Showing 9001 words to 12000 words out of 119425 words
Chapter 4 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
Ta juyo da kallonta ga kande mai cike da takaicin Allah ya wadaran naka ya lalace tace:
"Ke kuma kande wallahi kiji tsoron Allah ki tuba agareshi, akan k'ulle k'ullen munafuccin da kike
bi gida gida kinayi, saboda kin bar baya gaba ake wa gudu a turke ki acikin d'iyanki kiji kunya,
sannan zancen ki kira wata shegiya bai taso ba ma, saboda shi shegen ai a tsakanin ma'aurata
ake samunshi ko kin manta in tuna maki?"
"Sum sum Kande taja k'afafunta tabar gidan talkaminta a hannu"
Saboda tasan halin Dada yanzu ne zata bayyana mata yanda akayi aka haife uwarta ma balle
ita, saboda ita kande kullum acikin danbacewa sukeyi da mijinta, sannan akullum furta kalmar
saki abakin shi ba wani abu bane, sai dai in basuyi fad'a ba, don wannan sananne ne duk
lokacin da sukayi fad'a mak'ota sai sun gaji da jin kalmar ya saketa, amman da sun shirya sai
aci gaba da auren ayita hayayyafa.
Har saida 'yan unguwa suka kai k'arar zaman auren su a wurin mai unguwa, bayan an natsu
kowa yayi bayani sai aka gano ba aure atsakanin su, saboda yaran da take dasu da yawa sai
akace ya barta tayi zaman yaranta, amma kwatsam sai ga wani ciki ya b'ulla a jikinta, abunda
ya zama cecekuce ak'auyen, aka fito za'ayi masu ature, dak'yar aka samu rigimar ta lafa,
adalilin yarinyar cewar da tayi cikin kwanci ne, ya dad'e ajikinta sai alokacin ya tashi acewarta
fa.
Dada ta dawo da kallonta ga Iya kulu tace :
"Ke kuma sakarya da bakida hankali, sai Ki tsaya biye kande, tana shirya maki tuggun da zai
rufta dake "
Iya kulu ta fara gungunin cewa :
"Ai gaskiya ce ra fad'a idan har da gaske ba shegiya bace, wane daliline zai saka iyayenta su
jefar da ita, ai don suna gudun aga abun kunyar da suka aikata ne"
Tana dire zancen ta ta fisgi buta ta fad'a bayi, Dada ta bita da kallo acikin k'unar zuciya tace:
"Ke kam 'yar kuluwa da ana canza hali da na canza maki naki, kidon kiji dad'in zaman duniyar
da kowa saboda inhar mune yau, tofa ba mu bane gobe, akwai rai akwai mutuwa, wadda komi
sonka da k'aunar duniya dolene sai a barta, fatanmu kawai ubangiji ya yafe muna kurakuranmu"
Malam dake fitowa yace "Ameen"
Dada ta share k'wallar da ta zubo mata akan fuska ssboda tausayin rayuka biyu, bak'in halin '
Iya kulu, da rayuwar da izzatu zata tsinci kanta aciki anan gaba, idan har ba'a samu iyayenta
ba.
Malam yana hango baba tana kuka, ranshi inya kai million to duk sun b'ace, duk da tsananin
hak'uri irin nasa, 'yar kuluwa tana fitowa daga bayin ba'a tantance ba sai jin k'arar mari sukaji
har sau biyu, iya kulu ta dafe kumatun ta da suka sha marora, tareda kwantsama kuwa, acikin
fushi malam yace:
"Muddin kika sake yin abunda ya saka uwata kuka, to wallahi sai na cire maki hak'oran gaba"
Dada ba shiri ta k'araso akusa dasu tace:
"K'yaleta ayuba ai itama ta haifa, indai duniya ce tafi iccen bagaruwa jima, adai juri zuwa rafi
watarana tulun zai fashe, aure dai ne ko bayan raina ban yarda ka ace ka saketa ba, ka barta
taci gaba da cin albarkacin zumunta, ko don darajar zumunci"
Ahaka dai ranar gidan dukansu suka kwana, a tsakanin su ukun kowane da abunda suke
sak'awa acikin zuciyoyin su,yayin da iya kulu k'iyayyar izzatu tay mata tsaye a k'ahon zuciya,
wanda taci alwashin ita ko izzatu d'aya ne zai zauna a gidan don bazata so ta k'ara k'yalla ido ta
hango ta ba, duk ta hanyar da zata bi sai taga izzatu tabar gidan ko don kwanciyar hankali
agidan, tunda gashi ba'aje ko ina ba ta fara zamar mata matsala.
Allah sarki izzatunmuí ½í¸¢
í ½í¸”í ½í¸”í ½í¸”Bance akafta ba
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*PAGE TEN*
**********************
Koda safiya ta waye Dada bata jira iya kulu ta aza ruwan zafin wankan izzatu ba, tana k'are
sallahr asuba taje ta d'ora ruwan zafin, sai da suka tafasa sannan ta fara cika flack's da ruwan
ta kai ta ajiye, saboda yawan shan madarar da izzatu take yi akai akai, ta dama mata wata
madarar sannan ta jefa a cikin ruwan sanyi domin tayi saurin rage zafi, sannan taje ta d'ebo
ruwan zafin tayi mata wankanta, tareda yimata gashin cibiya, tasha madarar ta k'oshi sannan ta
koma baccinta.
Har ta k'are 'yan guntayen ayukanta na yau da kullum, da takeyi ta koma tana lazuminta,
amman iya kulu bata zo yiwa Dada ina kwana ba, duk da rashin ganin ta ya damar da Dada
sosai, amman ta share taci gaba da lazuminta hankali akwance.
Malam da Garzali sun dawo masallaci, suka zarce d'akin Dada domin suji ya suka tashi, bayan
sunyiwa juna ina kwana ne Malam yake baiwa Dada hak'uri akan abunda ya faru jiya, Dada
tace:
"Ba komi ai komi ya wuce fatanmu kawai Allah ya fahimtar da ita ta gano gaskiya"
Garzali ya nufi inda izzatu take kwance zai d'aukota, Malam yayi masa kashedi akan kar yaje ya
tada ita daga bacci, ya barta har sai ta tashi da kanta, sannan yaje ya d'auketan, Garzali ya
b'ata fuska ya koma gefe ya rakub'e, Dada ta kalleshi tayi murmushi tace:
"Daina fushi mutumina indai izzatu ce, taka ce na baka ita kyauta, don nasan ko bayan raina,
kaine wanda zaka tsaya kai da fata akan rayuwar ta, saboda shi ayuba ba kullum ne zai dinga
kasancewa agidan ba,don haka ba komi ne zai sani na abunda ke faruwa agidan ba, amman
kai jikina yana bani inhar dakai to izzatu ba zatayi maraici ba"
Dada ta share hawayenta, Malam jikinshi yayi sanyi, wata damuwa ta mamaye zuciyar shi,
acikin sanyin murya yace:
"Insha Allahu bazaki mutu ba har sai kinga girman uzzatu, kin auradda ita da hannun ki,
matuk'ar ba iyayenta suka bayyana ba suka karb'i abussu"
Dada tayi murmushi tace:
"Zanso hakan ta kasance ayuba, amma kasan da cewa ba komi ne kake so ba, kuma har ka
samu ya tabbataba, musamman ita mutuwa saboda rashin tabbas d'inta akeso akoda yaushe
kayita tunata kana ambatonta, don gudun shagala, saboda tana kusa damu a kowane taku da
mukeyi tana biye damu abayanmu, lokaci kawai take jira kamar walk'iya haka zata rik'e ka gam,
shikenan sai ashafe babin mutum acikin doron k'asa, shiyasa akeson kayita ganin tamkar yanzu
ne zaka mutu ba sai anjima ba, saboda rashin tabbas irin nata"
Ba malam ba har Garzali dake sauraren su, sai da jikin shi yayi sanyi, don shi malam jikinshi ya
mutu murus, saboda yana jin tsoron kada ace, Dada wasiyya ce take bar masu, murya asark'e
Malam yace:,
"Hakane Dada amman kinji ance, ka nemi duniya kamar bazaka barta ba, haka ma ka nemi
lafira itama tamkar yanzu ne zaka barinta, fatanmu kawai Allah ya bamu rai da lafiya, kuma
yasa mu cika da imani, idan lokacinmu yazo"
Garzali ya taso yazo ya lafe ajikin Dada ya lafe, Dada ta shafa kanshi tace:
"Allah yayi maka albarka, ya dafa maka acikin lamurranka na yau da kullum, ubangiji ya d'auka
ke ka, ya kareka da sharrin mutum da aljan"
Tana fad'a sunata amsawa da : "Ameen "
Malam jiki asanyaye yayiwa Dada sai anjima, sannan ya fita yaje ya shirya kafin lokacin fitar sa
yayi, saboda akwai kasuwar da yakeso yaje yaci aranar.
Garzali ya k'urawa izzatu dake ta baccinta hankali akwance idanuwa, wanda ko k'iftasu baya so
yayi, saboda kawai baya so ya d'auke kallon shi daga kanta, Dada tana kalle da shi, tayi
murmushi acikin zuciyar tayi ta sak'awa abubuwa da yawa, wanda take hange da wuya hakan
ta kasance idan ba tsananin rabo ne ya gitta ba, ba shiri ta sauke ajiyar zuciya tace dashi:
"Tashi kaje ka d'auko muna furar cen kazo musha, ko kai baka fara jin yunwar ba ne?"
Garzali ya tashi ba musu yaje ya d'auko furar, suka fara sha a cikin hikima ta fara ta bashi
labarai na ban tausayi, da jarumta,ak'arshe ta bashi na ban dariya, anan sukayi ta firar su suna
dariya, har lokacin da uzzatu ta falka daga bacci.
Iya kulu kam tana d'akinta ta k'ule, sai cin faman cin magani takeyi, ita ala dole anb'ata mata,
shiyasa yau ko zazafen tuwon da zatayi kowa yaci akarya kasa azawa tayi, bak'in halinta sai
nuk'urk'usar ta yakeyi, ta sak'a ta kwance, shi kawai take tayi, har sai da malam ya dawo daga
d'akin Dada sannan ta mik'e zata fito, aciki ciki tayi masa ina kwana, shima ya amsa irin yanda
tayi masa, bayan shigewar shi ta d'aga kafad'a alamar ko ajikinta.
Da taso kar taje d'akin Dada, amman dai ta hak'ura ta shiga abakin k'ofar ta tsaya ta gaidata,
Dada kam ko kallo iya kulu bata isheta ba, tayi banza da ita kamar bata jita ba, har sai da
Garzali yace:
"Dada fa iyata tana ta gaidaki "
Sannan Dada ta kalleta fuska ahad'e tace:
"Ai da kin rik'e gaisuwarki, don ni banga amfanin da zata yiman ba"
Iya kulu ta turo baki, kamar wata k'aramar yarinya, sannan aciki ciki tace:
"Nidai kiyi hak'uri tunda har kinga na b'ata maki"
Dada tayi mata wani kallon tafi bani wuri sakarya tace:
"Ko 'yar dubu ta dawo duniya, zaki iya yimata haka ballanta ni da ban haifeki ba, renon ki kawai
nayi, don haka kije kiji da halinki, nidai fatana akullum Allah ya ganar dake gaskiya ki shiryu ki
gyara halayenki"
Iya kulu ta fita fuu tana gungunin cewa:
"Ni halina agyare yake"
***
A haka rayuwa taci gaba da shurawa, yau fari gobe bak'i a tsakani iya kulu da Dada 'yar
tsohuwa, yayinda iya kulu take neman duk wata hanya da tasan zata raba izzatu da gidan,
amman Dada tayi tsayin daka awajen kare izzatu da jikinta da manyan addu'o'in da take ta tofe
ta dasu, kamar wadda aka sanar don izuwa wannan lokaci duk wata hidim ta izzatu itada
Garzali suke yinta, ba ruwan iya kulu da sabgar izzatu, hakan yayiwa Dada ciyo, amman kuma
taji dad'in faruwar hakan, kodon kare lafiyar marainiyar Allah,tayi b'ul b'ul abinta saboda
madarar ta karb'eta sosai, duk bayan sati take shanye gwangwani uku, farinta ya k'ara fitowa,
gashinta ma duk da Dada tasa reza ta aske shi tass amman kafin kace me ya k'ara cika kanta
fam, gashi bak'i sid'ik tamkar ka saceta ka tsere.
A zuwa lokacin labarin izzatu ya bazu acikin k'auyen, mutane sai turuwar zuwa ganinta sukeyi,
Dada kam data fahimci zuwan ba na Allah bane, sai ta kame abutta ta goye ram, akullum goye
take sai idan za'a bata madara asauketa, amman kam ko madarar takesha taji sallamar 'yan
ganin k'wam to zata katse bata madarar ta goyeta ta lullub'eta da zane shif shif.
Dadar mu ta mutuncií ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£
Akaftaí ½í²ƒí ¼í¿»
D/Auta ceí ½í±Œí ¼í¿»
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*PAGE ELEVEN*
**********************
Watan izzatu uku agidan, amma idan ka ganta zakace tayi wata biyar, saboda yanda madarar
ta karb'eta tayi k'iba tayi fari, tamkar d'iyar indiyawa, shiyasa Dada da malam suka k'ara k'aimi
wajen tofeta da addu'o'in tsarin jiki.
Gashin ta anannad'e acike fam, Garzali kam aikin shata ya same shi, domin kuwa shine mai
shace kan akullum akayi mata wanka, Dada tayi ta yimasa fad'a wai kada yasa kanta yayi ciyo.
Akwai ranar da inna hure tazo gidan da jaririyarta itama da bata wuce wata biyu ba, mai suna
Amina, ta iske ana diramar shatar kan atsakanin su, tayita dariya tace da Dada:
"Gyara ne fa ake yimata Dada, ko bakiso 'yar taki ta fito ne"
Dada tace:
"Ba wani gyara ni aske mata gashin ma zanyi, ko don ta huta da wannan K'ulafuci na Garzali,
aikin kenan akullum sai kace ibada"
Aiko Dada ta d'auko reza ta aske kan tas, sannan tace;
"Shikenan yanzu anhuta, kafin dai wata sumar ta fito ai kanta zai sarara da fisgar da yake sha"
Tana k'are maganar ta waiga gefen da Garzali yake azaune, taga wayam bashi awurin, ta dawo
da kallonta akan inna hure tace:
"Ke hure ina kika ganar man Garzali, bansan fitar shi ba, Allah dai yasa ba fush....."
Kafin takai k'arshen zancenta ne, suka jiyo sautin iya kulu tana ta fad'a tana dukan Garzali, da
sauri dukansu suka fito awaje, domin su ganarwa idanunsu abunda ke faruwa.
Ita ko iya kulun bata daina dukanshi ba har sai da inna hure ta tureta ta janye Garzalin, da
gudunshi yaje wurin Dada ya ruk'unk'umeta yana kuka, acikin jin haushin dukan da Iya kulu tayi
masa, Dada takai dubanta afuskarshi tace:
"Me kayi mata ne, har da zata yimaka irin wannan dukan? "
Garzali yana sheshekar kuka yace:
"Wallahi banyi mata komi ba, wai don ta ganni ina fushi ne, ta tambayan me akayi nace mata
aski kike yiwa izzatu, shine ta fara dukana, kuma tace in na k'ara tab'ata sai ta yankeni ta cire
mani kai tayi ferfesu ta cinye"
Dada saboda jin haushin iya kulu k'anzil bata ce ba, taja hannun Garzali shigewarta ad'aki,
inna hure ita ta tsaya maidawa iya kulu martani, suka fara sa'insa Dada ta fito tace da inna hure
ta daina biyeta, saboda ita masifa ce ke cin zuciyarta, abokin yi take nema abarta da halinta
shine zai horata, aiko bud'ar bakin Abu k'anen Garzali sai cewa yayi:
"Wallahi iyata ba masifaffiya bace, ke wayafiki masifa... "
Kafin yakai k'arshen zancen shi inna hure tasa hannu ta kwad'a masa mari, Dada kam bulala
tasaka ta zaneshi tas, iya kulu ta fara masifa akan donme za'a dakar mata yaro, aiko fad'a ya
rincab'e atsakanin inna hure da iya kulu, da abu yayi tsamari sai ga dambe ya kacame
atsakanin su, Dada ta tsawatar inna hure ce kawai taji maganar ta ta daina, amma ita iya kulu
sai zillo takeyi sai ta daki inna huren.
Dada tana kuka tace da inna hure ta d'auki 'yarta ta tafi gidan mijinta ta k'yaleta, aiko ba musu
ta goye 'yarta tazo zata fita, iya kulu ta fara cin mutunci tana cewa:
"In dai akan wannan tsintacciyar magen ce ake yiman cin kashi acikin gidan, to aci gaba kar
afasa, wallahi bazan tab'a son d'iyar shegu ba, haka kawai wata k'atuwa taje ayi mata cikin
shege, ta duk'a ta haifo y'arta shegiya ace ni inzo inyi mata reno akan mi?, wallahi bazata sab'u
ba, da inyi haka ai gara inje inyi sharar gidan karuwai a birni ana biyana, nasan aikin kud'i ne
nikeyi akwai ribar da na samu, amman wannan ba lada bale la'ada, haka kawai inyita wahala
abanza"
Inna hure zata maida martani iya ta kad'a ta tabar gidan, sannan ta juyo ta kalli iya kulu da
guntayen hawayen ta mak'ale acikin idanunta tace:
"'yar kuluwa ban tab'a tunanin rashin hankalinki yakai har haka ba, amman inason ki fad'a man,
shin ita wadda kike kira shegiya, kina da tabbacin cewa da gaske shegiyar ce?, wallahi ki kiyayi
bakinki, don gudun ki d'aukarwa kanki abunda baki iyawa, izzatu dai koda shegiyar ce, ai inajin
batada hak'k'in kowa sai wanda ya d'auki nata hak'k'in ire irenki ya d'orawa kanshi, saboda haka
kisani tunda bakyajin maganata, idan kika sake kiranta shegiya da kaina zanje gidan mai
unguwa ingaya masa irin cin fuskar da kike yiwa marainiyar Allah"
Iya kulu ta rikice ta fara borin kunya tana fad'in :
"Yo inba shegiya ba, a'ina aka tab'a haifuwar d'iyan sunnah aje ajefar, nidai ko a tarihi bantab'a
ji ba"
Dada ranta ya k'ara zafi, jikinta yana rawa ta d'aga murya tace:
"Ita wadda ta fara fad'a maki cewa d'iyan shegu kawai ake jefarwa, ki tambayeta ita shegunta
nawa acikin yaranta?, izzatu ko d'iyar magajiyar karuwai ce, aduk inda ta fito tafi k'arfin
matsayinku daga ke har kanden munafuka, idan har Allah yasa rayayya ce har acikin gidannan
iyayenta zasu zo nemanta, jikina yana bani izzatu d'iyar manyan mutane ce, zakuyi danasani
idan har wannan rana tazo kuka gano gaskiya"
Kande dake lab'e ajikin katangar da ta raba tsakanin gidajensu, ba shiri ta duk'e daga katangar
da ta haye turmi ta lafe tana kallon abunda akeyi, ashe ita Dada ta hango kanta shiyasa tayi
wannan habaicin.
Dada ta maida kallonta agefen katangar tace:
"Ahaka za'a k'are tsohuwar algunguma, kidaina lafewa ajikin katanga ki fito ki zagayo kigani da
kyau, in akwai abunda kika k'ara yin tanadi, ki isar dashi kafin ki tafi, don kinga wannan da kika
k'ulla yayi tasiri munafuka mai bacci da idanuwa d'aya"
Dada kam ta b'alle marfin fad'anta, baji ba gani har saida wani mak'ocinsu yayi sallama ya bata
hak'uri, sannan ne tayi shiru fad'an ya lafa, musamman da taji kukan izzatu.
Iya kulu kam shiru tayi, saboda tuno mak'udan kud'in da aka tsinci izzatu