Showing 81001 words to 84000 words out of 119425 words

Chapter 28 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

shiga k'aton hall d'in da za'ayi birthday d'in, suna shiga suka tarar
da wata 'yar karamar fitila da su kawai take haskewa, izzatu ta ri'ko hannun ammaah a cikin jin
tsoron ganin wani dake takowa a hankali izuwa wurinsu, ammaah tayi dubarar janye jikinta ta
shige duhun itama, izzatu ta waiga bata ganta ba da sauri ta juya zata fita aka dallaro haske ko
ina ya gauraye tareda had'a muryarsu gaba d'aya suka ce, "Happy birthday to you" da
sauri ta juya idanuwanta sukayi karaf da yayanta dake a tsaye hannuwanshi a cikin aljihu yana
yi mata wani kallon da su kawai suka san ma'anar shi da sauri ta dafe bakinta alamar mamaki
sannan ta d'aga murya tace, "wow."


Aiko a million taje ta rungumeshi wuri ya barke da tafi tareda saka wata had'ad'd'iyar wak'ar
birthday da akayi dominta kawai, ana ta buga wasu gangunma masu amsa amo mai dad'in
saurare a kunnuwa, Garzali ya b'anb'areta a jikinshi ba don yaso hakan ba ya ri'ko hannunta
suna tafe sai k'are masa kallo takeyi har suka je wajen da aka tanada na musamman domin
yanka wani k'atoton cake mai zanen sunanta, da wani had'ad'd'en candle mai bada wasu kalolin
wuta suna tartsatsi a sama, mutane suka zagaye ta sai d'aukar pic's sukeyi masu video suna yi,
Garzali yayi mata nuni da ido ta duk'a ta hure wutar da baki aka saka tafi raf! raf!, sannan ya
d'auko wata 'yar k'aramar wuk'a da tasha ado ya mik'a mata ta feshe shi da murmushi sannan

ta saka hannu ta karb'a, ta saita wuk'ar zata yaka Garzali ya aza hannunshi akan nata, shu'aib
dake a tsaye haushi kamar ya kar shi shima ya zulo ya aza nashi hannun a saman na Garzali,
suka yiwa juna kallon ido da ido shu'aib ya galla masa harara yayinda garzali ya feshi shi da
murmushin mugunta mai cike da tura haushi.
A tare dasu duka su biyun izzatu ta yanko cake d'in, ta d'auko k'iren cake d'in da ta yankan ta
d'an gutsura sannan ta nufi bakin shu'aib dake kusa da ita, saboda shiga tsakaninta yayi da
Garzali shu'aib ya bud'e baki a cikin alfakharin shi zata fara ba, amma ta buga masa wata
harara takai dubanta ga fuskar Garzali da sai wani annuri ke fita a cikinta, ta feshe shi da wani
tsadadden murmushi ta nufi bakinshi da cake d'in aiko ya saka hannu biyu ya k'ara rik'o hannun
ta tura masa cake d'in, aiko sai tafi ya karad'e wurin shu'aib ya bisu da wani kallo a cikin wani
bak'in ciki da ya mamaye masa zuciya, ya kallesu yayi k'wafa ya bar wurin fuu ya fita hall d'in
ma gaba d'aya, izzatu tayi kamar batasan yayi ba daga nan aka ci gaba da 'yan raye raye da
pic's kala kala, ana cikin shagalin ne wayar Garzali tayi k'ara alamar ana kiranshi, koda ya d'aga
wayar sai baya jin me ake fad'a sabosa ruguntsumin kid'an dake tashi, hannunshi a cikin na
izzatu yace da ita ta jirashi yazo ba don taso ba ta sake shi ya fita da sauri wayar shi a manne
da kunne yana magana.

Fitowarshi keda wuya ya d'an rab'a wani sak'o yana magana yaji an saka masa wani abu an
rufe masa fuska, wayarshi ta fad'i anan mutane kusan biyar suka rufu a kanshi suka daddaure
shi suka ja shi a cen bayan hall d'in, suka yar daga nan suka yi ta jibgarshi har sai da suka
tabbatar da ya lallasu sannan suka bud'e k'yallen da suka rufe masa fuskar dashi, suka ci gaba
da jibgarshi yayi minti biyar idonshi a rufe sannan ya d'ago ya k'are masu kallo d'aya bayan
d'aya, a cikin zafin nama yayi ciki da wani ya kada shi ya haye yana so ya kunce d'aurin ya jibgi
wanda ya kada d'in 'yan uwan shi suka yi ta kai masa duka yana karewa har ya samu sa'ar ciro
hannuwanshi daga d'aurin aiko yayi ta kaiwa wanda ke k'asa duka na hauka har sai da yaga
yayi mashi damage ga fuska, sannan ya koma ga sauran suka yi ta d'auki ba dad'i da guda
guda yayita raunatasu, domin idan ya lik'ewa d'aya har sai yaga yaci galabar shi sannan ya
koma wurin wani, d'aya daga cikinsu ya ciro 'yar k'aramar wuk'a ya zo yankawa Garzali a ciki ya
rik'e wuk'ar da hannunshi ta yankeshi har jini yana zuba, sannan ya kai masa duka a hannunshi
da k'arfi har sai da hannun yace k'as! alamun ya karye, aiko ya fad'i a wurin yana kuwwa
wanda kuwwar ce ta janyo security's dake wajen hall d'in karasowa wurin, Garzali ya fad'i a
k'asa ba shiri saboda jigatuwar da yayi hannunshi sai tsiyayar jini yakeyi.



Akafta🤾🏻â€â™€ï¸

D/Auta ceí ¾í´í ¼í¿»
[8/22, 1:56 AM] Auntyna: https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp





*�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*



*NA HADIZA D/AUTA*



*🔥BAKON YANAYI🔥 book ne da ke tafe da zafin shi kada ku bari abaku labari salonshi daban
yake da saura 200 kacal👌🏻 zata sa ki kasance d'aya daga cikin member ta 🔥BAKON YANAYI
🔥*

*KAR KU MANTA LITTAFAN HADIZA D/AUTA*

*Tartsatsi*
*Ruwa da kanra*
*Bakan Gizo*
Sai
*🔥BAKON YANAYI🔥 mai take da nashi kalar salo kar ku bari a baku labari sayen nagari
maida kud'i gidaí ¾í´í ¼í¿»*


*FIFTY FIVE*

**********************
Izzatu kuwa idonta a k'ofa sai kallon ta inda yayanta zai b'ullo takeyi, idan har wani ya rufe mata
inda zata hango k'ofar da kyau har wani tsalle takeyi domin kawai taga shigowarshi, da ta gaji
da wara idon ne ta ji shirun yayi yawa har lokacin bai dawo ba, ta d'age rigarta ta fara taku a
cikin sauri zata fita hall d'in,Ammi da ammaah idanuwansu da suke a kanta tareda duk wani
motsinta a wurin, saboda akan idanuwansu Garzali ya fita yana waya, kuma sunga yanda ta
damu da rashin dawowar tashi shiyasa ammi ta yi saurin biyota tareda d'an d'aga murya ta kira
sunanta, da sauri izzatu ta waigo ta kalli Ammi dake k'ok'arin k'arasowa wurinta fuskarta a
d'aure tace da ita, "Ina zaki je ne.?"

Izzatu ta fara 'yan kame kame Ammi tayi mata wani kallo tace,

"Ki rage wannan zumud'in da kikeyi yayi yawa fa, saboda ba'a nunawa namiji tsantsar so a fili ki
kiyaye."

Izzatu ta sunkuyar da kanta saboda jin kunyar idanuwan Ammi da ta gano wurin garzali zataje,
Ammi kam tana k'are maganar ta shige taron ta barta anan ammaah da ke tsaye a bayansu
kad'an, saboda ganin Ammi tana yiwa izzatu fad'a yasa bata k'araso ba don bata so ta shiga
hak'k'in su, har sai da taga wucewar Ammi'n sannan ta k'araso wurin izzatu tareda ri'ko
hannunta suka fito hall d'in.

Fitowarsu keda wuya izzatu ta fara waige waige bata hango yayanta, ba sai idanuwanta da
sukayi caraf da wayar garzali dake yashe a wurin, duk da ba wani tantance wayar tayi ba
amma zuciyarta ta bata cewa wayar yayanta ce, jikinta har rawa yakeyi taje ta d'auki wayar
tareda duddubata a cikin tashin hankali ta kira ammaah tace,
"Zo kiga wayar yayana wallahi amma jikina yana bani ba lafiya ba, tunda da wayar ya fito yana
ta magana amman yanzu gata a k'asa shi baya nan."

Ta k'are maganar tareda zubowar wasu hawaye masu zafi akan fuskarta, amma ta k'araso
idanuwanta akan wayar itama zuciyarta a cike da wasi wasi saboda ta hango lokacin da zai fito
yana wayar itama, da sauri ta jawo izzatu a jikinta tana lallashi tareda yimata kalamai masu
kwantar mata da hankali akan cewa ba abunda ya faru , izzatu kanta a kafad'ar ammaah taji
kamar sautin duka a bayan hall d'in, da sauri ta d'ago jikin ammaah tayi bayan da gudunta aiko
zuwanta yayi daidai da wani security da ya tallabo garzali a jikinshi saboda raunin da yaji a
hannu jini ya zuba sosai har ya fara bugar dashi yana mashalo.

Aiko a d'ari ta kai wurinshi tareda k'walla kiran sunanshi tana jijjigashi tana kuka,idanuwanta
suna kai ga hannunshi da har lokacin bai bar d'igar jini ba aiko ta k'ara rud'ewa ta ri'ko hannun
tana hura masa iska a baki tana kuka, me ta tuna a zabure ta saki hannun ta jawo leb'en
rigarta da yake ja ak'asa ta yago da k'arfi har sai da hannunta ya yanke, kasancewar rigar wani
yadin material ne mai arnen kyau ga k'wari, aiko ta saka shi ta fara d'aure masa hannun dashi
tana kuka, sannan ta bada umurnin ayi gaggawar kaishi gidansu a nemo masu duba shi jikinta
yana kyarma.

Koda ammaah ta k'araso har an fito wajen za'a sanyashi a mota, izzatu a firgice ta shiga motar
itama ta zauna tareda aza kanshi a cinyarta tana kiran sunanshi da yayi hak'uri sai sannu take
yimasa, a cikin tsawa tace aja motar su tafi, ammaah tana k'arasowa motar tana tashi itama ta
fad'a wata motar aka bi bayansu tareda rakiyar wasu sojoji har gida, tun kafin suje aka kira
wasu likitoci suna isa gidan suma suna k'arasowa, aka kai Garzali a wani had'ad'd'en d'aki aka
shinfid'e akan gado likitoci suka rufu akanshi da kayan aikinsu sai nuna k'warewarsu sukeyi,
bayan sun ciyo kan matsalar suka YI masa dressing d'in ciwukan suka yi masa allurar bacci
domin jikinshi ya sami hutu.

Izzatu zaune a tsakiyar gadon sai sannu take zuba masa duk da tasan bacci yakeyi, bayan
likitocin sun tafi amma ta k'araso ta zauna a ranta sai jinjina irin wannan so da izzatu take yiwa
Garzali, yanzu ta k'ara tabbatar da maganar da kallah ya fad'a mata akan shak'uwarsu tun suna
k'ananu.
Ammaah ta tabbatarwa zuciyarta tabbas soyayyarsu daga ALLAH ce, kuma muddin ana son
rayuwar izzatu ta inganta to dole ne a aura mata yayanta Garzali, domin rabata dashi tamkar an
jefa rayuwarta ne a cikin had'ari , taci alwashin zata yi iya k'ok'arinta domin ganin tabbatuwar
wannan aure nasu.
***

A cen wajen birthday d'in kuwa wad'annan 'yan iskan da suka daki Garzali an watsa su a motar
sojojin bayan an lallasasu da kyau, a cikin hall d'in kuwa ba wanda ya lura da izzatu bata nan in
ba Ammi ba, aiko sai cashewarsu sukeyi har sai da lokacin tashi yayi aka watse taron, zuciyar
Ammi sai tunanin ina Ammaah da izzatu suka je har yanzu da basu dawo ba?, har suka dawo
gida tunanin da takeyi kenan ta d'aga waya ta kira ammaah tana tambayarta lafiya?, ammaah
tayi mata bayanin duk abunda ya faru da itama taji abakin wani security, tasanar da ita ga inda
suke aiko Ammi jikinta yana rawa ta nufo d'akin, ganin yawan dressing d'in da aka yiwa Garzali
yasa jikin Ammi ya k'ara yin sanyi k'alau daman ita mace ce mai tausayi, da sassarfa ta k'araso
tana k'are masa kallo a cikin tausayawa musamman yanda taga fuskar izzatu tayi ja saboda
tsananin kukan da tasha, wanda ita kanta tasan dole ne hakan ta kasance saboda yanda taga
shak'uwarsu.

Garzali ko sai sharar baccinshi yakeyi hankali a kwance,ganin hakan yasa Ammaah tace da
izzatu ta taso suje su barshi yayi barcinshi a nutse, izzatu ta kafe akan ita dai bazata bar shi shi
kad'ai ba, Ammi tayi saurin galla mata harara ba shiri ta sauko gadon ta fita fuu tana kuka,
Ammi ta girgiza kai a ranta tace, "Wannan yarinya a yaushe zatayi hankali ne.? "
Izzatu koda taje d'akinta fad'awa tayi akan gado tana wani irin kuka gwanin ban tausayi,
ammaah dake biye da ita a baya ta shigo d'akin tareda k'are mata kallo na tsawon mintuna,
sannan ta tako a hankali ta k'araso ta zauna akan gadon, itama fuskarta a cinkushe ba walwala
ta kira sunan izzatun a hankali, izzatu ta d'ago fuskarta da tayi sharkaf da hawaye tace,
"N'aam ammaah"

Amma ta sauke k'atuwar a jiyar zuciya tace, "kiyi hak'uri kinji 'yata insha ALLAH zaiji sauk'i,
ki kwantar da hankalinki ki tashi ki cire kayanki kiyi wanka ni da kaina zan raka ki wurinshi ki
k'ara ganoshi."

Izzatu tayi saurin share hawayenta tace,

"Nagode ammaah tah! Amman yanzu in har ya falka ba kowa fa.?"

Ammaah tayi murmushi har sai da hak'oranta suka bayyana tace,

"Akwai wad'anda zasu kula dashi ko baki nan ke naki kawai kije ki dubo jikinshi ki dawo."

Izzatu tayi saurin fad'awa a jikin ammaaah tana share hawaye tace, "Yanzu shikenan ni ba
sai naje na kwana a cen ba.?"

Ammaah ta zaro idunawa a waje tace,

"Zaki kwana acen amma ba yanzu ba har sai mun d'aura maku aure keda shi."

Izzatu tayi saurin rufe fuska da tafukan hannunta, tareda mik'ewa tsam ta shige toilet tana
dariya ammaah ta bita da kallon tana yimata dariya, bayan shigewarta toilet ne ta fito zata shiga
d'akinta ne taci karo shu'aib a tsakiyar falonta yana kai da kawo.

Ammaah tayi mamakin ganinshi a wannan lokacin don tasaN baya shiga wurinta da anyi
magriba, idonta akanshi ta karaso kafin tayi magana ya rigata da cewa, "Ammaah wai da
gaske ne wannan d'an k'auyen yana cikin gidannan.?"

Ammaah tayi mashi wani kallon tuhuma tace dashi, "Eh ya aka yine?"

Shu'aib ya wayance yace, "A'a ba komi daman maganar naji nace bari nazo na tabbatar."

A cikin rashin damuwa da maganar ammaah ta fara tafiya zata shige d'aki, sannan wani tunani
ya fad'o mata a zuciya ba shiri tayi saurin waigowa idanunta a kan na shu'aib tace, "ina fatar
dai ba kaine kasa aka yi masa wannan aikin ba?"


Shu'aib yayi wani munafukin murmushi yace, "Ni miye ruwa na dashi ne?ammaah? Amma
fa wallahi na fara gajiya da abunda yarinyar cen take yimani fa, kina kallo fa agaban kowa tayi
man wulak'anci bata shayin tozartani ko a ina ne, a hakan zamuyi auren bata ganin girmana.?"

Izzatu dake fitowa a d'akinta jin wannan maganar tayi saurin k'arasowa tareda rik'e kunkuru
tace, "wane aure kake fad'a?ai wallahi da in aureka gara in mutu banyi aure ba, da bakinka
ka fad'a kace ko a k'afa aka d'aura maka ni sai ka kunce, wani kalar zagi ne baka yiman ba nida
iyayena matsiyata 'yan k'auye?, sai yanzu zaka zo kana wani zancen aure a tsakaninmu.?"
Ta k'are maganar tareda murgud'a masa baki shu'aib ya rud'e saboda ganin yanayin kallon da
amma take yimasa, a cikin rawar murya yace, "Duk abunda kike fad'a ai a ada ne da
bansan 'yar uwata bace ke, amma ai yanzu tunda Abba ya yanke hukuncin zamuyi aure ai
kinga duk da bana so na hak'ura zanyi masu biyayya, amman ke a kullum idan baki
wulak'antani ba bakya jin dad'i."

Izzatu ta zaro idanuwa tareda kallon ammaah tace, "Kinji ko ammaah da bakinshi yace
ba sona yakeyi ba biyayya zaiyi, to bari kaji ni inada wanda nikeso kuma yake sona, saboda
haka kai tunda baka so biyayya ce zakayi ka aureni, to kaje an yafe wannan biyayyar akwai
hanyoyin samun lada da yawa idan anyi wa iyaye biyayya, don haka ni kam ko kaine autan
maza bazan tab'a aurenka ba wallahi, kuma ka sani duk wani k'ulle k'ullenku kai da mahaifinka
a tafin hannuna yake k'iris nike jira in fallasa sir.......... "

Karaf Ammi dake tsaye tana saurarensu ta kaiwa izzatu wani bahagon mari, gaba d'ayansu
suka juya suna kallonta ammaah ranta a b'ace tace da AMMI, "me 'yata tayi maki ne da zaki
daketa?, meye ruwanki a cikin maganar ne? ina fa sane da yanda kike takura mata fa ."

Ammi a cikin damuwa saboda ganin yanda ran ammaaah ya b'aci tace, "Kiyi hak'uri
ammaah amma fa kina kallo take ta tsigalewa yayanta, ko ba komi ai ya girmeta ballantana
kuma yanzu yana da matsayi biyu a wurinta."

Ammaah ta jawo hannun izzatu suka shige d'aki ba tareda tace da Ammi k'anzil ba, shu'aib
kuwa tunda yaji izzatu ta furta tasan sirrinsu shida Abba, wani gumi ya tsattsafo masa tun daga
kai har k'afafuwanshi saboda jin tsoron tonuwar asirinsu.

Ammi takai kallonta akanshi duba da yanayinshi da taga ya shiga ne itama ta zargi wani abun
aranata, amma ta yi kamar bata gano yanayin da ya shiga ba tace dashi, "Yi hak'uri shu'aib
akwai k'urciya har yanzu akan k'anwarka, ka barni da ita ni zanyi maganin abun."



Shu'aib ya fara inda indar fad'in ba komi Ammi nagode, ya YI saurin barin wurin ya fice
zuciyarshi sai kai da komo takeyi yana tambayar kanshi me izzatu ta sani dangane da sirrinsu?.

Ammi ta bishi da wani kallo sannan ta shige d'akin ammaah da sallamarta, koda taje ta iske
Ammaah sai lallashin izzatu takeyi akan tayi shiru, itama ta sami gefen gado ta zauna sannan
ta fara baiwa ammaah hak'uri, ammaah tace, "ba komi amman ki kiyaye takura man yarinya."

Daganan suka fara hira a tsakaninsu Ammi ta kalli izzatu tace, "ke wani sirri kika sani da har
kike barazana dashi.?"

Izzatu tayi dariya tace, "Wallahi ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login