Showing 117001 words to 119425 words out of 119425 words
Chapter 40 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
ta yafe masa kuma tace don ALLAH Malam da iya su yafe masa, duk dauriyar
Amina sai da ta yi hawaye saboda tausayin da ya bata.
A cikin kukan yace da Izzatu idan taje ta cewa d'iyan Kande Mari da indo su yafe masa keta
masu rigar y'anci da yayi, a nanne ma Amina take sanar da shi abunda ya faru bayan baya
nan, waton k'afar Iya da aka cire da tserewar da mari tayi bayan Haifu abun baizo da rai ba,
sannan yanzu Haihuwar 'yar da Indo tayi masa mai suna Jidda, Abu ya k'ara fashewa da kuka
gwanin ban kuka yana rok'arsu su kawo masa yarinyar ya gani tareda Indo ya nemi yafiyarta,
yana cikin kukan ne lokaci ya cika aka jashi kamar wata dabba aka shige dashi, Izzatu da
Amina da Kuka kashirb'in suka fito gidan Yarin.
Kai tsaye gidan Malam suka nufa suna kuka suke sanar da Mama abunda ke faruwa, anyi sa'a
Malam baya gida Mama tayi ta lallashinsu tareda yi masu alk'awalin zata shawo kan Malam yayi
hak'uri ya yafewa Abu da Iya, don ita kanta hukuncin da ya yanke wa Iya bai yi mata dad'i ba.
Garzali kam yana cen yana fama da exam's wadda itace ta k'arshe da ya k'are ta zai dawo gida,
duk da damuwar da yake a ciki ta kewar matarshi da 'yan yaranshi, tareda bak'in cikin
matsalolin da gidansu ke fuskanta bai hana shi dukufa wajen jajircewa akan jarabawar ba, don
kuwa koda suka k'are resul ya fito a tashi d'aya suka rik'e shi saboda k'wazon da suka ga yayi
akan yayi aiko da su a manyan asibitocin dake k'asar na tsawon shekara d'aya, aiko yayi
farinciki sosai da wannan ci gaba duk da yaso ya dawo itama kasarshi ta amfana da iliminshi,
amman idan ya tuna shima aikin wani k'arin ilimin ne sai yaji dad'i kuma yayi godiya ga ALLAH
da hakan ta kasance.
Aiko kai tsaye ya garzayo k'asarshi ta gado waton Nigeria zuciyarshi cike da kewar k'asar da
mutanen kirkin da yayi acen.
Mama ta nemi alfarmar Izzatu ta koma gidanta domin ta tarbi mijinta, aiko ba Musu aka
tattarata aka mayar da ita tareda masu aikin da zasu dinga kula da su Amir bayan an yi mata
sabon gyara ciki da waje.
Garzali kam tun daga Airport da su Abbaah da malam ammaah da Mama da suka je tarbarsa
ya gaisa dasu a cen kai tsaye gidanshi aka wuce dashi, zuciyarshi cike da farin cikin dokin son
ganin Matarshi da yaranshi, aikuwa suna yin arba da gudu ta je ta rungume abunta sai kace
wad'anda suka YI shekara basu ga juna ba, cike da murnar ganinta yace
"Where is my kid's?"
Tayi masa nuni da d'akin da suke ya saketa da gudu ya nufi d'akin, yana yin arba dasu kwance
akan gado Ammar yana bacci Amir kam sai wutsil wutsil yake YI da k'afafuwa da hannu a cikin
shawul, yayi saurin bud'e idonshi yace, "What a amazing?" da sauri yaje ya d'auki Amir
dake ido biyu tareda bashi peck a goshi yana jin dad'in ganin yanda suka yi b'ulb'ul gwanin
burgewa, Ammar ya fara mutsu mutsu zai tashi yayi saurin d'aukarshi yace, "Come and
seeing your daddy."
Aikuwa ya d'auko shi shima ya had'asu waje d'aya ya rungumesu a jikinshi zuciyarshi fari k'al da
ganin 'yan biyunshi, yayita lallashinsu har dukansu suka yi bacci ya lallab'a ya ajiye su, sannan
ya sauke ajiyar zuciya, idonshi suka kai akan fuskar Izzatu da suna had'a ido tasha mur, tana
tsaye jikin k'ofa tana kallonsu cike da burgewa amman a fuska tayi fushi, da sauri ya taso yace
"Na shiga d'ari me nayiwa my sugar take fushi dani?"
Ta bud'e d'akin ta fito ya biyo bayanta tareda rungumeta yana shak'ar numfashinta ido a rufe
yace,
"Muje a bani hak'k'ina wallah."
Yanayin da yayi magana ya bata dariya sosai, amman ta mazge tace "Yanzu kasanni bayan
kafi son yaranka dani."
Da sauri ya zaro ido yace, "Sharri da rana haka za'a likamun kashin kaji?"
Yanayin da yayi maganar ne yasa ta k'yalk'yale da dariya ba shiri, aiko ya fara sarrafa kayanshi
duk magiyar da take yimasa akan ya bari yaci abinci ya huta amman ina, har sai da ya jik'a
alkalaminshi sannan hankalinshi ya kwanta, sannan yaje yayi wanka ya dawo falo yana cin
abinci suna firar yaushe gamo.
Kasancewar dawowar dare ce yayi takanas ya kaiwa masu aiki yaran ya k'ule da matarshi ya
darji amarcinshi, har sai da yaran suka yi ta kuka sannan Izzatu ta karb'osu suka dawo wurinsu,
suka ci gaba da Reno.
Aiko koda safiya ta waye ya nufi gudansu Abaabh bayan sun gaisa yayi wa Abbaaah bayanin
da zai yimasa dangane da abunda ya shafi karatun da aikin da aka daukeshi, Abbaah yayi
murna sosai kuma ya jinjinawa kwazonshi nan ne yake yimasa bayanin Asibitinshi da ake
ginawa wadda saura k'iris a k'are, sannan da alkawullan da yayi masa akan ci gaban k'auyen
duk anyi wasu anfa wasu kuma har an kammala, yaji dad'i sosai yayi murna, aka kira su
Ammaah da Ammi suka zo suma suka gaisa tareda taya shi murna, sannan ya fito zuwa
gidansu Malam.
Malam yaji dad'in ganin Garzali cikin natsuwa tareda hutu da kwanciyar hankalin da ya bayyana
gareshi, yayi hamdala ya godewa ALLAH da ya albarkace shi da samun d'a irinshi, sun dad'e
suna tattaunawa da Malam akan ya yafewa Abu da Iya dak'yar ya shawo kanshi, don ita Mama
har tayi maganarta ta k'are k'anzil baice da ita ba, dole ta hak'ura ta bar maganar tunda ta
fahimci ya hau da yawa, yanzunma don yana shi d'in shiyasa ya amince akan zasu je k'auye
gobe, sannan kafin suje su biya gidan yari su gano Abu.
Aiko tunda sassafe suka shirya dukansu Malam da Mama Izzatu da Garzali tareda Ammmah
Ammi Amina da tsohon cikinta tareda Dr suka dunguma mota mota suka rafi ganin Abu, ba
b'ata lokaci aka fiddo masu shi yanayin da suka ganshi yasa dukansu jikinsu yayi sanyi, anan
take Ammaah ta bada umurnin a sake shi, aikuwa aka cire masa ankwar dake hannunsa da
k'afa, aka kaishi wani tsabtataccen toilet yayi wanka aka bashi kaya ya saka sannan aka
badeshi da turare, sannan suka shiga mota zuwa k'auyensu Malam, kowa zuciyarshi cike da
alhinin ganin Abun, don ko baka da Imani ka ganshi sai ka tausaya masa, kai tsaye gidansu
Malam aka nufa aka bud'e k'aton falonshi kowa ya zauna, mai unguwa da mukarrabanshi suka
zo aka had'a Abu da Indo tareda su Iya da kande da mijinta, sannan Garzali ya fara magana
kamar haka,
"Wannan taro anyi shine saboda a had'u a yafewa juna abunda ya faru a baya, saboda haka
don ALLAH dukanmu muyi hak'uri mu yafi juna ALLAH ubangiji ya yafe muna gaba d'aya "
Gaba d'aya falon aka ce "Ameeñ" Iya kulu ta fashe da kuka tana rok'ar Izzatu ta yafe mata
abunda tayi mata, Izzatu tace ai ita wallahi tuni ta yafe mata saboda daman cen bata kullaceta
ba ita, kande ma rarrafo ta kama k'afar izzatu tana rok'on ta yafe mata, itama tace ta yafe mata
Abu kam fashewa yayi da kuka gwanin ban tausayi yaje wurin Malam ya rik'o hannunshi yana
rok'arshi akan ya yafe masa, shima yace ya yafe masa sannan ya dawo wurin kande itama ya
rok'eta sannan idonsh suka tsaya akan Indo da take ta sharar hawaye, yana kuka yana rokonta
yafiya itama sai kukan take, ba kunya yace
"ina 'yata indo"
Indo ta sunne kai tareda yi masa nuni da Inda Iya da ke rungume da yarinyar, yaje ya durk'usa
gaban Iya yana kuka yace ta yafe masa itama tana kuka tace ta yafe, ya saka hannu ya karb'i
'yarshi wadda yake jinta har cikin jininshi, ya rungume yana kuka daganan Malam yayi gyaran
murya yace, "Alhmdllh tunda har Indo ta haifu lafiya ina nemawa Abu neman aurenta
ALLAH ubangiji ya yafe masu laifukan da suka aikata dukansu muma ya yafe mu gaba d'aya "
Kowa yace Ameen Babansu Mari cikin jin dad'i yace, "a matsayina na mahaifinta Na ba Abu
auren Indo duniya da lahira."
Gaba d'aya wurin ya d'auki kabbara, Garzali ya fito da kud'i aljihunshi rafar 1k ya ajiye, sannan
yace, "Ga sadakin idan ba damuwa ko yanzu za'a iya d'aura masu aure."
Kowa yayi na'am su Ammaah suka fito suka shiga sashen Mama hassatu, Mai unguwa yasa
aka kawo dabino aka rarraba a tsakaninsu ba b'ata lokaci aka d'aura auren Abu da Indo akan
sadaki nera dubu d'ari, sannan taron ya watse sai ALLAH sanya alkhairi ake yiwa auren.
A cen sashen Mama kuwa Iya kulu da kande basu daina neman yafiyar IZZATU ba, Ammah
cike da mamaki ta tambaya abunda ya faru ba wata kwana Iya ta fayyacewa su Ammaah da
Ummi duk abunda ya faru, tun daga ranar da Malam ya tsinto Izzatu har lokacin da iftila'o'an da
suka yi ta faruwa ga rayuwarsu da suka sani da wanda baije kunnuwansu ba, aiko a take itama
Ammaah ta fashe da kuka saboda tuno itace tsanin komi, don itace tayi sanadin raba izzatu da
gidansu har wasu suka dinga shegantata, ta rik'o hannun Ammi da Izzatu tana ta rok'arsu yafiya
tana kuka, Ammi ma duk taji zafin sheganta mata 'ya da aka yi amman bata kullace kowa ba ta
yafewa kowa, har itace ke basu baki akan su daina kuka komi ya wuce, Izzatu kam daman cen
ta riga da ta yafewa kowa itama ta shiga aka dinga basu baki akan suyi hak'uri su daina kuka.
Ammaah da Ammi suka koma gida zuciyoyinsu cike da alhinin abunda ya faru, su malam kam
kwanansu biyu a garin bayan anyi d'an shagalin biki sama sama, sannan suka bar Amarya da
angonta tareda surukarsu Iya kulu,don Malam yaso su koma cen birnin abar Abu da matarshi
da 'yarshi anan, amman tace a barta nan kawai zata zauna dasu.
Auren Abu da wata d'aya Amina ta haifu, ta sami d'anta k'atoto ranar suna aka saka masa
sunan Baban Dr.
Su Ammar suna da wata biyar Izzatu ta sami wani cikin lokacin ma har sun koma London inda
Dr Garzali yake aiki a wata k'atuwar asibiti, ita kuma take ci gaba da karatunta ga yara biyu ga
d'an tayin ciki, abubuwa suka runtumewa Izzatu taso a zubar da cikin amman yak'i bari, da
taimakonshi na matsayinshi na mijinta da taimakinshi da shawarwarinshi na babban Dr ta sami
yaranta suka gyagije sunada wata tara suka iya tafiya, ko ina suna zuwa da gudunsu amman
yak'i bari a yaye su har sai da ta haifu, sannan aka cire su daga Nono, ta ci gaba da shayar da
yarinyar da ta haifa mai sunan Ammaah wadda suke kira Mimi.
****
ALHAJI sani kam sai da yasha gwalwgwale sannan ya YI bayanin duk tuggun da ya had'a da
bakinshi, wanda laifin Shu'aib kad'an ne fiye da rabi duk nashi ne, yasha wuya a hannun sojoji
har sai da suka makanceshi saboda azaba, sannan ne Abbaaah yace su kyaleshi aka kaishi
asibiti yayi jinya sosai amman idanuwa sun tsiyaye dole sai na roba aka saka masa, sannan ne
yayi nadamar abunda yayi yana sanar da sauran 'yan uwanshi komi, tiryan tiryan yayi masu
bayanin duk makircin da ya k'ulla don su daina ganin laifin Abaaah, aikuwa dukansu sunyi
nadamar cin zarafin da suka yi masa, kacokam suka d'aura lefin kanshi Musamman saboda
halbin da yayiwa Shu'aib wanda asanadin hakan hannunshi ya daina motsi, duk da yasha jinya
yaji sauk'i amman jijiyoyin hannunshi duk sun katse, yanzu haka hannun ajiye kawai yake baya
amfana masa komi, daga shi har Alhajinshi sunyi nadamar abunda suka aikata sunyi ta neman
yafiyar Abbaaah, lokacin da Izzatu tayi arba'in taje gidansu sunyi ta rok'onta akan ta yafe masu,
ta tausaya masu halin da suke ciki a take ta yafe masu.
Yarinyar Abu kam tana 'yar shekara biyu ta fito k'ofar gida tana wasa ne wani d'an shayeshaye
yayi mata fyad'e, a take a wurin ta mutu ko shurawa bata yi ba kuma Ya tsallaketa ya tafiyarshi.
Sai da yaran unguwa suka kawo ta gida matacciya iya kulu tana yin arba da ita tareda jin
abunda ya faru, jininta ya haye ta fad'i tun kafin aje asibit tace ga garinku nan, ALLAH ya karb'i
ran Iya Kulu a sanadiyyar fyad'en da aka yiwa jidda d'iyar Abu.
Anyi sadakar sati d'aya da rasuwarta sannan su Malam suka koma gida su Garzali ma suka
koma london tareda yaransu.
Shima kanshi Abu tashin hankalin da ya shiga ba kad'an ba, saboda ba k'aramin so yake yiwa
'yarshi ba shiyasa yayi ta rok'on ALLAH tareda istigfari akan abunda ya aikatawa Mari da Indo,
ashe haka iyaye suke ji idan an b'ata masu yaransu, ya jinjinawa iyayen da hakan take faruwa
dasu saboda shi kanshi da aka yiwa 'yarshi da ba ma ta hanyar aure aka sameta ba yaji zafi
balle 'ya'yan sunna, ALLAH ya k'ara tsare muna yaranmu gaba d'aya matan da mazan duka.
Bayan shekara biyar GARZALI da IZZATU sun k'are karatunsu sun dawo gida an kammala
masu ginin k'atuwar asibiti mai zaman kanta mai suna MARYAM HOSPITAL HOSPITAL, waton
sunan Dada bayan itama aka yi wata acen k'auye aka zuba maaikatan likitoci Doctor GARZALI
da Dr IZZATU sun duk'afa ceton rayuwar al'umma a birni da k'auyensu da ya zama wata alkarya
saboda abubuwan ci gaban da aka kawo masu suna amfana.
Anan na kawo k'arshen LITTAFINa mai suna RUWA da KANKARA, abunda nayi kuskure
Ubangiji ya yafe mani inda nayi daidai ALLAH ya bani lada, ina k'aunarku masoyana aduk inda
kuke kusani HADIZA IBRAHIM D/AUTA K'AURA ZAMFARA STATE tana k'aunarku Son so
fisabilillah alkhairin ALLAH ya kai maku a duk inda kuke NAGODE
Mu had'u a book d'ina mai suna BAKAN GIZO kar ku bari abaku labari kuma kuzo a kafta da
ku♀️♀️♀️♀️♀️♀️
Tammat bihamdullah