Showing 21001 words to 24000 words out of 119425 words
Chapter 8 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
shine Abu ya fito
fitsari yaga zata sokawa kanta wuk'a yazo hanawa suka yankeshi a gefen cikinsa, gashinan jini
yana ta zuba amm...."
Kafin Garzali yakai k'arshen maganarshi ne, wani ya cira kulki ya makawa iya kulu and baya,
aiko kamar had'in baki, wasu daga cikin zugar 'yan k'auyen suka yita laftar iya kulu da
sandunansu, iya kulu da taji zafin duka a d'imauce ta fara kiran:
"Yanzu nice ba su bane, Wallahi nice ba su bane, su sun wuce ni kad'ai ce suka bari, sune suka
aikata suka tsere, wayyo ni kuyiman rai, na tuba bazan sake ba, in har na sake ku cemani ba
'yar kuluwa ba"
Da k'yar malam ya dakatar dasu, don wasu har sun fara kiran akashe shegiya kawai a huta,
aljanun k'arya ne, bak'in kishi ne, malam yana jin lafuzzansu ya fara yimasu bayanin cewa da
gaske tana da aljanu sune suka sakata wannan aika aikar, don in sun tashi a kullum lafazinsu
kenan sai sun kasheta.
Kande dake tsaye tana kallo, ba shiri ta dafe bakin tana dariyar k'eta.
Jikin 'yan garin yayi sanyi, domin sun yarda da maganar malam d'ari bisa d'ari, sanin da suka
yimasa mutum ne mai gaskiya, sannan gashi mijinta ne, dole ne yafisu sanin wacece ita, aiko
suka fara bada hak'uri, acikinsu akwai mai bada maganin miki, aka rakashi yaje gida ya d'auko
kayan aikinshi irin na gargajiya, ya fara duba Abu.
A cikin k'warewa ya tsaida jinin dake zuba, sannan ya saka magani a wurin yankan, sai aka jik'a
masa wani yasha, sannan ya fara rage jin zafin rad'ad'in yankan ya daina kuka.
Sannan sukayi sallama da malam suka fara ficewa, Malam yayi hamdala tareda godiya a wurin
mai maganin, shima sukayi sai da safe ya fice, Garzali yaje ya rufo gidan ya dawo.
Malam da Garzali suka rik'a Abu a hankali suka kaishi d'akinsu, Malam ya tofesu da addu'o'i
sannan yace da Garzali ya rufe d'akin, a gabansh ya rufe sannan ya juyo zai shige d'akinshi
batareda ya kalli ko gefen da iya kulu take ba, ya shige abunshi, hassatu dake tsaye cike da
mamakin wannan abu da ya faru, ta sauke ajiyar zuciya, ta saka ma bud'i ta bud'e d'akinta, ta
shige ta k'ara saka makullin ta dantse.
Iya kulu kam tana nan a tsaye ko motsawa ta kasa yi, saboda jikinta gaba d'aya ciyo yake yi
mata, saboda mazgar da tasha bilhak'k'i da gaskiya, ga goshinta ya k'ara suntumewa, ga
hannunta da take tsammanin ma ya goce,saboda wani dukan da aka kawo mata, ta saka
hannun ta tare, ba shiri taji hannun yace k'ut!.
Tun a nan taji ta jimu, ba shiri wani marayan kuka yazo mata, sai Allah ya isa takeyi a cikin
zuciyarta, da taga tsayin ba zai fisheta ba, dole taja jikinta tana d'ingishi ta shige d'akinta, sai
k'ara tsinewa hassatu da izzatu takeyi a cikin ranta, ta k'ara cin alwashin sai taga bayasu
dukansu, tunda suka sakata ta aikatawa d'anta mafi soyuwa a zuciyarta, sannan ga dukan da
tasha ba zato ba tsammani.
A zuciyarta tace:
"Ai duk munafukin cen ne ya jaza man, da yaje ya kwaso zugar mutane don suzo su kassarani,
su kaini barzahu ba tareda na shirya ba".
A haka dai dukansu suka kwana zuciyoyi ba dad'i, koda safiya ta waye, iya kulu jiki yayi tsami,
ko sallah ma dak'yar ta samu tayi, tana nan a kwance tana jinyar jiki, hassatu tayi sallama tana
rik'e da hannun izzatu sunci kwalliya irinta 'yan birni gwanin sha'awa, iya kulu tana k'yalla ido ta
hango su, wani mak'ok'on bakin ciki ya tokareta a mak'oshi, dak'yar ta had'iye miyau ta b'ata
fuska, hassatu ta k'araso ta zauna akan gadon da iya kulu take kwance, ta jawo izzatu ta aza
akan cinyarta, ta feshe iya kulu da wani munafukin murmushi tace:
"Sannu uwargida ya jikin Allah ya k'ara tsare gaba"
Tana k'are zancenta, bata jira taji me iya kulun zata ce ba, ta mik'e tsam ta jawo izzatu suka
fita, Iya kulu ta bisu da wata gawutacciyar harara, tayi tsaki ta juya kwanci, a cikin muryar mara
lafiya tace:
"Shegu biyu sai nayi maganinku, muga k'arshen dwandi"
Kuzo muje dubo iya kulu♀️♀️a aza mata ruwan zafi ta gasa jikinta
Akafta
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*INA GODIYA MY FAN'S *
*PAGE TWENTY ONE*
**********************
Shikam Garzali yana cen yana ta faman lallab'a Abu dake borin wai iya kulu tak'i zuwa ta
dubashi, bayan itace tayi silar shigar sa a cikin matsalar,ana cikin haka ne Malam ya shigo
tareda hassatu, suka dubashi, hassatu ta tausaya masa sosai ganin yanda yake ta fama.
Ba shiri ta fita sai gata ta dawo hannunta rik'e da flack's tareda izzatu da ta d'auko biredi,
hassatu tace da Garzali ya had'a masu shayin su sha su k'oshi, aiko ba b'ata lokaci Garzali ya
samo kofuka ya tsiyaya masu shayin, saboda an riga an had'a shi kafin a kawo masu, aiko suka
saki jiki suka sha abunsu suka k'oshi, sannan Abu ya daina borin rashin zuwan iya, ashe daman
yunwa ce take cinsa, malam ya samu wuri ya zauna, yana k'ara tambayarshi ya jiki?, hassaru
ma tayi masa ya jiki ta jawo izzatu suka fito, to a lokacin ne taje d'akin iya kulun.
Bayan fitar hassatu malam ya gyara zama ya kalli Garzali yace:
"garin yaya mahaukaciyar uwarku, tayi wannan karen aikin?don nasan ba wani aljannu da take
dasu"
Garzali kam jiki a sanyaye, ya fara baiwa malam labarin duk abunda ya sani, har ya kai
k'arshen zanceshi, malam bai katse sa ba, saboda wani firgicin da ya shiga, tareda tunanin ta
ina zai shawo kan wannan rashin hankali na 'yar kuluwa?.
Gashi aurensu, aure ne kamar na zobe ba'a rabuwa, saboda yana son ya cika wasiyyar da
Dada ta bar masa, akan duk tsanani kada ya rabu da ita, to shin ta wace hanya ce zai horata
har ta gano Annabi ya faku?,
Shi ba abun ya turata gidansu ba, ace saboda ganin yayi amarya ne, yasa zai fara cin amanarta
ya yi mata wulak'anci, amman duk da haka zai tauna takuwa ko don aya taji tsoro, don bazai
zura ido ba har watarana taje ta jawo masu abunda dukansu zasu shiga uku ba.
Yana k'are wannan tunani, ya tashi tsam ya nufi d'akin iya kulu, fuskarsa shimfid'e da b'acin rai,
yayi sallama har sau biyu yaji shiru, iya kulu tana ta sharar baccinta, a ta uku ne ya fad'a ya
d'aga murya da k'arfi, aiko ba shiri ta zabura tana fad'in :
"Sai na kashe ku, duk ku biyu d'in, ba wanda zan bari a cikinku"
Malam yana jin lafazinta ya gano inda zancenta ya dosa, aiko a cikin zafin nama yayi tattaki ya
zabga mata wani jarumin mari har sai da taga wasu tauraru, aiko ba shiri iya kulu baccin dake
idanunta ya wartsake, ta dafe kumci, tana kallonshi da mamaki akan fuskarta tace:
"Yanzu malam baka ji kunyar d'aga yatsunka biyar da Allah ya halitta maka ba ka saukesu akan
fuskar amanar da Dada ta bar maka ba?"
A cikin fushi yace :
"Ank'i a ji kunyar, ke kinsan kunyar kika aikata abunda kikayi a jiya, iya rashin kunya ta sauka a
kanki, tunda har kikaso ki kashe d'an da kika haifa da cikinki saboda kishi, kishi hauka ne?, da
hankalinki zai b'ace har ki tabka rashin imanin da zakizo kina da kinsani?, haka kawai ki saka
mutane shiga a bakin duniya?, to wallahi kinyi na farko kinyi na k'arshe kika k'ara bari
makamancin haka ya k'ara faruwa, wallahi sai na shayar dake gubar mamaki, don bazanji
kunyar tsinke duka igiyoyina dake kanki ba"
Ba shiri iya kulu ta fashe da kuka tace:
"Ba shi nayi niyya ba, tsautsayi ne kawai ya hau kanshi, amman wallahi nayi danasani da
wuk'ar ta yanki Abu, don ba shi nayi niyyar yankawa ba, azal ce ta fad'a kanshi "
Malam ya bita da kallon takaici yace:
"Me yasa ke k'wak'walwarki take ta kifi ne?, ke a ganinki Allah zai barki ki, kiyita cutar yarinyar
mutane?, kin mance maganar da na fad'a maki ko a ranar kenan?, to Alhmdllh da reshe ya juye
da mujiya, ko don ya zama iznah a gareki akan idan kin tashi gina ramenki na mugunta, to sai
KI ginashi a gajere, don idan kikayi wasa kece zaki rufta a ciki, don yanzu ma ga zahiri kin gani,
kin yanka d'anki kinsha duka, ga hannunki nan a kumbure, duk akan haukar ki k'waya d'aya tak,
in kunne yaji jiki ya tsira, amman kisani daga yau bazan sake d'aga maki k'afa ba, da kinyi abu
kad'an zanyita jibgarki, tunda naga har jikinki yana shanye dukan k'attin maza, to balle nawa
k'waya d'aya tak!, saboda haka ki kiyayi lokacin da zan sauke k'wanji na a kanki"
Yana k'are maganar ya fita, ba tareda ya jira yaji abunda zata fad'a ba, aikam iya kulu ta fara
kururuwar kiran sunan Dada tana sambatun fadin:
"Nikam dai 'yar kuluwa, mutuwa tayiman yankan k'auna, da ta d'auke mani Dada ta barni a
duniyar ina ta ganin tasku iri iri, wayyo ni Allah na duniya meyasa kika yimani d'aurin huhun
goro?"
Haka tayita sambatun ta har saida malam ya dawo tareda mai gyara, ya gyara mata gocewar
tana ta ihu tana b'arin hauka, bayan ank'are yimata gyaran ne, ta lallab'a ta dubo Abu da
jikinshi, sannan ta koma d'aki ta dunk'ule akan gado tana ta kukan zuci.
**
Bayan sati d'aya iya ta murmure garas, Abu ma yaji sauk'i sosai, malam kam da shi da 'yarshi
izzatu har k'iba naga sun k'ara, kwanciyar hankali ya samu a gidan, don iya kulu ta rage wannan
duk wasu miyagun halaye nata, ta zama wata saliha ko magana bata sonyi, amma fa kar ku
zaci ta shiryu a'a, tunda kande tazo dubata ne, da suka k'ule d'aki sukayi ta k'us k'us, tun daga
ranar ta zama haka, bata kula duk wata rawar kai da hassatu da Malam sukeyi a gidan, illah ta
bisu da wata gwarzuwar harara tayi kyafci, izzatu kam da ta kuskura ta matsa a kusa da ita ba
wani d'aga k'afa, take saka hannu ta make ta tayi saurin barin wajen sai dai aji kukan izzatu, a
tambayeta me akayi tace IYA ce.
**
Sati biyu da zuwan hassatu, ta fara cukucukun maida Garzali da Abu makarantar boko, wadda
shi garzali har ya k'are primaryn dake nan a cikin k'auyen nasu, don daman cen d'iyan k'auyen
iyakacinsu primary sun k'are karatun, ko ita d'in tsiraru ne suke jurar har su gama, wasu daga aji
biyu ko uku sai a watsar, Alhmdllh shi Garzali ya k'are, Abu ne kawai bai k'are ba, aiko tasaka
malam ya maida Abu and makarantar domin ya k'arasa, sannan aka saka izzatu itama.
Duk da ita kanta hassatun iyakarta prmary d'in, amma yanda taje birni taga ana fad'i tashi d'a
karatu, sai abun ya dinga burgeta, tayita sha'awar Allah ya bata haihuwa, ko don yaran su samu
ilimin da ita bata samu ba, sai gashi har mijinta ya rasu bata sami haihuwa dashi ba.
To shine yanzu tayi sha'awar su Garzali su sami ilimin suma koda zasu tallafi 'yan k'auyen nasu,
watarana ayi alfakhari da samun irinsu a k'auyen, musamman da taga Garzali yana son karatun
sosai, sab'anin Abu da komi bai sani ba a bokon, tunda ba kullum yake zuwa ba, sai yayi wata
baije ba, kuma malam ba zama gidan yakeyi ba, yana cen yawon cin kasuwanshi, k'auyukan
dake mak'otaka dasu, ita kuma iya kulu bata matsa masa akan sai yaje, Dada ma ba sanin ta
kan bokon tayi ba, balle ta saka baki akan sai yaje.
Garzali dake zuwan ma,ra'ayinsa ne ba mai cewa tafi makaranta.
Aiko hassatu ta baiwa malam shawarar a saka Garzali makarantar gaba da primary a cen birni,
ba musu malam ya amince, sai dai ya nuna mata aljihunshi fa ba nauyin da zai iya d'aukar
karatun Garzali zuwa birni, tace bakomi ita ya barta zata in da matsalar karatun, kawai dai yaji
da abunda zai ciyar da su.
Kasancewar hassatu ta sami gadon kud'i da kadarori a wurin mijinta na farko, bata sha wuya ba
wajen saka Garzali a wata makarantar kud'i dake birni ba, inda ta kasance ta kwana ce,ta
hanyar wata mak'ociyar su a cen birnin da ta kasance malama a makarantar.
Ansha gawurtaccen daru a wurin iya kulu akan cewa, ba wanda zai kai mata d'a a birni a saida
shi, haka kawai a yanka kanshi batada labari, har saida malam ya nuna k'arfin ikonsa akan
Garzali, sannan ta amince yaje, amma da kuka wiwi suka rabu.
Sai yazo zai fita, taje da gudu ta rik'eshi tana kuka, wai ya jira tayi masa ganin bankwana, sai da
malam yaga abun nata yayi yawa, sannan yaja Garzali suka fita, wanda shima kukan yakeyi
kashirb'an, ganin yanda za'a rabashi da izzatunsa ya daina ganinta, itama kukan takeyi,
saboda taga yana kuka shiyasa itama sai ta fara kukan, saboda shak'uwar dake a tsakaninsu.
Bayan fitar malam da Garzali ne, iya kulu ta fara yiwa hassatu tujara tana cewa:
"Duk bak'in cikin tanda sai munci waina, wato gurinki ki salwantar man da yaro, tunda kinga ke
ba haihuwar zakiyi ba, to ko ni yanzu kasuwa ta watse ai d'ankoli yaci riba, don na haihu uku, ke
ko fa nawa kikayi?, sai dai kije masai ki dinga tula k'aton kashi, amma haihuwa sai dai kiga
mata sunayi, a hayye nanaye sama tayiwa yaro nisa sai dai ya d'aga kai yayi kallo, kuma
wallahi ki sani duk abunda ya sami yarona banyafe maki ba, kuma wallahi in zan tafi zindir,
saboda rashin zanen d'aurawa sai nayi shari'a dake"
Anya iya kulu
Akafta amma fa kusani har yanzu muna akan shinfid'ar labarin akwai sauran rina a kaba
muje zuwa my gay's ♀️♀️♀️
D/Auta ce
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
*MY FAN'S GA TAKU I LOVE YOU ALL IRIN TRILLION
DINNAN❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️*
*TWENTY TWO*
**********************
Hassatu kam ko kallo iya kulu, bata ishet ba ma balle at kulata, a cikin ranta tace:
"Sakarya bazaki gane taimakon ki akayi ba sai a gaba"
A haka aka ci gaba da zaman k'ek'e da k'ek'e a tsakanin malam da iya kulu, k'iris tayi sai ya
nuna mata kuskurenta, tayita masifa akan cewa baya sonta ya tsaneta, idan har ya gaji da ita
ya sauwak'e mata, amma malam kam ya biyeta suyi tayi, har ya nuna mata darajar cewa, ai
darajar wasiyyar Dada taci da yanzu tuni yayi maganinta, tanajin haka zatayi muk'us ba shiri.
Amma fa kam kande shawarar da ta bata, akan ta bi bokaye ta k'wato mijinta, sannan ta kora
hassatu da izzatu su bar gidan, aiko shawarar tayi tasiri a kanta, domin kuwa a sace sukaje
wajen wani boka itada kanden, suka karb'o kayan surkullensu suka yo gida.
Iya kulu ta bada himma akan aiwatar da abunda akace mata, amma duk ta k'ulla mugun
abunta, sai malam ko mama hassatu sun wargaza mata tsari, duk da basuda masaniya da
abunda take k'ulla masu, wani zubin itama ce da kanta take lalace abun, saboda mantuwar da
takeyi, akan ta yaya zatayi amfani da surkullen, har sai ta aikata shirmenta, sannan ta tuno ba
haka aka ce ba, tayi ra jin haushin me yasa tayi kaza.
Hassatu kam dariya shirmen iya kulu yake sakata, ta maidata mahaukaciya, tayi amfani da
damar da ta samu ta mallake malam tass ba boka ba malam, izzatu ma malam ya sakata a
makarantar primary dake k'auyen, da kanshi yake kaita har aji, idan zaije cin kasuwarsa sai
yaga ta zauna a cikin ajin sannan ya tafi wurin sabgoginsa.
Garzali kam ana cen an duk'afa karatu ba kama hannun yaro,duk ranar visiting malam sai yaje
masa, tareda duk abunda duk abunda Allah ya hore, wani zubin Ma har da izzatu da Mama
hassatu sai sunje, Abu kam da iya kulu cewa sukeyi basu zuwa kar aje a yanke masu kai a
banza.
Shekaru sunja da dad'i ba ba dad'i, har Garzali ya jajirce ya k'are secondary, yayin da a lokacin
ne itama izzatu ta k'are primary zata je secondary a birni, amma malam yace sam baisan da
zancen ba, wanda har hatsaniya taso ta shiga a tsakaninshi da mama hassatu, don shi kam
tsoron shi d'aya ne, iyayen izzatu su ganta su k'wace 'yarsu, bayan su shak'u da ita.
Rikici yayi tsamari har hassatu tayi fushi ta koma gidansu da zama, malam ya d'au zafi yace
idan dai akan izzatu sai taje birni karatu ne, take fushi,har ta koma gida, to tasha zamanta.
Iya kulu sai murna takeyi tana jin dadi tana tunanin, bokanta ne yayi aiki a kansu.
Aiko rashin hassatu a gidan ya saka shiga izzatu a cikin matsalolin iya kulu, wanda jira kawai
takeyi malam ya bar gidan, aiki kala kala take sakata, daga wannan sai wannan, kasanceawar
a lokacin girma ya fara bayyana a jikinta, mak'erin 'yanmata ya fara bayyana irin tsantsar halittar
da ubangiji yayi mata.
Izzatu fara ce tass mai surki jaja