Showing 36001 words to 39000 words out of 119425 words
Chapter 13 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
mama hassatu da wani kallo tana mere, a cikin mamakin ganin kayan da ta zube
mata a kan gado, shin bata kayan akayi?, ko ko gani akeso tayi?, a cikin zuciyarta tace;
"Koma dai miye ne, ni tunda har suka shigo hannu na, wallahi in kaf garinnan zai taru, to ba
wanda zai sa in bada wad'annan kayan, tunda akazo har d'akina ana yiman kuri da gadara"
Ta shiga bud'a kayan tana jin dad'in samun su da tayi a b'agas.
Tun daga ranar da mama hassatu da iya kulu, sukayi wannan sa'insar, ba mai kula wani a
tsakanin su, sai zamansu ya koma irin na doya da manja, daman cen ba wani sakin jiki sukeyi
da juna ba.
Mama ta kama kanta sosai da iya kulu, sannan taja kunne izzatu akan kada ta kuskura tayi
wani abu da zai janyo iya kulu ta k'ara jifarta da wasu miyagun kalamai, don gudun ta fallasa
sirrin da suke ta jin tsoron iya kulu ta fallasa.
Aiko iya kulu ganin mama ta daina shiga shirginta ne, ta fara takale takalen abun da zaisa
mamar, ta biyeta suyita cacar bakin da takeso, don tunda taji malam bai yimata magana akan
jafa'in da tayiwa izzatu ba, tasan mama hassatu bata fad'a masa fad'an da sukayi ba. domin
kuwa da yaji tabbas da bazaiyi shiru ya k'yaleta ba.
Cikin mama hassatu yana da wata biyar, alamomi irin na mace mai juna biyu, suka fara
bayyana ajikinta, ta k'ara haske fau, ta k'ara jiki, cikin ma ya d'an fito amman sai ka kula dakyau
kake hangoshi, saboda cikin ya baje sosai a jikinta.
Kande da iya kulu suna zaune a tsakar gida, suna gulmace gulmacen da suka saba, mama
hassatu ta fito tana ta aikace aikacenta, saboda izzatu bata nan tana makaranta.
Kande tabi mama da kallo, tareda yimata k'uri da idanun ta na munafucci, ta gyad'a kai sai
faman kiran;
"Tabbas tabbas"ta keyi, iya ta kai kallonta gareta, sannan ta kai dubanta a wurin mama domin ta
ganarwa kanta, abunda kande take kallo tana kiran tabbas.
Da bata hango komi ba, ta kaiwa kande duka a cinya tace;
"Waike kande meye abun kallo a wurin hassatu, da har kike ta kallonta, salon kisa ta rena mu"
Da sauri kande tace;
"Reni?, na nawa kuma?, aike ta dad'e da gamawa dake gaba d'aya ma, bama reni kawai ba,
tunda har kikayi saken da kika barta tayi ciki a gidannan, aike taki ta riga ta k'are kuma, sai dai
ki barwa hassatu gida ya zama nata, don d'iya ne zata yita b'ulb'ulowa a gidan, shikenan ke
kinzama 'yar kallo tunda ke taki haihuwar an rufe maki magudanar ruwan ta tsaya cak! dole ne
kiyi hak'uri kiyi kallon masu d'uwawun haihuwa"
Ita dai mama hassatu ko kallo basu isheta ba, aikinta kawai takeyi tareda neman tsari da sharrin
su a cikin zuciyarta, iya kulu kam tunda taji lafazin kande hankalinta ya gushe na wuccin gadi,
har saida kande ta zungurota, sannan ta dawo cikin hankalinta, ba shiri ta zabura tace;
"Ci me?
Kande tace ;
"Ciki kuwa, nan da watanni k'alilan, Garzali da Abu za'a haifo masu d'an uba ko 'yar uba,
saboda haka sai ki fara tariyar kayan jarirai, kishiyarki zata haifo maki d'a, ashe rabon haihuwar
a gidan malam yake"
Iya kulu ta cika fam, sai huci takeyi, ba shiri ta shak'o wuyan kande, ta mak'ure saiga kande
idanu sunyi ja sun turo waje, sai k'ok'arin k'watar kanta takeyi, amma ta kasa, aiko tana samun
sa'a ta kaiwa iya kulu wani naushi a fuska, dole ta saketa don azabar da ta ziyarceta, kande taja
takalminta a hannu tana cewa;
"Bani na kar zomon ba, ni ko rataya ma ba'ani ba kije cen kiyi haukarki akan wad'anda suka
yimaki laifin bani ba, daga fad'in gaskiya?, shikenan kizo kice zaki sauke fushinki a kaina?, to ni
kinga tafiyata, na baki fili kiji da yak'in dake a gabanki"
Tana shiga gidanta ta haye katanga ta lab'e tana sauraren iya kulu
da tayi ta zuba ruwan bala'i iya bala'i, tayi ta masifa har bakinta yana kunfa, don kawai mama
ta biye ta suyi dambe ayi sanadin cikin, amma mama tak'i biyeta, iya kulu ko da taga wankin
hula zai kaita dare ne, ta fad'a har d'akin mamar ta kamata da kokawa, aiko mama hak'urinta ya
k'are ta rarumo wani k'aton flak's dake cike da ruwan zafi, ta bugawa iya kulu, aiko marfin ya
cire ruwan zafin suka zube kaf ajikin iya kulu.
Ruwan suna sauka a jikinta, taji zafin ruwan ya ratsa ta, aiko ta fara kururuwa tana neman
hanyar fita d'akin, tazo zata fito ne, ta saka hannu biyu ta ture Mama, ba shiri ta fad'i akan cikin
ta k'wallah k'ara, kafin kace me saiga jini yana gudana a k'afafunta.
Kande dake lab'e tana ganin iya kulu ta shiga d'akin mama, aiko saigata ta zagayo ko takalmi
babu, ta lab'e a k'ofar d'akin tana kallon abunda yake faruwa, ganin jinin da ke fita a jikin mama
yasa taji tsoro ta kwantsama kuwwa.
Izzatu dake k'ok'arin shigowa gidan ta dawo daga makaranta, aguje ta fad'o saboda jin kuwwar
kande, gabanta ya k'ire ya fad'i lokacin da tayi arba da mamarta a kwance, jini yana malala a
cikin d'akin, da sauri ta aza hannu akai taje ta rungumo mamar, tareda k'walla k'arar kiran
sunanta, mama ta d'ago dak'yar tace da izzatu taje gidan mai unguwa ta fad'o masa azo akaita
asibiti, aiko aguje ta fito, kande ta rik'eta tana kukan munafucci tace da ita ;
"Ki rufa muna asiri don Allah, kar ki fad'o wa mai unguwa"
Izzatu ta fisge daga rik'on da tayi mata,a cikin tashin hankali ta tureta, aguje ta nufi gidan mai
unguwa ta sanar dashi abunda yake faruwa, a gurguje yasa aka zo da mota aka kwashi mama
sai asibitin birni.
A gurguje aka shiga da ita emergency room, izzatu da direban da mai unguwa ya turo, suna
zaune akan wasu kujeru, sautin kukanta izzatu ne ya karad'e wurin, tana tanata wani irin kuka
na tashin hankali gwanin ban tausayi, direban da sauran mutanen dake wajen gaba d'aya ta
basu tausayi sai hak'uri ake ta bata.
Nima dai kam na tausaya mata
Akafta
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*I love you too my fans*
*PAGE THIRTY*
**********************
An d'auki lokaci mai tsawo kafin a fito da mama hassatu, a kaita wani d'aki da majinyata suke
jinya a ciki, aka kwantar da ita, izzatu tazo da sauri ta rik'e hannunta tana kuka.
Dr, dake biye da su ne yace ina mutanen mama hassatu?, direban mai unguwa, ya nuna
kanshi da izzatu yace;
"Gamu"
Dr ya kalleshi ya kalli izzatu dake ta kuka, ya mik'awa direban wata farar takarda yace dashi ya
biyoshi office, bayan sunje ne yake yimasa bayani kamar haka;
"Munyi nasarar tsaida cikin da yayi barazanar zubewa, Alhmdllh mun shawo kan matsalar,
saboda haka a sanadiyyar fad'uwar da tayi, jini ya zuba sosai a jikinta, wanda a yanzu haka
ake buk'atar a saka mata wani jinin a cikin gaggawa, tareda wasu magunguna da ake buk'atar
aje a siyo su yanzu yanzun nan, don tseratar da lafiyarta da ta abunda ke cikin"
Direban ya saka hannu a aljihu ya ciro kud'in da mai unguwa ya bada ya mik'awa Dr, a cikin
damuwa yace;
"Gasu sai ka rik'e a hannunka, ka taimaka a siyo magungunan da abunda ake buk'ata, yanzu
zanje k'auyen mu, in fad'awa mai unguwa abunda yake faruwa sai a nemo mijinta, domin asan
yanda za'a asamo jinin da ake buk'ata"
Dr ya karb'i kud'in jikinshi a sanyaye, yace dashi yayi sauri ya dawo, saboda ana buk'atar jinin
asaka a gaggauce, in ba haka ba rayuwarta tana cikin k'ila wa k'ala.
Da sauri direba ya tafi kamar ya kifa, saboda tausayin mama hassatu da ya mamaye zuciyarshi,
Dr d'in ya fito yaje yabada aka siyo abunda ake buk'ata, shiru shiru direba bai dawo ba, sai
kawai ya nufi d'akin da aka kwantar da mama, don yasan izuwa lokacin zata shiga yanayin da
ba'a fata.
Aiko yana zuwa ya iske izzatu rungume da ita tana ta wani marayan kuka,gwanin ban tausayi,
saboda shak'uwar da mama take tayi jere a jere, izzatu dafe da gadon hannunta cikin na mama
gwiwowiinta a k'asa tana kiran:
"Mama ki tashi kar ki mutu, don Allah kar ki mutu mamata, idan kika barni bansan ya zanyi da
rayuwata ba"
Tausayi ya mamaye zuciyar likitan, ganin yarinya kamar izzatu kyakkyawa ajin farko, ace ta
shiga gararin rayuwa, asanadiyyar ciyon mahaifiyarta, jikinshi yana b'ari yaje aka auna jininshi,
Alhmdllh zaiyi dai dai da nata idan an saka, aiko batareda wani jinkiri ba ya kwanta aka d'ibi
gora d'aya, ya bada umurnin aje asaka mata kafin mijinta yazo, aiko ba b'ata lokaci, aka
mak'alawa mama hassatu jinin, izzatu tana gefe sai kuka takeyi, idanunta da fuskarta sunyi ja
sosai, saboda tsananin kukan da tasha.
Bayan an k'are lak'awa mama jinin ne, izzatu ta tambaya ina direban da sukazo tare dashi, wata
nurse ta fad'a mata cewa yaje k'auyensu bai dawo ba har lokacin, shiyasa Dr ya bada jininshi a
sakawa mama, yanzu haka yana cen kwance kafin ya murmure ya fito, aiko ba shiri ta dubesu
tace ;
"Idan kunje ina gaida shi sosai don Allah kuyi masa godiya kafin yazo"
Suka ce "to" sannan suka fita, izzatu a cikin zuciyarta tana ta jinjina irin mutuncin Dr'n.
Bayan kamar minti talatin, sai ga Dr ya shigo, a lokaci d'aya ya rame ba kamar ganinshi da
izzatu tayi a farko ba, haka kawai taji ya burgeta, tana yimasa wani kallo irin na girmamawa,
saboda tsananin mutuncin da yayi masu, tareda tausayin da yakeyi na bayin Allah masu
buk'atar taimako.
A ladafce ta sunkuya ta gaidashi, tareda yi masa godiya akan abun alkhairin da yayi masu, a
cikin rashin damuwa yace:
"Ba komi ai yiwa kai ne"
Daga nan ya dudduba mama yace;
Idan jinin ya k'are ba wanda yazo daga cen k'auyen, za'a siyo mata wani jinin sai a k'ara mata,
izzatu ta k'ara yimasa godiya sannan ya fita, zuciyar shi fess take da farinciki, sabida ya hango
wa kanshi yabanyar da ta dace dashi, domin tunda ya k'yalla ido akan kyakkyawar fuskar
izzatu, yaji a duniya kaf ba macen da yakeso sai ita, daman shi cen ba gwanin soyayya bane,
amma gashi caraf izzatu ta tafi da tunanin shi.
Izzatu tana nan zaune har jinin ya k'are direban bai dawo ba, Dr ya shigo da wani jini da ya siyo,
ya sake mak'ala mata, yana cikin aikin ne, saiga Garzali ya shigo d'akin hankalin shi a tashe,
izzatu tana k'yalla idanuwa ta hango shi, da gudu taje ta fad'a jikinshi, tareda fashewa da wani
kuka mai tada hankalin mai sauraro.
Shima a buk'ace yake da ganin 'yar k'anwar tasa, ya saka hannu ya rungumeta sosai a jikinshi,
ya bubbuga bayanta alamar tayi shiru, saboda ya kasa furta wata kalma a bakinshi saboda
cunkoson damuwowi da suka yimasa yawa a zuciya.
A cikin dubara ya b'anb'areta daga jikinshi, saboda kallon da yaga ana ta yimasu, sannan ya
rik'o hannunta suka k'araso a jikin gadon mama, wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo akan
fuskarshi, duk da kasancewarshi jarumin namiji, wanda ba komai ne yake saurin sakashi kuka
ba, amman yaji tausayin halin da yaga mama a ciki, sannan ga iya kulu cen itama ya baro sai
kuka takeyi, saboda jikinta kaf k'unar ruwan zafi ne, ya rasa ina zai jefa kanshi yaji sanyi, gashi
anyita kiran number malam ba'a sameshi ba, k'arin takaicin kuma kukan da izzatu ta taresa
dashi.
Da sanyi jiki ya mik'awa Dr hannu suka gaisa, yayin da shi Dr haushin Garzali ya cika masa ciki,
ganin irin rungumar da yayiwa izzatu a gabanshi, wanda a ranshi yaketa sak'e sak'en Garzali ba
ciki d'aya suka fito da izzatu ba, shiyasa yana k'are abunda yakeyi ya fita yabar masu d'akin,
saboda takaicin narkewar da yaga izzatu tayiwa Garzali a jiki, yana ta faman lallashinta.
**
Hamshak'iyar hajiyar nan ce, a katafaren d'akinta da ya k'awatu, kamar baza'a bar duniya ba,
sai faman safa da marwa takeyi a tsakiyar d'akinta, fuskarta d'auke da d'inbin damuwar da ta
kasa b'oyuwa a gareta, sai faman tunanin mafita takeyi, sai sak'awa da kwancewa kawai takeyi,
a bayyane ta furta cewa;
"Ni Fatima ya zanyi da rayuwa ta ne?, nayi abu ya dawo ya dameni, fushin zuciya da sharrin
shed'an sun sakani aikata abunda idan ban tona asiri na warwareshi ba, har abada bazan tab'a
yafewa kaina ba, wanda nasan Allah ma bazai yafeman ba, na saka rayuka da yawa a
damuwa, don kawai in rama abunda aka yiman, sai gashi nice nafi kowa shiga damuwa akan
hakan, hak'k'in da na d'auka sai bibiyata yakeyi"
Ba shiri ta fashe da kuka, sai istigfari takeyi a fili da zuciyarta, tana datasani akan abunda ta
aikata.
Yafi tsawon minti biyar a tsaye yana kallonta, ganin ta saka kanta a damuwar da likitoci da yawa
suka ce ta daina shifa, tun yana d'aukar abun ba komi ba, to yanzu shi kanshi a sanadiyyar
halin da take a ciki baya da sukuni, duk da ruguntsumin siyasar da suke a ciki, amman yafi jin
damuwarta akan wannan.
A hankali ya tako har inda take, durk'ushe a jikin gado tana ta kuka, cikin murya mai cike da
tausayi ya kira sunanta yace;
"Hajiya fatima! Wai menene kike b'oye mani ne?, wanda har bakya son insani, wanda ya saka
ki a cikin damuwa shekara da shekaru, idan laifin da nayi maki ne na baki hak'uri, kuma kince
kin yafeman, koko dai matsalar da kike ta samu ne a wajen haihuwa shine yake saki wannan
damuwa?".
Hajiya fatima ta girgiza kai, a cikin damuwa yace;
"To me yayi zafi bintu?, ki fa yi imani da duk abunda kika ga ya sameki, ke mai ilimi ce,
yakamata ace kinyi tawakkali kin rungumi k'addararki"
Oh ni dije Shin meke faruwa da wannan ahalin?
Akafta♀️
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*FIRST CLASS WRTTERS ASSOCIATION*
*Albishirinku masoya littafan hadiza d/Auta akwai wani sabon buk dina zai fito kwanan nan mai
suna BAKAN GIZO... littafine mai kunshe da ban TAUSAYI, cin AMANAR KAUNA,Rashin
TAWAKKALI, tareda DAUKAR FANSA, dama sauran abubuwan da ba'a lissafo ba kar ku bari
abaku labari⛹♀️*
*PAGE THIRTY ONE*
**********************
Hajiya fatima ta k'ara fashewa, da wani gigitaccen kuka tareda cewa ;
"Bansan ya zanyi da rayuwata ba ABBAAH, tunda yarinyar nan ta b'ata natsuwata ta gushe,
farincikina yayi k'aura, komi na duniya ya daina bani sha'awa, shin taya zanyi in dawo da
farincikin da na rasa Abbah?, ka bani shawara don Allah nima nagaji da ganin kaina a cikin
wannan hali"
Anan take Abbaah'n ya had'e fuska, annurin dake kwance a fuskarshi ya gushe, a cikin jin
haushin kalamanta yace; ,
"Haba bintu wai meyasa kika kasa yarda da k'addara ne?, Hadizatou ma da ta haifo yarinyar
nan, izuwa yanzu ta hak'ura ta daina shiga damuwa akan b'atanta, amma ke kin kasa hak'uri ki
cire abun a ranki, haka kawai kin d'aukarwa kanki fitina kin d'orawa kanki, kin hana kanki zama
lafiya, kin hanawa mutane, lafiyarki tayi k'aranci duk a kan haka, shin wannan tashin hankali
har ina?, to bari kiji daga yau idan har baki daina irin wannan shirmen ba, to zan d'auki
mummunan mataki akanki"
Yana k'are maganar ya fita fuuu, ya bar mata d'akin, Hajiya fatima ta k'ara sautin kukanta,
tareda kiran sunan Allah akan ya kawo mata agaji, ya warware wannan matsala a cikin ruwan
sanyi, batareda mutuncinta ya zube a idanun duniya ba.
**
Dr ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai zarya yakeyi acikin office d'inshi, har ga Allah son izzatu
yayi masa shigar sauri, batareda zato ko tsammanin hakan ba, yana cikin farinciki, sai gashi
kwatsam zuwan Garzali ya rusa masa komi, a ranshi sai tambayar kansa yake, Shin meye
dangantakar Garzali da izzatu, don a zahirin gaskiya a son izzatu ba gudu ba ja da baya, har
sai yaga abunda ya turewa buzu nad'i.
Jikinshi har rawa yakeyi akan ya koma d'akin majinyatan, domin ya k'ara gasgata abunda yake
zargi.
Koda ya shiga ya iske d'akin a cike yake da mutane, shigowarshi ya katsae masu firar da
sukeyi, izzatu fuskarta a washe ta feshe shi da wani sihirtaccen murmushi, wanda ya ratsa tun
daga kanshi har zuwa tafin k'afarshi.
A ladafce izzatu ta nuna Dr ga malam dasu inna hure da wasu 'yan uwan mama hassatu da
sukayo angaya suka zo ganinta, tareda cewa;
"Kunga likitan nan ma ya shigo, shine ya bada jininsa aka sakawa mamata"
Gaba d'aya har had'a baki sukeyi wajen yimasa godiya, a kunyace