Showing 108001 words to 111000 words out of 119425 words

Chapter 37 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf

Advertisement

tashi
zumbur zata sauka gadon da sauri ya rik'o hannunta tareda tambayar "lafiya"

A cikin rawar jiki tace na mance ban shafo turaren ba, ya janyota jikinshi yana 'yar dariya yace
"Kwanta abunki ai sai gobe sharud'd'an za su fara aiki."

Cikin sanyin jiki ta kwanta ido cikin ido tace dashi "da ka bari na shafo."

Yana murmushi yace

"Na yafe na yau kiyi baccinki hankali kwance ba abunda zai same ki kinji?"

Sai a lokacin ta sami natsuwa kafin kace me tayi baccinta, shima cike da annushuwa ya fara
baccinshi mai d'auke da mafalkai kala kala tareda amaryarshi.


***
Ai kuwa tsakanin kwanakin ya darji amarcinshi hankali kwance zuciya zaune, duk da bai cika
zama gidan ba ai dare.
Bayan kwana biyu da maganarsu da Izzatu yajewa Abbaah da maganar shima yayi farin ciki
sosai har ma ya k'ara da tashi gudunmuwa a matsayinshi na Gwamnan jahar, ya yi masa
bushara da cewa makarantar boko da bohol bohol shi zai d'auki nauyin aikinsu, Masallaci da

islamiya ce kawai za'ayi cikin kadararsu, sai Company buga robobi da yake so a kafa cikin
garin, wanda yake so matasa da masu sauran k'arfi na garin da kewaye su zo afafata da su,
saboda a rage yawan zaman banza ga marasa k'arfin da ke yankin, aikuwa Garzali yaji dad'i
sosai yayi ta godiya.
Bayan kwana biyu suka fara shirye shiryen tafiya, wanda izuwa lokacin mutane sunyi ta zuwa
ganin Amarya, daga k'auyen cikin garin tsakanin 'yan uwan Abbaah masu goyon bayanshi
tareda abokan arzik'i ta kowane b'angare, saboda tafiyar da zasu yi ne mutane suka YI ta
tud'ud'uwar zuwa ganin gidansu tareda yi masu bankwana.
Daren da zasu tafi tun da safe Garzali ya d'auki izzatu ya kaita gidansu Malam domin tayi masu
sallama, Mama da Malam sun saka su a gaba suna ta yimasu jan kunne sosai akan suyi
hak'urin zama da junansu, iya kulu kam tsakaninta da izzatu ALLAH ya baku zaman lafiya kawai
take fad'i, saboda wani girma da take ganin Izzatu tayi mata a ido, har wani jin kunyarta ta fara ji
lokacin da izzatun ta shiga sashenta, ko idanuwa bata so su had'a saboda jin kunyar abunda
tayi mata a baya, Izzatu kam banda dariya ba abunda take yi a cikin ranta, saboda ganin wai
itace yau Iya kulu ke jin kunya?duniya juyi juyi.

Har k'arfe biyu Izzatu tana gidan, sannan Mama tace yaje ya kaita wurinsu Ammaah, aiko har
bakin motarshi suka yo mata rakiya kaf gidan har Iya kulun, Abu kanshi duk bak'in halinshi sai
da ya fito ana yi masu bankwana dashi kasancewar jirgin asuba zasu bi.

Amina ta janyota gefe tace, "Wai ko kinga yanda kika koma cikin kwanaki shida da aurenku?
cab lalle yayanmu baya wasa, nasan nan gaba idan mun sake ganinki ma kasa gane ki
zamuyi."

Izzatu ta kai mata duka tace "Rawar jikin me kike YI ai kema kin kusa zama kamar ni har ki
fini, amman in kin matsu sai a yi kome cikin sati d'aya a kai masa kowa ya huta."

A tare suka k'yalk'yale da dariya Mama ta k'walla mata kira sannan tazo ta d'auki ilham ta sakar
mata kiss a kumatu, sannan ta ajiyeta ta shiga motar ilham ta fasa kuka sai ta bita dole ta
janyota ta aza kan cinyarta sannan tace

"Mama zanje da ita don ALLAH "

Mama tace "Aje lafiya"

Ta rufo motar suka fara tafiya tana d'aga masu hannu suna d'ago mata sai ga wasu hawaye
shaaaa akan fuskarta, Ilham ta kalleta tace

"Aunty kuka kike yi?"

Izzatu ta k'ara rungumeta jikinta sai sharar hawayenta take yi, bayan sun d'auki hanyar gidansu

Ammaah ne ya yi saurin kai kallonshi gareta, saboda sheshekar kukanta da ya jiyo ga
kunnenshi duk da k'ira'ar sudes da ke tashi a cikin motar, yayi ta bata hak'uri har suka kai gidan
da gudu ta b'alle murfin ta fito d'auke da ilham tana gudu zuwa sashen Ammaah sai k'wallawa
su Ammar kira take yi, sai gasu sun fito dukansu har su SUDEIS da SADIS suka rungumeta,
kowa sai murnan ganinta yake yi Ammaah da Ammi ma ba'a barsu a baya ba, nan suka dawo a
main falon gidan suka yada zango suna ta murna da d'okin ganin juna, Ammi taji dad'in ganin
yanda Izzatu ta sauya cikin 'yan kwanaki, ta wayance da fad'in ina Yayan naki ko yana wurin
Abba....... , kafin ta rufe bakinta sai ga Abbaah Garzali biye dashi a baya sai sunne kai yake yi.

Nan ya zube yana ta kwasar gaisuwa wurin surukanshi, daga nan yayi masu sallama ya tafi da
nufin zuwa dare zai dawo ya d'auketa, aiko ta baje cikin 'yan uwanta sai fira suke yi, sai daga
baya Ammaah ta jata d'akin Ammi tace taje cen ta huta tabar biyewa su SADIS kar su saka ta
ciyon kai, wanda ita tayi hakan ne don Ammi ta sami damar ganawa da 'yarta, don ta fahimci
kawaici ne kawai take yi amman soyayyar 'yarta bayyane take akan fuskarta , aiko suna kulewa
tayi ta bata shawarwarin da zasu amfaneta, tareda koyar da ita yanda zata yi juriya da halin
mijinta a fakaice, don ta fahimci Garzalin ba k'aramin jarumi bane shiyasa da wayo tayi ta bata
dubarun zama da miji.

Sai daga baya Ammaah tazo aka ci gaba da ita, inda har ta k'ara kawo mata wata kaza da tasa
takanas aka dafo mata wadda taji kayan had'i sosai, cikin wayo suka yi ta hilatarta har ta
cinyeta tas bata sani ba, sannan ta koma gunguni saboda tuno abunda yayanta ya fad'i, taso ta
tambayi Ammaah domin taji k'arin bayani akan lamarin sai kuma ta tuna yace kar ta fad'awa
kowa dole tayi gum ba don taso ba, Abbaah ya kirata takanas yayi ta yi mata nasihohi akan
juriya da hak'uri, tana tareda da k'annenta har dare zuwa lokacin da ya zo d'aukarta anan ta
bar ilham wurin Ammi suka tafi gida.

Daren dai Garzali ya d'aga mata k'afa bai nemi shiga lanbum ba saboda tunanin tashin asubar
da zasu yi, aiko tayi baccinta mai dad'i hankali kwance har hud'u na asuba inda suka tashi suna
ta kimtsawa har aka yi asuba, ana sallame SALLAH scuritys suka zo tafiya da su airport.

Koda suka je sun tarar da su Ammaah da Abbaah tareda Mama da MALAM da iya kulu Ammi
dai cewa tayi bazata je ba, aiko Izzatu sai da tasa dukansu kuka, saboda yanda ta rikice gaba
d'aya saboda ganin za'a rabata da kasarta iyayenta 'yan uwanta tareda abokan arzik'i, akaita
inda bata san kowa ba kuma ba wanda ya Santa.
Dak'yar aka b'anb'areta jikin Mama hassatu da Ammaah tana wani irin kuka gwanin ban
tausayi,
Su ammaaah suna tsaye har jirginsu ya d'aga, sannan suka juya gida kowa jiki sanyi k'alau
saboda rabuwa da da 'ya'yansu kuma surukansu.


Nidai na mak'ale a tayar jirgin don yasin bani bari ayi babu ni.💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻�

Akafta�




D/Auta ceí ¾í´í ¼í¿»
[8/22, 1:56 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*


*NA HADIZA D/AUTA*



https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*â­â­â­TAURARI WRITERS ASSOCIATIONâ­â­â­*

(We entertain and educate according to our religion and ethnics)

*PAGE SEVENTY TWO*

**********************

Jiki a sanyaye su Malam suka wuce gida yayin da su Ammaah da Abaaah suka wuce nasu
gidan suma, zuciyoyinsu cike da alhini rabuwa da su Izzatu.

Iya kulu kam shigarta gidan keda wuya ta fara jin sautin nishi a d'akin Abu, wanda da ta kashe
kunnuwanta ne ta jiyo ashe ma ba shi kad'ai bane har da muryar mace, abunda ta ji wa
kunnuwanta yasa gabanta ya k'ire ya fad'i ba shiri, saboda idan ba kunnuwanta bane tabbas ta
juyo Abu yana fad'in,
"Ashhh washhhh mari tsotsa man sosai wayyo dad'i, Mari ci.... ga... ba cen.. ye... ni..... gaba
d'a..... ya.... "

Iya kulu a cikin wani zafin nama ta banki k'ofar da k'afa, aka yi dace ma ashe ba ko rufe take da
key ba, aikuwa sai gashi idanuwanta sunyi mata mugun gani, domin kuwa Abu da Mari ne
tumb'ur haihuwar uwarsu suna aikata masha'a.

Iya kulu ba shiri ta gwalalo idanuwanta kamar su fad'o a cikin rud'ewa tace

"Abu Mari daman abunda kuke aikatawa kenan?" a cikin kuka ta k'are maganar tareda yi cikinsu
da duka, da taga abun baiyi mata ba ta jawo extension d'in dake mak'ale da socket tayi ta watsa
masu, Mari sai kuwwa take yi tana tsalle har ta sami sa'a ta ture Iya ta fad'i ta shige d'akinta a
d'ari ta dantse da key, Abu kam ko gezau bai yi ba, ya dai ja kayanshi ya shige toilet, Iya ko da
tunda Mari ta tureta ta fad'i bisa hannunta dab'as aiko hannu yace " k'as!!" alamun ya karye, ba
shiri tace

"Wayyo ALLAH ta karye ni shegiya karuwa wallahi sai kin bar gidannan nan yau,Kande ma da
ta haifo ki ALLAH ya tsine mata tunda ta haifo bala'i ta kawo man cikin gida."

Iya kulu kuka take kashirb'in dak'yar ta samu ta Mik'e hannunta d'aya tallabe da hannun da ya
kare, ta fito sai k'ara tsinewa Mari take yi Abu kam yana ganin ta fita ya had'a inashi inashi ya
bar gidan, Mari tana d'aki cike da tashin hankali jikinta sai rawa yake, saboda duk bala'in da
iyar take yi a kunnenta don ko bata ce sai ta bar gidan ba, ita tasan dole ne ta barshi tunda har
ta kamata hannu dumu dumu da Abu suna tanbad'ewaesu da suka saba.

Iya kulu ta dannawa Malam da ke sashen Mama kira tana kuka take sanar dashi ta karye a
nemo mata mai gyara, a cikin tashin hankali Malam da Mama suka shigo sashen suna
tambayarta garin yaya ta karye?.

Ita ko sai kuka kawai take yi takasa maida bayanin abunda ya faru, saboda bak'in cikin da yayi
mata yawa a zuciya, Malam ya d'aga waya ya kira wani Mai gyaran kariya na K'auyensu,
sannan suka ci gaba da lallashinta, Iya kulu sai kuka takeyi kamar wata k'aramar yarinya tana
k'ara tsinewa Mari. Mari kam itama ta had'a kayanta kaf ta dinga lodawa a jakunkuna, tana lab'e jikin k'ofa tana
sauraren Iya har mai gyaran yazo, tana jin an fara gyaran hannun iya kulu tana ta zabga
kuwwa, ta fito sad'af sad'af hannunta duka biyu jaye da jakunkunan da ta ciko fam da kayanta
had'e da na iyar da take ta sacewa idan ta sami garara, har ta fita gidan tana jin sautin kuwwar
Iyar ana gyara mata hannun, shiyasa hankalinsu Malam ya d'auku basu ma san fitarta ba, tazo
bakin gate ne Amina ta fito daga sashen Mama zuwa sashen iyar saboda jin kuwwar da take yi
wadda ta karad'e kaf gidan saboda tsananin azabar da take sha wajen gyaran.

Amina ta bita da kallo batareda tace da ita k'anzil ba, itama Mari ta bita da harara tareda
murgud'a baki saboda 'yar tsama ce a tsakaninsu basa shiri, Amina ta d'auke kanta tayi sashen
Iyar inda ta tarar har ank'are gyaran, idonta sunyi ja sosai sun kunbure yayin da hannun ya
haye yayi suntum a lokaci d'aya, amma har lokacin bata daina Kuka tana tsinewa Mari ba,
saboda ganin take YI itace taja raayin Abu ta koya masa wannan masha'a, shiyasa tak'i fad'awa
su Malam ainahin abunda ya faru, ta dai ce masu Mari ce ta tureta ta fad'i.


Mari kam tana fita ta tari adaidaita ta kaita inda ake shiga motar garinsu, minti goma sha biyar
sai gata a k'ofar gidansu, aiko k'annenta da yaran unguwar suka fara murna suna fad'in

"Ga mari ga mari"

Suka rik'a mata kayan har cikin gidansu, Kande kam sai rawar kai take ga 'yarta mai arzik'i ta
zo, aiko ta shiga rawar k'afar ganinta tareda sauran 'yan k'annenta sai haba haba ake yi da ita,
ita kam sai murmushin yak'e take yi duk da izuwa lokacin zuciyarta bata tsoron asirinta ya tonu
ace ga abunda tayi, tsoronta d'aya ne Iya kulun ta turo mata 'yansanda su tafi da ita, tun tana
cikin zullumi kwana d'aya biyu har zuwa uku har ta gyagije ta ci gaba da sha'aninta, saboda
tace da su kanden Iyar ce tace tazo taga gida ta koma.

Wasa wasa Mari sai gata da kwashe wata d'aya a k'auyen, izuwa lokacin duk zama garin ya
gundureta ga zazzab'in da ya sata a gaba kullum sai amai take kelayawa, shiyasa ma Kanden
ta matsa mata akan ta koma don ita tunaninta ko cimar da suke ci ce take sakata amai saboda
sabon da tayi da jin dadi a birni, Ita ko ta kafe akan bazata koma ba sai taji sauk'i, aiko Kande
taja wata budurwar 'yarta mai suna indo suka nufi gidansu Malam, saboda Indon ta maye gurbin
Mari kafin ta mirmije ta dawo bakin aikinta.

Iya kulu tana zaune a falo abun duniya ya sha mata kai sasai saboda Abu tun da ya fita har
zuwa ranar bai dawo ba ko a waya bai kirata yaji ya lafiyarta ba, saboda tana da tabbacin yaji
lokacin da take kururuwar Mari ta karye mata hannu, amman sai gashi har lokacin bai waiwayo
gida ba, don ita ko kad'an tafiyar mari bata dameta ba don koda bata tafin ba ita sai ta korata
dole ta bar gidan.

Iya kulu tana k'yalla ido ta hango Kande aiko ta fara balbalin bala'i, duk da hannun da take
tallabe dashi wanda har lokacin tana fama dashi, Kande ta marairece duk da batasan laifin da
Mari tayi ba sai bada hak'uri take yi, Iya ta rufe ido taciwa kande Mutunci tsaf amman Kande ko
a jikinta saboda gurinta d'aya ne iyar ta d'auki Indo aikin Madadin Mari, aiko dak'yar ta shawo
kanta ta amince amman da sharad'in daga ita har Marin kada ta sake ganin k'eyarsu a gidan, in
don kud'in aikinsu zata sa akawo masu har gida, Kande kam ko ajikinta tunda buk'atarta ta biya
don bata son arzik'in da suke samu ta k'ark'ashin iyar ya sub'uce masu, haka ta baro gidan Iya
ko k'wandala bata bata ba balle kud'in mota,har sai da ta biya sashen Mama sannan ne taci
abinci Mama tayi mata alkhairi duk da tasan Munafucci ne da kwad'ayi yasa ta zo wurinta.

Mari kam cikin wata biyu alamomi irin na masu ciki ya fara bayyana a wurinta, amman daga ita
har Kanden ba wanda ya gano hakan har sai da cikin ya kai wata biyar sannan ne suka fara
ganowa, saboda tsirfar masu ciki kala kala da take yi aiko abu ga k'auye labari ya bazu gari
akan Mari tayi cikin shege, kyara da tsangwama babu wadda bata sha ita da Kande da 'yan
kannenta, don ko shima kanshi baban nasu sai da fita ta gagareshi a k'auyen.

Da abu yayi yawa sai ga labari yakai har fadar mai unguwa, yasa kirata da mahaifanta aka saka
Mari a gaba tareda yi mata titsiyeta akan sai ta fad'i inda ta samo cikin shege, tana kuka ta fad'i
cewa Abu ne gaba d'aya wurin kowa jikinshi yayi sanyi, mai unguwa yace taje gida shi zai yi
magana da Malam sannan suka fito, yara da manya suka biyo su duuu mutanen gari sai wak'a
suke yimata ana amshi,

"Duk garinnan wa yayi cikin shege?"

Sai yara su amsa suce

"Mari d'iyar Kande"

Mari me ya kaiki cikin shege?"

Yara su ce

"Kwad'ayi"


Haka aka raka SU ana wak'a har gida, sai da Mai unguwa yasa aka kora mutane sannan suka
watse, amman fa garin ko'ina ya d'auka Mari tayi cikin shege.



Dad'i na da gobe saurin zuwa, ashe da gsk ne da aka ce rana dubu ta b'arawo, rana d'aya tak
ta mai kaya shin ya wannan rikici zai kaya🤔shin wai ina bak'in london ne🤣🤣🤣🤣.


Akafta


D/Auta ceí ¾í´í ¼í¿»
[8/22, 1:56 AM] Auntyna: *�RUWA DA KANKARA⛈ï¸*



*NA HADIZA D/AUTA*



https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*â­â­â­TAURARI WRITERS ASSOCIATIONâ­â­â­*

(We entertain and educate according to our religion and ethnics)

*PAGE SEVENTY THREE*

**********************

*Mutanen london*

Amarya izzatu da angonta Garzali kuwa suna cikin jirgi sai aikin lallashinta yake yi, saboda jirgi
yana tashi sautin kukanta ya k'aru dak'yar ya samu ta daina kukan ta koma ajiyar zuciya, ta lafe
jikinshi yana ta aikin lallaminta har ya samu tayi bacci, sannan ya sauke ajiyar zuciya tareda
k'ara rungumeta gaba d'aya a jikinshi, kanshi a saman fuskarta bai damu da kallon da ake
yimasa ba, shi dai gurinshi kawai ta sami natsuwa aiko sai da tasha bacci sosai sannan ta
falka,ta d'an ci abinci kad'an ta koma baccin yayinda shima baccin yaci idonshi suka had'a kai
wuri d'aya suna yin abunsu gwanin ban burgewa, har sai da wata mai service d'in abinci tazo
zata wuce ta gansu tayi murmushi tace

"Luv bird's"

Gaba k'i d'aya wurin aka saka dariya saboda mutane da yawa soyayyarsu ta burge su, saboda
yanda Izzatu ta narke masa tana ta rigima shi kuma Og Garzali sai lallashi yake yi kamar wata
yarinyar goye.

Saukar jirginsu keda wuya sai ga wani driver da wani d'an katako wanda aka yi zanen photon
izzatu da Garzali sai d'aga shi yake yi sama yana warar idon ta ina zai gansu, aiko idanuwan
Garzali ya kai a kan photonsu ya nufi mutumin, yayin da shima baturen ya hango su da sauri
ya k'araso wurinsu yana farin ciki, bayan sun gaisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login