Showing 15001 words to 18000 words out of 119425 words
Chapter 6 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
*INA JIN DADIN COMMENT'S DINKU YANA SANI FARIN CIKI BA KADAN BA ALLAH YA BAR
ZUMUNCI BA*
*KUYI HAKURI BAN SAMU DAMAR BAKU REPLY AKAN COMMENTS DINKU BA AMMA KU
SANI NAGA NA KOWA KUMA NAGODE INA JIN DADIN ADDU'O'IN KU AKAINA DUKAN KU I
LOVE YOU WUJIGA WUJIGA❤❤*
*PAGE FIFTEEN*
**********************
Garzali bai daina kallon shi ba, har saida idanuwanshi suka daina hangoshi, sannan ya dawo da
kallon shi akan izzatu, dake ta sharar baccinta hankali a kwance.
Sannan a cikin zuciyar shi yace:
"Bazan koma gida a yanzu ba, har sai zuwa lokacin da malam zai dawo"
Yana k'are wannan tunanin, ya kinkimi izzatu ya goye ta, ita ko ta lafe a bayansa luf saboda taji
dad'in goyon, sannan ya fara tafiya a hankali sai gidan inna hure.
A gajiye ya isa gidan, inna hure tana ganinsa, tayi saurin karb'ar izzatun taje ta shinfid'e ta,
sannan ta dawo ta kalleshi kallo mai cike da tausayi tace;
"Daga ina haka?"
Garzali ya waske yace:
"Daga gida, izzatu ce take fitina, nayita lallashi tak'i daina kukan, shine nace bara na goyata
nazo gidannan nasan kafin mu k'araso tayi bacci"
Inna hure ta kalleshi da kyau ba don ta amince da zancen nashi ba, yanayin shi kawai da ta
gani tasan akwai abunda ya faru a tsakaninsa da iya kulu, baya dai son fad'a ne, shiyasa bata
takurashi ba akan sai ya fad'a, ta share zancen sannan tace:
"To zo ka zauna in zubo maka abinci, kafin izzatun ta tashi daga baccin itama sai taci"
Aiko ba musu ya zauna, ta lafto masa tuwo yaci ya k'oshi yayi hani'an, sannan ya shige a cikin
matasan yaranta maza sukayita sabgogin su, atak'aice dai basu bar gidan ba har saida Garzali
ya tabbatar a lokacin malam ya dawo, sannan ya d'auki izzatu suka koma gida.
Kanshi a tsaye ya shiga gidan da guntuwar sallamar shi a baki, iya kulu tana ganinsu ta fara
fad'an cewa:
"Gidan ubanwa ka fito ne?, ace tunda safe da ka fita sai yanzu kaga damar dawowa gidan"
Garzali yana k'ok'arin kare kanshi ne, malam ya fito shima ya dasa tashi tambayar da cewa:
"Me aka yimaku ne a gidan?, da kukaji bakwa iya zama kuka fita tunda safe?"
Garzali zai fara magana, iya kulu tayi saurin fad'in:
"B'aceman da gani tun kafin in sauya maka kamannu, haka kawai zaka tsirowa kanka yawo a
banza, abunda ba halinka ba, ka ara ka yafa, wallahi gobe ka koma fita yawo sai na karya maka
k'afafu, daga kai har wannan farar kurar"
Garzali ya wuce abinshi yana dariya, malam ta bashi dariya, amma ya dake yace:
"Ai da kin barshi ya fad'i abunda yasa shi fitan, tunda ke da kanki kinsan yawo ba halinsa bane"
Iya kulu tayi gum, don tasan da maganar tayi tsawo, dole ne sai an samu matsala rayuka sun
b'ace, don ta fahimci malam tunda Dada ta rasu, abu k'iris tayi sai ya taso mata da fad'a,
sab'anin lokacin da Dada tana raye baya biyeta suyi ta musayar baki.
**
Kwana biyu a tsakani malam ya fara gyaran gida, iya kulu bata tantance ba, sai gashi malam
yana ta fiddo da kayan su Garzali dake wani d'ayan d'aki, inda suke kwana, yana kaiwa d'akin
Dada, bata sha mamaki ba har sai da taga anfara shigo da bulo bulo ana ginar wani d'akin acen
bayan d'akunansu, don daman cen d'aki uku ne ajere da juna, na iya kulu a gefe sai na malam
atsakiya sai nasu Garzali a kusa da na malam d'in.
Tambayar duniya tayiwa malam, akan me yake nufi da wannan gyare gyaren, amman yayi
banza da ita, tun tana d'aukar abun wasa har ta tub'ure, asanadiyyar ganin da tayi anhad'e
wannan sabon d'akin da akayi da tsohon d'akinsu Garzalin, ya zama ciki da falo, sannan yabi
d'akin ya shafe da fenti, itama yace ta kimtsa komatsanta ayi mata fentin.
A lokacin ne tunanin ta ya bata cewa aure malam zaiyi, aiko ta fara zazzaga ruwan masifa tana
Allah wadai da rashin halacci irin na malam, bakinta yana kumfa saboda masifa tace:
"Ashe dama jiran kakeyi k'asa ta shafe idon Dada kaci zarafina?, to wallahi baka isa ba, in ma
banda k'addarar aure ni me zanyi da talaka ma irinka, Allah ya jik'anki Dada, gwara da baki ga
zuwan wannan ranar , ta cin amanar marainiya 'yarkuluwa ba"
Ta k'are maganar tareda fashewa da wani bajimin kuka, kande dake lab'e a jikin katanga, ba
shiri ta k'yalk'yale da dariya har turmin da take hawa tana tsegumi, ya b'angwale ta fad'i kasa
tana dariyar mugunta.
Malam dai Ci kanki baice da ita ba, su Garzali ma sukayi cirko cirko suna kallonta,izzatu kam
ganin tana kuka itama sai ta fara kukan, ba shiri iya kulu ta maka mata dundu a baya tace:
"Rufa min baki munafuka, ai duk wani bala'in dake b'ub'b'ugowa a cikin gidan, kece kika tono
shi, shegiya dangin gayyar na'ayya, nikam ko wa yayi cikinki Allah ya'isa tsakanina dashi, don
kuwa nice aka k'unsowa masifa"
Garzali ya d'auketa yana lallashinta, malam ya fito, ya baiwa Garzali kud'i ya siyo mata kayan
k'walam, sannan yaja hannunta suka shige d'akinshi, aiko ya k'ara turawa iya kulu haushi,
k'iyayyar izzatu ta k'ara linkuwa a cikin zuciyarta, ta dinga jifanta da miyagun kalamai, yinin
ranar zir haka ya k'are tanata zuba masifa ruwa ruwa, har sai da ta gaji don kanta tayi shiru.
**
Da safiya ta waye akazo za'a yimata fentin tace bata so, dole aka k'yaleta akaje d'akin Dada
aka fente, inda su Garzali suka koma, duk da kasancewar d'akin ginin k'asa ne aka yiwa yab'en
siminti, shima ya fito fes su Garzali sai murna sukeyi.
**
Bayan sati d'aya malam yaci kwalliya da babbar riga da takalminshi sabbi k'al, yaje har d'akin
iya kulu sai zuba kamshi yakeyi, ya zauna a kan gadonta yana murmushi yace:
"Uwargida ki shirya tarbon bak'i, saboda yau ne za'a d'aura man aure da amaryata ta birnin sin
da kikace in kawo, wadda zata rik'a man izzatu idan tazo, kuma a yau zata tare a gidannan
insha Allahu, kiyi hak'uri uwargida abun ne yazo a k'urarren lokaci"
Ya zaro kud'i a aljihunshi ya k'ara cewa :
"Ga kud'i nan ki baiwa Garzali yayo cefane, domin adafawa bak'in da zasu zo abinci, saboda
yanzu 'yan jere zasu zo suyi jeren, d'akin abud'e yake idan sun zo"
Iya kulu kam, ba shiri tayi suman wuccin gadi, dak'yar ta samu kanta, har ta tattaro kuzarin
maka masa wata gagarumar harara, da jajayen idanunta, da suka daina samun bacci isashe a
cikin 'yan kwanakin, saboda tashin hankalin da take ciki ma har sun koma 'yan k'ananu, kafin
ta shirya abunda zata fad'a har malam yakai bakin k'ofa, yana murmushi yace:
"Ni na fita sai na dawo, hure zata zo ku had'a k'arfi ku tarbi bak'in"
Yana fita ya kira Garzali da Abu yace suje su k'ara share d'akin, a gabanshi suka fara aikin
sannan ya bar gidan.
Shokikuzo mu kwaso shoki
Akafta
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*SABODA JIN DADIN COMMENTS DINKU YASA NI KARO MAKU WANI TYPING
*
*MY FAN'S KUZO MUSHA RUWA DA KANKARA ⛈♀*
*PAGE SIXTEEN*
**********************
Garzali da Abu suna cikin d'akin suna shara ne, inna hure tayi sallama ta shigo gidan, tareda
zugar yaranta da suka zo ayi bikin dasu.
Inna hure tayita rafka sallama iya kulu tayi banza da ita, sai su Garzali ne suka amsa mata, jiki
ba kuzari ta ajiye kayan da tazo dasu, ta nufi d'akin iya kulu tareda maimaita sallamarta.
Iya kulu zaune ta shiga duniyar tunanin shin miye mafita, a tsakiyar kai taji sallamar inna hure,
ba shiri ta zabura tareda cewa:
"Wannan k'ulafuci har ina, zaki zo ki cikawa mutane kunne da makararriyar sallamarki"
Inna hure ta shanye b'acin ranta, a cikin kulawa tace:
"Ki fito ki bada asiyo kayan abincin, domin muyi sauri mu k'arasa kafin mutanen suzo"
Ba shiri iya kulu ta maka mata wata shahararriyar harara, mai cike da sak'on kashedi, sannan
tace da ita:
"To ashshibi, yabon da kikeso ayi maki ni bani buk'atar shi, kuje cen kuji da munafuccin ku, kud'i
ne dai wallahi ficika bazan bada ba,na danne abuna a matsayin cin amanar da aka yiman, Allah
ne ya tsaga da rabona, don haka sawunki a likkafa ki fita ki bar man d'akina, tun kafin infito maki
da sifar ta 'yar kuluwa ta gaske.
Inna hure kam gaskiyar da tayi mata yawa k'anzil bata ce ba, ta fito ta fara k'ok'arin gyara kayan
miyan da tazo dasu, kamar tasan za'ayi haka, tazo da shirinta, domin duk wani abu da ake
buk'ata sai da ta tanada tazo da abunta.
Iya kulu taji haushin da inna hure bata biyeta ba, sukayi tashin hankalin da zai wargaza farin
cikin kowa ba, shiyasa ta fito ta fara zazzaga ruwan rashin mutuncinta da ta saba tana cewa:
"Ku bak'in suka dama idan ta nice ma, motar da zata kwaso su gayyar tsiyar, ta fad'a gada
dukansu su margaya zuwa lahira, wallahi ni ko ajikina ballantana in tarbesu da wani abinci cen,
don nikam ai kije ma kiyita istigfari, saboda zunubin naki gawurtacce ne"
Inna hure tayi kamar ba da ita take ba, ta tattaro yaranta dasu Garzali, kowa ta raba masa aikin
da zaiyi, kafin kace me har sun dafe jalof d'in shinkafa, sai kamshi gidan yakeyi, ta d'auko
babbar fanteka ta zuba abincin 'yan jeren, sannan ta zubawa yaran sukaci suka k'oshi, sunata
jin dad'i.
Rabon kaddara, izzatu rik'e da kwanon abincinta, tana ci ta nufi d'akin iya kulu, dukansu
hankula sun d'auku ba wanda ya kula da shigarta a d'akin, aiko sai jin k'ararta aka yi, sai gasu
da rige rigen zuwa d'akin domin suji me take yiwa kuka, suna zuwa suka isketa kwance
magashiyya babu alamar numfashi a tattare da ita, Garzali yana k'yalla idanu ya hangota
kwance a k'asa kamar matacciya, ya kurma kuwwar kiran sunanta, inna hure tayi saurin
d'aukota ta fito da ita waje da gudu ta kinkimo ruwan tukunya masu sanyi ta watsa mata, aiko
sai ga izzatu da sauke wata k'atuwar ajiyar zuciya tana kuka, inna hure tasa zane ta goyeta, duk
da a lokacin ta fara wuce goyo, sannan ta fara jijjigata tayi bacci.
Yaran duka sai kuka suke tayi, musamman Garzali da ya aza hannu akai, yana ta zabga kuka
na tashin hankali, don shi a tsammaninsa, izzatun shi mutuwa tayi.
Iya kulu ta fito tana borin kunyar cewa :
"Gobe don ubanki in kina da shi, ki k'ara zuwa d'akina kiyiman b'anna, wallahi sai nayi maki
dukan da yafi wannan"
Inna hure tayi mata wani kallon, ke gudu mahaukaciya, sannan tace:
"Duk cutar da kike yimata, ta fili da b'oye kisani Allah yana kallon ki, kuma da sannu sai ya
sakamata akanki wallahi"
Iya kulu tayi shewa mai k'arfi, sannan tayi gud'a, har sai da kande dake jikin katanga ta k'ara
kwalalo idanuwa, bakin iya kulu har rawa yakeyi, wajen fad'in:
"Ko zaki rama mata ne kafin zuwan lokacin?"
Inna hure zatayi magana sai ga sallamar, masu jeren sunzo, nan ta bar iya kulu, taje ta tarbosu
da fara'arta, sai lale da marhaban takeyi dasu.
Iya kulu kam tana hango shigowarsu, kamar walk'iya ta fad'a d'akinta, kirjinta yana dakan
luguden uku uku.
Kuzo a danni k'irjin uwargida sarautar mata
Akafta
D/Auta ce♀
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*RAWA DA GIRGIZA ZANYI GABANKU IN JUJJUYACOMMENT'S DIN DA KUKE
INA JIN DADI*
*PAGE EIGHTEEN*
**********************
Aiko sai naga ashe har mutane sun fara watsewa a cikin gidan,sai tsararun mutane da aka bari,
cen na hango inna hure tana had'in kayanta, tareda had'a kan yaranta tana cewa suzo su tafi
gida.
Aiko ina tsaye a gabana, suka kimtsa kayansu, inna hure ta nufi d'akin amarya tayi mata
addu'ar zama lafiya, sannan sukayi sallama da juna ta fito, ta nufi d'akin iya kulu badon ranta
yaso ba, saboda gudun abunda zaije ya dawo, don tasan izuwa lokacin a wuya take da kowa,
musamman ita dai k'iris take jira tayi AYI uwar watsiya.
Taje bakin k'ofar ta iya kulun ta d'aga murya daga wajen tace:
"To 'yar kuluwa mu mun wuce sai wani jik'on"
Iya kulu daga cen d'akin itama, ta d'aga muryar tace:
"Umma ta gaida Aysha munafukai, bazaki jira ayi zaman auren dake ba?"
Inna hure tayi murmushi, ta fara tafiya sannan tace:
"Wani garin ai yafi gaban kunu, babban goro ai sai magogin k'arfe, kedai ki zauna ayi tayi dake,
a sannu zaki gane cewa ashe shayi ruwa ne sai an saka masa madara yake sauyawa"
Iya hure tana k'are maganarta ta saka yaranta a gaba suka bar gidan, don gudun haukar iya
kulu ta motsa su rabawa kansu abun fad'a acikin tsirarun mutanen da suka rage a d'akin
amarya.
A hankali mutane suka sulale aka bar iya kulu da amarya, sai su Garzali da suka shige d'akin
amaryar yayin da amarya hassatu ke rungume da izzatu a jikinta, tana basu labarai sunata
dariya, sab'anin abu dake kallonsu yana jin haushin SU gaba d'aya, da ya gaji da kawaicin ya
buga masu tsaki ya bar d'akin.
Amaryar malam ta bishi da kallo a cikin mamakin ganin rashin kirkin da ya aikata, Garzali yaji
haushin abunda Abu yayi, shine ya fara baiwa amarya hak'uri a cikin ko in kula tana murmushi
tace dashi :
"Ba komi"
A tare sukayi sallah da Amarya, har bacci ya sace izzatu a jikin amaryar, tace da Garzali yaje ya
d'auko kayan shinfid'ar izzatu na bacci ya kawo mata, aiko sai gashi ba jimawa ya dawo dasu
ya mik'a mata kasancewar a kullum sai ya wanke kayan tass, ko tayi fitsari ko batayi ba, don
izuwa lokacinma ta daina yin fitsarin kwancen.
Amarya ta shinfid'awa izzatu shinfid'ar akan makeken gadonta mai kyau, sanna ta d'auketa ta
kwantar a kai, aiko izzatu taji laushin katifa ta baje tana ta baccinta har da su minshari.
Garzali yaji dad'in abund amaryar malam tayi, wanda farin ciki ya kasa b'oyuwa akan fuskarshi,
har saida ya kalli amaryar yace:
"Mun gode iya"
Amarya tayi murmushi tace:
"Daga yau sunana MAMA ba iya ba"
Garzali yayi dariya, tareda gyd'a kai yace:
"To Mamarmu"
Amarya tace dashi yaje ya kwanta yayi bacci don yayi saurin tashi yayi sallahr asuba, aiko ba
musu yayi mata sai da safe ya fita yana ta jin dad'i.
Misalin k'arfe tara da rabi, malam ya shigo gidan, bakinshi d'auke da sallama, kai tsaye d'akin
amaryar shi ya shige, yana mai jin kansa a cikin wani tsatsar farin ciki, bayan ya zauna akan
gadon gefen da izzatu take akwance, bai kula da itaba yazo zai baje shima ya d'and'ani dad'in
gadon amaryar tashi ne, Mama Hassatu tayi saurin fad'in:
"Allah yasa dai idanunka su bud'e ka hango 'yata dake bayanka kar ka tada man ita tana
baccinta"
Ba shiri malam yakai dubansa akan izzatu, ya zaro ido awaje yace:
"Allah ya soni, wallahi ban kula da tana a gun ba, sai yanzu"
Mama hassatu, ta feshe da wani tsadadden murmushi, sannan tace:
"Taya zaka sani tunda idanunka arufe suke da ganin sabuwar amarya dal akwali"
Malam ya dafe bakinshi yana dariya, sannan yace:
"Sherin da zakiyi man kenan, a cikin dare?"
Hassatu tana dariya tace:
"Sha kuruminka, gobe ma zanyi maka a cikin rana"
Gaba d'ayansu suka tuntsure da dariya, aiko sai jin sautin iya kulu sukaji tana cewa:
"Cin amanar ta fara aiki tun a daren farko?, to wallahi bazan tab'a lamunta ba, ace inaji ina gani
amaidan borar k'arfi da yaji, a cikin gidan aure na ba"
Malam yayi tsam ya tashi, sannan yace da hassatu ta sameshi a d'akinshi, don shi bazai kwana
anan ba, haka ko akayi yana fita ta k'ara kimtsawa, sannan ta fito tana canki in cankar ina ne
d'akin malam d'in?,ta gane d'akin ne ta sanadiyyar talkaminshi da tagani ajiye a k'ofar d'akin.
Da sallama a bakinta ta shiga, idonta suka sauka akan k'wayar idanun iya kulu dake zaune ta
zurawa k'ofar idanu, tana jiran taga shigowar amaryar, domin taga wace mai ganganci ce, da
zata had'a kishi da ita!, aiko sai gashi taga hassatu ce da ta sani, waton tsohuwar masoyiyar
malam da yaso aure Allah bai nufa ba, aiko ganinta yasa gaban iya kulun ya k'ire ya fad'i,a nan
take jib'i ya dinga kwaranya a duk wata k'ofa dake jikinta, jikinta ya d'auki rawa tamkar ana kid'a
mata gsngunma.
Hassatu ta wayance ta fara gaidata, amma ina iya kullu an lula kogin tunanin makomarta,
saboda ita kanta tasan kishi da