Showing 78001 words to 81000 words out of 88612 words
Chapter 27 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
Bata bashi amsa ba haka kuma bata buɗe idon ba.
Fudhal ya saki haɓarta ya sake kamo hannunta da hannunsa duka biyun yariƙe yana kallon
zanan Jan lallan da fulawan da akayi mata.
"Kai amma yayi kyau flawer ɗin yakai hannun nata bakinsa ya sunbata, Aynu ta janye hannunta
da sauri tana kallonsa sai kuma ta sake sauke idanuwanta kasa.
Yarima Fudhal bai kuma cewa komai ba ya jawo pillow ya kwanta abinsa ya barta nan tsaye,
tsayin lokaci a haka.
Aynu na ɗago kai taganshi kwance abinsa idanunsa a rufe yanayin yanda yake fid da numfashi
ne ya tabbatar mata da yayi bacci sosai abin ya bata mamaki ƴan mintuna kaɗan amma ace
yayi bacci?, sai kuma ta tuna ai bashi sa lafiya ne.
Ƙarasawa tayi dai-dai kansa ta gyara masa pillow ɗin tare da ɗora masa hannunsa dake miƙe
kan gado bisa ƙirjinsa ba tayi aune ba sai jinta tayi ta faɗa kan ƙirjin nasa da sauri ta zaro ido
waje sabida tsorata da tayi.
Yarima Fudhal ya sanya dariya.
"Ba kyaso inga kwalliyar in yaba ne?".
Kai kawai ta girgizama masa alamun Aa tana kici-kicin kwace hannun amma ta kasa sabida irin
riƙon da yayi mata, turo ƙofar da akayi ne yasa ta samu damar janye hannun nata tana duban
mai shigowar.
Anwar ne tare da Doctor suka shigo.
Yarima Fudhal yaja guntun tsaki tare da kau da kai gefe, Anwar yayi murmushi kawai, Aynu
kuwa kunyace ta lulluɓeta taji kamar ƙasa ta tsage ta shige.
Doctor ya tambayi jikin nasa tare da dubashi sosai ya juyo kan Aynu yana faɗin.
"Ya kamata a dinga bashi Magani akan lokaci sabida gujewa samun matsala".
Aynu ta gyaɗa kai dai-dai sanda Zainab ta shigo ita ma ta nemi guri ta zauna, Doctor na gama
duba shi zai fita kenan su Hajiya sukayi sallama suka shigo ɗauke da kulolin abinci da kayan
Fudhal.
Aunty Sadiya ce ta buɗe baki tana tambayarsa mai zai ci yanzu?.
Ya bata amsa da faɗin.
"Ko mene ma bani inci".
Ta koma kan kulolin tahau zubo masa makaroni da miya taji naman rago, tare da tsiyaya masa
lemo a cofi.
Ta kai masa gabansa ta ajiye.
A hankali ya ɗauki cokali yahau ci jefi-jefi yana kai kallonsa kan Aynu shi kan shi ya rasa dalilin
da yasa ya kasa daina kallonta haka kawai yake jin daɗin kallon nata duk da ita bata sanma
yanayi ba hirarsu kawai suke da Zainab.
"Ku tashi muje in mai daku gida ko?".
Cewar Anwar kenan yana mai miƙewa daga kan kujerar da yake zaune, Yarima Fudhal najin
haka ya ajiye spoon din dake hannunsa take yaji ya ƙoshi ya ture abincin gefe.
Suka miƙe tare da yiwa Hajiya da Aunty Sadiya sallama, sannan suka ƙarasa inda Fudhal yake
zaune sukayi masa sallama tare da faɗin.
"Allah ya ƙara lafiya".
Wanda duk Zainab ce take maganar Aynu kunya ta hanata ko ɗaga kai.
Haka suka fice daga ɗakin koda sau ɗaya Aynu bata kuma bari sun haɗa ido da Yarima Fudhal
ba, shi kuwa abin da ya ƙara baƙanta masa rai kenan take yaji zaman asibitin ma baki ɗaya ya
gundure shi.
*YARIMA FUDHAL*
NA
FIRDAUSY S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
45
Zaune take cikin lambun dake farfajiyar gidansu akan wata tat-tausar darduma gefanta matane
su biyar zagaye da ita ga kayan mar-mari kala-kala ajiye a gabanta.
Ƴan matan sai hira suke mata na ban nishaɗi tana dariya can ta ɗan bata rai tana duban su
dukansu suka sha jikin jikinsu.
Tsaki ta ɗanyi tana mai duban matar dake gefan hannun damarta.
"Ku bani shawara Jummai akan batun aurena da Yarima Jaleel mana".
Wacce aka kira da Jummai ta gyara zama tare da rissinawa.
"Haba Gimbiya aike kanki kinsan yanzu kin wuce ajin Yarima Fudhal, Yarima Jaleel shine
wanda yafi dacewa dake a wannan lokaci, sabida ba girmanki bane ba kuma ajinki bane ace ki
auri mai mata matarma Baiwa gaskiya da ance kin ci baya".
"Yanzu kuna ganin aurena da Jaleel shine yafi?".
"Sosai kuwa ranki ya daɗe".
Sukayi maganar cikin haɗa baki, Gimbiya Safiyya tayi murmushi wanda har sai da fararen
haƙoranta suka baiyana waje.
"Kuce ingayawa Babana na amince kenan?".
"E mana".
Suka sake bata amsa.
Gimbiya Safiyya tamiƙe da sauri ta nufi cikin gida suka take mata baya.
***
"Ladidi duk laifin kine wallahi kece kika haddasamin wannan masifar.!".
"Kamarya Hajiya?, ai bokan da kansa yace sawun Yarima Jaleel aka kai bana Yarima Fudhal
ba, kinga kenan laifin na wanda ya ɗebo sawun ne bana wanda ya kai ba".
Fulani Sokoto tayi shiru tsayin lokaci tana kallon Ladidi kafin tayi ajiyar zuciya tace.
"Yanzu kenan meye abin yi?".
"Mene kuwa abin yi?, Yarima Fudhal dai ya samu abin da yake so, Yarima Jaleel ma haka,
Gimbiya Jalilah kuma an ɗaura mata malamin islamiyya, ke ya kamata ki yanke wannan
hukuncin Hajiya ba ni ba".
Fulani sokoto tayi tsaki mai tsayi tana huci.
"Ni auren Jalilah da wancan faƙirin shine yafi komai ɗaga min hankali wallahi taya zan samu a
wargaza komai idan yaso maji da matsalar Fudhal da Jaleel".
"To ki kira shi awaya muji mana".
Fulani Sokoto ta janyo wayarta dake gefanta tahau dad-dan nawa alamun tana neman layin
nasa, ringing biyu ya ɗaga tare da ƙunduma wani ashar itama Fulanin ta mayar masa kamar
yanda yayi kafin ya kece da wata irin dariya yana faɗin.
"Basai kin faɗa ba munsan komai ai sun sanar damu".
"To annemo mafita akan matsalar?".
"Aure dai mutu ka raba ne babu yanda za'ayi mu iya raba auren, kuma zan faɗa miki abu guda
ɗaya muddun kika matsa akan raba auren to tabbas zaki mutu..!".
Dammm gaban Fulani ya buga ta saki wayar ta faɗi bisa carpet ɗin tsakar falon tana duban
Ladidi, Ladidi tayi saurin ɗaukan wayar tana faɗin.
"Lafiya Hajiya?".
Da ƙyar Fulani Sokoto tayi ƙarfin halin faɗin.
"Yace aure babu rabuwa kuma idan muka matsa akan raba auren tabbas zan mutu".
Ladidi taja tsaki.
"To kuma Sai ki yarda da abinda da yafaɗa?, yanzu hakama kawai gani yayi bazai iya aikin ba
shiyasa yace dake haka, kawai tun da abin hakane mu canja wani malamin kawai".
Fulani Sokoto shiru tayi tsayin lokaci tana nazari kafin ta gyaɗa kai.
"Kuma maganarki akwai ƙamshin gaskiya fa, dannima kwanakin nan naga aikinsa baya tafiya
yanda ya kamata yanzu wajenwa kike ganin zamu je?".
"E to akwai wani acan kauyen SAMU NAKA ance shima aikinsa kamar yanda wuƙa inaga
muje muji mai zaice shima".
"Yanzu yaushe zaki je?".
"Yanzuma idan kin bani dama sai in tafi inyaso gobe na dawo da safe".
"Ai hausawa sunce da zafi-zafi akan daki ƙarfe ungo wannan maza kije".
Ta miƙo mata rafar ' yan ɗari biyar-biyar, Ladidi tayi godiya ta miƙe tare da ficewa
daga cikin ɗakin.
"Sannu Jaleel ya jikin naka?".
"Da sauƙi Abba sai dai ciwon ciki yana takuramin sosai cikin kwanakin nan".
"OK Allah ya ƙara lafiya, ai likita yace babu wata matsala indai kana shan magani cikin ƙa'ida
zai dai na".
"To zan kiyaye Abba".
Magaji Saifa dake gefe ya dubeshi tare da faɗin.
"Wani babban albishir zan maka yanzu amma sai kayimin alƙawarin ba zaka kuma shan wani
abin maye ba".
"Nayi alkwari wallahi bazan kuma sha ba".
Magaji Saif da Sarki Ubaiyd sukayi murmushi
"Kasan dai mahimmancin alƙawari dai?".
"Na sani Abba kuma zan kiyaye".
Magaji Saif yayi murmushi a karo na biyu tare da dafa kafaɗar Yarima Jaleel kafin yace.
"An sanya ranar auren ka da Safiyya Sati mai zuwa idan ka fito daga asibiti".
Take wani sanyin daɗi ya lulluɓe Jaleel bai san sanda ya rungume Magaji Saif ba yana godiya
har da guntun hawayensa.
Sun jima sosai suna hira kafin su koma ɗakin Yarima Fudhal suka barshi daga shi sai Jalilah
domin Fulani Sokoto bata dawo ba.
Yana zaune gefan gado yayi shiru can gefe kuma su Hajiya ne da Aunty Sa'ida yau Aunty
Sadiya bata zo ba sabida anjima kaɗan da yamma zasuje ɗaukan amaryar Fudhal wato Aynu
amma shi Fudhal bai san da hakan ba.
Magaji Saif ya dubeshi yana faɗin.
"Yadai Fudhal tunanin me kake kuma?".
Fudhal yayi murmushi.
"Babu komai Kawu".
Murmushin sukayi dukansu yace.
"Yau dai muna fatan Doctor zai sallameka mu huta da mita kullum akan angaji da zaman
asibiti".
"Kawu ai gani nayi na warke sumul mai kuma zanyi anan?".
"Gaskiyarka babu abin da zakayi kuwa".
Yakai maganar tare da ƴar dariya.
Doctor ne ya shigo a bayansa Anwar ne suka gaisa Anwar ya nemi guri ya zauna yayin da
Doctor yahau duba Fudhal har sai da ya gama sannan ya dubi su Sarki Ubaiyd yace.
"Ga takardar sallama nan akula da maganinsa kuma sosai, Jaleel ma inaga zuwa gobe zamu
sallameshi".
Wani irin daɗi ne ya lulluɓe Fudhal har sai da farin cikinsa ya kasa ɓoyuwa.
Tuni Aunty Sa'ida da Hajiya suka miƙe suka hau haɗa kayansu, Anwar na kaiwa mota yana
sakawa har sai da suka gama kaf sannan suka fita zuwa harabar asibitin.
Anwar ne yayi driven ɗinsu Hajiya da Fudhal, su Abba kuma driver ne ya ɗaukesu.
Suna dosar layin suka fara jin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe na tashi na murnar dawowar Yarima
Fudhal.
Gidan cike dam-ƙam da al'umma sai kaiwa da komowa suke haka suka yi ta ratsa mutane ana
gaishesu suna amsawa har zuwa cikin fada Sarki Ubaiyd ya zauna Anwar da Fudhal suka wuce
ciki zuwa ɗakin Fudhal.
Suna shiga kai tsaye Fudhal toilet ya nufa domin ya watsa ruwa yana fitowa yahau shiri cikin
wata da kakkiyar farar shadda wadda tasha aikin zare light blue hular kansa da takalminsa har
zuwa agogonsa duk light blue ne ba karamin kyau yayi ba a wannan lokacin.
Anwar dai na kallonsa bai ce masa komai ba har sai da yagama sannan ya dube shi yace.
"Wai ina zaka haka kake ta faman shiri?".
Yarima Fudhal ya ɗan tsaya daga fesa turaren da yake ya dubi Anwar yana bashi amsa.
"Ina zanje wanda ya wuce wajen mata ta,".
Anwar ya sanya dariya yana faɗin.
"Tab..ai tuni ka makaro domin yanzu haka ana kan hanyar zuwa kaita gidan Aunty Sadiya ne.
Yarima Fudhal ya ajiye kwalbar turaren ya juyo gaba ɗayansa yana duban Anwar.
"Mai zatayi a gidan Aunty Sadiya kuma?".
"Wannan sai dai ka tambayi Hajiya kuma itace ta bada wannan umarnin".
Yarima Fudhal yayi tsaki take wata irin gajiya ta ziyarce taking yayi wurgi da hularsa bisa katifa
ya cire babbar rigar ya wurgar ya nemi guri kan katifar ya kwanta.
Anwar ya bishi da kallo kawai abin sosai ya bashi dariya amma sai dai ya kanne domin sanin
halin mutumin nasa.
Har akai kiran sallar maghriba yana nan kwance shi bai ma san sanda Anwar ya fice daga ɗakin
ba sai da ya buɗe idonsa sannan yaga baya nan.
Miƙewa yayi yayo alwala yayi sallah ya ɓata tsayin lokaci azaune yana addu'o'i tare da godewa
Allah.
Can ya miƙe ya nufi inda babbar rigarsa take ya sanya ya mai da hularsa ya sake feshe jikinsa
da turaruka ya ɗauki wayarsa ya kunna tare da key din mota ya fice daga gidan.
Akan hanya ya kira Anwar yana tambayarsa yana ina?, gashi nan zuwa, Anwar ya bashi amsa
da yana gidansu Saima, tsaki Fudhal yaja yana faɗin.
"Da maghribar nan me zakayi mata me zatayi maka?".
Dariya sosai Anwar yasa ka yana faɗin.
"Idan kazo zan baka wannan amsar ".
Ya kashe wayar, Fudhal ya ajiye wayar a gefansa yana mai ci gaba da kallon titi tuƙinsa yake a
nutse yayinda kira'ar sudes ke tashi kaɗan-kaɗan cikin motar.
Yana isa bakin gate yayi parking motarsa ya fito ya knocking ƙofar gidan mai gadin ya leƙo
ganin Fudhal yasanya shi buɗewa da sauri domin ya sanshi sosai.
Yana shiga ya kirashi yazo mintuna biyar sai gasu sun fito a tare da ka gansu kaga waɗanda
suka jiƙe a mayen so da kaunar junansu.
Duk da Saima yanzu Anwar take so kuma take burin aure Amma ganin Fudhal bai hana ƙirjinta
bugawa ba sosai taga yayi mata kwarjini fiye da koyaushe haibarsa ta ƙaru wani irin sihirtaccen
kyau na bayyana a jikinsa ganin kallon da take masa ya sanya shi kau da kai yana murmushi ya
dubi Anwar.
"Sai ka janyota jin gulma kuma?".
Saima tayi ƙarfin halin yin siririyar dariya, Anwar yace.
"To meye a ciki ?, abin da nan da sati muma zamu angwance gara tasan irin matsayinta a
wajena tun yanzu".
Yarima Fudhal ya gyaɗa kai kawai yana faɗin.
"Baka koya mata gaisuwa ba kenan?".
Saima tayi saurin faɗin.
"Barka da dare".
"Riƙe gaisuwarki bana buƙata".
"Kaga mallam sauri fa nake ka sallameta mu tafi kawai".
Saima ta danne ɓacin ranta kawai domin tasan halin Fudhal shi ba abin damuwarsa bane disga
mutum gaban kowa, hakan kuma ko a takalminsa bare abin ya dameshi kai da akayiwa sai dai
haushi ya kashe ka.
Anwar yace.
"Ai munyi sallama dama zuwa tayi ku gaisa kawai".
"OK mutafi to muna bata time, nagode Saima ki gaida su Mama".
Abin da yace kenan yana mai kama hanya ya fice daga cikin harabar gidan, Anwar yabi
bayansa yana ɗagowa Saima hannu itama ta mayar masa da martani.
Anwar ne yayi driven nasu har zuwa ƙofar gidan Aunty Sadiya yana parking Yarima Fudhal ya
fice daga motar baiko jira Anwar ɗin ba.
Gidan shiru kamar babu kowa sai da yayi sallama kusan sau biyar daga bakin ƙofar falon
sannan Aunty Sadiya dake can saman mijinta ta sauko tana amsa masa.
Ya shigo tare da neman guri kan kujera ya zauna yana tambayarta ƴan biyu.
"Suna ɗaki sunyi bacci ne".
Anwar yayi sallama ya shigo yana faɗin.
"Nagode Fudhal".
Ya juya gun Aunty Sadiya suka gaisa Fudhal dai baice komai ba illa baza ido kawai da yake can
dai ya kasa haƙuri yace.
"Ina Aynu take ne?".
Dubanshi Aunty Sadiya tayi tana faɗin.
"Ganin Aynu ba yanzu ba".
"Kamarya ba Yanzu ba?".
"E mana umarmi aka bani".
"Nasanma wasa kike nidai dan Allah tana ina?"
"Allah ba wasa ba, umarnin Hajiya da Abba ne".
"Ya Allah..!"
Yarima Fudhal ya furta yana mai dafe kai.
"Sai yaushe to ?".
"Sai nan da sati wato randa za'a kawo matar Jaleel ranar za'a kai maka taka kai ma".
Tsaki yaja mai tsayi tare da kwafa.
"Amma dai gaskiya ba'amin adalci ba inason ganin Aynu wallahi Aunty".
"Sai dai fa kayi haƙuri aikin gama ya gama".
Yarima Fudhal yayi shiru yana duban Aunty Sadiya da Anwar kawai yama rasa mai zai ce.
*YARIMA FUDHAL*
NA
FIRDAUSY S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
46
Nacin duniyar nan Yarima Fudhal yayi amma Aunty Sadiya tace bata san zancen ba, a kan
dole suka tattara suka bar gidan ba tare daya samu ganin Aynu ba zuciyarsa ta cika fam da
haushi.
Hakan yasa duk surutun da Anwar ke tayi masa a mota bai kulashi ba domin sosai yau
haushin kowama yake ji gani yake kamar ba sonsa suke ba.
Har suka isa gida Yarima Fudhal bai kula Anwar ba haka Anwar ɗin yayi masa sallama ya wuce
gida domin shi al'amarin Fudhal ma dariya yake bashi, idan yana abu wani time ɗin sai kaga
kamar wani ƙaramin yaron goye.
Anwar na fita Yarima Fudhal ya rage kayan jikinsa ya shige toilet domin watsa ruwa sabida wani
irin zafi da yake ji a lokacin, daya fito kaya ya nema marasa nauyi ya saka ya fice daga part
ɗinsu zuwa part ɗin Hajiyarsu wato Fulani Bingel.
Da sallamarsa ya shiga falon babu kowa ciki illa Hajiyartasu dake zaune tana kallon tashar Zee
world, ta jiyo cikin fara'a tana amsa masa sallamar.
Yarima Fudhal ya ƙarasa inda take zaune ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafuwanta yana faɗin.
"Barka da dare Hajiya?".
"Muna lafiya, ya ƙarin ƙarfin jikin naka?".
"Alhamdulillahi".
"Masha Allah..!, Ina kaje ne na shiga wajen naka baka nan?".
"E munɗan fita nida Anwar ne".
"Fita kuma?, daga fitowarka daga asibitin haka FUDHAL