Showing 48001 words to 51000 words out of 119425 words
Chapter 17 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
dani"
Mama ta had'e fuska sosai tace da ita;
"Kul! Kada na sake jin kin k'ara magana irin wannan , yau kika fara sanin halinta ne?, da zaki
damar da kanki akan zantukanta?".
Hawayen da suka cika idanunta, suka gangaro a kan fuskarta, tasa hannu ta share sannan ta
d'auki ilham, suka shige k'uryar d'aki domin ta shirya.
Mama hassatu ta bita da kallon tausayi, a zuciyarta tace;
"Allah ya bayyana maki iyayenki, kodon mu fita a cikin wannan fargaba da muke ciki kullum"
Amina ta shigo da shirinta, tayi kyau gwanin sha'awa, ta gaida iya kulu, tayi mata wani kallon
banza tace;
"Gayyar sod'i an zo?, to adai bi a hankali kar ayi k'auyanci"
Amina tayi dariya tace;
"Ko zaki rakamu ne sai muje dake?"
Mama tayiwa Amina dak'uwa don tasan Aminar kar, bakin tsiwa ne da ita, bata shayin yiwa iya
kulu bak'ar magana, Amina ta shige d'akin mamar tana dariya, aiko iya kulu inda take shiga ba
anan take fita ba, har Dr yazo bata daina banbamin fad'an ba.
Izzatu ta fito a cikin shigar ta mai kamala, wata doguwar rigar jallabiya ce bak'a da Dr ya siyo
mata ta saka, sannan tayi Rolling d'in d'ankwalin rigar a kanta, farinta ya k'ara fitowa tamkar
wata balarabiya a k'asar sudan, izzatu daman cen kwalliya ba damunta tayi ba, iyakacinta
powder da lip a baki, ko jan baki bata cika shafawa ba, amma ranar ta d'an shafa kad'an, aiko
dress d'in yayi mata kyau sosai matuk'a.
Saboda tunda mama tazo gidan, ta dinga koyar da ita komi irin na 'yan birni, bata barinta yin
d'ige d'igen kwalliyar da 'yan garin sukeyi, shiyasa Amina itama ta dinga koyar kwalliyar izzatu,
duk da ita ko a had'i batayi wayewar izzatu ba, don ko a makaranta primary kawai tayi, saboda
mijin mama hure babban malamin zaure ne, bai yarda da yabar 'yarshi karatun gaba da primary
ba, yafiso yayi mata aure idan ta sami mijin da ya kwanta mata suka daidaita, yanzu haka
zaman jiran miji takeyi ayi mata aure.
Mama ta biyo su goye da ilham, da aka sakata baccin dole, don kawai kar tayi kuka idan su
izzatu zasufita, don izzatun taso taje da ita mama ta hana.
Mama tayi masu addu'a tareda nanacin abunda ta tsara masu suyi, da wanda tace kar suyi idan
sunje cen.
Dr idonshi a k'ofar gidan k'yam, yana son yayi tozali da gimbiyarshi, aiko suna fitowa da ka kallo
ya bita har suka k'araso a jikin motar, da kanshi ya bud'e masu suka shiga.
Kande da yaranta 'yanmata da suka rasa mijin aure, sai turereniyar juna sukeyi, wajen kallon Dr
da su izzatu, don tunda ya ajiye motar shi suke lab'e soron gidansu suna kallonshi, suna inama
ace a cikinsu ne yakeso da sun cab'a.
A gaban idonsu Dr ya ja motar tareda bad'a masu k'ura suka bar k'auyen, suna tafe Dr yana jan
izzatu da fira har suka kai gidan.
Gida ne madaidaici, shiba na manyan masu kud'i ba, shi ba na talakawa tilis ba, tsaka tsaki dai,
ba laifi akwai rufin asiri sosai a gidan, anyi masu tarba ba yabo ba fallasa, don a yanda sukayi
tsammanin ganin izzatun ba haka suka ganta ba, don dai ya fada masu a k'auyen da take, da
sun k'aryata shi, tun k'arfe sha d'aya suke a gidan har k'arfe biyu, bayan sunyi sallah sukace
wucewa zasuyi, mamar Dr tayi masu kyautar turare guda biyu, dr ya kwashe su sai wata plaza
ta mallakin BADAWI FAMILY.
Izzatu duk da farincikin da ta tsinci kanta a ciki, na ganin sunan BADAWI tayi, bai hana ta
tambayar Dr ba, akan lafiya ya kawo su wurin?.
Dr yayi murmushi yace ;
"Saida ku nazo inyi"
Amina tayi caraf da maganar tace;
"Aiko da ka baiwa mai sayenmu aiki babba, don ni kaina wuk'a bata iya yanka shi, sai dai in
izzatu"
Gaba d'ayansu suka YI dariya, sannan yayi parkin yace dasu su fito suje, a hankali suke
takunsu kamar wasu wayayyu, har suka he wurin wasu kujeru da Dr ya nuna masu suka zauna,
yasa akayi masu odar abinci da abin mak'ulashe har saida aka cika table d'in dake tsakiyarsu,
ya kalli izzatu da wani duba mai k'unshe da sak'onni da yawa, yace da ita;
"Bisimillah hajjaty"suka nuna masa sufa a k'oshe suke, anan take ya b'ata fuska yace;
"In cen gidanmu kunya ta hana kuci abincin, to a nan wa kuje jiwa kunya?, kuyi sauri kuci muje
inkai ku gida, zanje ciki in ga manager, kafin in dawo kun k'arasa"
Dr yana murmushi ya shige cikin wani office inda da alama cen ne na manager'n wurin, su
izzatu suna ganin ya shige suka fara loda abunda duk sukeso, sunaci suna yanga kamar wasu
wad'anda suka saba zuwa ire iren wad'annan wuraren.
Sunja lokaci suna kwasar gara kafin Dr ya fito hannun shi sark'e da na wani abokinsa, wanda
da alama akwai sanayya sosai a tsakanin su, duba da yanda suketa cisgar dariya.
Su izzatu suna ganin sun nufo wurin suka shiga taitayinsu, abokin Dr yana k'arasowa wai sai
naga ashe ma shu'aib ne, kan izzatu a duk'e dr yake yiwa shu'aib bayanin ta a matsayin wadda
zai aura.
A cikin farin ciki shu'aib yace;
"Sannu Amaryar mu, ashe mun kusa zuwa ashafa fatiha da...... "
Izzatu a cikin jin kunyar maganarshi ta d'ago fuskarta da nufin ta jawo gefen d'an kwalin ta rufe
fuskarta, karaf shu'aib ya hango fuskarta, da sauri ya matso yana tabbatar da itace, ya fara
salati, a cikin wani fushi da ya ziyarceshi ba shiri, yace;
"Kanbala'i Dr wa nike gani kamar wata shegiyar yarinyar dana tsana a wani k'auye da muka je
campaign, cab ke ubanwa ya kawoki a garinnan?, yanzu kai don shafewar basira me zaka yi da
wannan abar, wannan matsiyaciya ni wallahi ko a k'afa a d'aura man ita sai na since, cab amma
wallahi Allah ya isarwa maza sabida ka gama cutar su iya cuta"
Daga izzatu har shi Dr d'in kallon shu'aib sukeyi cike da mamakin shi, ba shiri izzatu ta fashe da
kuka ta tashi ta fice wajen ta nufi bakin titi tana kuka, sai ga AMMI ta doso motar ta acikin
plazar, Fahat da ammar suna bayan motar da ladidi.
Caraf idanunta suka sauka akan izzatu dake bakin titi ta madubin motar ta, sai sharar hawaye
takeyi.
Rigiji gabji
D/Auta ce⛹♀️
yanzu dai baa
[8/23, 1:54 PM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE THIRTY SEVEN*
**********************
Ba shiri gaban Ammi ya k'ire ya fad'i da sauri ta tsayar da motar, jikinta yana rawa ta b'alle
murfin motar tafito kafin taje inda izzatun take a tsaye, har ta tari d'an acab'a ta haye sun lula titi
sai balbala gudu yakeyi, a cikin tashin hankali Ammi ta koma motar ta fisgeta da karfi tabi
bayansu, d'an acab'a sai zuba gudunshi yakeyi a sanadiyyar umurnin da izzatu ta bashi, don
bata son ace Dr ya cimma su tafi son sai dai ya sameta a gidansu, don miyagun lafuzzan
shu'aib sun cusa mata k'iyayyar Dr, a cikin lokaci k'ank'ani taji auren Dr ya fice mata akai gara
ta tsaya a k'auyensu tayi aurenta ba wanda zai mata gori.
Ammi dake biye dasu bata hange komi sai d'an acab'ar da take kallo, sai over taking take yiwa
mutane duk don k'ok'arin ta samu ta cimmasu idanunta a rufe, saura k'iris ta sha gabansu sai
kawai taji ta bugi wata mota dake a gabanta, aiko mutane sai lalati sukeyi ba shiri hankalinta ya
dawo a jikinta, da sauri ta samu ta saki titin tayi gefe tayi parking, yayin da mai motar da ta daka
shima ya samu yaci birki da sauri, aiko gaba d'aya mutanen dake tafiya akan titin suka tsaida
abubuwan hawansu, suka yo kan mai motar da Ammi ta daka ana duba lafiyar shi.
Allah ya tsare baiji wani rauni sosai ba nan mutane suka yo kan Ammi da zagi, kowa da kalar
zagin da yake yimata duk da sun ganta mace amma basu d'aga mata k'afa ba, Ammi da ladidi
suka fito jikinsu yana rawa musamman Ammi, saboda taji tsoro sosai shiyasa bakinta har rawa
yakeyi wajen bada hak'uri, har wajen mai motar sukaje suka bashi hak'uri yace ba komi su tafi
kawai k'addara ce, sannan ta ja motar jikinta a mace suka koma gida ko plazar da tayi niyyar
zuwa bata je ba.
Dr kuwa tun daga lokacin da yaji miyagun lafuzzan dake fita a bakin shu'aib, wani b'acin rai ya
ziyarci zuciyarshi sai mamakin yakeyi mi Izzatu tayiwa shu'aib ne har yayi mata wannan
mummunar tsana, wadda baya shayin tozarta ta a ko'ina kuma ko a gaban waye, kafin ya
tantance abunyi sai ganin yayi izzatu takai titi ya so ya bita amma yafison sai yayi wa shu'aib
wankin babban bargo don kada ya bar bak'in cikin da yake ji ya tafi a banza, aiko jikin shi har
b'ari yakeyi wajen kaiwa shu'aib wani mummunan duka a baki, kafin kace me sai ga dambe ya
kacame a tsakanin su, aiki hankalin mutane ya dawo a kansu kafin a raba shu'aib ya lallasu a
hannun Dr, sabida k'arfi ba d'aya ba akwai banbanci a tsakanin mai cin tuwon dawa da mai cin
na shinkafa, dak'yar a ka raba wannan kokuwa sai suka koma fad'a da baki, a cikin fushi Dr
yace "Kaci sa'a akwai mutane wallahi da sai na yimaka dukan kawo wuk'a a wurinnan, gobe
ko ba matata ba sai kayi shayin tozarta wata mace a gaba na, useless kawai, dabba mai
k'wak'walwar kifi, ka rasa da wacce zaka tsaya kayi rigima sai mace macen ma k'aramar
yarinya, wallahi anji kunya girma yayi k'asa indai akan izzatu ne to nafison ni da kai daga yau
komi ya k'are a tsakaninmu."
Yana k'are maganganun yace da Amina ta shiga mota suje, aiko shu'aib sai so yakeyi ya k'wace
daga rik'on da aka yimasa yaje su ci gaba da caskaluwa, a zafafe ya d'aga murya yace "Sai
kasan ka cira dakeni wawan banza wai akan mace kake hauka."
Dr ya tada motar shi ya lek'o kanshi yace "OK ina jiran duk wani tanadin ka"
Yana k'are maganar ya fusgi motar shi ya mik'a titi, koda yazo dai dai inda su Ammi suke yaga
taro anata maganganu, amma bai bi kan ba'asin komi ba ya wuce sabida zuciyar shi a k'age
take da ya cimma izzatu, don yasan izuwa lokacin ta kusa kaiwa a garinsu.
Aiko ya take motar sai wuta yake bata sai gasu ya tarar dasu a wurin wani mai fetur a kan
hanya, ana sakawa d'an acab'an man fetur a mashin d'inshi, da sauri yayi parking a dai dai
gefen titin, izzatu tana ganinshi ta b'ata fuska sai kace ba izzatun shi ba, jikinshi a sanyaye ya
fito yana bata hak'uri akan tazo suje ya kaisu gida, a cikin b'ata fuska alamar ba wasa tace
dashi,
"Kaje kawai zan isko ku a gida."
Tana k'are maganar tazo zata haye mashin d'in, da sauri ya sallami d'an acab'an yace dashi ya
tafi kawai, aiko yaja mashin d'inshi ya tafi yana murnar kud'in da Dr ya bashi linkin kud'in da
sukayi jinga da ita.
Izzatu ta koma gefe tayi kicin kicin da fuska, Amina ta fito tana bata baki akan tazo su tafi, Dr
ma ya marairece fuska a cikin damuwa kamar yayi kuka yace, "Haba my izzah!, kinsan fa ba
laifina bane kiyi hak'uri kizo mu tafi, sai mu k'arasa maganar acen kinga a nan mutane sai
kallonmu sukeyi"
Aiko ta waiga sai ko taga idanuwa da yawa akansu, dole ba don taso ba ta shiga motar suka
tafi.
Sai da ya biya dasu BADAWI SHOPPING COMPLEX, yayi masu siyayya sannan suka kama
hanyar zuwa k'auyensu izzatu, Amina sai hak'uri take bata tana ta bata labarin abunda akayi
bayan tafowarta, jikin izzatu yayi sanyi k'alau saboda taji akanta Dr yayi fad'a da abokinshi, a
nan take ta saki jikinta kamar ba'ayi komi ba suka ci gaba da firar su, amman fa taji haushin
abunda shu'aib yake yayi mata, taci alwashin a karon su na uku ba zaiji dad'inta ba, don sai ta
shayar dashi gubar mamaki, sai ta banbance masa a tsakanin 'yar k'auye da 'yar birni.
Koda suka je gida izzatu ba wani tsayawa tayi fira da Dr ba, ta dai yimasa sallama tareda
godiya suka shige gida ita da Amina, wadda hannuwanta suke d'auke da ledodin siyayyar da Dr
yayi masu.
Shigar su gidan keda wuya suka ci karo da iya kulu, aiko tana ganinsu da ledodi nik'i nik'i ta fara
habaice habaice, dukansu ba wanda ya kulata suka je k'ofar mama inda take zaune akan
tabarma tana baiwa ilham abinci suka zazzauna, mama ta kallesu fuskar ta a washe tana farin
cikin ganin sun dawo lafiya, sai dai a kallo d'aya da tayiwa izzatu ta gano cewa lalle izzatun ta
tayi kuka, a nan take taji ranta ya sosu ba shiri ta tashi tsam tace dasu su shigo daga ciki, suka
kwashi ledodinsu suka shige d'aki, iya kulu tana ganin haka ranta ya b'aci don taso ace an
bud'a ledodin taga abunda ke ciki, aiko ta fara bala'i tana cewa,
"Munafunci dodo ne wallahi maishi yake biya, ni za'a nunawa bak'in hali?, to ni banda rabo na a
nesa yake ai da yanzu ina gidan wani hamshak'in attajiri a birni, wallahi da yarinya kallon tsiya
ma bata isa inyi mata ba, ku huta da k'unbiya k'unbiya duk abunda kukaci na yaron nan wallahi
Allah ya isa ce kuke ci, don nasan iyayenshi bazasu tab'a barinshi yayi wannan aure na
yaudara ba, don ranar da duk asirin ku ya tonu to ina tabbatar maku a gidan yari zaku k'are
rayuwar ku."
Tana k'are maganar ta juya aiko idonta sukayi karaf da malam, jikinta ya d'auki rawa ta dafe
baki tace "Don Allah kayi hak'uri sub'utar baki ne."
Malam ya maka mata harara yace "Ko ki b'ace man da gani ko nima hannu na ya sub'uce inyi
ta jibgar ki wallahi anan wurin."
Iya kulu jiki yana rawa ta fad'a d'aki tareda dafe k'irji tace,
"Oni 'yar kuluwa nikam da sa'a ta 'yar dubu ta haife ni."
Mama hassatu ko ta saka su izzatu a gaba da tambayoyi, har sai da taji komi sannan hankalinta
ya kwanta, tayita baiwa izzatu hak'uri amma tace muddin ya koma tarar gabanta da cin zarafin,
kar ta koma kuka tayi jarumta wajen nuna masa cewa ita fa daban ce, a cikin duk wasu
k'auyawan da ya tab'a gani a duniya.
Mama ta d'auki kayan da Dr ya siyo ta kaiwa malam, daga nan aka baiwa Amina nata kaso tayi
gida, iya kulu ma anbata ta karb'e amma ko gidiya babu bale sa albarka.
***
Shekaru sun mik'a abubuwa da dama sun faru, a ciki hadda cin zab'en da YAHAYA BADAWI
yay na d'ale kujerar gwamna, mutane sai sanbarka sukeyi, yayin da d'aya b'angaren suke bak'in
cikin rashin nasarar da sukayi.
Sannan Garzali ya k'are karatunshi har ya tafi service, wanda izuwa lokacin soyayyar izzatu tayi
masa nauyin da ya kasa b'oyewa, a fakaice sai k'ara cusa mata soyayyarshi ta gaskiya yakeyi a
zuciya, don ko lokacin da yaji labarin Dr ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba, har sai da
malam yayi masa katanga mai k'arfi a tsakaninshi da ita, sannan ya rage damuwar da ya
sanyawa kanshi, don kafin ya bar garin k'aura yayi daga gidan ya koma a d'akunan su samarin
d'iyan inna hure, don bayason malam yaga bai bi umurninsa ba, don muddin in yana ganin
izzatu to bazai iya jure b'oyon soyayyar ta ba, aiko lokacin service d'inshi yana zuwa ya lula
k'asar inyamurai yabar izzatu da kewar rashin shi, da d'inbin soyayyar shi da ta dank'are
zuciyarta tana hak'uri ne kawai da Dr don taga yanda malam yakeso ta aure shi.
Malam yana ganin Garzali ya tafi yace da Dr ya turo iyayen shi ayi maganar auren izzatu, don a
nufin shi ayi komi a gaggauce tun kafin Garzali ya tone asirin da suke ta rufewa, a sanadiyyar
soyayyar izzatu da hango ta rufe masa idanuwa, komi zai iya aikatawa akan ya sameta.
A lokacin Izzatu tana Ss3 a makaranta suna gaf da k'arewa, aiko Dr yaji dad'i a cikin zumud'i ya
sanar da iyayenshi, iyayenshi suka turo a b'oye ayi masu binciken wacece izzatu da halin
iyayenta.?
A binciken farko suka gano izzatu d'iyar tsintuwa ce, suka buga kansu akan cewa Dr bazai auri
izzatu ba, shi ko ya kafe akan cewa sam baisan zancen ba, dole ne sai ya auri izzatu.
Takanas mahaifiyar shi da mak'arrabanta sukayi tattaki suka je har k'auyen, koda suka je gidan
suka iske iya kulu a tsakar gida, ba tareda b'ata lokaci ba mahaifiyar tace,
"Kece mahaifiyar izzatu?."
Iya kulu ta zabura tace
"Rufani ki saya kin dai ga d'akin marik'iyarta, amma nikam Allah ya tsari gatari da saran shuka."
Iya kulu ta k'wallawa Mama kira tace,
"To hassatu a fito ga ranar girbar abunda kuka shuka tazo."
Mama hassatu jin muryar iya kulu a sama yasa