Showing 93001 words to 96000 words out of 119425 words
Chapter 32 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
ya shiga cikin lamarinmu, dangane da zuwan su Malam makkah ma idan
lokaci yayi ko kuna cen za'a yi komi insha Allah ."
Daga izzatu har Garzali farinciki ya lullub'e su, daga nan Garzali ya fara kukan murna goma da
ishirin yana yiwa Abaah godiya har sai da Abaah ya hanashi, sannan yace da shi yaje ya sanar
da su Malam zuwanshi gobe da safe wajen nema masa auren Izzatun.
izzatu kam saboda farin ciki rungume Abbaah tayi itama tana kuka, Abbaah yana ta aikin
lallashi ne Amaaah ta shigo tana yi masu tsarguwar kukan da suke yi, sannan Abaah ya basu
umurnin tafiya suka fito kowane idanuwa sunyi ja saboda kukan farin ciki.
Bayan sun fito ne Izzatu taje ta rungume Garzali shima gam ya manneta jikinshi a tare suka
sauke wata k'atuwar ajiyar zuciya, Garzali kanshi a kafadarta yace, "Ba nida bakin da zan
gode maku K'anwata kun gama yi mani komi a rayuwa addu'a d'aya ce zan dinga yiwa Abaah a
duk lokacin da na kai goshina nayi sallah, akan ubangiji ya saka masa da gidan aljannah, ya
k'ara tsareshi da sharrin mak'iya da mahassada da sharrin mutum da sharrin aljan, ko wani
abun halitta mai cutarwa da shi da ahalinshi gaba d'aya duniya da lahira."
Ammi da ke bayansu tace "Ameeñ" da sauri suka saki junansu saboda muryarta da suka ji a
cikin kunnuwansu ba shiri, jikin Garzali yana rawa saboda kunyarta ya sunne kai yana gaidata,
itama ta amsa a cike da jin kunyar surukantaka sannan ta yi wurin Abaah da yake nemanta.
Garzali da izzatu suka kalli juna suka yi murmushi, sannan suka yi sallama tayi masa rakiya har
gindin had'ad'd'iyar motarshi, ya ja suna yiwa juna bye bye ya nufi gidansu zuciyarshi cike fam
da murna had'e da farin cikin da ya mamaye masa kafatanin zuciya. Motarshi ce da ya saya a
cikin miliyoyan kud'in da izzatu ta mallaka masa, sannan ya fara aza dank'areren gida naji da
fad'i bayan ya bud'a k'aton shago ya zuba yara Malam yana jagorantar komi, tareda taimakon
d'iyan INNA hure maza da yake ji dasu tamkar d'iyan da ya haifa, wad'anda suma malam ya
nema masu muhallin zama da matayensu a cikin birnin, domin kawai su tallafa masa tunda shi
Abu ya fand'are masa dole ya zuba masa idanu don sai yayi wata ma bai saka shi a
idanuwanshi ba.
Akafta♀️
D/Auta ce
[8/22, 1:56 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*BAKON YANAYI book ne da ke tafe da zafin shi kada ku bari abaku labari salonshi daban
yake da saura 200 kacal zata sa ki kasance d'aya daga cikin member ta BAKON YANAYI
*
*KAR KU MANTA LITTAFAN HADIZA D/AUTA*
*Tartsatsi*
*Ruwa da kanra*
*Bakan Gizo*
Sai
*BAKON YANAYI mai take da nashi kalar salo kar ku bari a baku labari sayen nagari
maida kud'i gida*
*PAGE SIXTY THREE*
**********************
Mari ta k'araso ta zauna sai sunne kai take yi tak'i bari su had'a idanuwa da Garzali, ko gaisuwa
a cikin tsoro tayi masa ita saboda tana jin tsoron ya tona ta iya Kulu ta koreta, ita ko yanzu a
duniya ba abunda ta tsana irin ta koma k'auyensu.
Garzali ya kafe idanuwanshi a kanta yace, "Meye tsakaninki da Abu?"
Mari ta fara inda inda tana susar kai, Garzali ya daka mata wata tsawa tareda zaro mata
idanuwa yace, "Meye tsakaninku nace?"
Mari ta fara kuka tana bashi hak'uri tana fad'in bazata koma ba, Iya kulu ta zura mata idanuwa
saboda alamun rashin gaskiyar da taga sun bayyana gareta ran Garzali a b'ace yace da ita,
"Ki kiyayi abunda zaisa in saka hannu in doke ki, ke wace wawuya ce da baki san 'yancin kanki
ba?, to bari kiji mutuncinki darajarki idan kika yi sake kika rasa su ke ce a wahale, saboda shi
namiji ba ruwanshi tsaf zai iya zubar maki da mutuncinki a banza matuk'ar kika yi sake, duk
kusancinki da shi ko wallahi zai maki sakiyar da babu ruwa ko d'ige a ciki, sai daga baya k'i
dawo kina cizon hannu bayan kece kika bada k'ofar komi, in kunne yaji to jiki ya tsira ni dai na
fad'a maki gaskiya har ga ALLAH mun fita hak'k'inki, ruwanki ne ki ji ki yi amfani da maganata ki
kama kanki, haka ma ruwanki ne ki watsar duk wanda yak'i ji to fa ba zai k'i gani ba."
Yana k'are maganar yace da ita ta tashi ta bashi wuri, Iya ko da take cike da mamakin
maganganun Garzali ta kai kallonta gareshi tace, "Me marin tayi ne?"
Garzali bai b'oye ba ya sanar da Iya abunda ya gani sannan ya k'ara da cewa, "Sai kin saka
ido sosai akan Mari da Abu, in ba haka ba su jawo wa mutane abun magana."
Iya kulu hankalinta ya tashi ta fara banbamin fad'a, ta iske Mari har d'aki tayi ta jibgarta sannan
tace da ita ko kallon Abu ta sake yi sai ta bar gidannan, ta tsorata sosai shima da Abun ya dawo
tayi ta b'ab'atunta amman shi ko kallo bata ishesa ba, balle yaji tsoron fad'anta k'arshe ma da ya
gaji da kwakwazonta taso mata yayi kamar zai doketa a zuciye ya jawo jakarshi ya bar mata
gidan, Iya kulu ta fashe da kuka tareda yin danasanin gatan da ta nuna masa a cen baya tana
kuka tace, "ALLAH ya jik'anki Dada ashe duk fad'an so kai ne kike yi mani, yau ga gaskiyarki
da kike fad'a mani ta fito fili, ashe haka ne da kika ce kaso naka duniya ta k'i shi, ka k'i naka sai
duniya ta so shi".
Garzali dai bai k'ara cewa komi ba ya ficewarshi d'akinshi da ke farkon sashen Mama hassatu,
yayi wanka sannan ya fito wajen Malam suna tsara yanda zasu tarbi Abbaah gobe, Malam ya
d'aga waya ya kira mai unguwa ya sanar da shi duk abunda ke faruwa, mai unguwa yaji dad'i
sosai don shima yana cikin mahajjatan, suka yi ta taya juna murnar wannan karramawa da
Abaah yayi masu, sannan suka yi sallama akan shima gobe tun da sassafe zai zo ayi komi
dashi.
Aikuwa da safe k'arfe goma cif Abbaah ya yi tattaki zuwa gidan Malam, domin nemarwa Garzali
auren IZZATU tareda rakiyar wasu mutanenshi, saboda danginshi wad'anda suke d'aki d'aya
da Alhaji sani, sun ce ba ruwansu da shi da auren 'yarshi tunda ya tozarta masu d'an uwa,
mutum d'aya ne daga cikinsu ya fahimci illar abunda Alhaji sanin yayi, wanda tare dashi ma
aka yi wannan tafiyar don yace baya goyon bayan rashin gaskiya.
Tarba ta mutunci su Abbaah suka samu wurinsu Malam da mai unguwa da wasu dattijan
k'auyen wad'anda Malam yayi zaman lafiya dasu a cen, bayan an k'are 'yan gaishe gaishe ne
Abaah ya fara gabatar da abunda ya kawo su, a cikin tsantsar farin ciki Malam ya amince da
had'in auren 'yarshi izzatu da Garzali, Abbaah ya YI umurni da a kawo masa wata jaka, jikin
wani scurity yana rawa ya ajiye jakar a gaban Abbaah a cikin ladabi, Abbaah ya saka hannu a
jakar ya d'auko bandur d'in 'yar dubu har guda biyar ya ajiye a gaban Malam yace, "Ga
sadakin yarona Garzali mun takaita ne saboda muyi koyi da sunnar ma'aiki, idan kuma ance
sai mun k'aro za mu cika su zamo 1.million don bama son uban amarya yaga kasawarmu."
Gabaki d'aya wurin aka saka dariya sannan Malam cike da farinciki yace, "Tunda abu ne na
gida tuwo na maina a barsu haka ma sun isa, fatanmu kawai ALLAH Ubangiji ya sanyawa
auren Albarka."
Dukansu suka ce, "Ameen."
Daga nan Abbaaah ya gyara zamanshi yace, "Muna neman alfarmar a saka muna rana,
amma fa da wuri muke so kada aja muna lokaci."
Malam yana murmushin jin dad'i yace, "Wata d'aya yayi maku?."
Abaaah yana murmushi yace, "Yayi muna tsawo amman tunda har haka uban Amarya ya
saka dole ne muyi hak'uri, ALLAH ya nuna muna lokacin lafiya kuma ya sanya alkhairi a cikin
lamarin."
"Ameen Ameeñ " kawai kake ji tana tashi a bakunansu, dukansu kowa ya tofa albarkacin
bakinshi tareda yiwa auren fatar alkhairi, Garzali har k'asa ya duk'a yana yiwa Abbaah godiya
saboda karamcin da yayi masu saboda ba kowane mutum ne zai iya yin hakan ba, amman shi
duk da girman matsayinshi sai gashi ya yi abunda ko wasu na k'asa da shi ba zasu iya yin
hakan ba.
Suka rabu a cikin mutunci da girmama juna kowa sai sambarka yake yi, bayan ya yiwa su
malam da mutanen k'auyen tasu kyauta ta musamman, ya dunk'ulo kyauta mai tsoka yace a
baiwa iya kulu da mama, sannan aka YI masu rakiya tareda yiwa juna fatar ALLAH ya nuna wa
kowa lokacin.
Bayan sun tafi ne mai unguwa da wad'anda suka zo suma suka koma k'auye, suna cike da
farin cikin abun alkhairin da suka samu, sannan da jinjina wannan karamci na mai girma
Gwamna, bakunansu sai addu'ar gamawa lafiya suke yi masa ba gajiyawa.
Bayan kwana biyu da saka rana Garzali ya koma wurin bautar k'asarsa, wadda bai wuce kwana
uku da su kammala ba, amman yana lik'e da 'yar amaryarsa a waya sai soyewarsu sukeyi
hankali kwance, saboda yanzu sun tabbatarwa zukatansu sun zama mallakin juna babu wata
fargaba .
**
Saura kwana biyu da saka ranar auren ne SUDEIS da SADIS suka dawo gida, saboda sun
kammala karatunsu na secondary gaba d'aya, bayan anje d'aukosu ne Amaaah tace da izzatu
tayi shigar manyan mata taje falon Ammi ta zauna, don ayi masu surprise aga ko zasu iya
banbance Ammi da ita, aikuwa izzatu tasha kayan Ammi ta hakimce saman kujera, sai ko gasu
sun shigo da gudunsu har suna haki suka zube a jikin izzatu suna fad'in "Ammi oyoyo."
Izzatu ta fara bubbuga bayansu tana shafa kawunansu tana murmushi, su kuma saboda jin da
suka YI Ammi bata ce masu komi ba yasa SUDEIS ya d'ago yana fad'in,
"Ammi ko mu koma har sai kinyi dokin ganinmu ne?."
SADIS ya d'ago fuskarshi ya k'are mata kallo zuciyarshi cike da mamakin ganin Ammin ta k'ara
zama yarinya, a cikin mamaki yace, "Gaskiya Ammi wannan yanayi yayi maki dad'i kinga
yanda kika koma.?"
Izzatu tace, "Sannunku da zuwa 'yan yarori anzo lafiya? ya hanya?" tana k'are maganar ta
fashe da wata k'atuwar dariya harda rik'e ciki, dukansu suka bita da kallo a cikin
mamaki,saboda muryarta da suka ji ta banbanta da Ammi, sai ga Ammaah da Fahat da Ammar
sun fito suma sunata yi masu dariya, Amma tana dariyar tace,
"Ku d'aga man 'ya kar ku tsofar man da ita tun kafin zuwan lokacin, kuje ku nemo Amminku
wannan kam 'yata ce izzatu kuma yayarku."
Ammi ta fito itama tana dariyar yayinda suma suka fara yiwa kansu dariyar, Ammi ta kallesu
tace , "Ku in banda abinku baku sheda ta ba ne halama? duk photunanta da kuka yi ta shan
gani."
SUDEIS yana dariya yace, "Ni fa na gano ba ke bace Ammi na dai yi shiru ne kawai, amman
SADIS nasan shi kam bai gane ta ba kam."
SADIS ya harareshi yace, "Kaji yaro ni da kai wa ya fara ganowa ba ni ba?."
Daga nan suka ci gaba da zolayar junansu, sannan suka nutsu suka fara gaisawa tareda firar
yaushe gamo, aikuwa fira ta b'alle a tsakaninsu musamman da suka ji an kusa bikin izzatu,
suma sai suka fara tsara yanda zasu yi nasu bikin.
**
Anfara tsara shirye shiryen bikin ta kowane b'angare, lefe ma Abaah ne ya baiwa Ammaah kud'i
taje da kanta har dubai ita da Mama hassatu suka lafto wa izzatu kaya tamkar ba za'a bar
duniya ba, haka kuma tamkar basu tab'a sanin zafin neman kud'in ba, komi yaji ta kowane
b'angare saboda idan nace zan tsaya fad'in abunda ke ciki sai an d'auki dogon lokaci ban gama
lissafin kayan ba.
Ana saura sati biyu bikin ne aka kwashi lefe himili guda aka kai gidan Malam d'akin uwar
Amarya wato mama hassatu.
Wannan ahali biyu da suka dunk'ule suka zamo d'aya kwatanta irin farin cikin da suke ciki ma
ba zai misaltu ba, domin kuwa sun had'e kansu waje d'aya sai nunawa juna karamci suke yi ba
banbanci, b'angaren kayan k'arin ni'ima kuwa bayan Ammaah tayi nata Mama hassatu ma
takanas ta samo, wata wadda ake kira hajiyar jin dad'i ta zo ta dinga gyara izzatu ta ko'ina ciki
da wajenta, har sai da Ammaah taga za'a kassara mata 'ya sannan ta rok'i alfarmar akai izzatu
Niger domin taje ta gano dangin mahaifiyarta, aiko ba musu aka shirya izzatun tareda rakiyar
Ammah da Garzalin domin shima ya kai gaisuwarshi wurin dangin Ammi.
A cen d'inma hakan ce takasance domin kuwa duk wani nau'in abunda suka san zai saka ango
manta sunanshi, to sai da suka bata na ci ta canye na sha ta shanye na tsugunnawa ma haka,
tun izzatu tana jin dad'in abun har ta kai ita kanta abun ya fara damun jikinta, ta zama wata lazy
bata da aiki sai kwanciya saboda abubuwan sun ratsa jikinta sosai, Garzali kwananshi biyu
acen ya juyo gida Nigeria saboda shirye shiryen da ke gabanshi,duk da ya samu an kammala
ginin gidan komi yaji babu ce kawai babu a ciki.
Ammaah da izzatu satinsu d'aya a cen suka dawo aka ci gaba da hidimar biki, wanda aka tsara
Kamu a ranar laraba Alhamis Aje k'auye gidan mai unguwa ayi wani shagalin bikin irin nasu na
k'auye, wanda mutanen garin suka shirya domin taya Izzatu da Garzali farin cikin wannan aure,
Jumu'a ayi walima asabar ayi yinin biki gidan malam wato mother's Day, da k'arfe biyar na
marece a d'auki amarya izzatu zuwa gidan angonta Garzali.
Bayan ankaita gidan mijinta da k'arfe takwas daidai a shiga had'ad'd'iyar dinner'r da mai girma
Gwamna zai had'awa ango da Amarya,ta taya su farincikin wannan aure, wadda manyan
mutane da dama zasu halarta, domin taya Abbaah murnar aurar da 'yarsa ta farko da yayi.
Rigiji gabji fan's Ruwa da k'ank'ara ku matso kar ayi bada mu ba ♀️♀️na tafi in
had'a jakar kayana
[8/22, 1:56 AM] Auntyna: https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp
*⭐⭐⭐TAURARI WRITERS ASSOCIATION⭐⭐⭐*
(We entertain and educate according to our religion and ethnics)
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*BAKON YANAYI book ne da ke tafe da zafin shi kada ku bari abaku labari salonshi daban
yake da saura 200 kacal zata sa ki kasance d'aya daga cikin member ta BAKON YANAYI
*
*'yan mata da kwarya suna kidansu zasu kai amarya shawara na baki cikin
gidanki kiyo biyayyasannu zan yo maki domin yanzu kin zamo amarya jin
dad'i rashinsa sai kin jure sannan zaki samu so da rahusa*
*SIXTY FOUR*
**********************
Ranar laraba ranar da aka tsara ce za'ayi kamu, tun kafin lokacin mutane suka fara isa k'aton
hall d'in da aka tanada domin wannan bikin kawai, wanda aka gayyato makid'a da mawaka
domin su zo su taya mutane gwangwaje wannan biki, an tsara wurin yayi masifar kyau saboda
takanas aka keta hazo domin lodo kayan k'awata duk wani events da za'ayi a bukin har a k'are.
Da misalin k'arfe biyar na marece ne manya manyan motoci suka fara parking a bakin harabar
hall d'in, inda zuk'a zuk'an mata suka yi ta b'ulb'ulowa tamkar wad'anda injin ke yiwa wanka, duk
wanda ka kalla ya kur'e adaka tamkar bazasu taka k'asa ba, mutane sai tururuwar shiga k'aton
hall d'in sukeyi suna samun muhallin zama suna hakimcewa tareda shan k'amshi, masu kid'a
sai aikinsu kawai sukeyi,nima dai naci kayan sallata na sami kujera na zauna sai kallon mutane
nikeyi d'ai d'ai, don kar a gano 'yar lek'en asiri ce ni a kora ni waje, ina nan hakimce akan tawa
kujerar sai ga Mc ya fara bayanin cewa ga amarya da ango zasu shigo, aikuwa na k'ara baza
idanuwana domin in basu abinci, cen na hango wasu manyan Alhazawa suna shigowa inda
masu kid'a suka sauya wak'a zuwa wake iyayen amarya da ango, d'aya bayan d'aya suna ta
shigowa tareda samun wurin zama su hakimce, cen na hango Mama hassatu da Amaah
fuskarsu sai annurin farinciki ke fita ,cen na hango wata hajiya taci arniyar kwalliya sai taku
take k'wask'was, ta sagala wata jaka a hannu tana wani d'agiyar hanci sama, abun mamaki
tana k'arasowa na gano ashe iya kulu ce, na k'ara gwalalo idanuwana domin in tantance shin
itace d'in kuwa KO mai kama da ita?, ai kuwa idanuwa na suka tabbatar man ita d'in ce ba
tantama, suma suka sami wurin zama suka zazauna, daga nan aka k'ara sanarwar ga ango da
amarya nan zasu shigo, tareda canza salon kid'an da wak'ar aiko naga kowa ya bazawa k'ofar
idanuwa, yayinda wasu suke ta jawo wayoyi suna jiran shigowar Amarya izzatu da angonta
Garzali.
Aikuwa sai gasu sun shigo Amina da Dr hashim a gaba suna taka rawa a hankali suna shigowa,
sannan wasu 'yanmata da samari bayansu a jere sai ga