Showing 114001 words to 117000 words out of 119425 words
Chapter 39 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
sannan aka sallomoshi, da k'udurin idan safiya ta waye ya kora
iyar ta koma cen k'auye da zama har sai d'iyan Kande sun haifu, don yayi rantsuwa ba zai
zauna gida d'aya da d'iyan shaggu ba.
Aiko cikin dare sai ga gangar 'yan fashi sun dira gidan. Malam da niyyar su ta Kashe shi, anyi
bata kashi tsakaninsu da masu gadi da scuritys d'in dake tsaron gidan, amman duk da haka
sai da suka ci nasarar shiga sashen iya kulu, a tsammaninsu Malam d'in a cen yake aikuwa sai
ga jami'an tsaro anturo masu mota mota, da suka ga basu sami sa'ar ganin Malam ba iya kulu
tana fitowa a rud'e tana kuwwa, wani daga ciki ya saita bindigarshi ya sakarwa Iyar bullet a
k'afa, saboda jin sautin jiniyoyin motar 'yan sanda da sojoji, sun tabbatar da an ritsa su shiyasa
d'aya yaji haushi ya sauke fushinshi gareta, ba shiri ta fad'i k'asa tareda k'walla k'ara wanda
yayi dai dai da shigowar dubban sojojin, Abu dake cikin gangar 'yan fashin ya cakumo wanda ya
halbi iyar a cikin karaji yace, "Mamata ce fa"
A cikin zafin nama ya saita d'an fashin ya halbeshi a k'irji, halbin yayi daidai da k'arasowar
jami'an tsaron suka saita shi da bindigogi ba shiri ya yi hand's up, suka tasa keyarshi tareda
sauran 'yan fashin suka tafi dasu, aka bar wasu suka ciccib'i iyar da take a some suka fito da
ita.
Malam da ke lab'e tareda Mama hassatu sai jibin wahala tareda tsoro suke yi, musamman da
suka Ji yo k'arar halbe halbe, Ilham ta fasa k'ara sauran ma'aikatan da ke gidan suma suka
k'ara tsurewa, zuwan jami'an tsaron yasa hankalinsu ya d'an kwanta, Malam yayi k'arfin halin
fitowa ya lek'o aiko sai yaga an taso k'eyar 'yan fashin a gaba hannuwansu a sama, sai kuma
ga wasu jami'an sun d'auko iya kulu ranga ranga, ai afujajan ya iso wurinsu hankali a tashe
yake kiran sunanta a rude dashi aka shiga motar wasu 'yansanda suka ja motarsu da k'arfi
suka nufi asibiti mai zaman kanta da ita, yayin da wasu suka tafi da 'yan fashin wasu suka tsaya
tsaron gidan.
Da k'yar aka samu jinin da ke zuba a k'afar iyar ya tsaya, sabida ga tsintsiyar k'afa aka halbeta
gaba d'aya k'afar ta ragargaje, dole Malam yasa hannu akan za'a yi mata aiki a cire k'afar don
ta tashi aiki kwata kwata gaba d'aya , an d'auki awanni kafin a fito da ita kwance sambal kamar
matatta, an saka bandeji an nad'e gundulalliyar k'afar da aka yanke.
Koda safiya ta waye labari ya bazu a ko'ina akan b'arayi sun shiga gidan surukan d'iyar
Gwamna, Gidan TV gidan Radio tareda jaridu duk baza labarin ake yi, sai dai an b'oye sunan
Abu don kare martabar gidan Malam da gidan Gwamnati, saboda gudun zubewar mutuncinsu.
Iya sai da tayi sati bata farfad'o ba tasha gorunan jini tareda gorunan ruwa sunfi a k'irga, koda ta
falka ta ganta da gundulalliyar k'afa taci kuka kamar ranta zai fita, musamman idan ta tuno
ganin da tayiwa Abu a cikin gangar 'yan fashi, a take hawan jini ya rufe ta har sai da bakinta ya
karkace, ko Malam kanshi k'arfin hali ne kawai yake yi amma da za'a aunashi da ance shima
jinin nashi ya haye saboda bak'in cikin jin sana'ar da Abu yake yi wadda har yayi amfani da
damar yazo da mutanenshi akan a kashe shi.
Malam yayi kuka yayi kuka musamman idan ya tuno irin bala'o'an da ya haddasa, d'iyan Kande
biyu duk ya d'irka masu ciki, gashi yazo har gida da nufin ya kashe Malam ALLAH bai nufa ba
sannan gashi sanadin hakan Iya ta rasa k'afarta d'aya, kuma duk akan sakaci tareda son zuciya
wajen gurbata tarbiyyar Abu da Iyar tayi, yanzu gashi an b'ata goma biyar bata gyaru ba,
shiyasa Malam ya rok'i Abbaah akan hana sanarwa da su Garzali abunda ya faru, don dole ne
idan yaji zaice sai ya dawo to kuma gashi karatun nashi mai zafi ne, wanda shekara d'aya ce
kacal zai yi karatun acen.
Bayan wata biyu Iyar taji sauk'i aka sallamota tareda k'afar roba da aka yi mata, wadda kullum
ta kalleta sai tayi kuka tareda rok'on gafarar Ubangiji don tasan hak'k'in Izzatu ne yake bibiyarta.
Cikin Mari a lokacin watanshi takwas yayin da na Izzatu yake cikin wata na shidda, Indo kuma
nata yana wata hud'u.
Iya kulu ta koma ta ALLAH kullum da carbi a hannunta tana lazumi tareda istigfari tana rok'on
ALLAH akan ya yafe mata abunda tayi a baya, kullum bata da aiki sai kuka saboda an yanke
wa su Abu hukuncin daurin rai da rai a gidan maza, saboda sassaucin da aka nemar masu don
farko hukuncin kisa aka yanke masu ta hanyar rataya.
Watan haihuwar Mari yana kamawa Malam ya maida Iya k'auye aka dawo mata da indo da Mari
a wurinta, ita aka barwa kula da su da komai nasu duk da itama ba wata lafiya ce da ita ba, aiko
wani dare nak'uda ta kama Mari aka kwasota zuwa asibitin birni, zuwansu bai fi minti biyar ba ta
haifo d'anta k'ato guda amman ko shurawa baiyi ba ya rasu, asubar farin aka nemi Mari sama
da k'asa aka rasa ba'a ganta ba ta tsere, hankulan mutane ya k'ara tashi aka bazama nemanta
lungu da sak'o na garin ba'a ganta ba, dole aka zubawa sarautar ALLAH ido, wata d'aya a
tsakani sai ga labari yazo anga Mari gidan Karuwai na garin, ta fetsare iya fetsarewa bata kunya
kuma bata shayin kowa akan sana'arta ta karuwanci da ta fara, dole aka zuba mata idanuwa
don ta riga da ta fitsare k'afafunta.
Cikin Izzatu yana Wata takwas Ammaaah taje cen London ta zauna tareda da ita har sai da ta
haihu, saboda cikin yayi girma sosai kamar ba haihuwar farin ba, gashi yana bata wahala
matuk'a don ko k'afafuwanta sun kumbure suntum, ga k'afarta d'aya da ta mak'ale dak'yar take
iya tafiya, tayi ta kuka tana rok'on ita dai acire mata cikin hakanan ta gaji, Ammah da Garzali
suyi ta aikin lallashi da ban baki.
Aiko ranar haihuwa ba k'aramar azaba tasha ba tun safe ta fara nak'uda har marece, tun ana
tsammanin zuwan haihuwar har aka yanke shawarar ayi mata CS, Garzali yana kuka saboda
tsananin tausayinta ya saka hannu, ana shirye shiryen shiga da ita d'akin tiyata ne nakudar tazo
gadangadan, likitoci suka rufu a kanta cikin ikon ALLAH sai ga d'anta ta haifo k'ato guda, ana
cikin murna ta k'ara santalo wani yaron sai dai shi bai kai girman na farkon ba, murna wajen
Garzali da Ammaah abun ba magana.
Bayan an shirya yaran ne aka mik'awa Garzali su duka biyu ya karbesu ya rungume a jikinshi
yana shak'ar kamshinsu, sai godiya yake yiwa Ubangiji da ya azurtashi da samunsu, a take yayi
masu hud'uba da sunan AYUBA da YAHAYA waton dai sunan Malam da Abbaah, sannan ya
mik'a su ga Amaaah ya fita cike da murna tareda tsananin farin cikin, sai kiran wayoyi yake yi
yana sanar da mutane abun alkhairin da ya same shi.
Bayan kwana biyu da sallamosu ne jirgin 'yan Nigeria masu zuwa ganin jarirai ya isa London,
kowa sai Murnar ganin jariran yake yi, Iya kulu yaran rungume a jikinta ta fashe da kuka tana
rok'on Izzatu ta yafe mata, Izzatu ta ce da ita ai ita tuni ta yafe mata duk abunda tayi mata, don
ALLAH ta daina dawo da hannun agogo baya, Iya kam duk ta motsa bata fasa rok'on yafiyar
Izzatun ba, saboda a ganinta iftila'o'an da duk suka sameta suna da nasaba da zaluncin da tayi
mata, sai a lokacin ne ake yimasu bayanin abunda ya faru da wanda yake kan faruwa, Izzatu
tayi kuka sosai da taji abubuwan da suka faru bayan basu nan, tayi ta nanata yafiyar da tayi wa
iya Kulu ko don ALLAH ya tsayar da sakamakon iya hakanan, Kwanan Iya biyu jirgi ya juya da
ita Nigeria saboda Indo da ta baro ciki ya tsufa don a lokacin watanshi bakwai.
Ta bar sauran wad'anda zasu tsaya ayi bikin sunan dasu, Amina ma duk da cikin da take dashi
d'an wata biyar bai hanata halartar ganin jariransu ba, dangin Abbaah ma da suke ganin lafinsa
akan hukuncin da ya yanke wa ALHAJI sani da shu'aib, da suka gano gaskiya daga baya duk
sun bi don ma da yawansu sun zo ganin jariran, anyi shagalin bikin suna cikin natsuwa da
kwanciyar hankali sannan suka dawo tareda kewar juna.
Bayan sati d'aya da suna IZZATU ta kammala jarabawar k'arshen shekararta ta farko Ammaah
ta kwasota suka baro London tareda 'yan jariranta da suka ci sunan AMIR da AMMAR,
HASSAN shine AYUBA wanda ake yiwa lak'abi da AMIR sai HUSSAINI shine YAHAYA wanda
ake cewa AMMAR, suka garzayo k'asa Nigera da zummar idan shima Garzali ya kammala
karatunshi da ya rage saura wata biyu zai biyo bayan su.
Akafta
D/Auta ce
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp
*⭐⭐⭐TAURARI WRITERS ASSOCIATION⭐⭐⭐*
(We entertain and educate according to our religion and ethnics)
*PAGE SEVENTY FIVE*
*******************
Ammi da Abaaah sunji dad'in ganin 'yan biyun jikokinsu, SUDEIS da SADIS dasu fahat sai
murnar ganin jarirai suke yi, Ammar kam yafi kowa jin dad'i saboda sunanshi da aka sakawa
mai sunan Abbaah, a kullum yana nanuke da mai sunanshi ko daukarsa baya so ayi, Ammaah
da Ammi kam sai kula da 'yan jikokinsu suke yi tareda mahaifiyarsu Izzatu mai jego, Mama tana
iya k'ok'arinta wajen zuwa ta gansu ko tasa akawo mata su su yini wurinta, soyayya da kulawa
fa mai jego da 'yan yaranta suna samu sosai, wata d'aya da haihuwarsu sunyi b'ulb'ul da su
gwanin sha'awa, itama kanta tayi jiki abunta saboda ba wata wuyar wahalar reno take sha ba,
iyakacinta da su idan zata basu nono kuma da sun sha za'a karb'esu, shiyasa take bajewa tana
ta shan soyayyarta da angonta na k'arni, Pic d'inta da na jariran kullum safiya sai ta tura masa
sannan idan tana shayar dasu video call suke yi yana ta kallo yana jin dad'i, ya matsu sosai ya
dawo gida yaga matarshi da 'yan yaranshi, a gefe d'aya kuma yana so yazo yaga Iya kulu da ta
koma k'auye tana jinyar Kanta tareda kula da Indo da duk dawainiyarta ta koma kanta, ya damu
sosai da jin halin da yaji d'an uwanshi ya ke a ciki, waton zama gidan kaso na tsawon rai da rai.
Indo kam watan cikinta yana shiga tara ta fara nak'udar tsaye, har zuwa lokacin da nak'udar
gasken ta zo aiko cikin k'ank'anin lokaci ta haifi 'yar d'iyarta salun alun, tun kafin ma ace za'a
kaita asibiti, aikuwa Iya kuu tayi Murna ganin yarinyar sosai, saboda kama sak da take yi da
Abu lokacin da ta haife shi, sai dai abun bak'in da ta tuno da bafa ta hanyar sunnah aka same
shi ba, bayan angyara yarinyar da Mahaifiyarta Iya tana rungume da Jaririyar ta fashe da kuka,
saboda ta tuno lokacin da MALAM ya tsinto Izzatu tana jaririya,ta tuno da Kalaman da tayi ta
jifar IZZATU da su lokacin da Kande ta zugata, tareda maganganun da Dada tayi mata a cikin
b'acin rai sunata yi mata amsa amo cikin kunnuwa, ba shiri ta rungume 'yar jinjirar tana ta wani
masifaffen Kuka, indo dake rakub'e tana kallonta itama sai kukan take yi gwanin ban tausayi,
Sai ga sallamar Kande asama ba tareda ta jira an amsa mata ba ta hankad'e labulen ta shigo
idonta akan indo tace, "Tunda kin haife mata cikin to taso muje gida kin gama naki aiki, sai
susan yanda zasuyi da abunda aka haifa ke kuma ALLAH ya isar maki akan cutar da aka yi
maki."
Ta jawo indo kiii zasu fita Iya ta ajiye jaririyar da take ta wutsil wutsil cikin towel tana tsutsar
hannu alamun tana neman nononta, Iya ta yunk'ura da lafiyayyar k'afarta taje ta rik'o hannun
indo,tana kuka wanda har ya ta kasa yin magana, Kande ta saka hannun cikin zafin nama ta
fusgo Indo sai ga Iya kishim k'asa ta fad'i, Kande bata tsaya kula da abunda tayi ba ta fice gidan
tana ta bala'i rik'e da hannun indo.
Iya ta yi k'ok'arin tashi zaune saboda kukan da jaririyar ta canyara, jiki ba kuzari taje ta d'auketa
tana girgizata tareda k'arin sautin kukanta, a zuciyarta sai Istigfari take yi tareda nadamar
abunda ta aikata a baya, tana cikin Kukan sai ne sai ga Indo ta shigo d'akin da gudu tana kuka,
saboda a tsammaninta Iyar tana nan kwance har lokacin, tana ganin Iyar rungume da yarinyar
taji tausayin iyar ya kamata matuk'a, taje tasaka hannu ta karb'i yarinyar a hannun Iyar ta zauna
tareda d'ora yarinyar a cinyarta, Iya tana kallo ta fiddo nono ta fara shayar da yarinya, iya ta
sauke ajiyar Zuciya sannan ta zauna tana kallon indo da yarinyar tausayinsu ya kamata, ta dafe
baki ta shige k'uryar d'akin tana wani irin gunjin kuka zuciyarta cike da nadama tareda danasani
akan rayuwarta ta baya, tana ina ma za'a iya maido hannun agogo baya da ta gyara miyagun
halayenta da a kullum Dada take kuka akansu,acikin kukan tace, "Dada uwa tagari ALLAH ya
jik'anki da rahama, yau na gano abunda kika dad'e kina nusar dani, ashe ita k'addara zuwa take
yi babu wanda yafi k'arfinta sai wanda ALLAH ya tserar, yau gashi 'yar da nike shegantawa tayi
mani rana Iyayenta sun zamo silar arzikinmu, amman duk da haka ALLAH ya mayar man da
mugun nufina akaina, nida mai zugani muna sheganta 'yar mutane wadda ta zamo tsatson
sunna mai kyakkyawan asali,sai gashi hak'k'inta yau yana ta bibiyarmu har gashi mune a yau
rungume da abun kunyar, Ya ALLAH ka yafe muna nida Kande "
Ta k'ara fashewa da wani kukan sai ga Indo ta shigo goye da 'yar jinjirarta da tayi bacci, ta
zauna tareda share hawayenta tace da Iyar, "Na rungumi k'addarata ALLAH ya yafe muna
kurakuranmu duka, kema kiyi hak'uri ki rungumi kaddararki haka ALLAH ya tsara mutum bai isa
yayi jayayya ba, da ke da Innarmu kuyi tuba ga Ubangiji akan abunda kuka yi abaya, ALLAH
maji rok'on bayi ne zai yafe maku laifukanku. "
Kande da ke lab'e tana saurararsu ta shigo hawayen nadama suna zuba akan fuskarta, saboda
shigarta bayi Indo ta sulale ta dawo gidan, koda ta fito bata ganta ba tayo tsinke gidan, tun a
bakin k'ofar d'akin ta jiyo kukan Iya Kulu da sambatunta, jikinta yayi sanyi tana k'ok'arin shigowa
ne taga Indo ta shiga d'akin goye da 'yar jaririyarta, imani ya k'ara kamata musamman da taji
kalaman Indon, ta sami wuri ta zauna tana kuka ta fara magana, "Lalle yau na yarda da
hak'k'in IZZATU ne yake bibiyarmu, munyiwa yarinya k'age mun shegantata yau ga shege an
haufar muna muna kallo ba yanda zamuyi, asanadin haka ma yau Mari ta shiga duniya duk
akan sanadin alhakin yarinyar Mutane da muka d'auka, yau ga Abu cen gidan yari d'aurin rai da
rai tareda horo mai tsanani, ALLAH ka yafe muna saboda wannan izna ne ga duk mai halaye
irin namu, yaji tsoron ALLAH ya daina ya tuba ga ubangijinsa sannan ya nemi yafiyar wad'anda
ya zalunta, tun kafin zuwan ranar nadamarshi."
Gaba d'aya suka runtume suna ta kuka gwanin ban tausayi aka rasa mai lallashin wani, har sai
da suka in sallamar wata matar Mai unguwa sannan suka tsayar da kukansu.
Bayan an bata Umurni ta shigo take sanar dasu sak'on mai unguwa da yace tazo taga abunda
aka haifa kafin yazo.
Kafin kace me gari ya d'auka Indo ta haife cikin shegenta, aikuwa sai 'yan gutsuri tsomar gulma
kawai ke tashi gungu gungu na tsofaffi da matasan gari, har ma da matan cikin gida masu zuwa
ganin k'wak'waf, har sai da mai unguwa ya yi kashedi akan kada wanda ya sake zuwa gidan,
sannan ne aka sami sauk'in masu zuwa barkar Munaficci, Malam kam baizo ba kuma ya hana
kowa yazo sai dai ya aiko da komi da ake buk'ata na jaririya da mai jego, tsakanin kayan barka
dana abincin da zasu ci da abubuwan da zasu buk'ata sai da ya aiko , don kuwa har ragon kauri
sai da ya aiko aka soyawa mai jego, ranar suna yarinya taci sunan Iya Kulu wato Hauwa'u ina
kiranta da suna jidda, 'yan gulma sunyi iya yinsu har sun gaji sun bari don kansu.
Izzatu tayi arba'in taso tazo k'auyen amman Malam ya hana, iyakacinta gidajen 'yan uwa da
abokan arzik'i da ke cikin birnin, duk da aranta taso taga Iyar da abunda aka haifawa Abu
amman Malam ya hana, sai dai a sace taje ita da Amina gidan yari sun gano Abu, yayi bak'i ya
rame jikinshi gaba d'aya shatin buloli ne sun yi masa tambo tambo, kallo d'aya idan kayi masa
bazaka so k'ara kallonshi ba, har k'asa ya duk'a yana rok'on IZZATU gafara akan abunda ya yi
mata a baya, tana kuka tace dashi ba komi ita tuni ta yafe masa, ya nemi da ta bashi yaran ya
gani Amina ta harareta alamar kar ta bada amman tayi mata kamar bata gani ba, ta mik'a masa
yaran duka duk da warin da ke tashi a jikinshi, yana kuka ya dinga kallonsu yana yaba tsantsar
kyawon da ALLAH yayi masu, sannan ga kuma kamar d'an uwanshi sak shi suka biyo kamar an
tsaga kara, Amina ta saka hannu ta karbesu saboda kukan da taga yaci k'arfinshi, sai nanacin
yake yi Izzatu