Showing 24001 words to 27000 words out of 119425 words
Chapter 9 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
jaja, gata da hanci santam kamar biro, ga idanuwa darara
masu d'auke hankalin wanda ta kalla, gata da d'an k'aramin bakinta gwanin sha'awa, ga gashi
har gadon bayanta bak'i sid'ik, gata dirarrar mace son kowa, wadda a kallo d'aya idan kika
mata, zaki gano idan ta k'ara shekaru ta zama cikakkiyar 'yanmata, za'ayi mace mai suna mace
a wurin,.
Amman duk da wannan tsantsar kyaun da Allah ya wadaceta dashi, iya kulu bata ko son
ganinta, saboda k'iyayyar da take mata, shiyasa a yini zungur a bautar iya kulu take k'are shi,
idan dare yayi ta kwanta tayita juye juye, jiki yayi tsami, da abun yayi mata dad'i ma har da talla
ta tsira d'orawa izzatu.
Idan ta fita yaran k'auyen suyi ta kiranta da sunan ruwa da k'ank'ara, saboda sunan da iya da
Abu suke kiranta dashi kenan, abun yayi ta bata mamaki,saboda ita dai tasan sunanta izzatu, to
miye ma'anar sunan da wasu suke kiranta dashi wai RUWA DA KANKARA, saboda ita a iya
saninta Mama hassatu ce ta haifeta, malam ne babanta.
Saboda tun kawo hassatu a gidan yaja hankalin iya kulu da kowa na gidan, akan koda wasa
bai lamunta a nunawa izzatu ba shine ya haifeta ba, shiyasa duk izgilin iya kulu bata yarda ta
furta cewa ba hassatu ce ta haifi izzatu ba, shiyasa hankalinta ya natsu da cewa su malam ne
suka haifeta.
A duk lokacin da ta d'auki tallar, bata zuwa ko'ina sai wata daba ta matasan k'auyen, inda wajen
ya zama kamar wata 'yar k'aramar kasuwa, da taje da tallar maza suyi mata rumfa su saye,
masu jawo mata hijabi daban, masu yimata kalaman banza ma daban, a haka zata baro
kasuwar tana kuka, tazo gida ta fad'awa iya kulu, amma bai hana ta k'ara loda mata wata tallar,
haka zata d'auki tallar tana kuka har taje ta saida ta dawo.
Duk wainar da ake toyawa malam baida labari, shiyasa take ta cin karenta babu babbaka,
saboda a d'an tsukin lokacin malam idan ta fita sai dare yake dawowa, saboda takaicin hassatu
da take fushi dashi, kuma ya kasa zuwa yayi bikonta ta dawo, 'yan k'auyen har sun fara yimata
Allah ya k'ara, suna ta yimata habaici kala kala, amma duk ta saka auduga ta toshe
kunnuwanta, saboda son tsakani da Allah take yiwa Malam, duk wani kushe da mutane sukeyi,
bata bi takai.
Izzatu tana a cikin wannan halin ne, ta d'auko talla zataje kasuwar, akan hanyarta tane wasu
samari su biyu suka b'oye a cikin duhun gero da yayi tsayi a wata gona, tana tafe tana 'yar
wak'arta sai kawai taji motsi a bayanta, da sauri ta juya, aiko tana hango su Dahiru roja, ta dafe
tallarta ta balbala da gudu, aiko suka bita suma, kafin kace me har sun cimmata sun cafko ta,
ba shiri ta fara kuwwar neman ceto, Roja yana dariya yace:
"Yau sai munga me kike b'oyewa a cikin zane, da bazaki bari mu tab'a ko gyalenki ne muji sanyi
ba, to yau dai yasin ko ina sai mun lagude a jikinki, wannan jiki haka luguf bazamu bari muyita
had'iyar miyau a banza ba"
Yana k'are maganar ya kai hannu da nufin ya cire mata hijabi ne, yaci saukar wani bahagon
duka a fuskarshi, ba shiri ya rafka k'ara.
Da sauri izzatu ta waiga, saiga wani bawan Allah mai siffar majiya k'arfi, da sauri tayi bayansa
ta b'oye jikinta yana ta rawa, tana kiran sunan Mama hassatu.
A cikin fushi wannan mutumin ya saki k'wanji yayita jibgar su roja, saida yayi masu ligya ligya
sannan yasaka su rankaya and na kare, bayan yayi masu kashedi da idan suka kuskura suja
maimaita, to ba su ba har iyayensu sai sunyi zaman kaso a birni.
Ya dawo akan izzatu ya tambayeta me yahad'ata dasu tayi masa bayanin duk abunda suke
yimata idan taje tallar, a cikin jimami yace da ita, kayan tallar na nawa ne ake azo mata, ta fad'a
masa ya saye kayan kaf ya bata kud'in har da rarar canjin sama, yace da ita a kullum ta dauko
tallar ta tsaya a dai dai nan inda suke zaizo ya dinga sayewa tana komawa gida ba sai taje
kasuwar ba, aiko izzatu taji dad'i tana ta murna tana godiya, don dama ba son tallar takeyi ba,
don ba yanda zatayi ne shiyasa, idan ta sulale taje wurin mamarta hassatu tana kuka ta fad'a
mata komi harda abunda 'yan iskan samarin suke yimata, sai tace tayi hak'uri na d'an lokaci ne
ta kusa dawowa, amma fa baza masu samata idanuwa a tarbiyyar izzatu,a cen kasuwar don
wani zubin har dambacewa akeyi a tsakanin wad'anda da hassatu take biya kud'i akan kula
mata da izzatu, shiyasa suka daina takurata a cen wurin tallar sai ga abunda ya faru a yanzu
har wannan bawan Allahn ya taimaketa ya garfad'eta sosai akan kar ta fad'awa kowa tayi shiru
taimakon rayuwarta zaiyi a tsakani da Allah bazai cutar da ita ba.
Suka rabu da wannan bawan Allah, shi a cikin matsananciyar damuwa wadda sai da ta saka shi
zubda hawaye, ita kuma ta tafi tana ta murnar jin za'a dinga saye mata sana'arta a kullum ta
d'auko.
Haka ko aka dinga yi a kullum ta d'auko, shine zai saye ya bata kud'inta cas, ta koma gida, iya
kulu sai murna akeyi ganin kud'in dake shigota, amman duk da hakanan bata tab'a tambayar ta
a ina yimata juyen tallar ba, saboda ita kud'in ne kawai a gabanta ba tarbiyyar izzatu ba, don
inta itace ma anhad'e ba'a farkata biyu ba k'arewar fyad'e.
Izzatu tabi ta rame haskenta ya fara dusashewa saboda azabar da iya take bata, tallah kuma a
kullum idan batayi biyu ba zatayi uku, kuma duk wannan bawan Allahn yake sayarwa, har saida
masu kula da izzatu suka je suka sanar da hassatun izzatu ta daina zuwa tallah, taji dad'in
dainawar da tayi, amma tace su dinga lura da shige da ficenta a k'auyen, aiko a kwana biyu
sukaje suka sanar da ita wannan bawan Allah dake yima juyen, hankalin hassatu ya tashi da
kanta taje taga mutumin, duba da yanayinshi da tayi ta gano baya kama da mutumin banza,
ainahi ma har wani kwarjini yayi mata, amman duk da haka taja kunnenshi sosai tareda gargad'i
akan basu buk'atar abunda yakeyi ya daina, a cikin magana mai dad'i hassatu ta fahimtar dashi,
yaji dad'i kuma ya amince da hujjojinta, suka rabu a cikin mutunci, yana mai jinsa kansa da wani
farinciki da jin dad'i.
Oni dije shi kuma wannan mutumin wanene???
Shin malam zaije bikon hassatu ta dawo ko ya abun yake????.
Zai amince da zuwan izzatu karatu a birni ko yaya???.
Akwai gumurzu a k'asa fa domin kuwa idan har ya sake ta taje birnin to daga lokacin ne wasar
zai fara ku biyoni domin kuji labarin RUWA DA KANKARA♀️♀️.
Wanda duk yaji dadin wannan page tayiwa mummyta addu'a Allah ya maidata gida lfy.
akafta
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*NAGODE DA COMMENT'S DIN KU TAREDA ADDU'O'IN KU GA MUMMY ALLAH YA BAR
ZUMUNCI*
Hassatu suna kan hanya itada izzatu, sai faman fad'a take ta yimata, saboda k'arancin wayonta
a lokacin, ya kasa hango mata illar, abunda mama hassatu take son ta fahimtar da ita, duk da
ita kanta hassatu bata ga alamun rashin gaskiya a tattare dashi ba, duk da karin maganar da
bahaushe yake fad'a ta cewa; MUGU BAIDA KAMA.
Izzatu kam ba wayo, sai zubawa hassatu labarin mutuncin da yake yimata takeyi, tana tafiya
tana ta tsalle tace:
"Wallahi mama yanada mutunci, nidai bazai yiman komi ba"
Hassatu tace:
To naji, amma ki kiyaye, ko ma wanene kar ki bari ya k'ara tareki a hanya yana yimaki juyen,
tallar ma insha Allahu kin kusa dainata, gaba d'aya a huta.
Saida hassatu ta rakata har kwanar gidansu, sannan ta juya tayi gidan mai unguwa, ba b'ata
lokaci ta samu ganinshi, bayan sun gaisa ne, tayi masa bayanin abunda ya kawota a cikin
mutuncin da suke ganin juna dashi, kasancewar shi shugaba a garin, ita kuma matar aure, a
ladafce tayi masa bayanin tallar da iya kulu take d'orwa izzatu, wadda shi malam bai ma san
tana yi ba, saboda rashin zaman gidan da baya yi, ta nuna masa tana so akira malam, domin a
sanar dashi abunda yake faruwa, saboda ya hana a k'ara d'orawa izzatu tallar, amma ta nemi
alfarmar a sakaya sunanta a yayin da za'a yimasa bayani.
Mai unguwa yaji dad'in abunda Mama hassatu tayi, saboda shima yaji labarin tallar da izzatun
ke yi, kuma yanada niyyar tsawatarwa akan hakan, amma yana jin nauyin idanun malam,
kasancewar rik'on da yayiwa izzatu tsakani da Allah, tareda mahaifiyarshi wato marigayiya
Dada, amma yaci alwashin zai kirashi, a cikin magana mai dad'i ya fahimtar dashi, sannan
sukayi sallama da juna ta koma gidansu .
Sab'anin da aka samu a ranar, wanda ya hana malam dawowa gida shine, yayi dare a garin da
sukaje saboda ruwan da aka tafka, kamar da bakin k'warya, gashi ba abun hawan da zai
kawosu k'auyensu, saboda ruwan ya hana duk wani motsin kirki a inda suka ci kasuwar,
kayansu ma suna jibge basu saida ba, shine abokan tafiyar suka yanke hukuncin su kwana
acen kawai, sai gobe sai suje suci wata kasuwar, dake a kusa da inda suka je d'in, idan sun
k'arasa siyar da kayansu, sai su dawo gida a cikin lokaci, dukansu suka aminta da wannan
shawara, saboda wani zubin suna kwana acen idan buk'atar hakan ya taso.
Aiko sukayi kwanciyarsu acen, da safe suna k'arewa suka juyo gida, shigar malam keda wuya a
cikin k'uyen da zumud'in yaga iyalinshi, sai kawai aka sanar dashi mai unguwa yana nemansa,
bai kawo komi a ransa ba ya nufi fada, saboda yasan dai ba abunda ya aikata, sai da izzatu ta
fad'o masa a rai ne yaji gabanshi ya fad'i rass, jikinshi yayi sanyi k'alau, d'an kuzarin dake tare
dashi, na son yaje gida yaga halin da suke a ciki ma, ya nemesa ya rasa, saboda yana jin
tsoron ace iyayen izzatu ne suka bayyana.
A haka dai yaja k'afunshi ya nufi fada, bayan sun gaisa ne a cikin tattausar magana, mai
unguwa yayi masa bayanin abunda ke faruwa a gidanshi, ba tareda yasan anayi ba, malam
hankalinshi ya tashi, jikinshi ya d'auki rawa, sai ga wani jib'i da ya tartsatso masa tun daga kaai
har tafin k'afafunshi, acikin b'acin rai yabada hak'uri sannan yace insha Allah zai d'auki mataki
akan hakan.
Sannan ya fito ya nufi gida, acikin fushi wanda ke shimfid'e a kan fuskarshi, tun a k'ofar gidan ya
jiyo sautin kukan izzatu, tana ta baiwa iya kulu hak'uri,a kan bazata sake ba, a d'ari ya shuri
k'ofar gidansu mai lanlanga ba shiri saiga k'ofa a k'asa ta fad'i, don dama katakon yaji jiki canji
yake nema, iya kulu kam bata maji k'arar fad'uwar k'ofar ba, saboda hankalinta ya d'auku wajen
dukan izzatu da takeyi tana masifa tana cewa:
"Shegiya nice ajalinki, tunda kike so ki k'ulla man salalan tsiya, saboda kin k'ware da munafucci,
shine zaki fad'awa mutane kisa abarni da tuwo tsibi guda, ki dawo dashi don kiyiman asarar
dukiya, kinsan ko nawa na kashe da zakije ki jaza man asara to wallahi duk inda zakije ki nemo
man kud'ina kije, ni ba abunda ya dameni kud'in kawai na sani ungo ki koma in zaki kwana acen
kar ki dawo sai kin sai..."
Maganar ta mak'ale ne a sakamakon, juyowar da tayi tayi ido biyu da malam dake a bayanta, ya
rungume hannuwa yana kallon ikon Allah, tareda nanata innalillahi wa'inna ilaihurraji'un a
zuciyarshi, don baya son ya sauke duka fushinsa akan iya kulun.
Iya kulu tana ganinsa ta fara rawar jikin yimasa sannu da zuwa, da taga kallon da yake yimata
batareda ya tankata ba, sai ta fara borin kunyar cewa :
"Wai fa tuwon dawa na aza mata talla da miya, shine da taje wajen tallar duk wanda yace mata
yarinya tuwon mine?, sai tace tuwon dawa, ace miyar miye wai don tana ja'ira sai tace, miyar
guro da kuka ce aka had'e, waifa don kawai nazo kad'a miyar guron bai isaba na had'a da kuka,
ashe ta gani shine taje ta fallasa don tana asararriya tasa aka k'i siyen tuwon ta dawo dashi,
saboda tana son inyi asar.... "
Malam bai bari ta k'arasa zancenta ba, ya saka k'afa yayi ball da kwanonin tallar tuwon, gaba
d'aya miyar da tuwon suka tarwatse a cikin k'asa, saiga mulmulallen tuwon dawa, bak'i k'irin da
miya a k'asa warwas sun zube, sannan ba b'ata lokaci yayi ciki da iya kulu yana ta kaimata
duka, ta ko ina sauke mata jibga yakeyi, da gudu ta fad'a d'akinta ta rufe, malam yana huci yake
fad'in :
"Gara da Allah bai baki haihuwar d'iya mace ba, don kuwa wannan bak'in son kud'in, naki, tsaf
zaki maida 'yar jari kina turata tana nemo maki kud'in, haka kawai ki jazawa mutane bala'i, to
wannan salon rashin mutuncin naki ba a gidana ba, ki tattaro kayanki ki barman gida, kije cen
gidanku har sai na nemeki, zaki fito ko sai na b'alla k'ofar?".
Sumui sumui iya kulu ta bud'e d'aki ta fito, zata fara bashi hak'uri yayi saurin cewa da ita, duk
kalmar da zata fito bakinta a lokacin to a bakin aurenta ne.
Aiko jiki ba kuzari taja k'afafu ta fita gidan, tana ta kuka wiwi tabar gidan, kande da ta kasa
kunne take saurare tayi shewa ta buga cinya tace:
"K'urunk'us kan d'an b'era"
Izzatu dake rakub'e tana kuka, malam yaje ya tada ita yakaita d'akin hassatu ya tambayeta
abunda ya faru, aiko bakinta a sake ta fara yimasa bayanin duk azabar da iya kulu take bata,
malam har saida yayi hawaye saboda tausayinta, suna cikin firar ne Garzali ya dawo daga birni,
saboda wata jarabawa da yaje yi ta fagen share karatun shiga jami'a direct, da suka zana
tsawon sati biyu duk yana cen a birnin, duk wannan badak'alar da akayi, baya gidan yana cen
wajen fafutukar zana jarabawar.
Garzali yayi mamaki sosai da yaga baiga, mama hassatu da iya kulu ba, bakinshi yana rawa ya
tambayi malam ina sukaje ne?,malam ko saboda damuwowin da suka cunkushe zuciyarsa
sunyi masa yawa, ba b'ata lokaci ya fara zayyanawa Garzali abunda ya faru a tsakaninsu duka.
Jin abunda ya faru Garzali hankalinsa yayi k'ololuwar tashi, jiki a mace ya fara baiwa malam
hak'uri, akan ya dawo dasu, malam ransa a b'ace yace:
"Koda zanje bikon hassatu ta dawo, to ba zancen zuwan izzatu karatu a birni, 'yar kuluwa kuma
sai ta horu, sannan zata dawo a gidannan"
Duk da garzali yaji zafin, abunda iya kulu tayiwa izzatu, amma yaji haushin hukuncin da malam
ya yanke mata, amman ya b'oye damuwarsa, ya fara nunawa malam amfanin karatun izzatun,
saboda ko halin da take a ciki idan ta samu ilimin, koda ta gano wacece ita daga baya, to
damuwar bazata yimata yawa ba in tana da karatunta, zai amfaneta har wasu su amfana da
baiwar da Allah ya bata.
Malam ya shiga zurfin tunani na 'yan lokuta, sannan ya d'ago kai yace:
"Koda zan amince da karatun, to sai dai idan zata dinga zuwa ta dawo a kullum ta kwana a
gida"
Garzali yayi murmushin jin dad'i, sannan yace:
"Akwai makarantar jeka ka dawo ta 'yanmata zallah za'a iya sakata a cen, amman fa akwai aiki
ja, idan akace kullum taje ta dawo, zirga zirgar zai bata wahala sosai"
Malam fuska a had'e yace:
"Abunda na riga naji zan iya kenan, saboda ku taso muje dukanmu, mu baiwa mamarku hak'uri
ta dawo, tunda dama dalilin fushin da takeyi kenan, to anyi abunda takeso sai a zauna lafiya"
Aiko suna zuwa, suka bata hak'uri, duk da taso ta d'an ja aji, amman dai tausayin izzatu da
yanda taga malam duk ya rame yasa ta amince zata dawo d'in, don itama a takure take zaman
da takeyi, saboda son zama da malam yafi mata komi a rayuwa, haka suka gangamo suka
dawo gida, a cikin farin ciki da kewar juna.
Dawowar mama hassatu da kwana biyu ne, aka fara yiwa izzatu cuku cukun neman makaranta
a birni, aka samu wata makarantar kud'i ta 'yanmata zallah aka sakata, mama hassatu ce ta
biya kud'in makarantar, a kullum Garzali ne yake rakata makarantar, yayin da shi kuma yake
wucewa wajen wani aikin gini da akeyi, yayi dace aka d'aukesa, a yini dubu d'aya ake badawa
idan sun k'are, saboda shi iya aikin nasa dai dai lokacin tashin su izzatu makaranta ne sai
abashi d'ari biyar, sai yaje ya d'auko ta su shiga mota su tafi gida.
Haka sukeyi har lokacin da sakamakon jarabawar su Garzalin ta fito, aka yi dace ya canye
duka, inna hassatu ta baiwa malam shawara aka sayar da wata k'aramar gonar shi, ya biyawa
Garzali kud'in shiga jami'a, akayi komi a wadace ya tafi University, ya fara karatu a sashen
lafiya.
Tafiyar Garzali ta saka wasar zata ta fara bugawa, muje zuwa mutanena yanzu wasa zata
fara♀️♀️⛹♀️.