Showing 69001 words to 72000 words out of 119425 words
Chapter 24 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
taji zafi tayi 'yar k'ara, yayi
murmushi mai sauti yace, "ke a tunaninki akwai wani abunda zai sauya mani ra'ayi akanki,?,
never wallahi domin kuwa zuciyar Garzali da son izzatu take rayuwa, tun bansan minene so ba
har izuwa wannan lokaci, soyayyarki mahad'in rayuwa tace, duk wani bugun numfashi na da
soyayyarki yake tafiya, akanki idanuwana sun rufe ruf na kasa hango wata 'ya mace da zata
kamo kafarki ma balle tace zata jera kafad'a dake farincikin zuciyata, saboda haka, ki ma daina
wannan zance da baya da tushe balle makama."
Jikinshi har rawa yakeyi ya sauko k'asa yayi obeying a gabanta, idanunshi akanta ya k'ara
cewa, "ni Garzali ba'a halicceni don ko wace mace ba sai donki ke kad'ai izzata, don Allah
ki soni koda quarter'r son da nike yi maki ne k'anwata, i love you over and ever, my special
diamond in my life."
Izzatu shauk'in son Garzali ya k'ara jefata a cikin farfajiyar tafkin kogin kaunarshi, ba shiri ta
sauko itama suna facing din juna jikinta yana b'ari tace,
"Ni taka ce yayana don kai kad'ai kawai aka halicceni,zuciyata da gangar jikina duk naka ne,
kasani ina maka son da NI kaina bansan iya adadin shi ba."
Garzali ya fito da wani d'an karamin zobe a aljihunshi yana k'ok'arin saka mata yace, "Zaki
aure ni.?"
Izzatu ta share hawayen da ke kwarara akan kyakkyawar fuskarta tace, " kayi yanda kake so
dani da rayuwata yayana, ka saka a ranka cewa ni taka ce har abada, ruwa da iska bazasu iya
rabani da kai ba."
Garzali ya saka mata zoben suna kallon juna suna murmushi, zai k'ara yin wata magana ne aka
dallare su da hasken fitila, dukansu suka shiga taitayinsu, jiki ba kuzari suka tashi sukayi tsaye
cirko cirko, suna jiran mai haske su da fitilar ya k'araso.
Aiko sai ga shu'aib ya bayyana wanda har a lokacin bai janye fitilar akansu ba, aiko a zafafe
izzatu ta buga wani bajimin tsaki, saboda jin haushin katse masu fira mai dad'i da yayi, a zuciye
ta saka hannu ta buge fitilar ta fad'i a k'asa, jikinta yana rawa saboda masifa tace,
"A cikin makafin kai wani tsohon lalataccen makaho ne?, da duk wannan haske dake shinfid'e a
lungu da sak'on gidannan, ace baka gani har sai ka saka fitila kayi yadiya.?"
Shu'aib bai bi ta kanta ba yakai kallonshi akan fuskar Garzali da yake Jin tamkar ya rufeshi da
duka, a cikin had'e fuska shu'aib yace, "Yanzu kai ka rasa wacce zaka saka lungu a lungu
kana k'wak'ula, sai matar da aka bani sadaka na aura?, amman lalle wannan d'an k'auyen ka
tarowa kanka aradu da k..... "
Kafin yakai k'arshen maganar shi izzatu tayi tsalle ta faska mashi mari a zuciye, ba shiri shu'aib
ya dafe gefen da yasha marin yace, "laa la la yanzu don bakida kunya ni kika mara?"
Izzatu ta d'aga murya tace, "an mareka d'in kai wanene banda d'an lasar arzik'i, wallahi ka
kiyayi fushina tun kafin in saka ka barin gidannan talkaminka a hannu."
Shu'aib bai jira komi ba yayi ciki da Garzali ya fara kai masa duka na farko, da sauri Garzali ya
rik'e hannuwansa duka biyu ya matse da k'arfi har sai da yayi k'ara, a fusace yace dashi, "Ka
kiyayi ranar da ta kuskure na gwada k'wanji na anka, don kasani wallahi sai na sumar dakai
k'aramin mara kunya."
Aiko shu'aib da yaji azabar matsa sai gashi yana ihun neman taimako, ba shiri su malam suka
fito suka tarar da Garzali ya bank'arewa shu'aib hannuwa duka biyun, a cikin fad'uwar gaba
malam ya katsawa Garzali tsawa yace, "Me nake shirin gani Garzali sake shi nace."
Aiko koda Garzali ya sakeshi ba k'aramar galabaita yayi ba, ya fad'i a kasa sharaf yana maida
numfashi, a cikin fushi malam yace, "Me yayi maka ne da zaka jiwa yaron mutane, ka ja
mana tashin hankali muna zaman zamanmu?."
Garzali dai baice k'anzil ba saboda zuciyarshi ta kawo wuya, sai shigewa da yayi inda aka
saukar dasu yana huci, malam yakai dubanshi ga izzatu yace, "me ya had'a su ne
halan?"
Izzatu tana kallon shu'aib yana maida numfashin wahala ta k'ume dariya tace, "Ai shi yaja
fad'an shiyasa malam, kasan yayana baya jan fad'a sai dai ajashi, kuma duk wanda rabon
wahala ya hau kanshi to zai gano kuskurenshi."
Tana k'are maganar ta dallawa shu'aib wata jar harara, malam ya fahimci izzatu sarai gugar
zana ce take yiwa shu'aib d'in, shiyasa ya fara bashi hak'uri, a zuciye ya tashi ya nuna su
dukansu yace, "wallahi ya jawo maku shiga uku sai kunsan dani kuje zancen."
Izzatu ta had'e fuska ba shiri tace, "kai ko a tara ma zaka saka kanka wallahi muddin kayi
gangancin shiga hurumina nida iyayena."
Shu'aib ya duk'a ya d'auki fitilarshi yayi fuuu ya bar wajen, izzatu ta d'aga murya tace, "in
kunne yaji yasin jiki ya tsira."
Mama ta dungure mata kai tace, "wai ke ba mijinki bane?"
Izzatu ta zaro ido a waje tace, "Wallahi mama sai dai in mutu banyi aure ba."
Ta k'are maganar tareda b'ata fuska, malam yace da mama su je su kwanta dare yayi, sannan
suka yi masu sai da safe suka wuce, izzatu taso mama tabarta ta kwana anan wurinsu, amma
mama tace dole sai ta koma wurin hajiya fatima ta kwana acen, aiko ta d'auki ilham har tana
bacci ta sab'a ta a kafad'a suka tafi, mama ta girgiza kai tace, "Wannan yarinya kina da abun
dariya wallahi, to asauka lafiya sai da safe."
Takai kallonta ga iya kulu dake baje a tsakiyar falon tana ta sharar baccinta har da minshari, a
cikin zuciyar ta tace, "Sannu kura"
Saboda ganin kular farfesun da ta ci ko rufeta ta kasa yi, saboda ta canye fiye da rab'i duk
girman kular kuwa.
Koda safiya ta waye bayan sun kimtsa ne aka yi masu iso har cikin gidan, inda su hajiya fatima
da hadizatou, iya kulu sai rabon idanuwa takeyi tana jinjina irin wannan daular arzik'i da
idanuwanta suka yi tozali, a cikin ranta tace, "Ni ko a lahira na sami rabin rababar hakan
ai na more, balle a nan gidan duniya, wai kodai sun d'auka bazasu mutu ba ne?, oni 'yar kuluwa
ashe inda ranka kasha kallo."
Mai girma Gwamna yayi masu godiya tareda goma sha tara ta arzik'i da rakiyar motoci tamkar
wad'anda za'a kai amarya har k'auyen, aiko mutanen k'auyen suka cika k'ofar gidansu malam
kowa sai barka da zuwa yake yimasu, sai zura ido sukeyi suga ta inda izzatun zata fito, domin
kaf k'auyen har garuruwan dake kewaye dasu sun san da labarin IZZATU d'iyar Gwamna ce.
Dak'yar su malam suka kutsa suka shiga cikin gidansu, iya kulu sai d'age hanci takeyi sama
alamar tana jin warin su, saboda ita in ta ita ake bi ko k'auyen bazata dawo ba, shigarsu gidan
keda wuya kande ta shigo gidan a d'ari domin tazo taji labari a wurin 'yar kuluwa, ta mance duk
kashe din da malam yayiwa mijinta akan kada ta sake shigar masa gida, jikinta yana b'ari take
yiwa su malam sannu da zuwa, iya kulu dai sai wani kallo take yimata kamar bata tab'a sanin ta
ba, kande tace, "haba 'yar kuluwa abun ba ko magana?, ko duk ruwan gidan Gwamnan da
aka shawo ne ake yimuna gani gani."
Iya kulu tayi mata kallon hadarin kaji ta zuge wata jaka da tazo da ita, ta ciro wata leda ta bud'e
aiko sai ga k'amshi ya bugi hancin kande, ba shiri ta cafko ledar tace,
"Bari in bud'e maki ranki shi dad'e"
Iya kulu tasa k'afa ta shure hannun kande a zafafe tace,
"Dad'ina da talaka kenan masifaffen kwad'ayi ne dashi, ai kya jira kiga abunda zan baki ba sai
kinyi zalama ba, ni wallahi bani son jarababben kwad'ayi."
Kande ta b'ata fuska tace, "To ke 'yar kuluwa ai k'uda ma ya shafa maki lafiya indai ta
bangaren kwad'ayi ne."
Iya kulu tace, "duk yadda na lalace ai na fiki, keda ko marayar baki tab'a zuwa ba balle kiga
Gwamna a idanunki, ni ko fa har kwana nayi a gidan Gwamna na dangwali arzik'in Gwamnati
nayo gida, ki bini a sannu koda zan d'auki mariya in je da ita birni ta dinga yiman aikatau, kema
ki sheda kin had'a makotaka da 'yar kuluwa mai k'ashin arzik'i."
Kande jiki a sanyaye tace, "nayi biyayya nabi ALLAH na bi ma'aiki na bi ki 'yarkuluwa, aike
yanzu dole ne ma adinga a lallab'a ki."
Iya kulu taji dad'in furucin kande ta bud'e ledar ta kwaso naman cike da hannunta ta mik'awa
kande tace,
"Tafi gida kici keda yaranki ni bacci nikeji"
Aiko kande ta zuba nama a mayafin zanen da ta yafo ta k'ulle jabau tace da iya kulu, "Taka
lafiya mai k'ashin arzik'i a fito lafiya nagode."
Iya kulu ta shige d'aki tana tafiyar tak'ama.
*****
Izzatu kuwa tasha kuka sosai saboda rabuwar ta da su malam, hajiya fatima sai lallashinta
takeyi, dak'yar ta samu tayi shiru, aiko ta iske Abbaah har k'aton falonshi na alfarma, tace dashi
tana so a siye gidan da su malam zasu dawo a cikin lokaci, mai girma Gwamna ko anan take
ma ya buga waya ya bada umurnin a nemo masa gida mai kyau, izzatu tace dashi mai part biyu
takeso don kowace ta zauna sashenta ba takura, amman a cikin zuciyarta taso hakan ne don
bata son iya kulu ta koma saka mamarta a cikin damuwa, aiko kafin tabar wajen sai gashi
ankira ance ansami gidan,a take ya bada kwangilar gyaran gidan ta ciki da bayanshi, izzatu tayi
masa godiya sosai sannan ta fito zuciyarta fes, domin tana son taga mamarta a kusa da ita, duk
da tasan baza'a dinga barinta tana fita sosai ba saboda tsaro.
Takanas hajiya fatima tasa aka kai IZZATU shopping complex ta zab'o duk abunda take buk'ata,
ta b'angaren suturu takalma kayan kwalliya da mayukan shafawa masu kyau da sabulansu,
harta kayan k'walam da mak'ulashe bata bari ba, aiko ta saki jiki ta jibgo kaya na ji da fad'i itada
ilham da mamarta, malam da iya kulu da yayanta Garza kowanensu sai da ta jido masu uwar
siyayya, wad'anda ya dace akai d'inki aka je aka bada.
Kafin sati d'aya izzatu fatarta ta fara canzawa i zuwa kalar larabawan asali sak!, ta k'ara kyau
hutu ya fara ratsata.
An gyara gidansu malam komi yayi tsaf tamkar daman cen sabo ne aka gina, mai girma
Gwamna yasa aka kwaso su daga su sai kayan jikinsu suka tare a sabon gidansu, inda komi
yaji tamkar gidan wata sabuwar amarya d'iyar mai hannu da shuni.
Congrats í ½í²ƒí ¼í¿»í ½í²ƒí ¼í¿»í ½í²ƒí ¼í¿»í ½í²ƒí ¼í¿»ALKHAIRI danko ne ALLAH ya bamu zuciyar shuka alkhairin
Akaftaí ¾í´£
D/Auta ceí ¾í´í ¼í¿»
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈ï¸*
*NA HADIZA D/AUTA*
*in ba comments yasin zan fara hutun shekara*
*PAGE FORTY NINE*
**********************
A ranar da su izzatu suka yi bikin k'are makaranta, Dr yaje har makarantar domin kawai ya taya
izzatu murnar wannan rana, ganin su malam a wurin shi yasaka shi barin makarantar ya koma
gida, don baya son malam ya ganshi ya zargi wani abu dangane da shi, tunda yasan yayi masa
kashedi akan bashi ba izzatu.
Koda ya koma gida ya bud'a TV a falon magaifiyarshi yana kallon duk abunda ke gudana live a
gidan Tv'n, ana hasko fuskar izzatu da mai daraja Gwamna yana kabbarar, yayi saurin
k'wallawa mahaifiyarshi kira ta fito a firgice, saboda bacci mai nauyin da takeyi ya tada ita, ta
sami gefen d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna, idonta a kanshi tana mashi kallon tambayar
me ye mak'asudin wannan kiran mafarautan da ya danna mata?, aiko da sauri Dr idonshi akan
tv'n yace da ita,
"Matar da naso aure ce kuka hanani saboda rashin asali, to yanzu dai gatanan a gaban kowa
gaskiya tana son bayyana ashe d'iyar yahaya badawi ce."
A cikin kwalalo idanuwa mahaifiyar Dr ta k'urawa TV kallo, akayi dace a lokacin hadizatou
rungume da izzatu, masu camera sai haska fuskokinsu masu kama da juna sak! sukeyi, a
zabure mamar Dr ta mik'e tsaye tareda dafe k'irjinta dake bugawa da sauri da sauri, hannun ta
yana rawa tayi nuni da photon izzatu da hadizatou, da ake ta haskowa a bayyane k'uru kur'u a
cikin gilashin tv'n tace,
"Yanzu kana nufin 'yar k'auyen yarinyar cen ce wannan?."
Dr ya d'aga mata kai hannuwanshi duka biyu yayi tagumi dasu, idanunshi akan tv'n ko k'yaftawa
baya son yi saboda mamakin wannan al'amari, musamman fuskar izzatu da matar Gwamna da
ake nunawa ta saka shi shiga shock sosai, sabida kamar da suke yi da juna tayi yawa matuk'a.
Mamar Dr taje jikinta yana rawa ta kashe tv'n ta fuskance shi tace, "wai bazaka kalleni muyi
maganar fahimta ba zaka maidani wata sakarya.?"
Dr ya mik'e tsaye yana kallonta a cikin wata sabuwar damuwar da ta ziyarceshi a lokaci d'aya,
saboda jin haushin rabashi da izzatun da suka yi, fuskarshi cike da takaicin abunda aka yimasa
yace, "wace maganar fahimta kike so muyi?, bayan lokacin da ni naso ku fahimceni ban samu
wannan damar ba, to ai yanzu gashi nan gaskiya tayi halinta ashe ma asalinta har yafi nawa
matsayi nesa, domin kuwa ke kanki kinsan wanene yahaya badawi, don kinfi kowa sanin duk
wani tink'ahon Abbanmu na Yahaya badawin ne, kinsani in banda taimakon da yayiwa Abba da
yanzu ko abunda zamu saka a bakinmu sai yayi muna wahala, domin shine tsanin rufin
asirinmu gaba d'aya gidan duka, shiyasa hausawa suke cewa ka dai ga mutum amma bakasan
irin baiwar da ALLAH yayi masa ba, to yanzu dai kinji izzatu mai cikakken asali ce d'iyar yahaya
badawi ce, wanda kowa ya sanshi a fad'in garinnan har da kewaye, tun kafin ya zama Gwamna
cikakken attajiri ne na gaske."
Dr yana k'are fad'ar maganganun yayi fuu zai fita yabar falon, mahaifiyar ta d'aga murya tace,
"To yanzu ya zancen auren naku.?"
Dr saboda jin haushin maganar bai san lokacin da yace, "Tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa
kan doka."
Ya fita fuu ya shige d'akin shi tareda rufo k'ofa garam, mahaifiyar shi ta biyo shi da sauri tana
fad'in, "Tunda na fara ganin yarinyar, na hango son da take yimaka a k'wayar idanuwanta,
kaje na yafe maka ka dawo da matarka ka aura, ai dama don rashin sanin asalinta ne yasa
muka ce a'a, amman yanzu tunda har gaskiya ta bayyana, angano iyayenta na ai'nahi sai ayi
auren kawai wallahi mun amince."
A cikin d'akin azafafe Dr yace, "To ai sai kuje ku nemo min auren, tunda daman cen kune
kuka b'ata shi."
Mahaifiyar ta zaro idanuwa kamar tana ganinshi tace, "Rufani ka saya inba so kake ayi
rugurugu da nama na a gidan Gwamna ba, ai ko mahaifinka bai kai matsayin da zai tunkari
Alhaji yahaya ba, yace yazo neman auren 'yarsa gareka ballantana ni ni a suwa?, kare da
gudun layya rufani kasaya da dai kai ka jaraba tunda tun farko kai aka sani."
Dr bai sake cewa da ita k'anzil ba saboda haushin da ya kume shi,domin in yakeyi tamkar a
lokacin ne aka raba shi da masoyiyarshi izzatu.
Aiko har ta gama zugar surutun ta bar wajen a cikin danasanin abunda suka aikata, musamman
ita da har k'auyen tayi tattaki taje sukayo rashin mutunci, donma Allah ya taimakesu sun sha
dak'yar don ta dad'e tana jinyar kafafuwanta saboda sukar da k'aya tayi mata a cikinsu, a
sanadiyyar gudun fanfalak'in da suka sha.
*Shin wane taimako ne yahaya badawi yayiwa baban dr????*
A wata rana ne Abbaah yaje shopping d'inshi domin ya ganewa idanunshi yanda kasuwar take
tafiya, ya fito da wasu kud'ad'e a cikin wata leda mai d'auke da tambarin sunan shagon, a bakin
shagon ne ya had'u da wasu mutane ya tsaya suna gaisawa, bayan sun k'are wajen k'ok'arin ya
shiga mota ya mance shaf ya saki ledar a wurin, tada motarshi keda wuya sai ga baban Dr d'an
acab'a ya ajiye shi a daidai wajen, yana k'yalla idanuwa ya hango ledar yashe a k'asa sannan
ya hango motar da ta tashi a lokacin, zuciyarshi ta tabbatar masa ledar mai motar ce, da sauri
ya d'auki ledar ya bud'a yaga damin kud'i d'auri d'auri, aiko ya hau acab'an suka bi motar har
tsohon