Showing 54001 words to 57000 words out of 119425 words
Chapter 19 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
Allahu saura k'iris ya rage iyayenta su bayyana a gareta, a nan ne ma take yiwa
mama bayanin matar da ta had'u da ita a BADAWI SHOPPING, mama taji dad'in jin wannan
labari, domin hakan ya nuna tana gaf da sanin iyayen izzatu.
Takanas Garzali ya aiko ma izzatu da waya ta hanyar wani akokin karatun shi da aka turasu
service d'in a garin inyamurai, aiko izzatu taji dad'in wannan waya domin kuwa ta rage mata
rabin damuwar da take a ciki, saboda a kullum tana lik'e da wayar suna fira da yaya Garzan ta,
malam ma ya karb'i wayar yayi masa bayanin duk abunda ya faru, ba k'aramin dad'i Garzali yaji
ba, saboda hakan ya nuna cewa izzatun sa zata zamo mallakin shi, a kullum sai k'ara dulmiya
sukeyi a kogin k'aunar junan su wanda a gefen iya kulu ko kad'an bata son wannan bak'ar
lik'ewar da izzatu takewa Garzali, don tasa a ranta in dai itace ta haifi Garzali to tabbas za'ayi
yak'in badar na biyu,don kuwa ko bazata bari Garzali ya auri izzatu ba.
Lokacin k'are makarantar izzatu yayi malamai suka shirya masu k'wark'waryar bikin k'are
makaranta, an gayyato manyan mutane kasanceawar makaranrar ta d'iyan shafaffu da mai ce,
shiyasa da aka tashi ba'ayi k'asa a gwiwa ba wajen gayyato mai girma his Excellency Alhaji
YAHAYA BADAWI, tareda wasu jigajigan 'yan siyayasa tareda manyan sarakuna, da manyan
malamai zasu halarci taron bikin k'are makarantar tasu.
Izzatu sai d'oki takeyi akan zatayi ido hud'u da wannan hamshak'in gwamnan, wanda tun a
ganin farko da tayi masa taji ya kwanta mata a rai, tun a daren ranar bikin take ta jin yawan
fad'uwar gaba, ta rasa meke damunta, jin kanta takeyi kamar bata son zuwa taron bikin, amma
kuma a wani b'angaren tana farin cikin zuwan ta ko don saboda abu biyu, yaya Garzanta yace
zai zo shima ayi dashi, sai kuma d'okin ganin wannan Gwamnan da takeyi.
A ranar bikin tun da safe mai gari ya bada mota suka cikata fam, Mai unguwa da malam, sai
mama hassatu da iya kulu da ita izzatun, ansha uwar barafasa da iya kulu kafin malam ya
shawo kanta tazo, bikin, don a cewar ta ita bazata zo ba a had'a baki aje a saida mata kai tana
sake da baki ba, malam ya tilasta mata sai taje ne saboda wani malamin su izzatu ya sanar
dashi duk rabin kyautukan izzatu ce ta cenye, to yana so taje taga irin bauwar da Allah yayiwa
izzatun, koda Allah zai sa ta rage tsanar izzatu a zuciyarta.
Aiko taro yayi taro wuri ne na sai wane da wance,iya kulu sai rabon ido takeyi tana kallon
manya manyan hajiyoyi tareda zunduma zunduman motoci, a wani k'aton fili ne akeyin taron
yayinda aka k'awata wurin da rumfunoni na alfarma, kasancewar makarantar shafe take kaf da
b'urji shiyasa kowa ka hango tsaf tsaf yana takun gwadin ina tsaarata?.
Bayan an zazzauna manyan bak'i sun hallara sai kawai akayi sanarwar ga gwamna nan zuwa,
aiko gaba d'aya wuri ya rincab'e da sowa saboda ana son shi sosai, saboda yana mulkinshi a
cikin adalci da sanin makamar aiki, kafin kace me wuri ya hautsine da kuwwar ganin gwamna, a
cikin tsanaki yake takunshi fuskar shi d'auke da wani mayalwacin murmushi, sai hannu yake
d'agawa mutane yana mik'a gaisuwa, security's a gaba da bayanshi, har suka kaishi wani
k'awataccen muhallin da aka tanadar masa ya zauna, mutane sai lik'e suke yau gasu ga
Gwamnan jahar su.
Cen na hango iya kulu ta zula kai tana so ta yimasa ganin k'wak'waf don taji dad'in bada labari,
sai d'aga masa hannu takeyi daga nesa tana kiran,
"Taka lafiya baya goya marayu,mijin hawainiya mai tafiyar k'asaita, sukari bakayi farin banza
ba"
Abun mamaki sai gashi na hango Hajiya fatima da Ammi Hadizatou tareda baba kallah a
bayansu, yayi fari ya k'ara jiki alamun kwanciyar hankali ya bayyana a jikinshi, sai ga wasu
security's gaba da bayansu suma sai tafiyar k'asaita sukeyi, aikuwa sai mc ya fara kururuwar
zuwan matan Gwamna, wuri ya k'ara hargitewa sai mamaki akeyi ga Gwamna har da matanshi
biyu a taro d'aya, lalle wannan biki ya amsa sunan shi, aka bubud'a masu hanya, aka yimasu
masauki a kusa da maigidansu, d'aya a gefen dama yayin da d'aya take a gefen hagu, daga
nan aka natsar da jama'a sannan aka gayyato wani shahararren malami a jahar yazo ya bud'a
taro da addu'a, sannan aka kira sunan IZZATU AYUBA da tazo ta bud'a taron da karatun
alk'ur'ani.
K'irjin izzatu ya buga dam!! ba shiri ta janyo lik'abin da mama sako, tun a cikin mota da zasu zo
ne ilham ta cire shi a saman kan mama, shine izzatu ta rik'e mata a hannunta, aiko tana jin an
kirata ta saka shi ta rufe fuskarta ruf, ta fito a tsakiyar filin ta fara rero karatun alk'ur'ani tamkar
wata balarabiyar makkah saboda a makaranrar akwai sashen karatun arabic to ko ina da ita ake
karatun, a nan ta koyi karatun k'ira'ar Hafs, aiko jikin mutane yayi sanyi saboda muryarta dake
fito da k'ira'a mai kashe duk wata zuciyar mai imani.
Malam da mama har kukan farin ciki sukayi saboda jin dad'in ilimin da izzatu ta samu.
Bayan taje ta zauna ne aka fara gudanar da shirye shirye, daga nan aka tsunduma rabon
kyaututtuka,a dai dai lokacin ne Garzali ya k'araso filin taron, yana jin ankira sunan izzatun shi
ya kutsa taro ya shiga ya tsaya a bayan ta, kyauta ta farko da aka bata, tana k'ok'arin barin
wajen ne yasha gabanta da sauri ta d'aga lik'abin kad'an ta kai kallonta akan fuskar shi, aiko
tana ganinshi wani farinciki ya mamaye zuciyarta, ya zura hannu ta mik'a masa kyautar, daga
nan aka sake kiran sunanta ta saki lik'abin ta dawo, ta karb'i kyautuka sun fi goma kuma duk
wadda ta karb'a shi take baiwa.
Bayan ank'are kiran sunan ta ne akace taje ta zauna, yaya Garzanta ya rik'o hannunta a cike
da farin ciki, sun je kan wasu kujeru sun zauna kenan aka sake kiran sunan IZZATU AYUBA,
akan ta fito mai girma gwamna zai bata tashi kyauta ta musamman.
A nan take wurin aka d'auki tab'i izzatu ta tako a hankali tazo tsakiyar filin, mai girma Gwamna
ya taso tareda ss nashi masu take masa baya ya tsaya idon shi akan izzatu, dake a tsaye
sanye da lik'abinta shif shif baka ganin komi nata sai k'wayoyin idanuwanta, sannan aka baiwa
mai girma Gwamna damar ya fara magana ta hanyar mik'a masa microphone yayi magana, ya
kalli izzatu tun daga saman tafinta har kanta yaji dad'in shigar da yaga tayi na cikakkiyar 'ya
tagari mai tarbiyy, ya fara jinjina mata akan shigar kamalarta da k'wazonta, sannan ya fara jero
albishir d'in da yayi niyya a gareta, bakin shi a washe ya fara magana kamar haka,
"A bisa yanda naga jajircewar ki da k'wazon ki, nayi maki alk'awalin kujerar makkah, sannan
nayi alk'awalin d'aukar nauyin karatun ki izuwa k'asar london,idan har iyayenki sun amince
domin k'ara farfad'o da karatun ki, saboda samun irinki 'yan baiwa abu ne wanda ya kamata ace
an tallafa maku, ko don al'ummah ta amfana da irin baiwar da Allah yayi maku, sai kyauta ta ta
uku kuma ta k'arshe, amma ita kam bazan bada ta ba har sai naga hafizar mu ta bud'e fuskarta
sannan ta karb'a, don bana farin ciki idan aka watse wannan taro ace banga fuskar 'yata 'yar
baiwa ba"
Izzatu ta saka hannu ta bayan kanta a hankali ta kwance k'ullin da tayiwa lik'abin, ta janye shi
daga fuskarta ba shiri zuciyoyin mutum biyar a wurin suka buga a lokaci d'aya.
Daram dam dam tashin bomb nima tawa zuciyaresai dakan lugude takeyi.
Akafta♀️
D/Auta ce
[8/22, 6:52 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*MY SPECIAL GIFT TO YOU MY MUM &MY SUNSHINE DAUGHTER*
*mum luba yakamata(mum of 3ful H)*
*My lovely daughter Roophaeda Auwal idris*
*PAGE FORTY*
**********************
*Shin wad'anni zuciyoyin ne suka buga???*
Da sauri mai Girma Gwamna ya yarda microphone d'in dake hannun shi, saboda bugawar da
zuciyar shi tayi ba shiri, tareda k'are k'ule hasken fitullun gilashin idanun shi akan kyakkyawar
fuskar izzatu.
Hadizatou AMMI itama da hankalinta yake a kan mai gidanta da wannan d'aliba, wadda a lokaci
d'aya taji tana muugun k'aunar yarinyar tana ta ina ma ace itace ta haife ta, saboda yarinyar ta
tafi da tunaninta wanda har yasa ta tuno yarinyar da ta gani a bakin titin BADAWI PLAZAR,
saboda izzatu ta burgeta sosai, anan take tsohon mikin dake a cikin zuciyarta ya taso, abun
mamaki anyi mata bazata cin karo da fuskar yarinyar, da taso tayi accident domin neman
ganinta ido a rufe, sai gashi yau gata a gabanta tana kallo tamkar wata majigi.
Hajiya fatima AMMAH, itama k'irjinta yafi na kowa bugawa, duk da tana da masaniyar izzatu ko
wacece, amman dai bata tab'a ganin ta ido da ido ba sai a yanzu, saboda duk ganin da take
yimata a cikin photo ne, amma yanzu ganin zahiri da tayi mata ya tabbatar mata da cewa, da
gaskiyar Kallah da yace mata yarinyar tana tsananin kama da Hadizatou tamkar kwabo da
kwabo, sannan k'arin tashin hankalinta a yau duk wata k'unbiya k'unbiyar da take yi ta k'are.
KALLAH shima tashi zuciyar ba k'aramar bugawa tayi ba, saboda yau ne ranar tonon asirin da
suke rufewa a tsawon shekarru, wanda tabbas fasuwar wannan k'wai dai dai yake shigar
rayuwar shi a cikin garari, don koda anyi masa uzuri kunyar idanuwan mutum uku bazasu tab'a
barin shi yaji dad'in zama a kusa dasu.
Mai gayya mai aiki izzatu bud'e fuskarta da tayi a cikin d'inbin dubban mutane, ga y'an jaridu
'yan gidan radio da masu d'auka a gidan television sai aikin su sukeyi, shi ya fara saka zuciyarta
bugawa, d'ago fuskarta da tayi ta jefa kallonta akan fuskar mai Girma Gwamna, ya k'ara saka
ta a cikin wani fad'uwar gaba wanda ta kasa tantance shin wai na miye, tayi k'ok'arin wanke
fuskarta da wani tattausan murmushi.
Mai girma Gwamna a cikin d'imaucewa ya d'auko microphone yace da ita, "'yata miye sunan
ki na gaskiya.?"
Izzatu tayi wani murmushi tace, "sunana IZZATU AYUBA."
Mai girma Gwamna jikinshi yana kyarma yace, "A wani Gari kike.?"
Izzatu tace, "A k'auyen D'anlasau"
Mai girma Gwamna ya k'ara da cewa, "shekarar ki nawa.?"
Izzatu tace, "Shekarata goma sha tara."
Mai girma Gwamna yayi wata kabbara wadda ta baiwa kowa mamaki yace, "ALLAHU
AKBAR ALLAHU ASSAMADU ALLAHU ASSAMI'U ALLAHU AL'ALIMU ALLAHU AL'BASIRU
WALLAHI TALLAHI ALLAHU WAHIDUL K'AHHAR NE"
Sai mai girma Gwamna ya fashe da kuka, aiko gaba d'aya wurin yayi tsit sai mamakin wannan
abun al'ajabi dake faruwa da mai girma Gwamna ake yi.
Hajiya fatima jikinta yayi sanyi k'alau wani imani ya k'ara shigarta, nadama tazo mata taji idan
bata bayyana wannan gaskiya ba, to tabbas kamar mutuwa zatayi a wurin, wanda take ta
hango idan fa ta mutu a lokacin a wuta za'a jefata, jikinta ya d'auki rawa tamkar wani mazari, ta
tashi tsam k'afafunta suna hard'ewa, da wasu hawayen masu zafi da suke kwaranya a kan
fuskarta, ta saka hannu janyo hannun hadizatou dake zaune tamkar wata mutum mutumi, har
sai da takaita a gaban izzatu ta rik'o hannun izzatu ta had'a da na hadizatou, kamar wani
magnet haka hannunsu ya had'e gam sai kallon juna sukeyi ko k'yaftawa babu.
Hajiya fatima ta karb'o microphone ta kalli mai girma Gwamna yanda yake kuka hawaye wasu
suna biiyar wasu, itama wani kukan yazo mata da sauri ta share hawayenta, ta aro wata
jarumta ta ta yafa, ta kalli Hadizatou ta dawo da kallonta akan izzatu, tayi tattaki tazo tsakiyar fili
ta tsaya ta fara magana kamar haka,
"HADIZATOU GA 'YARKI DA TA B'ATA TSAWON SHEKARA GOMA SHA TARA DA SUKA
WUCE, IZZATU GAKI GA MAHAIFIYARKI TA CIKIN KI WADDA TAYI SILAR KAWO KI DUNIYA
DAGA YAU SUNAN KI IZZATU YAHAYA BADAWI EXECUTIVE GOVERNOR OF...... "
Ba shiri wurin ya d'inke da sowa kowa sai albarkacin bakinshi yake fad'a.
Hajiya fatima ta fashe da wani bajimin kuka a cikin tashin hankali, zata k'ara wani bayani ne mai
daraja gwamna ya rungumo ta a jikinshi yana lallashi, aikuwa wuri ya k'ara d'inke da kuwwa.
Hadizatou jikinta yana kyarma ta rungumo izzatu a jikinta tamkar wani zai k'wace mata ita,
IZZATU dai a tsaye take sai walainiya da idanuwa takeyi, amma gaba d'aya gangar jikinta ta
daina aiki, har sai da ta hango yayanta Garza yana so ya shigo a cikin filin yazo wurinta, wasu
security's suka hanashi zuwa, shi kuma ya nace akan dole sai yazo wurinta.
Aiko wani soja ya cira hannu ya kwad'a masa mari, wasu 'yansanda suka rirrik'eshi, wani soja
ya d'aga bindiga zai daki kanshi, ba shiri izzatu ta k'walla wata razananniyar k'ara ta k'wace
jikinta da ke mak'ale da hadizatou ta nufeshi da gudu tana kiran sunan shi.
Tana zuwa ta fad'a a jikin shi tana wani kuka wanda ita kanta batasan ko na minene ba, shima
kamar zaki haka yayimata wata wawar runguma sai kukan yake tamata, gaba d'aya sai kallo ya
koma kansu, masu video da d'auka a gidan television live sai haskawa sukeyi, haka 'yan gidan
Radio sai bada labarin abunda ke faruwa sukeyi, yayinda a ko'ina a fad'in jahar abunda ake
kallo da sauraro kenan.
Rigiji gabji akwai ruguntsumi da cakwakiya a gaba wallahi
Ku biyoni don jin yanda zata kaya♀️♀️♀️♀️♀️♀️.
Akafta♀️
D/Auta♀️
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: *RUWA DA KANKARA⛈️*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Dole inji da k'arfi a jikina dole in maku komi da gumina babu iya yimaku komi a gaba
na naji duk sharhin da kukayi akaina kuma ya shiga raina dole ne in dauro d'amarata a
tare musha madara*
*Wai shin gudu nake ko tafiya nike, wai zafi ake ko sanyi ake,idona gani yake kamar
budo muke kutsaya ni nagaji ku bani agajiakan ku bani ji a zancen post bazan yima ku
hijira ba*
*PAGE FORTY ONE*
**********************
Mama hassatu da malam da suke zaune suna kallon abun da ke faruwa, gaba d'aya suma
kukan sukeyi sai k'ara jinjina wa hikimar Allah sukeyi, yanzu izzatun su itace d'iyar gwamna?,
lalle Allah buwayi gagara misali ne kawai zai iya wannan lamari.
Iya kulu tana gano abunda ake nufi,, magana ta tabbata lalle izzatu d'iyar Gwamnan ce, ai kuwa
da gudu tayi wani lungu tareda tsintar wata leda a k'asa, afujajan ta duk'a sai zawo take
zubawa sai da tayi iya cikinta, sannan ne ta saka ruwan gorar dake hannunta ta wanke ta fito,
jin takeyi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a k'auyensu, a k'auyen ma a cikin d'akinta, a d'akin ma
a k'ark'ashin gado tana addu'ar Allah ya d'auki ranta ta huta kafin su malam su dawo su risketa,
don kuwa tasan tabbas had'uwar ta da wannan hamshak'in Gwamnan ba abu bane mai kyau,
iya kulu tana hango izzatu rungume da matar Gwamna da gudu ta koma lungun ta kara bajewa
sai nishin wahala takeyi, kafin kace kwabo iya kulu idonta sunyi zuru zuru saboda tashin
hankali, sai hango kan ta takeyi a gidan yari ana ta lafta mata buloli tareda gana mata azaba
kala kala.
Mama hassatu hango Garzali da tayi rungume da izzatu jikinta yana rawa ta zagaya, dak'yar ta
samu ta kutsa ana turinta amma bata daina yunk'urin isa wurin su ba, a cikin d'aga murya ta
dakawa Garzali da izzatu tsawa tace,
"Garzali da izzatu a kul d'inku da wannan rashin kunya a gaban mutane sai d'aukar ku photo
akeyi, da sauri izzatu ta saki garzali a d'ari taje ta rungume Mama hassatu tana ci gaba da
kukanta mai tsuma zuciyar mai sauraro, izuwa lokacin idanunta har sun kunburo fuskarta tayi ja
saboda tsakanin kukan da tasha.
Mai Girma Gwamna da kanshi ya tako har inda su mama da izzatu suke a tsaye, ya saka
hannunsa ya rik'o hannunta ya feshe ta da wani murmushin farin ciki, itama ba shiri ta fad'a
jikinshi ya saka hannu biyu ya rungumeta, tareda bubbuga bayanta akan tayi hak'uri kukan ya
isa a hakan, daga nan izzatu ta d'ago ta kamo hannun mama tace dashi, "Wannan itace
mamata wadda ta nuna man so fiye da yanda uwa take nunawa d'anta, bansan zafin rashin
uwa ba saboda ni tawa uwar mai adalci ce, bata barina a cikin damuwa balle inyi kuka"
Tana cikin maganar ta hango malam da mai unguwa daga cen baya a tsaye da kanta tayi tattaki
taje har wurin su malam ta rik'o hannun shi tace,
"Taho baya goya marainiyar Allah izzatu, kaine ka hanani inyi kukan maraici, bansan zafin
rashin uba ba saboda ka tare dama ka tare hagu na ta kowane b'angare, yanda bazan gano ba
kaine ka haifeni ba nagode