Showing 27001 words to 30000 words out of 88612 words

Chapter 10 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8310

shima abin da tayiwa Fulani haka tayi masa, sannan ta juya kan Jalila
itama haka tayi mata, mudai sakar baki mukayi muna kallon ikon Allah dan wannan ya zame
mana saban al'amari aganinmu idan zata rungumi Fulani da Jalila ai bai kamata ta rungumi
Yarima Jalil ba?.
Neman guri tayi ta zauna tana fad'in.

"Ku bamu waje ko?".

Duk kanmu muka mik'e muka fito zuwa waje, kowa ya kama gabansa, ni da Zainab neman

waje mukayi muka zauna muna hira, bamu jima ba akayi kiran Zainab a b'angaren Fulani
Bingel, ta barni nan zaune gashi ni inba Zainab ba bana shiga harkar kowa nan nayi ta zaune
har zaman ya isheni na mik'e nima na nufi b'angaren Fulani Bingel tunanina inje intaya Zainab
aikin da take, ko ba komai yafi zaman da nake ni kad'ai.

Ina tafe ina 'yan wak'e-wak'ena sai ji nayi anjawo hannuna cike da tsoro na bud'e baki zanyi ihu
yasa hannunsa ya rufan bakin yana fad'in.

"Sarkin tsoro !".

Fuskarsa d'auke da murmushi, ajiyar zuciya na saki tare dayin k'asa da kaina, Yarima Fudhal ya
tsareta da idanuwa yana fad'in.

"Yau dai kinga kishiyarki ko?".

Aynu batasan sanda ta jefeshi da wat uwar harara ba, Yarima yayi murmushi yana mai cigaba
da fad'in.

"Mene na kishi a kaina kuma?, bayan bakya sona?".

Sai lokacin Aynu ta lura da abin da tayi kunya ta rufeta sosai, murmushi yayi mai sauti.

"To yau dai sai kin fad'amin kina sona ko bakya so na?".

Aynu tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta.

"Baki ce komai ba?, ko bakya so na?".

Ta girgiza kai alamun a'a.

"To kina so na?".

Ta gyad'a kai alamun ehhh, tana mai rufe fuskarta da tafin hannunta, murmushin dake kan
fuskar Yarima ya sake fad'ad'a, sosai yake jin wani sanyin dad'i na ratsa dukkan sassan jikinsa,
har yanajin kamar ya rungumeta tsabar farin ciki.

"AYNU...!".

Ya kira sunanta da wata irin murya, bata d'ago kanta ba illa amsawa da tayi kawai tana jiran taji
mai zai ce.

BAN HAK'URI

Ku k'ara hak'uri dani dai, naso nayi muku typng mai yawa sakamakon jiya banyi muku post ba,
sai dai Allah bai yarjemin ba wlh bbu chaji awayana yanzu kuma kunata jirana shiyasa na
k'ok'arta nayi muku wannan zuwa anjima insha Allahu indai na samu chaji zaku sake jina
nagode sosai da kulawa.
*YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®

SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.



17



Ya cigaba da fad'in.

"Tabbas naji dad'i sosai da jin amsar data fito daga bakin ki, yau rana ce ta musamman agare
ni da bazan tab'a mancewa da ita".

Yayi shiru yana mai cigaba da kallonta, har lokacin Aynu bata iya d'ago kanta ba, sanya hannu
yayi ya d'ago kan nata yana mai duban fuskarta cike da so da k'auna, Aynu ta rintse ido domin
bata iya juran kallonsa, sakin fuskarta yayi ya ce.

"Hak'ik'a kin bani farin ciki wanda nake fatan d'orewarsa har aba da !".

"Bari inje Mai Martaba na kira na, zan zo yau da dare gidan ku !".

Kai kawai Aynu ta gyad'a masa ya tsaya yana kallonta kamar kada ya tafi, da k'yar dai ya juya
yabar wajen.

Aynu tabi bayansa da kallo tafiyarsa kanta abar burgewa domim Yarima idan yana tafiya da
gaba d'ayan jikinsa yake tafiya, gyaran muryar da ta jine ya sanyata juyawa da sauri domim

ganin waye?.

Yarima Jalil ne tsaye yana binta da kallo ya nad'e hannunsa ak'irjinsa fuskarsa babu yabo
babu fallasa.

Aynu tad'an risina ta gaishe shi, ya amsa tare da fad'in.

"Ya had'u ko Yayan nawa?".

Yayi maganar yana mai d'aga mata gira, murmushi Aynu tayi ba tare data iya cewa dashi komai
ba.

"Anyi masa mata to !, dama kin barshi kindawo wajena Beauty".

Aynu dai batace komai ba, ya d'an matso kad'an zuwa wajenta adai-dai kunnenta ya rad'a
mata.

"Dani kika fi dacewa, nine zan baki dukkan k'auna !, duk naji abin da yake fad'a miki ki watsar
da batunsa, ki fuskanci batuna domin dai ga matar da zai aura nan, bayan ita kuma akwai
wacce akayi magana su biyu zai aura ya angwance !".

Ya k'arashe maganar cikin dariya ciki-ciki.

Aynu da sauri ta dubeshi da kallon tuhuma tana son tabbatar da maganarsa, gira ya d'aga
mata tare da wani guntun murmushi a saman fuskarsa.

"Ko baki yarda dani bani?".

"A'a na yarda mana, amma ni nace maka akwai wani abu atsakanin mune ?".

"Baki fad'aba amma idanuwanku sun shaida hakan, kiyi tunani sosai akan Fudhal dani Jalil
waye zaifi dacewa da rayuwarki ?, indai har zaki yarda da soyayyata zanbar dukkan wani abu
mai muni da nake aikatawa kuma zan rayu dake ke d'aya babu wata ".

Yayi shiru yana karantar yanayinta kafin yad'an cije leb'e ya cigaba da magana.

"Shin aganinki wanda zai auri mace kamar Safiyya zaiyi tunanin kuma auren wata 'ya mace
ne, ki tuna bayan ita akwai wata, itama kuma ba baya ba wajen kyau da kud'i da komai n".

"Zan barki kiyi tunani akan hakan duk shawaran da kika yanke zaki iya fad'amin".

Ya juya yabar Aynu da jijiyoyin jikinta baki d'aya sun tsinke tsoro ya ziyarci zuciyarta sosai, take
taji zuciyarta nayi mata zafi wajen Zainab d'in da bataje ba kenan tayi tafiyarya gida aganinta

zatafi samun nutusuwa da kwanciyar hankali idan ta koma gidan.

Sai dai ba anan gizo yake sak'arba ko da ta koma gida kasa aikata komai tayi inbanda aikin
tunani babu abin da take yi, aranta tanaji Yarima Fudhal ya cuceta, duk da k'asan zuciyarta ya
kasa gasgata hakan.

Ummanta tayi tambayar duniya ko akwai abin da yake damunta amma Aynu tace babu komai,
daga k'arshe da taga Umman ta damu sai tace kanta ne yake ciwo tasha magani tayi
kwanciyarta.

***

Haka Aynu ta kwana bacci sai dai b'arawo, amma a cikin daren sai da tasamawa kanta
mafita, duk da wani b'angaren na zuciyarta ya kasa yarda da hukuncin data yankewa kanta.


Washe gari kuwa ko da takoma aiki abin da ya kaita kawai tayi, kuma daman ta tarad su
Yarima sun fita tun asuba hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba, amma tana gama aikin da
zatayi neman guri tayi falo ta zauna tare da fuskantar wani k'aton frame na hoton Yarima Fudhal
da aka d'aukeshi gaba d'ayansa yana sanye da farar coat da wando fari hatta takalmi da
agogon hannunsa fari ne, sosa Aynu takeson hoton tun ba yanzuba haka kawai takanji dad'in ta
zauna tana kallon hoton domin kamar kace Yarima ya amsa hoton ya d'auku sosai.




11:30am.


Basu dawo ba sai k'arfe sha d'aya da mintuna ya turo k'ofar d'akin ya shigo cike da sallama,
Aynu bama tasan ya shigo ba domin tayi zurfi cikin tunani, wani dad'i yaji alokacin da idonsa
yakai inda Aynu take kallo murmushi yad'anyi tare da k'arasawa wajen da take zaune ya dafa
kafad'arta.
A firgice ta d'ago kai sai kuma ta saki ajiyar zuciya ganin Yarima.

Turo k'ofar da akaine ya sasu juyawa baki d'ayansu, Gimbiya Safiyya ce ta shigo cikin takun
k'asaitar nata tabisu da wani kallo wanda Aynu takasa tan-tance kona menene?.

"Wace wannan?".

Ta jefawa Yarima tambaya, Yarima Fudhal ya nemi guri ya zauna batare daya bata amsaba, sai
ma fad'i daya hauyi.

'kawomin breakfast Aynu".

"A'a ta barshi ai tafe muke da shi, Larai...!".

Gimbiya Safiyya ta kira wata mai aiki dake bakin k'ofa, Larai ta shigo hannunta d'auke da tire ta
ajiye gaban Gimbiya Safiyya data nemi waje kusa da Yarima Fudhal ta zauna.

Larai ta juya ta fice, Gimbiya Safiyya ta d'auki Apple ta kai masa baki Yarima ya kau da kansa
gefe yana fad'in.

"Tea nake buk'ata Aynu zoki zuba min".

Gimbiya Safiyya ta kaiwa Aynu wani kallon wulak'anci tana fad'in.

"Au dama baki fita ba, fita ki bamu waje !".

"Babu inda zata domin kafin zuwanki ita ke ci da ni".

"To yanzu tun da nazo ba sai ta huta ba?".

Takai maganar tana hararar Aynu, Aynu tayi k'asa da kanta ba tare da tace komai ba.

"Zo ki serving d'ina".

Ya sakewa Aynu magana, Aynu tamik'e tazo tayi serving komai ta koma gefe ta zauna.

Gimbiya Safiyya tad'auki kofin tea d'in takai masa bakin wai zata ci da shi ya d'auke kansa tare
da fad'in.

"Na gaya miki bana buk'ata".

"Amma kasan aure zamuyi?, mene danna ci da kai tun yanzu ai treaning nake yi".

Yarima tsaki yaja yana mai kau da kansa gefe cike da takaici, Gimbiya Safiyya ta sake duban
Aynu cike da masifa tana fad'in.

"Wai ke wacce irin macace akace ki fita ko?".

Aynu tamik'e ta fice aranta tana jin zafin wulak'ancin da Gimbiya ke yi mata, amma ak'asan
zuciyarta sai taji babu komai domin ita 'yar aiki ce kuma baiwa ita kuwa 'ya ce ga Sarki guda.

Yarima Fudhal bai yi magana ba har Aynu ta fice tana goge kwallar dake gefan idonta, ransa

idan yayi dubu yab'aci take yamik'e ya fito shima yabar mata d'akin.

Ran Gimbiya yab'aci sosai ta fito itama ta nufi b'angaren Fulani Sokoto tana kuka wai Yarima
Fudhal yafifita Baiwa akanta ?.


Rarrashinta Fulani tayi tare da fad'in.

"Ki kwantar da hankalinki zan san abinyi dani yake zancen !".

Jalila dake zaune gefe tsaki taja tace.


"Kema dai Aunty Safiyya kin manta waye Fudhal ne?, tun da kin taka kinje wajensa ai kuwa
sai abin da kika gani !, shi Allah na tuba baka shiga harkarsa ba ma ya wulak'anta ka bare kuma
ka shiga....!".

"Ke gidanku nace !, rufemin baki dan taje wajensa meye a ciki?, ina nan da kwanaki kad'an
mijin tane?".

Cewar Fulani kenan cike da fad'a, Jalila tsaki taja tana k'uk'uni.

"Nifa Momy ba haka nake nufi ba, Allah ya baku hak'uri".

Ta fad'a tana mai mik'ewa ta fice daga cikin d'akin.

Yarima Fudhal na fitowa neman Aynu yahauyi lungu-lungu amma bai ganta ba, sai da ya gaji da
nema ya tsaya jikin windown wani d'aki sai yadinga jiyo shash-shek'ar kuka bayan d'akin, zaga
yawa yayi domin ganin waye yake kukan?, Aynu ya gani ta had'a kai da gwiwa a hankali ya taka
zuwa wajen tare da kiran sunanta yana mai kama kafad'unta ya d'ago ta, fuskarnan
shab'e-shab'e da hawaye hannu yasa yahau share mata yana fad'in.

"Yi hak'uri kinji !, mene abin kuka kuma?".

Aynu ta janye jikinta daga nasa tana yi masa wani mugun kallo ta juya masa baya, k'ara juyo
da ita yayi ta kuma juyawa masa baya ganin da yayi tana k'ok'arin barin wajen ne yasa shi shan
gabanta yana fad'in.

"Wai lafiya kuwa?".

Tsaki tad'anja tana mai ratsewa ta gefansa tabarshi nan tsaye bin bayanta yayi da kallo,
zuciyarsa na k'una akan abin da tayi masa yaso binta amma kuma sai ya fasa.

D'aki ya koma ya kwanta yana tunanin laifin da yayi mata har tayi fushi dashi, jiya dai sun rabu
lafiya amma kuma yau tana fushi dashi kodan yace zaije bai jeba?.

Sai kuma tunanin abin da yafaru d'azu ya fad'o masa arai.

"Safiyya ce tajawo komai kenan?".

Ya fad'a cikin ransa mik'ewa yayi zaune tare da fad'in.

"May be kishi ne !, zanyi k'ok'arin shawo kanta".

Abin da yafurta afili kenan ya mik'e ya fito daga d'akin zuwa waje, ya sake dubawa amma bai
gantaba daga k'arshe ya tambayi Jakadiyya tace masa ta tafi gida tun d'azu, tsaki yaja aransa
ya nufi b'angaren Mahaifiyarsa.


Wunin ranar haka Yarima yayi shi sukuku da shi, b'angaren Aynu ma haka abin yake.

Ya so ya bari har dare yaje wajenta ko yasamu nutsuwa cikin ransa, amma kuma ya kasa
daurewa zuciyarsa nata faman azalzalarsa k'arfe hud'u da mintuna a shirin yayi parking motarsa
bakin layin gidansu Aynu.

Ya fito ya kulle motar ya taka har zuwa k'ofar gidan tun kafin ya k'arasa ya hango ta tsaye da
wani zuciyarsa sai da ta buga yayi k'arfin halin k'arasawa ya tsaya nesa dasu kad'an.


Yan da suke hiran Aynu na d'an murnushi abin sosai yake sosa ran Yarima, ji yayi kaman yaje
ya shak'e wanda suke tare, amma dai ya daure ya cigaba da tsaiwa har sai da wani yaro yazo
wucewa yace masa ya kirawo masa Aynu.

Aynu na sane dashi tunfarkon shigowarsa layin ta ganshi amma ta kau da kai suka cigaba da
hirar da suke da Yasayyadi Umar.

"Aynu kije inji wancan mutumin".

Yaron ya fad'a yana mai nuna Yarima Fudhal.

Tare suka d'ago ita da Yasayyadi suka dubi inda Yarima yake tsaye ya had'e girar sama data
k'asa.

"Waye wancan d'in?".

Ya Sayyadi ya jefa mata tambayar yana mai kallonta, Aynu ta k'ak'alo murmushi tana fad'in.

"Shine wanda nake yiwa aiki ai !, Yarima Fudhal ne".

Kai kawai Ya Sayyadi ya gyad'a yana fad'in.

"Jeki dawo to zan jiraki domin akwai maganar da zamuyi".

"To".

Abin da tace kenan, ta taka zuwa wajen Yarima wanda tun tawowarta ya kafeta da idanuwa
yana kallonta, da sallama tak'arasa wajen tana mai kau da kanta gefe, mai makon ya amsa
sallamar sai cewa yayi.

"Waye wancan?".

"Ya Sayyadi Umar kenan, malamin islamiyyar mune".

Ta bashi amsa, Yarima ya cize leb'ansa na k'asa yana mai cigaba da fad'in.

"Anan ma Islamiyyar kuke kenan?".

"A'a yazo duba Ummata ne".

"Dubiyar anan waje ake yinta?".

"A'a rakoshi nayi zuwa waje".

"Kinsan tsayin lokacin danayi anan, nasan kuma kafin zuwana may be kun jima tsaye".

"Ehh nasan kazo mana !".

Da sauri Yarima Fudhal ya dubeta jin amsar k'arshe data bashi, cikin kasa lallliyar murya ya
furta.

"Meke faruwa ne Aynu?".

"Babu komai n, yi hak'uri na barshi tsaye bari inkoma".

Bata jira mai zai ce ba ta juya kawai ta barshi nan tsaye, Yarima binta yayi da kallo yama rasa
mai ya kamata yayi.


Ya bita ko ya rabu da ita ne????.

Hello makaranta


Sai dai fa kuyi hak'uri dani domin alk'alamina bazai iya zayyane muku irin son da Yarima Fudhal
ke yiwa Aynul-hayat ba, kamar yanda girman kai da jiji da kai ba zasu bar Yarima Baiyyanawa
Aynu irin son da yake yi mata.

Kawai sai dai ku ayyana irin son a cikin ranku....!.

ASHA KARATU LAFIYA.

*YARIMA FUDHAL*



Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jibour.


18



Yana cikin wannan tunanin wayarsa dake hannunsa tayi ringing, ya d'aga yakara a
kunnensa ba tare daya duba yaga waye mai kiran ba.

"Haba My...! Abbana yazo har gida anyi magana fa !, amma ko ka kirani mu tattauna batun
auren mu...!".

Cire wayar yayi daga kunnensa ya duba screen d'in wayar sunan Saima ne d'od'ar bisa screen
d'in, guntun tsaki yaja tare da mai da wayar kunnansa, ta cigaba da fad'in.

"Duk da ance mu biyu zaka had'amu zan amince ne kawai sabida son da nake maka.... !".

Cikin b'acin rai ya katse ta yana yana fad'in.

"Duk naji amma ki sani duka ku biyun babu wacce nakeso aciki, zaki iya kashe wayar !".

Ya fad'a yana mai kashe wayar ya jefata cikin aljihun wandonsa, ya mai da kallonsa kansu
Aynu dake tsaye har lokacin suna hira.

Tsaki yaja ya juya kawai ya bar wajen zuciyarsa cike da sak'e-sak'e da kokwanto kala-kala,
tare da dumbin tunanin nemawa kansa mafita tunkafin lokaci yak'ure masa.

Saima kuwa yana kashe wayar hawaye ya fara zarya bisa kuncinta zuciyarta na zafi da k'una,
a haka Momynta tazo ta tadda ita, dafa kafad'arta tayi tana fad'in.

"Haba Saima !, har zuwa yaushe ne zaki samawa kanki mafita abisa muguwar damuwar
dakika d'orawa kanki !, nad'auka damuwarki ta kau tunda har iyaye sunyi magana ?".

Saima ta fad'a bisa cinyar Momynta da ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login