Showing 102001 words to 105000 words out of 119425 words

Chapter 35 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

k'wak'walwarshi sosai,sai dai ya kasa dainawa ne domin jin yake yi
idan har ba sauke nauyin wahalar yayi ba to a ganinshi bazai rayu ba, aikuwa ya saki jiki ya YI
ta neman hanyarshi sai cen kuma naji Izzatu ta daina kuwwar sai kukan da take ta rerawa, ina
lab'e jikin k'ofar na zuro kaina zan lek'a ne domin inga meke faruwa ai kuwa sai Garzali ya zo da
hanzari ya rufo k'ofar d'akin da ya mance bai rufe ba da k'arfi, sai akan fuskata aikuwa na yi
baya da sauri saboda azabar da naji ta ziyarceni ba shiri, idona a rufe na ji saukar d'imi a
kussawar hancina a firgice nayi saurin shafa wurin aikuwa da sauri na bud'e idanuwana sai ga
jini nayi arba dashi, na bud'a baki zan k'walla k'ara ne naji Izzatu ta riga ni fasa tata kuwwar, da
sauri naje jikin k'ofar na lafe domin inji me take yiwa Kuwwa, sai kawai naji tana ta kiran,
"Wayyo Yayana kayi hak'uri Izzatunka ce fa k'anwarka Wayyo mutuwa zanyi wayyo Mama kuzo
ku gani yayana zai kasheni."

Da sauri na fad'i zaune dab'as saboda tsananin tausayin Izzatu da ya kamani, ba shiri naji
saukar hawaye akan fuskata na saka hannu na shafo fuskata, zafin da naji ya ziyarceni ne a
lokacin na tuna da fasa man hanci da Garzali yayi wajen tsegumi.

Tsananin Kukan da naji tana yi da magiya ne ya saka ni kwanciya a wurin ban shirya ba, ina
nan kwance nayi shiru ina saurare naji ta daina kuwwar cen kuma sai naji muryarshi yana bata
hak'uri, a raina nace, "Haba dai d'an air sai yanzu kasan da ka bada hak'uri, bayan ita ka kasa
jin nata hak'urin da tayi ta baka?, ai wallahi sai ALLAH ya saka mata."
Ba shiri na dafe baki saboda tuno da nayi ashe fa ba laifi yayi ba, a raina na k'ara cewa,
"Ku kuka jiyo ni miye nawa ma a ciki ne?"

Daga nan bacci yayi awon gaba dani anan wurin ba tareda na tantance ba, ina cikin baccina
mai dad'i ne naji anyi ball dani, a zabure na mik'e tsaye ina waige waige jikina sai rawa yake yi
saboda tsananin firgicin da nayi, aikuwa idanuwa na suka sauka akan Garzali da ya ke sanye
da jallabiyya bak'a yana sauka k'asa da saurinshi, na duba agogon hannuna sai naga asuba
ma ashe tayi a raina nace, "Kila masallaci zai je shine ya yi man wannan halbin d'an renin
hankali."

A zabure na fad'a d'akin aikuwa sai ga Izzatu naga tana fitowa daga toilet da alamu ma wanka
ta fito sai taku take a hankali tana cizon leb'e, kamar wata mai koyon tafiya haka naga tana
tafiya, hawayen idonta kuma har lokacin basu daina tsiyaya akan fuskarta ba, a daddafe ta
zura doguwar riga tareda saka hijab ta tada sallah, nima da sand'a naje bayin nayo arwallah na
lab'e gefen akwatunanta a gurguje nayi sallahta, ina nan zaune ina kallonta bayan ta k'are
addu'o'i ne tayi kwanciyarta akan carpet d'in sallahr sai sharar k'wallah take yi tana sharb'ar
kuka a hankali, sai ga Garzalin ya bud'e k'ofa ya shigo aiko na k'ara makurewa jikin akwatunan,
kai tsaye wurinta yazo ya kira sunanta yana wani Munafukin murmushi yace "k'anwata tashi
kije kan gadon ki kwanta kiyi baccinki kinji."

Madadin ta tashin kamar yanda yace d'in ko kuma tayi magana sai kawai ta fashe masa da
kuka, da sauri ya tallabota ya had'ata da jikinshi yace, "Nasan nayi maki laifi amman don
ALLAH kiyi hak'uri kinji wallahi nima naso nayi dauriya amma na kasa, kiyi hak'uri ki yafe man
kinji ba laifina bane ni'imar da ke cikin lambunki ne tasa ni d'imaucewa, na hak'ura ne kawai ba
don na so datse shan zumar ba sai dai kawai tsananin tausayinki da naji, amman har ga
ALLAH ba don naso hakan ba saboda ke mace ce da idan antara dubu ba za'a fiddo kamar ki
ba, yanzu na gano ashe ni d'in ba k'aramar gata aka yi mani ba, don wannan zuma da kika lasa
man ba zanso ace nayi missing d'inta ba koda na minti biyu ne, idan ta ni ne ma mu dawwama
a hakan ina ta zuk'ar zumarki duk tsawon second ko awa ko yini ko kwana balle sati zuwa
shekara, to kisani bazan tab'a gajiyawa da ke ba saboda ke mace d'aya ce amma tamkar da
miliyan a wurina, Ubangiji ALLAH yayi maki albarka ALLAH ya saka maki da gidan aljannah
firdausi, Iyayenki Kuma yanda suka farantaman Ubangiji ALLAH yayi ta faranta masu a kullum
safiya har zuwa ranar tashin k'iyama, tashi muje kiyi baccinki kinji."

Izzatu ta k'ara nok'ewa tareda zubowar wasu ruwan hawayen tace,

"Barni a nan nafi jin dad'i."

Garzali yayi wani murmushi tareda shafa d'an k'aramin gemunshi yace, "To ai ko anan zan iya
k'ara shiga lambuna tunda ba kya son cen."

Aiko zumbur ta Mik'e daga jikinshi tana jan baya har ta kai jikin gini ta makure tana kuka mai
sauti, Ya danne dariyar da yake son yi ya b'ata fuska yace, "Oya to muje ki kwanta idan ba
kya so ni ba zan takura ki ba."

Ya k'are maganar tareda rik'o hannunta ta mik'e tsaye jikinta sai rawa yake yi, da yaga ma takun

zai bata wahala ya rungumota ajikinshi ya kaita kan gadon, sannan ta kwanta jikinta cure waje
d'aya tana kyarma saboda tsananin tsoronshi da take ji, ya YI murmushi tareda yi mata wani
kallo sannan ya gyara mata kwanciyar, ya zagaya ya kwanta sannan ya janyota ya had'a ta da
jikinshi ya sauke k'atuwar ajiyar zuciya, don ya kwantar mata da hankali ma yayi magana mai
kama da rad'a yace mata, "YI baccinki ba abunda ni zan yi maki wannan ma da na samu na
gode ALLAH yayi albarka."

Sannan ta saki jikinta ta yi shiru minti biyu a tsakani tayi bacci, ya k'urawa fuskarta kallo yana jin
soyayyarta tana k'ara shigewa a cikin duk wani lungu da sak'o na zuciyarshi, haka ma duk wata
k'ofar gashi dake cikin jikinshi sai mik'ewa yakeyi, bai san lokacin da ya kai mata wani zazzafan
kiss a kumatu ba, tareda runtse idonshi yana jin wani NISHADI a birnin zuciyarshi, Murmushi
akan fuskarshi har shima wani bacci mai dad'i yayi awon gaba da shi.

Ina ganin haka na lallab'a na bud'e k'ofar d'akin a hankali na fito, saboda nima inje in d'an
runtsa in biya bashin baccin da naci wajen ganin K'wak'waf kafin su tashi daga baccin, tareda
jinyar hanci da bakina da ya suntume suntum橙提橙提橙提橙提橙提.



Akafta�





D/Auta ce踫潤蕃
[8/23, 1:54 PM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA儭*



https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*潃潃潃TAURARI WRITERS ASSOCIATION潃潃潃*

(We entertain and educate according to our religion and ethnics)


*Barka da SALLAH all da fatar ALLAH ya maimaita muna ya nuna muna ta bad'i lafiya踫潤蕃踫潤蕃踫潤蕃
amman fa ni har ynz banga nawa k'ullin naman ba踫saura kuma kuce man kun cenye 踫yasin
da mun had'u sunnah TV da yarinya踫橙提*


*PAGE SIXTY NINE*

**********************

Kai tsaye gidan Gwamnati ya nufa tareda rakiyar wasu scuritys da suka mara masa baya, a
cikin tsananin jin nauyi ya dinga gayar da Abba, kanshi a sunkuye saboda wata sabuwar
kunyarshi da ta lullb'eshi , Abbaah ya kalleshi yana murmushin jin dad'i yace, "Yau ni yarona
yake jin kunya?, ALLAH yasa ba surukuta ce kake so kayi dani ba?."
Garzali ya k'ara sunkuyar da kanshi yana murmushi, Abbaah ya saka hannu ya danna wani
Abu har sau biyu sai ga Ammaah da Ammi sun shigo, saboda kiran da suka ji Abbaah yayi
masu ya tabbatar masu da cewa abu mai muhimmanci ne yasa ya kira sun a tare, suna
shigowa suka tarar da Garzali Ammi ta d'an ja birki ta kasa k'arasowa, yayin da Ammaaah ta
k'araso ta zauna sannan fad'ad'a murmushinta saboda jin dad'in ganinshi idonta a kanshi tace,
"A'a wannan ango ne nake gani haka?to sannu da zuwa ina ka baro man 'yata?."

Garzali ya k'ara sunne kai ya waske da tambayar Ammaah ya koma gayar dasu,don baya son
yayi abunda zasu ranfo shi, Ammah ta amsa fuska cike da jin dad'in ganin wannan girma da
yake basu, Ammi kam gefe ta samu ta zauna a cikin jin nauyin ganin Garzali.

Bayan sun gaisa ne Abbaah yace dashi su fara shiri saboda tafiyarsu tana nan kamar yanda
aka tsara, Garzali ya tank'washe k'afafu ya fara zuba godiya a cikin kalamai masu dad'i,
wad'anda ba Abbaah kawai ba har Ammi da Ammaah sunji dad'in yanda ya saki jiki yanata
zuba masu addu'o'i, bayan sun k'are tattaunawar ne Garzali ya yi sallama da su, har yazo zai
tafiya ammaah tace, "Jirani in zo in baka sak'o ga 'yata."

Ta k'are maganar tana 'yar dariya ta biyo bayanshi suka fito waje sannan suka tsaya, Ammaah
ta sassauta dariyarta tace, "Daman sak'on naka ne ba nata ba don ALLAH alfarma nike nema
a wurinka akan ka tausayawa 'yata ka bita a hankali har ta saba."

Garzali ya dafe baki a cikin jin nauyin maganar sannan yayi murmushi ba tareda ya yi magana
ba, Ammaah ta k'ara da cewa " don ALLAH Ka bita sannu a hankali kaji ALLAH ya baku
zaman lafiya tareda hak'uri da juna, kuma ya yiwa aurenku albarka ya kawo zuri'a d'ayyiba."

Garzali yana sosa kai yake ta fad'in "Ameen Amee簽."
Sai ga su Su SADIS nan ya biye su suna ta zuba fira, kamar daman cen sun san juna har
lokacin SALLAH yayi.
Sai da yayi SALLAHr azahar tareda su SUDEIS sannan ya koma suka k'ara yin sallama bayan
ammaah ta bashi sak'on ya gayar mata da IZZATUn, sannan ya fad'a motarshi scuritys suka
raka shi har gidan Malam, amma a cikin zuciyarshi sai nanata zancen Ammaah yake yi yana
murmushi tareda shafar gemu wanda shi kad'ai yasan ma'anar murmushin.
Kai tsaye sashen Mama ya fara shiga wanda har lokacin wasu 'yan uwanta da suka zo bikin
suna nan basu tafi ba, tun a kan hanya ya fara gaisawa da mutane don kafin yaje wurin Mamar

har tasan da zuwanshi, saboda muryarshi da ta jiyo yana gaisawa da mutane, bayan ya shigo
ne ya zauna suka fara gaisawa sannan yace, " Ilham da Amina fa? Ban gansu ba ko duk
gajiyar bikin ce ta b'oye su."

Mama tana y'ar dariya tace, "Halan ba daga gidan ka fito ba? ai suna cen ita da Amina
saboda Izzatun ce ta matsa akan su zo , to shine Amina taja ilham d'in suka je don dai ta matsa
kawai amman da basu je sun takurata ba."

Garzali ya fara 'yar dariya yace, "Gara da suka je Mama don tun d'azu na fito ina gidansu
Ammaah."

Mama ta fad'ad'a murmushinta sannan tace "Masha ALLAH daman zancen da nike son inyi
maka kenan gara da kaje hakan yayi sosai."

Daga nan Mama tayi ta yimasa nasihar hak'uri da iyali tareda fahimtar dashi amfanin hak'uri a
wurin magidanci, Nasiha sosai tayi masa sannan suka yi sallama ya tambayi Malam tace dashi
yana sashen Iya Kulu aikuwa ya fito ya nufi sashen.

Abun mamaki koda yaje sashen ya tarar da ba kowa gidan tsit kamar ba anan aka yi kacaniyar
biki ba, sai iya kulu da ya tarar falo tana kallo Mari zaune k'asan carpet tana yi mata wankin
k'afa a cikin wata roba mai fad'i da ke ajiye gabanta da ruwa a ciki, Garzali ya kalleta yanda
tayi ture ka ga tsiya tana latsar remote tana canza tashoshi, sallamar shi da taji ne yasa ta yi
saurin kai kallonta gareshi tareda ajiye remote tana fad'in,

"Ango kasha k'amshi sannu da zuwa ina ka baro man 'yar tawa ne?. "

Garzali ya zauna yana murmushin jin dad'in yanda Iya ta ke nuna k'aunarta ga izzatun, ya fara
gaidata a cikin ladabi itama Mari ta gaidashi sannan taci gaba da aikinta, Garzali yana 'yar
dariya yace, "Naga gidan ba kowa ina 'yan bikin ne? ko har sun wuce gida haka da sauri?."

Iya ta yi wani mere sannan ta k'ara d'age dankwalinta sama tace, "Ni na kora su saboda na
gaji da bak'ar kazantar da suke yi muna a gida."

Garzali ya d'an b'ata rai yace, "Ai da kin barsu nazo munyi sallama sannan."

Iya ta fara hurar hanci tace "Ai Malam ya basu kud'in mota to kai miye na wahalar da kanka
akan mutanen da suka nuna man K'iyayyar sai yanzu da suka ga ALLAH ya rufa man asiri
sannan zasu zo suce sona suke yi?ai ni wallahi kar nike kallonsu babbak'un Kwad'ayayyu, da
sun d'auka banda k'ashin arzik'i shiyasa suka yi ta wulak'anta ni, to ai yanzu gashinan nayi
masu fintinkau shiyasa aka ce d'an hakin da ka rena shi zai tsone ma idanuwa. "

Malam da ke fitowa yace, "Tabbas ko don gashi kema hakin da kika ta renawa a baya yayi
maki rana, gashi kina ta cin arzik'in d'iyar da kika sheganta, yau gashi iyayenta sunyi maki ranar

da har ki mutu ba zaki daina cin gajiyarsu ba, don haka ki daina gori wurin wad'anda kika san
sune k'ashin bayanki, don ba ke kika baiwa kanki ni'imar ba ALLAH ne ya baki har kika ci
albarkacin wasu amma ba don halinki ba."

Iya Kulu ranta ya b'aci sosai amman duk da haka jikinta yayi sanyi da bugun gorar da MALAM
yayi mata, tana shirin bashi amsa taga Mari ta saki baki hanci da ido tana kallonsu, Iya ta d'aga
hannu ta kwad'a mata mari sannan tana huci tace, "Munafuka ta saki hanci da baki tana
kallon Mutane, tashi ki kwashi kayan munafuccinki ki fice tunda ke bakida wayon in kinga d'ana
yazo ki bamu wuri mu tattauna, algunguma a samu abun nad'a a fad'awa Uwa ita ko taje tana
bazawa K'auyawan mata irinta."

Malam yayi mata wani kallo sannan ya koma babban falonshi, saboda daman cen a cike yake
da iyar don bada son ranshi ta kori 'yan uwanta ba, ya dawo wurin SALLAH ne ya had'u dasu
kowace da kayanta nik'i nik'i suna yimasa sai watarana, yace dasu su jirashi yazo aiko koda ya
shigo gidan ya tarar da Iyar sai banbamin fad'a take yi, tun daga nan ya fahimci itace ta koresu
ashe, bai bi ta kanta ba yaje d'auko kud'in ba tareda ya kulata ba ya kai masu su shiga mota,
sunata godiya sannan suka wuce ya dawo yaga iya tana lek'enshi aiko ta buge da borin kunyar
fad'in, "Me yasa ka basu kud'in ai da ka barsu su je cen su k'arata. "

Malam yayi banza da ita har sai da zai shige falonshi sannan ya waigo yace, "Kije ki karb'o
kud'in tunda baki so aka basu ba."

Iya ta zunb'uro baki ta d'age d'ankwali tana girgizar jiki ta k'walawa Mari kira tareda sauran 'yan
aikin da ke mata hidima, ta tasa su a gaba sai da suka gyara gidan tsaf sannan aka feshe gidan
kaf da freshner mai mugun k'amshi lungu da sak'o , bayan an had'a da turaren wuta sannan ta
hakimce falo tasa Mari ta wanke mata k'afafu, shine Garzali ya tarar da su sai gashi Malam ya
kwafsa mata a gaban Mari shiyasa bata yi watawata ba ta sauke fushinta akan Marin saboda
tasan MALAM yafi k'arfin reninta yanzu.

Bayan malam ya shige ne Iya tace, "Ai dai komi ya wuce kuma na nemi yafiyar yarinya to tone
tone nami za'azo ana yiman nikam?"

Ta k'are maganar tareda murgud'a baki kamar wata yarinya, Garzali ya k'ume dariyarshi ya
tashi k'yam ya bi bayan Malam, yana yar dariya marar sauti saboda ganin yanda take magana
tana d'aga ido sama tana hurar hanci tareda turo lab'b'a kamar wata k'aramar yarinya.

Bayan sun fara gaisawa da malam ne Garzali ya gyara zamanshi yace, "wani tunani nayi
MALAM shiyasa nace bari in sanar da kai sai inji naka ra'ayi akai.
"

Malam ya nutsu da kyau sannan yace, "Ina saurarenka me ke tafe da kai?."

Malam yace, "Dangane da kyautukan da muka samu nida Izzatu, nayi nazari akan mu

sadaukar da dukiyar ayiwa k'auyenmu k'aton masallacin Jumu'a sannan a gina makarantar
islamiya a k'ara fad'ad'a makarantar bokon da ke garin sannan a saka Bohol Bohol na ruwa
domin a raya k'auyen amman kai me ka gani a kan lamarin?."

Malam ya sauke k'atuwar ajiyar zuciya sannan yace, "Kayi tunani mai kyau amman wani
hanzari ba gudu ba ka yi maganar da Matarka? Koko gaban kanka kayi?"

A cikin ladabi yace "A'a bamuyi maganar da ita ba gaskiya."

Malam yayi murmushinsu na manya sannan yace, "To ka tuntub'eta kaji ta bakinta duk
shawarar da kuka yanke sai ku sanar da Mahaifinta ka bar masa komi a hannushi, ni iyakaci na
addu'a Ubangiji ALLAH ya baku ladar niyyarku ta alkhairi, kuma ya k'ara had'a kanku ku yi
zamanku lafiya Ubangiji ALLAH ya albarkaci aurenku."
Sai "Ameen Amee簽" Garzali yake ta fad'i sannan suka k'ara tattauna maganar bayan sun k'are
ne suka yi SALLAH tareda MALAM sannan ya fito gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login