Showing 45001 words to 48000 words out of 119425 words

Chapter 16 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

ko mama hassatu.

Aiko yau da gobe bata bar komi ba, ance rana dubu ta b'arawo rana d'aya tak! ta mai kaya, sai
gashi labari ya fara bazuwa a k'auyen, izzatu biyar Alhazan birni takeyi suna sharholiyarsu,
saboda a kullum sai an ganta wani Alhaji ya d'auketa a bakin titi, kuma idan lokacin dawowar
makaranta yayi, sai ya dawo da ita ya ajiye, tana lab'awa da makaranta tana yawon barikinta.




Injisu fa� ba injini ba🤭






Akafta🤾🏻â€â™€ï¸





D/Auta ce😹

[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*


*NA HADIZA D/AUTA*


*ROKON ALLAH NIKEYI HADANI DA MASU SO NA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻BAKANDAMIYA NIKE YI
ALLAH BANI BANI BANI MASU SONA KO GIDA KO DAWA 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*

*DARE DA YAWA RANA DA YAWA ZASUYO GUSHEWA GA RUWAN SAMA YAYYAFI

LOKACI NA DAMANA ZAIYO WUCEWA💃🏻💃🏻💃🏻*

*AYYE TAMBARI SAI SARKI SAI SARAUNIYA TAMBARI NA DOKA DAKU NAKE YAKU
JARUMAI NA GAGARAGASA💃🏻💃🏻💃🏻*


*PAGE THIRTY FIVE*


**********************

Labari har gidan mai unguwa, malam ma aka tareshi ana yimasa shagub'en, abunda ake
zargin izzatu tana aikatawa,duk da malam yaji zafin abun, amman zuciyarshi ta kasa amince
masa izzatu zata yi hakan, shiyasa da yaje gida baija abun da tsauri ba, ya dai kira mama
hassatu ya sanar da ita, mama hassatu ranta ya b'ace sosai akan wannan k'azafi da aka yiwa
izzatu, amman tace da malam, su jira izzatun ta dawo sai suji ta bakinta.

Aiko baba kalla yana kawowa a dai dai inda yake ajiyeta ya Parker, izzatu zata bud'e k'ofar ta
fito, sai ga fadawan da mai unguwa yasa su lab'e, akan su sakashi a gaba har sai sun kaishi
fada, aiko suna zuwa ba b'ata lokaci d'aya ya shiga gaban motar ya zauna, yayinda d'aya ya
bud'e baya inda izzatu take a zaune ya zauna.
Baba kallah da izzatu sai rabon ido sukeyi a cikin fargaba, suna mamakin abunda yake shirin
faruwa dasu, kafin baba kallah ya samu abin cewa, fuska a had'e sarkin fada yace dashi;

"muje k'ofar gidan mai unguwa, yana son magana dakai"

Izzatu tana jin haka, tayi saurin bud'a k'ofa zata fita, jikinta yana ta rawa, sarkin fada ya daka
mata wata arniyar tsawa yace;

"Gidan ubanwa zakije ne?"

Bakinta yana rawa tace;

"Gidanmu zanje"

Don tsawar da sarkin fada yayi mata, ta firgita ta, har fitsarin da take ta matsewa ya fito sha!,
yana biyar k'afafunta, ba shiri ta koma ta zauna, sai had'iyar yawun wahala takeyi.

Baba kallah baice dasu k'anzil ba, har sukaje k'ofar gidan mai unguwa, wanda izuwa lokacin
labari ya bazu a garin, akan cewa ankama izzatu da Alhajin da ke d'aukarta a mota, kafin kace
me k'ofar gidan ta cika mak'il kowa da abunda yake fad'a, wasu su kare izzatu, yayinda wasu
suke ta aibantata, tareda tofin alatsine akan asalinta.

Jiki a sanyaye Baba kallah ya fito motar, saboda ganin cincirindon mutane, 'yan ganin
k'wak'waf da suka baza ido suga me za'ayi, domin kada suyi mantuwa idan sunje bada labari,
amma ganin yanayin baba kallah da kwarjinin da ke fuskarshi, yasa mutane da dama suka sha
jininsu, musamman yanda sukaga izzatu ta fito tana ta wani marayan kuka, saboda ita ba komi
yake sakata kuka ba, sai tuno abin kunyar da ta jawa su malam a k'auyen.

Baba kallah da mai unguwa, tareda sauran masu fad'a aji a k'auyen, suka saka izzatu a tsakiya
suna tambayarta miye had'inta da baba kallah, izzatu tana kuka tayi bayanin tun farkon
had'uwarsu ranar da ya taimaketa a hannun 'yan iskan da sukaso suyi mata fyad'e, har izuwa
ranar, amman ta b'oye abincin da yake bata, don ta rage girman tuhumar da ake yimasu, baba
kalla ma yayi masu guntun bayanin taimakon da yake yiwa izzatu, sannan ya k'ara da cewa;

"Izzatu tamkar 'yata na d'auketa, bazan tab'a bari a cutar da ita ba ma, balle har ni in aikata da
kaina, ni katanga ne a wurinta,raina fansa ne a wajen kare lafiyar izzatu, saboda ni kaina idan
wani abu ya sameta, kwatankwacin wanda kuke zargi a yanzu, to wallahi tabbas bazan tab'a
yafewa kaina ba, wanda nasan Allah ma bazai yafe man ba, da kunsan kowanene ni a wurin
izzatu nasan da baku zargeni ba, amman ba komi nayi maku uzuri, saboda rashin sani ne ya
kawo hakan"

Yana k'are maganar wasu hawaye suka zubo masa, ya ciro kud'i a aljihunsa, dami guda ya
ajiye a gaban mai unguwa yace;

"Ga kud'i nan a siye mashin d'in da zai dinga jigilar kaita makaranta na barku lafiya"

Ya tashi ya fita, ya fisgi motarshi da k'arfi, yabar k'auyen, tareda rakiyar 'yan iskan garin suna
yimasa a ture.

Gaba d'aya wanda ke fadar jikinshi yayi sanyi, saboda dukansu sunsan matsayin izzatu ga su
malam, shiyasa suka shiga tambayar junansu, kodai shine baban izzatun?,idan ma ba shi bane
to akwai wani abu da yasani dangane da izzatun, shiyasa sukayi tsit kamar ruwa ya cisu, mai
unguwa yayi gyaran murya yace;
"Sarkin fada aje a sanar da mai shela ya shiga lungu da sak'o na garinnan ya fad'awa mutane,
Allah ya wanke izzatu daga zargin da ake yimata, wannan Alhajin da yake kaita makaranta d'an
uwanta ne a birni"

Aiko kafin kace me gari ya rincab'e da guutsuri tsoma, wasu sun amince, wasu kuma sun
d'auka kareta ne kawai akeyi, su malam Ma suna cikin gida sukaji wannan sanarwa, hankalinsu
ya d'an kwanta, amman dai sunfison suji a bakin izzatun.

Har gida mai unguwa yasa aka rako izzatu, tareda yiwa su malam bayanin da mai shela yakeyi,
sannan aka sanar da malam mai unguwa yana nemansa, iya kulu dai farinciki fal ranta, amman

bata ce uffan ba don tana jin tsoron abunda malam zai kad'ata gidansu, da ta kira k'addararren
gida.

Amma tana ganin fitar shi, ta fara k'yalk'yala dariya tareda yin gud'a ta buga cinya tace;

"Yau dai kun fara girbar abunda kuke shuka,watak'ila ma watanni ne a tsakanin uwar da d'iyar,
hassatu sai a fara murnar zuwan d'a da jika d'an boko ayyururui nanaye sama tayi ruwa k'asa ta
shanye, yarinya gado sai d'an gado"


Mama hassatu da tirtsetsen cikinta ta tashi tsam, taja hannun izzatu suka shige d'aki, suna
shiga ta jawo wuk'a tace da ita, ko tayi mata bayanin abunda ke tsakaninta da Alhajin ba, ko tayi
mata gunduwa gunduwa.

Aiko izzatu jiki yana kyarma tayiwa mama bayanin komi tass, mama hassatu ta zaro ido awaje
tace;

"Waton duk kashedin da nayi masa ashe baiji ba ko?, to wallahi idona idonshi, taimakon dole
ne?"

Haka dai mama hassatu tayi ta yiwa izzatu fad'a kamar zata daketa, tace kuwa muddin ta sake
kulashi, sai ta tsine mata tunda haka takeso, izzatu sai kuka takeyi tana bada hkr akan bazata
sake ba,iya kulu har da saka tab'arya a turmi tana kid'a tana wak'ar, habaici kala kala.

malam ya dawo yana yiwa mama bayanin abunda mai unguwa ya sanar dashi akan baba
kallah, wanda shi kanshi malam jikinshi yayi sanyi da yaji, don ya tabbatar kallah yasan wacece
izzatu, tunda har ya bada kud'i asiye mashin a dinga kaita makaranta dashi, mama hassatu ma
ta zargi lalle kallah, yanada masaniyar asalin izzatu, a nan take yiwa malam bayanin juyen da
ya dinga yiwa izzatu, a lokacin da iya kulu take d'ora mata tallah, aiko dukansu suka aza alamar
tambaya akan baba kallah, shin miye dangantakar sa da izzatunsu?.

Mai unguwa ya bada an siyo mashin d'in, sabo dal ya kira malam yace dashi idan akwai wanda
zai dinga kaita makarantar, sai abashi, malam ya fad'awa mama hassatu, tace dashi a baiwa
Abu ya dinga kaita, idan ya ajiyeta sai ya d'an zagaya yayi acab'arshi, har zuwa lokacin da ya
daidaici an tashi, sai yaje ya d'aukota su dawo gida, iya kulu tayi tsalle ta dire akan Abu bazai
koma baya ba, ya rasa aikin da zaiyi sai jigilar kai izzatu yawon gantali.

Abu ma da yazo akayi masa bayani, saida ya zunduma uwar asharr sannan yace ;

"Wallahi ko na rasa aikinyi, bazan tab'a d'aukar wannan munafuka inkaita yawon ta zubar ba,
sai dai tsiya takasheni da in zama bawanki, shegiya wallahi muddin kika yarda na d'auke ki, sai
dai adawo da k'asusuwanki, na kakkarya ki acen"

Mama hasatu tace tunda abu yak'i abaiwa, ummaru yaron hure na biyu, aiko inna hure ta dinga
godiya, ummaru akwai zafin nema, gashi yasan ciyon kansa, don ko anan k'auyen baya rena
sana'a, aiko a kullum yazo har gida ya d'auketa, ya kaita makarantar, idan ya ajiyeta yaje
sabgoginsa, a cikin sati d'aya ummaru ya fara gano, ba k'aramar bajinta akayi masa ba, yaji
dad'in wannan abun alkhairin da Mama hassatu tayi masa silar samu.

**

Cikin mama hassatu ya shiga watan haihuwa, tana fara jin nak'uda tace da malam akaita asibiti,
kamar wasa suna zuwa akace haihuwa ce, cikin ikon Allah mama hassatu ta haifo 'yarta
santaleliya, murna a wajen malam da danginta ba kama hannun yaro, bayan angama bincikar
lafiyarta da 'yar jaririyar, aka tabbatar ba wata matsala suka garzayo gida, cike da farincikin
wannan k'aruwa da ubangiji ya basu.

Izzatu tana dawowa gida, tayi arba da 'yar jaririya, ta fara murna, a kullum tana nanuke da
jaririya, mutane sai zaryar zuwa ganin jaririya akeyi, ana taya mama murnar ganin 'yarta a
duniya itama kamar kowa.

Iya kulu kam, bak'in cikin kamar ya kasheta, amman duk da haka tayi sha'awar ace itace ta haifi
'yar, sabida yanda take kwad'ayin haifuwar macen Allah bai kawo mata ba, har kuka ta shige
d'aki tayi tana rok'on Allah akan ya bud'e mata mahaifa hakanan itama ta haifo macen taji me
ake ji, a huta da yimata rawar kai.
Ranar suna yarinya taci sunan Dada, wato MARYAM, izzatu da mama da malam a tsakaninsu
sai ka rasa banbance wa yafi son maryam, saboda kulawar da suke bata, tarairayarta sukeyi
tamkar k'wai, wanda hakan shi ke b'atawa iya kulu rai, tayita maka masu harara, tana mere.

Garzali yazo yaga maryam kwana d'aya ya koma, saboda suna cikin jarabawar shekara ta biyu
a jami'a.
Dr ma yana zuwa jefi jefi, yana kawowa su mama gaisuwa, tareda alkhairin shi ga maryam ko
izzatun, har saida malam ya zaunar dashi, yayi masa godiya, sanan ya dakatar dashi da
wannan d'awainiya da yakeyi, a cikin dubara ya fayyacewa malam gaskiyar abunda ke kawo
shi, malam yayi jim, sannan ya d'ago fuska a cikin damuwa yace dashi;
"Naji dad'in yanda ka nuna k'aunarka ga izzatu, amman wani hanzari ba gudu ba, izzatu ba mu
muka haifetab, tsintar ta mukayi, shin kaji ka gani zaka aureta da zuciya d'aya?"

Dr yayi shiru na d'an lokaci sannan yace;

"Tsakani da Allah nike son izzatu, ko ta wace hanya aka sameta, naji na gani zan iya aurenta"

Malam yace;

" Alhmdllh, to kaje kayi shawara da iyayenka, idan sun amince kazo zamuyi mgn dakai"



Tofa malam ko ka mance da Garzi😒






Akafta�







D/Auta ce🥰
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*


*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*MEERAHGEE, DA K'AWATA BILKISU, WANNAN PAGE NAKU NE SUKUTUM KUYI YANDA
KUKE SO DASHI NAGODE DA KARAMCIN KU A GARENIí ¾í´í ¼í¿»*


*Ina alfakhari daku mutane na inayin ku over wallahi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*


*Ruwa da kankara fan's ga jinjinar ban girma, saboda kaunar da nike maku zan iya shanye
gorar sob'o🤪*

*PAGE THIRTY SIX*


**********************

Bayan kwana biyu Dr ya dawo, ya sanarwa da malam cewa, iyayenshi sun amince, malam yaji
dad'in abun sosai, yace da Dr yaci gaba da nema idan Allah yayi matar shi ce shikenan, zasu
taya shi murna.

Farin ciki ya mamaye zuciyar Dr, saboda jinsa yakeyi tamkar Ma har an bashi auren izzatun,
don yasa a ranshi ruwa da iska bazasu hanashi auren sahibal-k'albinsa gimbiya izzatu
ba,amma duk zuwan da yakeyi ya kasa fitowa k'arara ya sanar da izzatu sonta yakeyi, sai dai a
duba d'aya idan kayi masa, zaka gano tsantsar k'aunar da yake yimata.
Malam ma bai sanar da kowa wannan magana ba, ko mama hassatu batasan abinda ke faruwa
ba, amman dai itama jikinta ya bata Dr son izzatu yakeyi, tun asibiti, sai gashi kuma uwar
siyayyar da yayi mata, a ranar da aka sallamota daga asibitin, ya nuna tabbas da zafinsa ya fito
nema, amma a yanayin izzatu da ta gani har yanzu bata gano Dr sonta yakeyi ba, ita iya
saninta da k'urciyarta, mutunci da ke tsakaninsu ne yake kawo shi gidansu.

Garzali bai cika dawowa k'auyen ba, saboda ya tsani halayen iya kulu da take yi a gidan, idan
ma yazo da b'acin rai suke rabuwa, shiyasa yafi gane ma yayi zamanshi a cen, yayi ta buga
bugarshi yana samun, abunda zai rik'e kanshi dashi,idan yaso ganin izzatu sai yaje makarantar
ya dubota.
Yaji dad'i da yaji ummaru yana kai izzatu makaranta, izzatu tayi masa bayanin mai unguwa ne
ya bada mashin a dinga kawota, yayi ta yiwa mai unguwa addu'ar gamawa lafiya.

**

Wasa wasa soyayyar Dr, ta fara shiga zuciyar izzatu, saboda a sannu sannu yake ta koya mata
yanda zata soshi, sai gashi akayi dacen hankali ya k'ara shigarta, ita da kanta ta gano, ashe da
gaskiyar yayanta Garza da yace Dr sonta yakeyi.

Soyayya mai k'arfi ta k'ullu a tsakanin Dr da izzatu, duk da a gefen zuciyarta a kullum tafi
girmama son Garzali akan Dr, ta dai jingina abun ne da cewa soyayya ce irinta 'yan uwan juna.

Mama hassatu har ga Allah ba dr taso ace izzatu ta aura ba, amman dai tabar maganar ne, don
ganin malam bayason maganar, shiyasa baiyi shawara da kowa ba ya amince wa Dr, a kan ya
kafa soyayyarshi a wurin izzatu, don a k'ara tabbatar mata da cewa sune suka haifeta, mama
hassatu tayi ta nunawa malam, Garzali ne ya dace ace ya auri izzatu ba Dr ba, malam yayi
tsayinshi akan idan dai ba iyayen izzatun ne suka bayyana ba, to tabbas ba wanda zai auri
izzatu sai Dr, don ya yaba da mutuncinshi, kuma yana da tabbacin izzatu zatayi rayuwar farin
ciki a gidan shi.

Duk zuwan da Dr yakeyi, bai amince yazo da kowa a wurin izzatu ba, saboda yana jin tsoron a
ganar masa ita, haka kawai yakejin tsoron bayyanata a wurin abokanshi, don gudun yana jin
tsoron wani yayi masa shigar sauri, amman yakai labarinta gidansu, sai dai ya b'oyewa

iyayenshi wacece izzatu.

Sunyi mamaki da sukaji, a k'auye yake neman aure, duk matan dake birni ba wadda tayi masa
sai 'yar k'auye, yayi ta kwatanta masu irin had'uwar da izzatu tayi, amman dai su har lokacin,
zuciyoyinsu basu natsu da auren 'yar k'auyen da yake so ya yi ba.

Shiyasa ya yanke shawarar, kawai ya kawo masu izzatun su ganta da idanunsu,koda zasu
gasgata cewa ita daban take da 'yar k'auyen da suke fad'a.

Aiko watarana da yaje fira yayi mata zancen zuwa gidansu, ta nuna masa sai abunda malam
yace, aiko baki a sake ya rok'i malam alfarmar, a bar izzatu taje ta gaida iyayenshi,.

Mama hassatu bataso izzatu taje ba, don ita duk da mutuncin da Dr yake dashi, tafi sowa
Garzali ita da shi.

Amman malam saboda jin nauyin Dr da yake yi, yasa ya amince da zuwanta, amma da
sharad'in bazata je ita kad'ai ba, sai dai suje ita da d'iyar mama hure Amina, Dr yaji dad'in
wannan karamci da malam yayi masa, yace gobe zaizo ya tafi yana murna akan gobe zai zo su
tafi.
Koda safiya ta waye da shirin zuwa gidansu Dr izzatu ta tashi, tana zaune mama tana shace
mata tsibin gashinta da baya kitsuwa, a kullum sai dai mama tayi mata kitso k'wara biyu ko uku
da gashin, amma baya kwana uku yake kwancewa, saboda sulb'in gashin.

Mama da izzatu sai firar su sukeyi a tsakaninsu, maryam 'yar shekara biyu tana kukan ala dole
sai an bata abun shartar kan itama ta shatawa izzatu, mama ta hana saboda bata son Dr yazo
yayita jira.

Izzatu ta janyo ta, ta d'ora ta akan cinyarta, tace;

"Zo nan ki zauna my ilham, k'yale mama kina zuwa muje dake ko?"

Ilham ta d'aga kai, izzatu ta lakuce mata kumatu tace ;

"Zaki shiga mota ko?"

Aiko carab sai a kunnen iya kulu, aiko ta k'yalk'yale da dariya ta fara banbamin ta da ta saba,
mai had'e da habaici tana cewa;

"A hayye su mota manya, inda ba'asan asalin kaza ba, da tace daga makkah ta fito, oni 'yar
kuluwa kwad'ayi dai mabud'in wahala ne, anga mai kud'i an lik'e, to adaiyi a hankali, don idan
ba'a iya kama b'arawo ba, sai shi b'arawon ya kama mutum, sai amfani akeyi da farin komo ana
tatse bawan Allah, wannan yaro yana bani tausayi a gidan duniya, an yi masa rufa rufa za'a lik'a

masa kaska rab'i kisha jini, Allah dai ya ceci wannan yaro shikam don an riga anyi masa kamun
fatsa"

Mama hassatu jin iya kulu tana k'ok'arin b'aro zance, tace da izzatu ta tashi taje ta shirya, ranta
a dagule ta kalli mama tace;

"Wai mama ni me nayiwa iya ne da bata sona ne?, sai inji tana ta wasu maganganu da ni nike
rasa gano abunda takeso ta sanar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login