Showing 12001 words to 15000 words out of 119425 words

Chapter 5 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

tare dasu, wad'anda ta
gansu ido cikin ido ba labari aka bata ba, jikinta sanyi k'alau ta shigewarta d'aki tana tunanin
cewa:

"Oh ni kulu tabbas da gaskiyar Dada, don wannan yarinya daga ganinta wanda yayiwa uwarta
cikinta ba k'aramin attajiri bane, watak'ila daya d'irka mata cikin shegen ta haife, suka sako
kud'in akwali tareda 'yar suka jefar, to idan haka ne, ai ni bawai son 'yar zasuyi ba bale suzo
neman ta, kai wallahi nikam bazan iya wahalarwa d'iyan shegu ba cab gaba gaibu shegiya mai
ido atsakiya kai sai warai warai takeyi dasu, kamar tsohuwar mayya"

Yinin ranar Dada tayi shine, acikin b'acin rai d'a damuwar abunda iya kulu tayi, sannan da tarin
tausayin izzatu da ya mamaye mata zuciya.

Koda malam ya dawo haka ya risketa da damuwa, yayi ta tambayarta amma tak'i sanar dashi
abunda ya faru, saboda batason wata sabuwar hayaniya, domin tasan shi sarai duk da
hak'urinsa idan yaji, bazai k'yale iya kulu ba, tana gudun wani sabon fad'an ya k'ara tashi,
shiyasa tayi gum, amma bakinta bai daina yiwa iya kulu adduar shiriya ba.
Kwanaki sai shurawa sukeyi,sati yazo ya wuce, wata ya danno kai, shekara tazo ta wuce,
kamar wasa saiga izzatu da shekara biyu, izuwa lokacin, ta iya tafiya, ko ina tana zuwa, acikin
gidan, Duk da Dada bata barinta zuwa b'angaren d'akin iya kulu, amman yaro da k'urciya har
acikin d'akinta take shigewa tayo mata b'anna, itako ba kunya zata saka hannu ta bubbugeta ta
turota waje, idan Dada taji kukanta ta fito tayi ta fad'a, amman bai hana gobe ma iya kulun ta
zaneta idan ta k'ara shiga d'akin.

Ga Abu k'anen Garzali shima sai cin zalinta yakeyi, har jira yakeyi tayi masa abunda zai daketa,
Garzali ko ya rama mata su kacame da dambe, iya kulu tazo ta shigarwa Abu ba kunya, ita ko
Dada tayita fad'a.

Dada ta fara ciyo wasa wasa, sai ga ciyo ya kwantar da ita magashiyyan.





Ba akafta☹



D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*

*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*COMMENT'S DINKU SHIKE KARA MANI KUZARIN YIN TYPING PLSS KU DAURE KO BA
YAWA AYI YAFI AYI GUM DUK DA BA LAIFI WASU SUNAYI AMMAN DAI A KARA*


*YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING�*

*PAGE TWELVE*

*********************

Malam, da inna hure, da Garzali, sun shiga damuwa sosai akan wannan ciyo na Dada,
saboda akullum magani akeyi amma kamar ba'ayi, mai unguwa da kanshi ya turo aka Kai Dada

asibitin birni, tayi jinya ta tsawon sati d'aya acen, sannan taji sauk'i sosai aka dawo da ita
agida, kowa yanata farin cikin da samun sauk'inta, har iya kulu taji dad'in ganin ta samu sauki'.

Kwatsam sai ga ciyo ya dawo sabo, anso amaidata asibiti tace dasu, a'a su daina wahalarda
kansu akanta, ta kallesu d'aya bayan d'aya zata fara magana tari ya sark'e ta, su malam suka
rud'e sai sannu suke yimata, sai da tarin ya lafa, tayi jarumtar had'a kalamomi ta fara magana
kamar haka:
"Kuyi hak'uri kuyi hak'uri, inason kuyi man alk'awali koda k'asa ta shafe idona, zakuyi rik'o da
zumuncinku, ayuba kaine namiji kuma kaine jagora atsakaninsu, ka zamo mai adalci atsakanin
matanka da 'ya'yanka da k'anwarka hure da yaranta"

Malam yace: "Insha Allahu"

Hawaye suna kwaranya akan fuskokin su duka, saboda sunji ajikinsu,Dada wasiyyar bankwana
ce takeyi.

Dada ta juyo da kallonta akan izzatu dake kwance agefenta, tamkar wata mara lafiya, duk
kiriniya irinta izzatu, amma aranar sukuku ta wayi safiya, sai kuka takeyi anyi lallashi anyi
lallashinta har angaji amma abanza, itada kanta tazo gefen Dada ta kwanta.

Dak'yar Dada ta d'aga hannu ta shafo kan izzatu tayi murmushi sannan tace:

Ga amanar marainiyar Allah anan zan bar maku wato izzatu, idan har Allah ya bayyana
iyayenta, to kar kuyi wata jayayya kubasu 'yarsu, amma idan basu bayyana ba, duk tsawon
zaman da zatayi agidannan, kada ku koreta ku barta taci gaba da zama atare daku, ku rik'eta
tsakani d'a Allah, kamar yanda kuke rik'on 'ya'yan da kuka haifa, na yafewa kowa mima ku
yafe man Allah yayi maku albarka gaba d'ayanku."

Ta jawo hannun Garzali ta dad'e tana kallon shi, sannan acikin sautin muryar da tasha ciyo ta
disashe, ahankali tace dashi :

"Na baka amanar I.. z.. za.. t. u. na"

Dak'yar ta had'a kalmomin, saboda bakinta ya karye, daga nan ta fara kalmar shahada, su
malam sunayi tana amsawa, ta hanyar motsa bakinta da lab'b'anta har mala'ikan mutuwa, ya
zare ranta acikin salama.

Malam ya share hawayen fuskarshi, sannan ya saka hannu ya shafe fuskarta, idanunta suka
rufe, ya saka zane ya lullub'e fuskarta da jikinta gaba d'aya , inna hure ta kwantsama kuka
gwanin ban tausayi.

Garzali ko duk da yake da, k'ananun shekaru alokacin, amma yasan mutuwa, ba shiri ya kalli

Malam yace:

"Malam ka bud'e ta Dadar mu fa bata mutu ba"

Ba shiri ya fad'a ajikinta yana kuka yana kiran sunan ta, da ta tashi bata mutu ba, izzatu dake
kwance agefenta, ganin Garzali ya fad'a kan Dada yana kuka, itama taje ta aza kanta ajikin
Dadar tana ta kuka, Malam yaja Garzali suka fita, inna hure ta janyo izzatu, ta rungume ta tana
ta kuka, saboda tsananin tausayin yarinyar ya kamata, shikenan ta rasa gatanta.
Iya kulu tana rakub'e tunda Dada ta fara wasiyya, jikinta yayi sanyi k'alau, hankalinta bai kwanta
ba har saida taji Dada tace ta yafewa kowa, acikin zuciyarta tace:

"Nagodewa Allah da kika yafe man Dada,nima na yafe maki wallahi"

Ta k'ara rud'ewa lokacin da taji Dada tana kalmar shahada, sannan ne wasu hawayen suka
gangaro mata.




Abu kamar wasa yau Dada ta bar duniya, tabar izzatunta acikin maraici




Ba akafta





D/Auta ce


مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*

*�RUWA DA KANKARA⛈*


*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*

*KAR KU MANTA COMMENTS DINKU SHIKE KARA MANI KARFI GWIWA YA ZABURADDANI
AKAN INYI MAKU TYPING SABODA HAKA RUWAN SAMAN COMMENTS DINKU KAWAI
NIKE BUKATA*

*DUKAN KU I LOVE YOU MAZGA MAZGA�*

*PAGE THIRTEEN*

**********************

Kwana uku da rasuwar Dada, taron masu amsar gaisuwa suka watse, sai su inna hure da suke
zuwa su yini anan su koma gidajensu in yamma tayi.

Iya kulu idan ka ganta alokacin, zaka d'auka cewa wata ustaziya ce, don carbi ne a hannun ta,
tana ta lazimi ko magana ma bata son yi saboda mutuwar Dada ta dake ta ba kad'an ba,
kasancewar bata san wata uwa ba sai ita Dadar, koda ta bud'a ido itace tasani amatsayin
mahaifiyarta, sai daga baya ta gano ashe ba Dada ce ta haifeta ba.
Aranar bakwai Malam ya tara su gaba d'aya yayi masu nasiha mai ratsa jiki, tareda da jadda da
masu, amanar da Dada ta bar masu ta izzatu, inna hure ta nemi alfarmar abata izzatu taje da
ita, ta had'a da 'ya'yanta ta rik'e, iya kulu har ta fara murna, sai gashi taji malam yana yiwa inna
hure tuni, akan wasiyyar da Dada ta bari na abar izzatu ta rayu acikin gidan, har lokacin da
iyayen ta suka bayyana.

Inna hure dai dole ta hak'ura ba don taso ba, ta tattara yaranta ta koma gidan mijinta, tareda
alhinin rabuwa da izzatu, iya kulu kam taji haushin da ba'a baiwa hure izzatun ba, don ta tsani ta
wayi safiya tayi ido biyu da izzatu, tana shawagi acikin gidan.

Koda dare yayi, malam da hannun shi ya d'auki izzatu ya shinfid'e ta akan gadon iya kulu, don
sanin da yayi mata bata fitsarin kwance,duk da iya taji haushi amma bata nuna a fuska ba, don
itama sheda ce akan cewa izzatu bata fitsarin kwance, sai gashi akayi rashin sa'a koda safiya
ta waye ta malka fitsarin ta akan gadon.

Iya kulu tana k'yalla ido taga fitsarin, aiko ba wata wata ta fara dukan izzatu, gashi malam yayi
sammakon fita zuwa wata gaisuwa, Garzali ne yazo da zafin naman shi ya d'auketa, daga
dukan da iya kulu take yimata, hawaye yana zuba akan fuskar shi yace:

"Haba iya don tayi fitsari, zaki daketa tunda sassafen nan?"

Iya kulu mamaki kwance akan fuskarta tace:

"To tabbatacce ko zaka rama mata dukan ne?"

Garzali yana share mata hawaye yace:

"A'a kidai kawo in wanke fitsarin ba sai kin daketa ba"

Iya kulu ta galla masa harara, sannan tace:

"To ba'ayi yanda kakeso ba ya kenan?, wallahi Garzali ka kiyayeni, don naga kanka yana rawa
sosai, akan wannan ruwa da k'ank'arar, in banda rashin hankali irin naka, d'iyar shegun kake
damuwa akan an daketa, ai gara ni dukanta nayi iyayent fa da suka d'auketa kacokam, suka
jefar a daji fa?, kura da zaki suyi kalaci".
Karaf sai akunnen malam yana shigowa, aiko bakin shi har rawa yakeyi, wajen ya maida mata
da martanin cewa:

"Alhmdllh, Allah ba azzalumin kowa bane, tunda har kikaga, bai bari ko k'uda ya sauka a kanta
ba, to kinsan akwai wata manufa da ubangiji ya b'oye akan hakan, sannan ina son kisani shi
zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai yayi, saboda haka kije da
bak'in halin ki, dake d'awainiya da rayuwar ki, indai izzatu ce ki kwantar da hankalin ki, zan
kawo wadda zata kula man da ita, tsakani da Allah, wadda bata k'yamar ko ta wace hanya ce
aka sameta, sabida haka kije kiji da kanki"

Iya kulu ta zabura tana huci tace:

"Malam me kake nufi ne?, ka fito fili kayi mani bayani yanda zan gane, ai dai inajin wannan 'ya
ba kaine ka haifeta ba, don haka banga abunda har zaisa ka dinga fifita ta akaina ba, tunda ta
shigo a cikin gidan nan, na rasa natsuwa ta da walwala, haka kawai akan wannan tsintacciyar
magen za'a dinga yiman cin kashi kala kala, mai kula da ita kuma idan an tashi anemo ta a
birnin sin ma idan za'a iya ni ba damuwa ta bace"

Malam dai ci kanki bai k'ara cewa ba, ita ko sai da tayi fad'an har ta gaji don kanta, sannan ta
sauke akan Garzali dake baiwa izzatu d'imamen tuwo,ba zato yaji saukar dundu a bayan shi,
har saida ya gantsara, da sauri ya sosa wajen tareda b'ata fuska yace :

"Me nayi kuma ni yanzu da zaki dake ni?"

Iya kulu a masifan ce tace :

"Meye ne baka yi ba munafuki?, yanzu wannan uban tuwon da ka lafto, cikin gara ne da ita da
zata iya cinye shi?"

Malam ya fito yana saka talkamin shi, yace :

"In duka malmalayen tuwon zata cinye, a barta taci, don ba wani yake nemo man abincin ba, in
kuma akwai wanda yake taimako na, to daga yau ya daina bana buk'ata"

Iya kulu ta bishi da kallon mamaki sannan tace:

"Au abun har ya kai cen?".

Malam yayi banza da ita, ya saka hannu a aljihu ya ciro kud'i ya baiwa Garzali yace:

"Gashi idan tana buk'atar wani abu, sai ka saya mata, ni zan fita"

Abu k'anen Garzali ya fara kumbure kumbure yace da malam:

"Ni ina nawa kud'in?"

Malam kam, a cikin ko inkula ya fara tafiya sannan yace:

"Kaje uwarka ta baka"






Akafta



D/Auta ce


[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*


*INA JIN DADIN COMMENT'S DINKU NAGODE SOSAI MASOYANA DA MASOYA BUK DIN
RUWA DA KANKARAACI GABA DA RUWAN COMMENT'S NI KUMA INCI GABA DA
MURZO MAKU TYPING*

*PAGE FOURTEEN*

**********************

Malam yana fita, Abu ya maido da kallon shi akan izzatu ya galla mata harara sannan yace:

"Don ubanki sai kinbar gidannan munafuka, tunda kika zo gidannan kika sa malam ya daina
sona"

Yana k'are maganar ya k'wace kud'in ahannun Garzali yana muzurai yace:

"Ko k'wandala bazan bada asiyo maki wani abu ba, sai na gani in da mai k'watar su a hannu na"

Acikin fushi Garzali yayi ciki da shi, suka fara dambacewa, da yake k'arfi ba d'aya ba, Garzali
ya kada shi yanata duka, bayan ya karb'e kud'in.

Iya kulu tana d'aki ta jiyo kokuwar su, da sauri ta fito tana ta masifa dak'yar ta raba fad'an, ta
kalli Garzali tace:

"Uban mi ya had'aka fad'a da d'an uwanka har da su dambe?"

Garzali yana sauke numfashi, saboda damben da suka sha yace:

"Wai kud'in da malam ya bada, yace asaiwa izzatu biscuits sune ya k'wace gaba d'aya, wai ko
k'wandala bazai bada ba"

Iya kulu ta makawa Garzali harara tace:

"Yanzu akan wannan munafukar ne, ka saki k'wanji ka jibgi d'an uwanka?, saboda kana soko
zaka zab'i d'iyar shegu ka bar d'an uwanka ko?to ahir d'inka wallahi bazan lamunta ba, nikam
ruwa da kankara tayi kad'an, da ta shiga a tsakanin yarana, in banda nika tuno wasiyyar Dada,
da ayau d'innan sai na korata ta bar gidannan wallahi, inyaso idan malam ya dawo sai ya maida
gaba na a gabas ya yanka"

Abu yaje da gudunsa ya kwad'awa izzatu mari, yana huci yace:

"Shegiya sai kinbar gidannan, tunda ba.. "

Kafin ya k'arasa fad'ar abunda zai fad'a ne Garzali ya sauke masa nasa marin shima, Abu ya
dafe gefen da yasha marin tareda k'walla k'arar kiran sunan iya kulu, daman itama a zuciye
take, ba shiri ta nufi wasu karan dawa dake jingine ajikin katangar gidan, ta zaro wani k'aton
kare mai kauri, ta dingi laftawa Garzali yana ta tsalle, bata daina dukansa ba har sai da karen
ya kakkarye ajikinsa.

Sannan ta dawo da guntun wanda ya rage ta laftawa izzatu, aiko ba shiri ta k'walla k'ara, zata
k'ara kai mata wani dukan ne, Garzali yayi wani tsalle ya tare dukan, ya sauka a bayanshi, da
sauri ya d'auketa, yayi waje da gudunsa, ya sami gindin bishiyar dake k'ofar gidansu, ya zauna
yana ta lallashin izzatu dake ta faman kuka.
Shima baisan lokacin da ya fashe da kukan ba, saboda tausayin izzatun shi, musamman da
yaga dukan da iya tayi mata har wajen ya fashe, karen ya yankata, har jini ya fito, daga nan
inda yake azaune yana jiyo sautin iya kulu dake ta masifa, abun bai mata ba har saida ta lek'o
ko mayafi babu tana huci tace:
"Yau dani daku ne acikin gidan, tunda ka nuna k'iri k'iri kafi son bare akan d'an uwanka, yo niko
bazan tab'a d'aga maku k'afa ba, sai naga wanda zaici riba ni da ku"

Tana k'are zancen ta juya zata shige a cikin gidan, langa langar dake jikin k'ofar gidan ya rik'e
mata gefen zane, a cikin fushi ta fisgi zanen aiko sai ji kake b'arrrrrr zanen ya yage, ba tareda ta
bi ta kan zanen ba ta shige gidan.

Garzali ya share hawayen shi, da suketa kwarara ya maido da kallon shi akan izzatu dake
rungume ajikin shi, da take ta sauke ajiyar zuciyar kukan da tasha, da sauri ya tashi tana sab'e
a kafad'ar shi, yaje shagon d'anliti dake a kusa da gidansu, ya siyo mata minti da biscuit, da
ledar ruwa pure water d'aya, sannan ya dawo gindin bishiyar ya zauna, ya bata biscuit d'in tana
ci yana yimata wasa har ta ware ta saki jikinta tana dariya, ta cinye biscuit d'in tasha mintin,
sannan ya bata ruwa tasha ya wanke mata fuska da sauran ruwa, aiko sai gata tana ta jera
hamma ya rungumeta ajikinshi yana girgizata, kafin kace me tayi bacci, sai sauke numfashi take
a hankali, tana ajiyar zuciya.

Garzali hankalin shi ya kwanta, nutsuwa ta dawo masa, ba shiri ya sauke ajiyar zuciya, ya
maida kallon shi, akan wani mahaukaci dake yawan shigowa a cikin k'auyen nasu, wanda a
duk lokacin da ya shigo k'auyen, a nanne wajen zamanshi a jikin bishiyar, abun mamaki sai
yaga hawaye kwance akan fuskar mahaukacin, sai kwaranya sukeyi sun kasa tsayawa a
kwarmin idanuwan shi.

Saboda iya sanin su dashi, baya um baya um um, baya kula kowa da sabgoginsu, baya duka
baya zagi, amman da kaga shigar shi zaka gano mahaukaci ne, saboda farkon shigowarshi a
k'auyen, sai da mai unguwa yasa aka kawo masa shi, ya k'are masa kallo zuciyarshi ta natsu

dashi akan cewa ba mugu bane, sannan aka fita iskan shi yana ta shawaginsa acikin garin,
amma an saka ido akanshi, tsawon shekara har izuwa lokacin, ba'aga wata alama ta cuta
atattare dashi ba, shiyasa mutane suka d'auke idanuwansu a kanshi, ba ruwan kowa dashi.

Garzali ya k'ara bud'a idanuwa sosai, saboda yana so ya gasgata shin da gaske kukan ne
yakeyi ko kuwa?.

Mahaukacin kam da ya fahimci Garzali yana ta kallon sa, jiki ba kuzari ya tashi tsam ya fara
tafiya, ko waige bai k'ara yi ba har ya bar k'auyen.



Tofa shin wanene wannan mahaukacin?
Jama'a akwai lauje acikin nad'i fa�



Akafta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login