kina 'yar k'auyenki, ya zaki had'a kanki da ita?, kin
manta ance a duniya akwai mutanen da Allah ya halitta iri d'aya, ba tareda sun had'a jini ba,
wani ma ba'a k'asa d'aya dashi ake ba, to kema hakan ce ta faru dake ko yanzu"

Tana nan a tsaye jiki ba kuzari, har Dr ya fito hannuwansa rik'e da ledodi, ba tareda ya kula da
yanayinta ba, yana murmushi yace da ita;

Sorry my izzah! na b'ata maki lokaci ko?, to kiyi hak'uri muje gani na fito, amman meyasa baki
shiga daga ciki ba, sai kikayi tsayenki a nan?.

Izzatu tayi saurin saita natsuwarta, sannan tayi murmushi tace;

"Ba komi"

Dr ya kalleta tareda wanke fuskarshi da wani murmushi mai tsada, suna tafe suna 'yar firarsu a
hankali, har suka k'araso a jikin motar, izuwa lokacin Garzali ya cika fam, sai Harbin iska yakeyi
da hannu, don jinsa yakeyi tamkar ya kama Dr yayita jibgarsa, a zuciye ya b'alle murfin motar
ya fito, ya nufi titi ya tare wani d'an acab'a ya haye, izzatu ta kira sunan shi a cikin d'aga murya
tace;

"Yayana ina zakaje ne?, gashi muna ta sauri zamu wuce gida"

Garzali ya maka mata wata bajimar harara, yace da d'an acab'an su wuce, a cikin d'aga murya,
aiko d'an acab'a ya fisgi mashin d'in kamar walk'iya suka bar wajen, izzatu ganin hararar da
Garzali ya maka mata, ta saka jin kanta a cikin damuwa,a nan take wasu hawaye suka zubo
mata, Dr ya kalleta yayi murmushi saboda yagano kishi ne yake d'awainiya da Garzali, a cikin
sakin fuska yace da ita;

"Muje ko?"

Ta kalleshi da kyau tace;

"Mu jira ya dawo, don kar yazo ya tarar da bama nan, kasan bazai ji dad'i ba"

Dr yana murmushi yace da ita;

"Muje kawai nasan bazai dawo ba, idan munje, zamu tarar dashi a gidan kada ki damu zo
muje"

Izzatu ta k'ara b'ata fuska tace;

"Kuje kawai, NI zan jirashi a nan d'in, har sai ya dawo"

Dr yaji zafin maganar amma ya dake, yana murmushi yace;

"Kizo muje, don bafa zai dawo ba, ko bakiga fushi yayi bane?,"

Sannan izzatu ta tuno da hararar da maka mata, bayan ya haye mashin, jikinta a sanyaye ta
shiga, tana ta nuk'u nuk'un kukanta har sukaje gida, Amina sai hkr take bata, amma kamar k'ara
zugata takeyi, saboda zuciyarta ko kad'an bata yimata dad'i.

A bakin bishiyar dake k'ofar gidan Dr ya tsaya, yaran k'auyen, har sun fara taruwa wajen kallon
su, jiki a sanyaye izzatu ta fito,itada Amina har suna had'a baki a wajen yimasa godiya, Amina
ta shige gidan, izzatu ma ta juya zata shiga ne dr ya kira sunanta, da wata murya dashi kanshi
baisan yana da irinta ba sai a lokacin, duk da k'arancin shekarun izzatu, amman taji kiran ya
ratsa jikinta, a cikin ladabi ta juyo, tareda takowa har inda yake, idonta a kanshi tace;

"Allah yasa ba laifi nayi ba?"

Dr ya gyara tsayuwar shi yana murmushi yace;

"Kinyi laifi kam, tunda kika k'i tsayawa muyi sallama"

Izzatu tayi murmushin k'arfin hali tace;

"Sorry, nayi laifi ayiman afuwa, mungode sosai da d'awainiyar da kayi muna, Allah ya biyaka
yasaka maka da gidan aljannah, ya baka abunda kake nema duniya da lahira"

Dr sai Ameen yake fad'i, saboda yaji dad'in addu'o'in izzatu, tarbiyyar izzatu da shagwab'arta,
sune suke k'ara fisgar shi a soyayyarta, a cikin wani farinciki da ya tsinci kansa a ciki ya bud'a
motar ya ciro ledodin dake ajiye ya mik'a mata, bakin shi a washe yace ;

"Gashi idan kinje gida ki bud'a ki gani, naki ne tukuicin addu'ar da kika yiman"

Izzatu tayi jim tana tunani, sannan tace dashi;

"Kayi hak'uri idan naje dasu nasan malam zaiyi fad'a, tunda ko a asibiti yayi fad'a akan ka daina
wannan d'awainiya tayi yawa, abunda kayi ma mungode wallahi, don bazamu iya biyanka ba,
sai dai muyi maka fatar gamawa lafiya"

Dr ya b'ata fuska yace;

"Idan har da gaske kike fad'ar maganganunki, to ki karb'a kawai, idan kuma renawa kikayi
shikenan ba damuwa sai in hak'ura"

Izzatu ta saka hannu biyu ta karb'a tayi masa godiya ta shige gida, Dr ya bita da kallo har ta
shige sannan yaja motarshi yabar k'auyen, tareda jin kansa a cikin wani shauk'in so da k'aunar
izzatu.

Kuyi manage kwanan ina da matsala sosai akan rashin caji😥



Akafta�




D/Auta ce🥰
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*


*NA HADIZA D/AUTA*


*Na zaune baiga gari ba, ba sauri nike ba, sai inbar gudun fama,in waigo in k'i sufuri dole a
d'auki tabarma, nai nazari akan samu dole yafi zuwar wa mai nema💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*

*Da damana kwari sukeyin sansani, mara gaskiya a cikin idonsa zaka gani,ki gudu sai mu kira
masa sa gudu ya gani,raba gardama zaki cikin dawa yake sa natsuwa, da damana ni nasan
sama ke zubda ruwa💃🏻💃🏻💃🏻*


*PAGE THIRTY THREE*


**********************

Jiki ba kuzari izzatu ta shiga gida, ganin takalma da yawa a k'ofar d'akinsu ne,hakan ya tabbatar
mata d'akin acike yake da 'yan dubiya, tayi d'akin Garzali, saboda malam yasa an raba d'akin
Dada biyu, Garzali rabi Abu rabi, ganin rayuwar da Abu ya jefa kansa a ciki, saboda idan garzali
ya ajiye kayanshi, kafin yaje ya dawo Abu ya salwantar, da ya dawo ayita rigima, shiyasa
malam ya raba masu d'akin hankalin kowa ya kwanta.

A bakin k'ofar taja ta tsaya, har sai da ya bata umurnin shiga, sannan ta d'aga labule ta shiga
da sallama, ta ajiye kayan a gefe sannan ta zauna, ta tsurawa Garzali ido,ganin ko inkular da
yayi da ita ne, wasu hawaye suka gangaro mata akan fuska, da taga yak'i kulata ne ta fara kuka
a hankali tareda shesheka.
Ba shiri ya d'ago fuskarshi ya kalleta, ranshi gabaki d'aya a dagule yake, shiyasa tun shigowarta
a d'akin yak'i kulata, amman jin sautin sheshekar kukanta ne, yasa jikinshi yayi sanyi, a hankali

yace da ita;

"Me aka yimaki ne kike kuka?"

Izzatu ta d'ago fuskarta ta kalleshi ido cikin ido, sannan tace;

"Bansan laifin me nayi maka ba, da har zaka tsaneni"

Garzali ya tsura mata ido, zuciyar shi sai hasko masa izzatu da Dr takeyi, lokacin da suka fito
shopping complex suna murmushi, ya k'are had'e fuskarshi alamun ba sauk'i yace;

"Miye alak'ar ki da wannan Dr?"

Izzatu ta zaro ido a waje tace;

"Wani abu yace maka nayi masa halan?"

Garzali ya harareta yace;

"Ko kin masa laifin ai ba gani zaiyi ba,bale ya kawo k'ararki tunda yana sonki"

Izzatu ta k'ara zaro ido, tareda dafe k'irjinta dake bugawa tace;

"So fa kace yayana?, nikam ya zanyi da wannan k'atoton mutumin?, inyi yaya dashi?, kalleni fa
'yar k'aramata dani zai ce yana so?, wallahi mutunci ne kawai da yake dashi, amman ba wani
so a tsakaninmu yayana, ka yarda dani"

Ta k'are maganar tareda mayar da fuskarta kalar tausayi, Garzali kam yaso yayi dariya amma
ya dake, a fili yace ;

"Wannan tada hankali na miye?, bakya son shi ne?"

Izzatu ta rufe fuska tana dariya tace;

"Ni kam ba wanda nikeso kaf, duniyar nan"

Da sauri garzali ya zaro ido, tareda dafe k'ijinshi da ya buga dam! dam! Yace;

"Yanzu kina nufin harda ni bakyaso?"

Izzatu ta rufe bakinta tana dariya tace;

"To ai kai d'an uwana ne, taya zan auri yayana?"

Garzali kam a lokaci d'aya ya b'ata fuska, yaji wasu hawaye masu zafi sun zubo masa, a cikin
dubara ya share hawayen, sannan a cikin muryar kuka yace;

"Yanzu shikenan ashe ni ba sona kike ba"

Izzatu ta b'ata fuska ganin, hawayen da yake k'ok'arin b'oye mata, a cikin sanyin murya tace;

"Yaya Garza na!, kaf duniya idan aka cire malam da mama, babu wani wanda nike so sama da
kai, don bakasan yanda nike jin k'aunarka a zuciyata bane yayana, ko mama da tace dani, idan
nayi sallah na dinga rok'ar Allah ya bani miji nagari, to aduk na tashi rok'on da siffarka nike
rok'o, akan Allah ya bani miji na gari irinka, fuskarka, tsawonka, hasken ka, yanda kake d'an
gayen nan, to ka gani idan bana sonka taya zanyi wannan addu'ar"

Ba shiri wani farin ciki ya mamaye zuciyar Garzali, a cikin zumud'i ya ri'ko hannuwanta duka
biyu ya saka a cikin nashi, wasu hawaye suka kwaranyo akan fuskarshi, bakin shi yana rawa
yace da ita;

"Ina son kiyi man wani alk'awali k'anwata"

Izzatu Ma ganin hawaye a fuskar shi, hawayen takeyi, a cikin k'arfin hali tace;

"Nayi maka alk'awali matuk'ar ba sab'awa mahaliccinmu bane, to zan amince da duk abunda
kazo dashi yayana"

Garzali zai bud'a baki yayi magana, iya kulu ta d'aga labulen d'akin, ganin Garzali rik'e da
hannun izzatu ne yasa ta rafka salati, ba shiri suka saki hannun juna, iya kulu ta d'aga hannu ta
kwad'awa izzatu wani bahagon mari, tana kururuwar azo agani izzatu zata yiwa Garzali fyad'e.

Aiko duk mutanen dake gidan, masu zuwa ganin jikin mama hassatu sukayo d'akin Garzalin,
duk wanda ya lek'a yaga izzatu zaunenta har da hijabinta sanye, Garzali ma haka suturar shi,
sai ayi turus, saboda kowa ya kasa ganin illar abunda, iya kulu take so ta sanarwa mutane.

A hankali, mama hassatu ta tako, ta shigo d'akin tareda yimasu kallon tsaf, jiki ba k'arfi ta rik'o
hannun izzatu tace;

"Tashi muje d'aki, kai kuma ka shirya ka koma makaranta yanzu, ka gani naji sauk'i ko?, to aje
aci gaba da karatu, Allah ubangiji yayi taimako"

Mama hassatu ta fito d'akin hannunta rik'e da izzatu, bayan ta d'auko ledodin suka fito, kai tsaye
suka shige d'akinsu, iya kulu ko tana nan a tsaye k'ofar d'akin Garzali cike da mamakin ganin
yana had'a shirginshi yana lodawa a jaka, yana k'are had'a komi nasa ya fito, iya kulu mamaki
bai daina kama ta ba, har saida taga Garzali yana rufe d'akinshi da makulli, baki a sake tace;

"Au waton dai ashe da gaske ba donni kazo gidan ba, ii lalle abu ya girmama, an shanye uba an
shanye d'a"

Garzali bai kulata ba, fuskar shi a had'e yace da ita ;

"Ni na wuce sai Allah yayi dawowata"

Yana k'are maganar ya nufi d'akin mama yayi mata sallama a tsatstsaye, yaja jikar shi ya fice
gidan, izzatu ta fito d'akinsu da gudu ta nufi, bayan d'akunan su Garzalin, ta duk'a ta tone wani
abu a leda ta fita a guje, har yayi nisa ta k'walla masa kira, ba shiri ya waigo, ta isa tana haki ta
mik'a masa ledar, a cikin mamaki yace da ita;
"Miye a ciki ne?"

Ba tareda tayi magana ba, ta kwance ledar, saiga kud'i dami guda, ta ciro su ta mik'a masa,
yasaka hannu ya karb'a mamaki a fuskarshi ya lissafa kud'in,sannan yace da ita;

"Naga kud'i na minene?"

Izzatu ta b'ata fuska, sannan tace;

"Malam ne yace a baka, shine mama tace inkawo maka"

A nan take wani murmushi ya maye gurbin, b'acin ran dake kwance a fuskarshi, fuska a washe
yace;

"Malam ko ya manta ya bani kud'i kafin ya tafi?"

Izzatu tayi saurin fad'in ;

"Eh yana sane ai, yace ne ka k'ara, koda za'a buk'aci wani abu acen makarantar"

Garzali yayi murmushi yace;

"To kice dashi nagode sosai"

Shima ya ciro dubu d'aya a cikin kud'in ya mik'a mata yace;

"Kema gashi kije ki k'ara a kud'in break"

Izzatu tayi murmushi tace;

"Nagode yayana kaje kawai Allah ya kiyaye"


Da sauri ta fara tafiya da baya baya, tana yimasa bye bye, jikinshi a mace ya gyara goyon jakar
da yayi, sannan ya hasketa da wani shaharren murmushi yace;

"Sai na dawo ki kula da kanki"

Wasu hawaye suka zubo mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login