Showing 3001 words to 6000 words out of 119425 words

Chapter 2 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

share
hawayen shi, sannan ya mik'awa Dada ita yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka:

"Malam Ayuba"

Malam yace:

"Na'am ranka shi dad'e"

"Yace naji duk abunda ka fad'a ina takardar da kace ka gani acikin kud'in"

Malam ya ciro takardar ya mik'a masa, mai unguwa ya baiwa wani wanda yake wurin yace ya
karanta masa yaji, saboda shi mai unguwa baiyi boko ba,tiryan tiryan aka karanto takarda, mai
unguwa yace:

"Malam Ayuba zaka iya rik'e wannan yarinya a hannun ka?, ko zaka barta ahannu na ne har
zuwa lokacin da za'a sami iyayenta?"

Malam ya kalli Dada, tayi masa umurni da ido, atake ya d'au hannu yace:

"Zan iya rik'eta a hannu na ranka ya dad'e har zuwa lokacin da aka samu iyayenta"

Mai unguwa yaji dad'in furucin malam yace:

"Alhmdllh na amince dakai ayuba tun ba yau ba shiyasa ma ban musa wannan takardar da
kace ka gani aciki ba, saboda amanar ka ce ta saka har ka bayyana kud'in aka san da akwaisu,
nasanka mutum ne kai mai gaskiya da rik'on amana, saboda haka na amince da zata samu kula
sosai a wurinku, Allah ubangiji ya taya ka rik'o, kuma ya baku ladar taimakon da kukayi"
Duk d'akin aka had'a baki da cewa:

"Ameen"

Mai unguwa ya bada umurnin akawo goro a rarrabawa mutanen dake d'akin, akayi kamar
yanda ya buk'ata, sannan ya kalli malam yace:

"Wane suna kakeso asawa 'yarka?"

Malam yaji dad'in wannan karamci na mai gari, baki awashe yace:

"Ina son asa mata suna IZZATU"

Mai unguwa yayi murmushi sannan yace:

"Daga yau an rad'awa 'yarka suna izzatu,sannan kud'in kaje dasu kaci gaba da kula da ita
kamar yanda aka umurta, gobe sai kuzo da ita akaita asibitin birni aduba lafiyar ta, sannan
abata magunguna irin nasu na jarirai, sai a azata akan madarar da d'orata akanta adinga
shayar da ita, insha Allah zamu shiga binciken su wanene iyayenta, Allah ya rayata akan
tafarkin musulunci Allah ya zamo gatan ta damu baki d'aya"

Gaba d'aya akace "Ameen"

Daga nan taron ya watse su Dada suka fito, bayan sunyi sallama da mai unguwa, suna tafe
Garzali ya kasa hak'uri yace"

"Dada ita wannan jaririyar yanzu a gidanmu zata zauna?"

Dada tana murmushi tace:

"Ko baka so ta zauna gidan in maida masu da yarinyar su?"

Garzali yayi saurin fad'in :

"Cab ai ni dada naso ma ace iyarmu ta haifeta wallahi da naji dad'i, baturiya a gidanmu, ai kina
bani ita in d'auketa ko Dada?"

Ya k'are maganar acikin tsantsar farin ciki, Dada tana masa dariya tace:

"In kana son inbaka ita ka d'auka, to dole sai ka bada nera biyar"

Garzali yayi tsalle yasha gabanta yace:

"Zan baki in d'auki d'iyar indiyawa wallahi"

Ba Dada ba har da malam sai da yayi murmushi yace:

"Daga turawa sai indiyawa to sai munji gaba kuma k'ilan ta koma ta larabawa"

Firar da sukeyi kenan har suka shigo gida, iya kulu tana ganin su ta ajiye aikin da takeyi da
sauri ta sha gabansu tace:

"Allah dai yasa bai karb'e kud'in ba"

Dada ta harareta tace:

"To mutu kud'i bai karb'i ko k'wandala ba, yanzu ke nawa kikeso abaki naki kaso tun kafin su
k'are"

Iya kulu tasan halin Dada tas bak'ar magana ce ta buga mata, shiyasa nan take tayi kalar
tausayi ta kalli malam tace:

"Bani Hamsin d'in asiyo ma awaki na dussa"

Malam ba musu ya saka hannu aljihu ya mik'a mata nera d'ari yace:

"Ki ajiye hamsin har da na gobe"

Ya wuce abinshi ya barta anan tsaye sororo da nera d'ari a hannu, tana tunanin me yake nufi,
ta watsar da zancen ta koma kan aikinta.

Dada dai tana k'ara yab'awa iya kulu magana ta barsu anan ta shigewar ta ad'akin ta, Malam ya
shigo cikin d'akin da sallamarsa, sannan ya ajiye kwalin yace:

"Ga kud'in nan ki ajiye hannunki"

Dada ta girgiza kai tace:

"A'a je ka ajiye su ahannunka, duk lokacin da ake buk'atar wani abu sai ka bada"

Malam ya duk'a ya raba kud'in uku ya saka kashi d'aya a aljihu, ya tura mata kashi biyu yace:

"Ki ajiye a hannunki saboda tsaro"

"Dada tace to Ubangiji Allah ya bamu ikon rik'on wannan yarinya tsakani da Allah, amman ka
sanar da 'yar kuluwa abunda ake ciki"




Akafta�



Takuce

D/Auta

مس. الله رلا نمح رلا ميح
*______________________________*

*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________________*


*PAGE FIVE*


******************

Malam yana fita Dada ta fito itama, ba tareda tabi ta kan iya kulu ba, ta fara kici kicin aza ruwan
zafi, da sauri iya kulu tazo tana baiwa Dada hak'uri akan taje ta zauna ita zata aza ruwan zafin,
Ba musu Dada ta bar wajen, tareda fad'in:

"Wanka za'ayiwa Izzatu, idan sunyi zafin ki kawo man d'aki"

Iya kulu ta bita da kallo acikin mamakin jin sunan yarinyar da taji abakin Dada, saboda suna ne
na d'iyarta da ta haifa, wadda watan yarinyar hud'u a duniya tace ga garinku nan, sanadiyyar
rashin lafiyar da tayi ta fama da ita kafin ta rasu, gashi yarinyar ta shiga zuciyar kowa agidan,
tun daga kanta iya kulu bata sake haihuwa ba, ko b'atan wata bata sake yi ba shekara hudu
kenan da rasuwar izzatun, amman har izuwa lokacin bata fidda tsammani ba, akan cewa zata
sake samun wata izzatun
sai gashi kwatsam yanzu izzatun ta fad'o daga sama.

Agurguje ta gangand'a kara da guntu guntun itace, ruwan sukayi zafi ta juye ruwan ga wani

bokitin karfe, ta had'a da katuwar roba takaiwa Dada ad'aki, sannan taje ta d'auko tsohuwar
ajiyar ta, da take ta tsimi da tanadi, wato kayan jarirai na mata set biyu ta kawo ta ajiyewa
Dada agefen gado, sannan tace:

"Ga kayanan idan anyi mata wankan asaka mata, amman fa d'ari hud'u na sayi d'aya, d'ayar
kuma d'ari uku da hamsin, idan an had'a kud'in gaba d'aya zasu kama d'ari bakwai da hamsin,
sai abada d'ari bakwai d'in na yafe hamsin"

Dada dake kici kicin cirewa izzatu kayan dake jikinta,wanda tunda iya kulu ta fara magana bata
fasa abunda takeyi ba, aikin gaban ta kawai takeyi, har saida taji ta dire zancen ta, sannan ba
shiri ta d'ago fuskarta ta kalleta, bakin ta yana rawa tace da ita:

"Kibar kayanki ai ba rok'ar ki akayi ba ko?, balle ki fara yiwa mutane wani lissafin ki cen na
shirmen da kika saba"

Tana k'are zancen ta fara yiwa izzatu wankan acikin natsuwa tareda k'warewa, tana wanketa
lungu da sak'o.

Iya kulu ta b'ata fuska tace:

"Dubi kayan dakyau Dada masu kyau ne fa, ayi hak'uri asiye mata su kawai, saboda zasuyi
mata kyau sosai"

Dada bata koma bi takanta ba har ta k'are yimata wankan, sannan ta saka zane ta goye ta, tana
k'ok'arin fitar da kayan,ne, iya kulu tayi saurin kwashe kayan ta fita dasu, saigata ta dawo da
garwashin wuta acikin wani kasko ta ajiye, Dada ta saukar da izzatu ta fara yimata gashin
cibiya, sannan ta kalli iya kulu da kyau tayi murmushi tace:
"Da zaki ajiye son kud'inki 'yar kuluwa to da kinji dad'in rayuwar ki, amman ina kullum abu sai
gaba gaba yakeyi, Allah ya jik'an 'yar dubu, don itakam batada son kud'i irin naki"

Iya kulu ta tashi tsam ta fara tafiya zata bar d'akin, fuskar ta kicin kicin saboda maganganun da
Dada take yab'a mata ba k'aramin zafinsu takeji ba, Dada ta kira sunan ta, ta waigo, sannan
tace :

"Kinbar kayanki, ko kin barmata kyauta ne?"

Da sauri tace :

"Na zaci an siye mata ai?"

Dada tace :

"Tafi da kayanki, insha Allah gobe zaaje asiyo mata wasu"

Iya kulu ta duk'a ta d'auki kala d'ayar da tace ta siye d'ari hud'u, sannan tace:

"Ga kala d'aya nan asaka mata"

Dada tace :

"Yafi maki dai kam, kiyi don Allah koda zaki samu lada"

Iya kulu ta fita tana takaicin rashin siyen kayan da Dada batayi ba, acikin zuciyarta tace;

"Malam ne zai biya ai, don ni ba mai cin kayana abanza, sai dai in wuta bal bal ce za'aci, inaji
ina gani ga kud'i dami guda, abani hak'k'i na ankasa saboda kawai inyi magana, asani abakin
duniya, to wallahi dole ne abiyani kud'in kaya na, dari ta uku bazata tafi a iska ba, dank'ari
bazata sab'u ba don kuwa yasin zasu saiman dussar kwana biyar in baiwa akuyoyi na"
Idanunta arufe saboda b'acin rai, ba zato kawai taji tayi karo da malam, da sauri ta fara borin
kunyar cewa:

"Ai kayan zasuyi mata kyau gaskiya, ni ko d'ari biyu ma aka bada ba komi"



Oh ni dije



Akafta



D/Auta ce

مس. الله رلا نمح رلا ميح
*______________________________*

*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________________*
*BARKA DA SALLAH MY FAN'S ALLAH YA MAIMAITA MUNA*


*PAGE SIX*


**********************

Malam ya kalleta da kyau, saboda yasan iya kulu ciki da bayan ta, batareda ya bi kan maganar
ta ba yace:

"Ina su Garzali ne?"

Iya tayi saurin saita natsuwarta tace:

"Shi yana wajen Dada, Abu ko yana d'aki, ai tunda aka fara ruwan sama ya fara bacci har
yanzu bai tashi ba"

Malam ya fara tafiya yace:

"Ki tadashi dai kinsan ba kyau baccin marece"

Iya kulu tana tsaye har sai da taga shigewar sa ad'akin Dada, hannun ta agaba sannan ta
sauke k'atotuwar ajiyar zuciya tace:

"Wai Allah ya soni baiji ba, da na jawo wa kaina jangwam"

*SHIN WAI SU WANENE WADANNAN AHALI?*

Malam Abdulkadir jelani mai almajirai, shine ainahin sunan Baban malam Ayuba, mijin mairo
wadda kuka fi sani da suna Dada, wanda mutane suke kiranshi da sunan malam jelani,
kasancewar shi babban malami, wanda yayi suna acikin garinsu da kewayen shi, saboda
almajirai da ake kawo masa yana karantar dasu.

Yayi hidima sosai ga addini alokacin rayuwar shi, wanda har manyan dattijai na garin duk yana
basu karatu acikin gidanshi, wanda har izuwa yanzu wannan tarihi bai goge ba acikin zuciya da
idanun mutanen garin, saboda ahalin yanzu malam Ayuba shima malami ne masani akan
harkar addini, don dattawan garin masu ra'ayin neman sani akan karatun su, to awajenshi ne
suke d'aukar karatu, asati sau biyu ne sukeyin zaman .

Malam jelani matarshi d'aya ce ta aure wato mairo, yana da 'ya 'ya biyu rak da Allah ya
albarkace shi dasu, wato Malam Ayuba da hurere, wadda ake yiwa lak'abi da suna hure,
wad'anda su kad'ai ne suka rayu amatsayin 'ya'yansu, saboda matsalar da Mairo (Dada)take ta
samu awurin haihuwa, da ta samu ciki ya lalace.
Wanda alokacin aka canfa aljanu ne suke shanye abun d'an cikin cikin, saboda yanda malam
jelani har maganin aljannu yana badawa, shiyasa mutane suka canfa hakan, ganin da ta sami
cikin sai yak'i tsayawa, ak'arshe ma haihuwar ta d'auke d'if aka barsu tareda yaransu biyu
Ayuba da hure.
Ayuba yayi aure da iya kulu wadda ake kira da suna 'yar kuluwa, alokacin ganiyar budurcinta,
suma Allah ya albarkace su da yara biyu Garzali da Abubakar, sai izzatu da suka haifa wata
hud'u ta rasu, tun daga kansu har zuwa yanzu tsit, ko b'atan wata.

Hurere kuwa itama tayi aure da yaranta hud'u biyu maza biyu mata, don ko yanzu cikine da ita
yau ko gobe, inna hure kenan itama kunji labarinta.

*DANGANTAKAR DADA DA IYA KULU*

Dada da mahaifiyar iya kulu uwa d'aya uba d'aya suke, wadda ake kira da suna halima amman
ana yimata lak'abi da sunan ('yar dubu).

Yar dubu ta rasu wajen haihuwar 'yar kuluwa, ta barta tana jaririya ahannun Dada, itace ta
rik'eta har zuwa girmanta, saboda kiriniyar 'yar kuluwa da mugun son kud'inta, yasa Dada
tashin hankali ba kad'an ba, alokacin da girma ya fara zo mata samari sukayo mata caaa,
amma ita kam ba wanda yayi mata acikin su, don ita ayuwarta, tafi son ta auri mai kud'i, shiyasa
gaba d'aya samarin k'auyen nasu ta rena su.

Saboda ganin k'awarta da suka taso atare, wani alhaji abirni yazo ya aureta, shiyasa ta
k'wallafa ranta akan bata auren kowa sai mai kud'i, itama ta fantama yanda k'awarta takeyi,
musamman in tazo k'auyen ankawota da mota, suje suyita shafa motar suna k'auyanci, tayita
rok'on k'awar tata akan ta nemo mata miji d'an birni itama tayi aurenta acen itada k'auyen sai
dai idan zata wuce ta hango shi, aiko suka kitse magana atsakanin su, batared sanin kowa ba
'yar kuluwa tabi k'awarta abirni cen inda take aure.

Hankalin su Dada ya tashi, gari ya d'auka kulu ta b'ace, sai cen aka ji labarin tabi k'awarta
abirni, jiki yana rawa iya tasa aka kaita har cen gidan na k'awar tata, ta taso k'eyar ta suka dawo

k'auyen su, bayan tasha duka ba na wasa ba ahannun Dada, saboda takaicin hakan yasa ta
nemi alfarma awurin dangin baban ita kulun.

Akan tana son ad'aurawa Ayuba aure da ita kulun, saboda tana jin tsoron abunda zaije ya
dawo,na aibi ga rayuwar kulu, domin yanda tasawa zuciyar ta k'aunar kud'i, zaiyi wuya idan ta
k'ara girma ashawo kan matsalar, alokacin ko bacci takeyi, mafarkin kud'i takeyi.

Ba tareda sanin Ayubaba bale kulu aka d'aura auren su, da yake shi ayuba mutum ne wanda
yasan darajar iyaye ko afuska bai nuna yaji haushin auren ba, duk da ba ita yaso ya aura ba,
amman yayi biyayya ya rungumi 'yar uwarshi kulu sukayi ta zaman auren su, duk da botsare
botsaren da kulun ke yimasa, bai fasa kyautata mata ba, har izuwa yanzu lokacin da suka
hayayyafa, iya kulu bata saduda da son kud'in ba, har saima abunda yaci gaba.

*To kunji tarihin su sai adawo gundarin labarin‍♀wanda shine mak'asudin wannan littafi mai
suna RUWA DA KANKARA*

Ci gaban labari

Malam ganin yanda Dada ta shirya izzatu tsaf tareda maida mata da sock's d'inta da hularta da
aka tsinto ta dasu.

Farin ciki kwance akan fuskar malam yace:

"Rik'o man 'yata garzali, kabi ka kanainayeta, kamar wanda za'a k'wacewa ita"

Garzali yana murmushi ya taso ya mik'awa Abba y'ar, sannan yace:

"Da ka ganta ni zaka maida wa ita ko?, ba dada ba"

Malam yayi murnushi yace:

"Hannun amsa ai hannun mayarwa"

Dada tayi dariya tace :

"Dani kake zancen yaro, bayan ka mance da marairecewar da kayi ne a yanzu, akan in baka
ita nak'i, to gobe ko zan baka ita yaro kasani sai in kana da nera goma"

Garzali yayi saurin saka hannu ya karb'e izzatu a hannun malam yana dariya yace:

"Allah ya soni na d'auketa har da na goben, kinga goma ta sai ta huta"

A haka sukayi ta barkwancin su Garzali da Dada, suyi fad'a sudawo su shirya, malam dai

iyakacin shi murmushi idan sunyi abun dariya, har zuwa lokacin da iya kulu ta k'are abinci, anan
ta kawo masu suka baje sukaci abincin su.

Hadari ya k'ara had'uwa aka yita malala ruwan k'ank'ara gundum gundum gwanin ban firgici,
domin kuwa atarihi kaf basu tab'a ganin irin wannan al'ajabi ba, su malam suka rud'e sai zuba
addu'o'i sukeyi, garzali da Abu kam kuka reras suka sha, saboda tsoro, ita kanta iya kulun, sai
da tazamo tamkar wata sabuwar balaraba saboda salati da hailalar da takeyi.

Sai kace ba itace mayyar kudin nan ba‍♀‍♀‍♀‍♀






Taku ce

D/Auta
*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*



مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*PAGE SEVEN*

*********************

Itama kanta jaririya izzatu sai kuka takeyi, Dada tana ta lallashinta tana kiran:

"Tsarki ya tabbata ga ubangijinmu, wanda yake sauko muna wad'annan RUWA DA KANKARA,
lalle ke 'yar baiwa ce, samunki alkhairi ne awurinmu, Allah ya bamu ikon rik'on ki da gaskiya"
Su malam sukace: "ameen"

Haka dai akayita ruwan k'ank'arar guma guma, anraba dare ana ruwan sannan ahankali suka
fara ragewa har suka tsaya cak, zuwa lokacin iya kulu da su Garzali har sunyi bacci, amma
Dada da malam suna tsaye kai da fata sunata addu'o'i tareda jinjina girman wannan iko na
Ubangiji,.
Bayan komi ya lafa Dada tace da malam "suje d'akunansu su kwanta, saboda gobe zasuyi
sammakon zuwa birni domin sukai izzatu asibiti domin aduba lafiyarta"

Haka ko akayi Malam ya tada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login