Showing 57001 words to 60000 words out of 88612 words

Chapter 20 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

8385

ya taimaka".

Cewar fudhal kenan yana mai da kansa kan file d'in.

"Ni bari inkoma naga yau aiki kake sosai".

"Allah kiyaye".

Yarima ya bashi amsa ba tare daya d'ago kai ba, Anwar ya kama hanya ya fice daga office d'in.


DARE...!
8:30


Da dare misalin k'arfe takwas da rabi Anwar ne tsaye jikin motarsa cikin harabar gidansu
Saima, ya shafe tsayin mintuna goma kafin ya hango fitowarta cikin tafiyarta mai kama da
wacce bata son taka k'asa, har ta k'araso inda Anwar yake tsaye fuskarta babu yabo babu
fallasa .

Sallama tayi Anwar ya amsa mata, tad'an gaisheshi tare da tambayarsa gida da kowa, ya amsa
mata da "Duk suna lafiya, suna gaishe ki".


"Ina amsa kuwa".

Cewar Saima kafin shiru ya ziyarci wajen har na wasu 'yan dak'ik'u, Anwar ya katse shirun da
fad'in.


"Ina son sanar da ke wata magana amma ina fatan bazaki min mummunar fahimta ba?".

"E insha Allah, fad'i inajinka".

Saima ta bashi amsa agaggauce, Anwar ya cigaba da fad'in.

"Gaskiya Saima nazo wajenki ne ba dan soyayyar gaskiya ba, na zo ne kawai domin injanye
ra'ayinki daga kan Yarima Fudhal kuma tare da umarninsa na zo, domin baya son aurenki da
shi kamar yanda baya son auransa da Safiyya".

Zuciyar Saima sai da ta buga daga jin wannan zance cike da mamakin jin maganar Saima take
bin Anwar da kallo, kafin Anwar d'in ya cigaba da fad'in.

"Amma sai dai tunkafin aje ko ina na kamu da soyayyarki da gaske Saima ina fatan zaki
fahimce ni ku...!".

"Kaga dakata Anwar ...!".

Saima ta katse shi cike da b'acin rai kafin ta bud'e baki ta hau fad'in.

"Na fahinci komai Anwar na fahimta, wato ka zo ka yaudare ni ka rabani da wanda nake so da
gaske sannan kai kuma ka kama hanya katafi kabarni...uhmm to da kyau hakan nagodewa
Allah daya ganar dani gaskiya tun yanzu, amma kafin nan inaso kayi gaggawar barin harabar
gidannan tun kafin insa a fid da kai".
"Amma Saima...!".

"Nace ka tafi karabu dani babu wata kalma da zan tsaya ji daga bakin ka !".

Anwar kai ya girgiza kawai tare da kunna motarsa ya shige yabar harabar gidan, yana tafiya
Saima ta zube a gun cike da matsanancin kuka, kafin ta koma gida aguje bata tsaya ko ina ba
sai kan gadonta ta fad'a tana mai cigaba da ruggar kukanta.

K'arar hon d'in motar da yaji daga bayansa ne ya sanya shi dawowa daga tunanin da yake,
murmushinsa yak'ara falala saman fuskarsa domin ko babu komai yana ji a ransa wani abin
alkhairi ne zai fari tsakaninsa da Saima.

Bai tsaya ko ina ba sai cikin harabar gidansu Saima, ya kashe motar ya fito tare da zaro
wayarsa daga cikin aljihun wandonsa ya fara neman numberta domin ya sanar mata cewa ya
iso.


Mintuna kad'an sai gata ta fito tana takunnata data saba wanda yazame mata jiki a yanzu,
Anwar binta yayi da kallo cike da so da k'auna harta k'araso gareshi fuskarta fal murmushi
sab'anin lokutan baya daya saba zuwa.

Gaishe shi tayi ya amsa tare da fad'in.

"Gani gareki na amsa kiran ki".

Murmushin kan fuskarta ya k'ara fad'ad'a kafin ta ce.

"Mu shiga daga ciki to".

Tana fad'in haka tayi gaba ya bita abaya kamar rak'umi da akala yau ya cika da mamakin Saima
sosai domin yaune karo na farko da tayi masa iso cikin falon saukar bak'i.

Suna isa tayi masa nuni da kujera ya zauna, sannan itama ta zauna table d'in gabansu cike
yake da kayan marmari(Fruit) dasu juice kala-kala, Saima ta zuba masa juice a cikin d'aya daga
cikin kofunan glass d'in da ke kan table d'in.

Ya karb'a yasha har lokacin binta yake da kallo kamar yanda itama har lokacin murmushin kan
fuskarta bai gushe ba.

Gyaran murya tayi tare da sadda kanta k'asa tana wasa da yatsun hannunta ta bud'e baki
ahankali ta fara magana.


"Bansan ta inda zan fara ba Anwar, amma hak'ik'anin gaskiya na yarda da maganarka nayi
godiya da Allah sosai daya ganar dani gaskiyar Yarima Fudhal baya sona tun kafin ayi aurena
da shi, a ranar da ka barni har zuwa kwanakin da suka shud'e nayi kuka sosai tare da addu'a
akan zab'in Allah sai dai zuciyata da hankalina sunfi aminta da kai".

Anwar yayi ajiyar zuciya yana mai gyara zama sosai yake jin dad'in kalaman da take har baiso
daka tawarta ba, Saima ta cigaba da fad'in


"Bazan b'oye makaba naso Fudhal sosai a rayuwata Anwar, a dalilin sonsa nayarda na zamo
baiwa a gareshi domin kawai samun soyayyarsa, sai dai duk da haka ban samu abin da nake
so ba, hakan ya saka har asibiti na kwanta Abbana yayi binciken abin da yake damuna Momy ta
sanar masa shine dalilin da yasa yaje wajen Mai Martaba domin Yarima ya aure ni sabida
soyayyar da yakemin ni kad'aice 'ya a gareshi basa fatan su rasani suna son dukkan abin da
nake so kamar yanda suke k'in dukkan abin da nake k'i, ban samu lafiya ba har sai da naji cewa
Mai martaba ya yarda Fudhal ya aure ni duk da cewa mu biyu zai had'a amma hakan bai
dameni ba domin ina ganin indai zansamu abin da nake so Alhamdulillahi".

"Amma a yanzu na gayawa Abbana kai ne wanda nake so zan aura, na hak'ura da Fudhal
nasan shi ba mijina bane har abada".


"Kenan ke ce Saima wadda ke zuwa yiwa Yarima aiki, kuma kece Saima da kikaje wajen
Birthday d'insa?".

Anwar ya jera mata dukkan wad'annan tambayoyi lokaci guda, wani guntun murmushi tayi tare
da had'iyar wani yawu mai d'aci kafin ta bashi amsa.

"E duk nice Basaja ce kawai nayi domin samun cikar burin raina".

"Har yanzu kina son sa?".

"Ada dai zuciyata ta Yarima ce, amma a yanzu taka ce".

Tayi maganar tana mai rufe fuskarta da tafukan hannunta, wani sanyi dad'i ya tsarga dukkan
ilahirin sassan jikin Anwar, da sauri ya mik'e daga inda yake zaune ya koma kusa da ita yana
fad'in.

"Da gaske kike Saima?".

Kai kawai ta gyad'a masa domin a wannan lokacin muryar da yayi amfani da ita wajen
tambayarta baki d'aya ta kashe mata lakar jiki.



***

Zaune yake cikin falon Fulani Bingel ya takure waje guda ya sanya kansa cikin cinyoyinsa
tamkar wani k'aramin yaro, Fulani ce ta fito daga cikin d'akinta ta ganshi a haka da sauri ta
k'arasa gunsa ta dafa shi tana fad'in.


"Yadai Magaji lafiya kake kuwa?".

Yarima ya d'ago fuskarsa data jik'e sharkaf da hawaye.

"Subhanllahi...Magaji mai ya faru?".

"Hajiya Aynu ce...! ki taimaka kada ta auri wani dan Allah, wallahi zuciyata zata iya bugawa a
kanta...!".

Fulani ta zaro ido waje tana bin Yarima Fudhal da kallaon mamaki kafin ta girgiza kai tana
fad'in.


"Mai yasa baka iya sanyawa zuciyarka hak'uri da salama ba Magaji, ka fauwalawa Allah komai
kayi addu'a idan Aynu matarkace tabbas saika aureta, idan kuma ba matarka bace kome
zamuyi bazaka tab'a aurenta ba, bahaushe yace matar mutum k'abrinsa kuma mahak'urci ai
mawadaci ne Magaji dan Allah ka share hawayenka kamar ba namiji ba?".
Yarima Fudhal kai kawai ya girgiza ko kad'an maganganun Fulani basuyi ta siri aransa ba
domin shi kada'ai yasan mai yake ji a cikin zuciyarsa.


B'alle boturan rigarsa yayi ya kamo hannun Fulani ya d'ora dai-dai saitin zuciyarsa yana fad'in.

"Kinji fa Hajiya zuciyata zata fashe Hajiya kiyi wani abu dan Allah".

Kafin Fulani tayi wani yunk'uri hawaye yafara bin kan kuncinta domin yanda taji zuciyar Yarima
na bugu tare da wani matsanancin zafi da k'irjinsa ya d'auka sosai ta tsorata ainun ido waje take
kallon Fudhal ba tare data iya cewa komai ba.

*YARIMA FUDHAL*



Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-Namesy Phirdausy Jeebour.




Kuyi hkr dan Allah nayi mistake d'in number ne mai makon insaka 33 sai na sake mai maita 32
a wancen page fatan zaku fahimce ni nagode sosai.



34




Zaune yake bisa d'aya daga cikin kujerun falon, gabansa centre table ne cike da kwalaban
giya kusan guda biyar gefensa kuma Shisha ce sai karan sigarin dake rik'e bisa hannunsa yana
zuk'a lokaci-lokaci.

Idan ya zuk'i sigarin sai ya kora da d'aya daga cikin kwalaban giyar kamar wani tab'ab'b'e.

Tsaki yaja yana mai kashe karan sigarin ya jawo Shisha yahau sha, kafin ya mik'e tsaye yana
maiyin ball da shishar tare da d'aga centre table d'in baki d'aya kwalaban giyar suka rotse hatta
table d'in ba'abarshi abaya.

Juyawa yayi gefansa ya d'au wata giyar dake gefansa itama ya had'ata da bangon d'akin take
ta fashe ruwan giyar na bin bangon.


Komawa yayi ya zauna yana mai cusa hannunwansa biyu cikin sumar kansa yana sosawa
tamkar wani mahaukaci sabon kamu, duk wanda ya ganshi a wannan lokacin cikin wannan
yanayin dole ya tsorata da shi.

"SAFIYA....!".

Abinda ya furta kenan cikin ihu da k'araji badan babu kowa a harabar ba da babu abin da zai
hana mutane shigowa wajensa da gudu.

Mik'ewa yayi cike da layin giya ya nufi hanyar fita daga falon ko takalmi babu a k'afarsa, duk
inda ya wuce sai anbishi da kallo sabida yanda yake layi da had'a hanya, bai tsaya ko inaba sai
cikin falon Fulani Sokoto yana Shiga ya zube bakin k'ofa.


Fulani da muk'arrabanta dake zaune falon sukayo kansa suna fad'in.

"Subhanallahi....! lafiya Yarima Jaleel?".

Kama bango yayi yamik'e ba tare da yace dasu komai ba, Fulani na ganin haka ta fahimci halin
da yake ciki, umarni ta bawa kowa ya fice aka barta daga shi sai ita sai kuma Jalilah.


Kamo hannunsa tayi takaishi tsakiyar falon ta zaunar dashi tare da jinginashi da jikin kujera
kafin ta koma ta zauna tana mai binsa da kallon takaici.

Kafin tamik'e tsaye tana faman safa da marwa Jalilah kuwa sai bin Fulani da Jaleel take da
kallo.

Can Fulani ta koma ta zauna tare da sakin wata irin ajiyar zuciya kafin ta bud'e baki ta fara
magana.


"Haba Jaleel har yaushe ne zakayi hankali?, yaushe ne zaka nutsu kasan ka girma?, mai yasa
kake k'ok'arin ganin ka b'ata gobenka ne?".

"Kullum fad'i tashin da nake akanka ne, ina tufka kana warwara haba Jaleel ka nutsu mana ko
ka samu ka cikamin burina Jaleel".

Duk surutun da Fulani take Jaleel kawai binta yake da kallo amma a zahirin gaskiya ko kad'an
maganganun basa tasiri a kwakwalwarsa.

A hankali ya bud'e baki yana fad'in.

"Naji Momy zan daina amma ki taimaka ki auramin wacce nake so nima dan Allah".


Dogon tsaki Fulani taja tana fad'in.

"Au dama akan mace kake son ruguzamin burina Jaleel?, akan mace kake neman b'atawa
gobenka", wace ita? fad'amin ko wacece ni kuwa duk yanda zanyi sai na aura maka ita indai har
zansamu cikar burina Jaleel".

"Safiya ce ! Momy ita nake so".

"Safiyya kuma ! wacce kenan?".

"Gimbiya Safiyya Momy".

A razane Fulani take bin Jaleel da kallo cike da rud'u da tashin hankali, ba Fulani ba har Jalilah
dake zaune gefe tana jinsu ta girgiza dajin batun da Jaleel yazo da shi.


"Jaleel kana cikin hankalinka kuwa?".

"E Momy nidai ita nake so, idan na rasata zan iya rasa rayuwata Momy".

"Amma dai ina kasan angama magana Fudhal zata aura".


"Nasani Momy amma tun farko nine nake sont.....!".

Bai kai ga k'arasa maganarsa ba sai jin k'arar saukar maruka yayi a duka kuncinsa guda biyu,
cikin firgici ya dafe fuskarsa yana bin Fulani da kallo bai kuma magana ba yami'e cikin layi ya
fice daga falon.


Fulani ta koma kan kujera tazub'e dab'as zuciyarta na suya da k'una akan maganar da Jaleel
yazo mata da ita yanzu har ace yau Jaleel ne take fad'a yana fad'a.

"Meke faruwa ne?".

Abin da ta furta kenan cikin ranta da sauri ta mik'e tsaye kamar antsikareta duban Jalilah tayi
tana fad'in.


"Maza jeki saka a kirawon Larai...au namanta kefa baki da baki yanzu".

Takai maganar tare da jan tsaki, mik'ewa tayi ta fice daga falon tabar Jalilah zaune.


Kwance yake kan carpet ya d'ora kansa bisa kusun idonsa a lumshe kamar mai bacci amma a
zahiri ba baccin yake ba, domin daka kalli gefan idonsa ruwan hawaye zakaga yana fita
lokaci-lokaci, can ya mik'e zumbur kamar antsikareshi yana mai dafe kansa da yake sara masa
d'aga kai yayi ya dubi agogo lokacin k'arfe tara na dare 9pm.

Toilet ya nufa ya wanke fuskarsa yana fitowa yayi waje zuwa harabar gidan, yana tafe
zuciyarsa na cigaba da tsananta bugu amma duk da haka ya d'aure harya k'arasa bakin k'ofar
falon da sallamarsa yasa kai cikin falon ba tare daya nemi iso ba.


Mai Martaba na kishingid'e a falo yaji sallamar Fudhal d'in tare da shigowarsa, murmushi ya
fad'ad'a a fuskarsa Mai Martaba yamik'e zaune yana fad'in .


"Zonan zauna Magaji, kamar kasan yanzu nake zancen insaka a kirawomin kai".


Yarima Fudhal yayi k'ok'arin nemo murmushi ya d'ora a kan damuwar dake kan fuskarsa, ya
durk'usa ya gaishe da Mai Martaba tare da gyara zama danjin mai zai ce.


Gyaran murya Mai Martaba yayi yana fad'in.


"Munyi magana da Iyayen Saima sunce sun janye maganar aurenka da 'yarsu, sannan kuma
muntsai da bikinka kai da Safiyya nan da sati biyu masu zuwa hakan yayi maka ko a k'ara?".


"Duk yanda kukayi dai-dai ne Abba, amma ina da 'yar magana akan batun auren".

"Babu damuwa ina jinka fad'i".


"Abba ka taimaka dan Allah bawai zanyi jayayya da kai bane na yarda zan auri Safiyya amma
ka yarjemin in auri Aynu dan Allah Abba".

Mai Martaba bin Fudhal yayi da kallo kawai yana gyad'a kai kafin yayi murmushi yana mai
fad'in.


"Nima a matsayina na Mahaifinka zan umarceka da abu guda d'aya a yau koda bayan raina
kada d'ayanku yayi gangancin had'amin zuri'a da talaka !".

Cike da mamaki Fudhal yake bin Mai Martaba da kallo yarasa wacce irin k'iyayyace Abban
nasu keyiwa talaka haka?, ya bud'e baki zaiyi magana kenan sai ganin fad'owar mutum sukayi
cikin falon.

Jaleel ya tako da Sauri ya zube gaban Mai Martaba tare da kama k'afarsa yana fad'in.

"Dan Allah Abba kada ayi auren nan wallahi Abba nine nake sonta Momy ce tace kada nafad'a
inbari a aurawa Broda".


"Kai lafiyarka kuwa?, akan wa kake magana ne?".

"Gimbiya Safiyya Abba itace wadda nake so dan Allah Abba a auramin ita ni nafi dacewa da ita
ba Fudhal ba".


Mai Martaba mik'ewa yayi tsaye yana mai bin 'ya'yan nasa da kallo kafin ya koma ya zauna
yana fad'in.


"Wato kuna so kumai da ni k'aramin mutum ko?, mai yake damun kune?, kai da nake ganinka
mai hankali Magaji ashe kallon kitse nakewa mai?".


"To kutsaya kuji ni da kyau ko bayan raina babu kai babu auren 'yar matsiyatarnan Magaji
aurenka da Safiyya kuma babu fashi, kai kuma Jaleel ko zaka mutu bazan tab'a canja
maganata ba akan ka dai, yaushema kake da hankalin da zanyi maka aure yanzu kana tunanin
duk abin da kake aikatawa bani da masaniya a kai?, Ku tashin kuficemin daga nan kada insake
jin Wanda yazomin da makamanciyar irin wannnan maganar".


"Ku b'acemin daga nan nace...!".

Yayi maganar cikin tsawa ba shiri suka mik'e suka fice kowannansu zuciyarsa cike k'una da
b'acin rai.


Babu wanda ya tankawa wani har suka isa part d'insu kowa ya nufi d'akinsa.

Yarima Jaleel dai yana shiga d'aki fridge ya nufa ya d'auko kwalaban giyarsa yahau sha babu
ko k'ak'k'autawa bare yayi tunanin zata iya illata shi.


Fudhal kuwa yana shiga d'akinsa kwanciya yayi bisa katifarsa yana juyi yayin da zuciyarsa ke
cigaba da tsananta bugu tare da zafi.

Har kusan k'arfe biyun dare amma al'amarin nasa babu sauk'i sai da takai takawoma juyinma
da k'yar yakeyinsa.

Jiyayi amai na taso masa da rarrafe ya shige toilet amma sai aman ya koma, nan yayi k'arfin
halin mik'ewa yana dafa bango har ya fito daga toilet zuwa tsakar d'aki anan ya yanke jiki ya
fad'i numfashinsa na fita sama-sama.




Hello

My luvly fans
Har yau dai bazan gajiya da baku hak'uri ba, abubuwane suka rik'eni amma yanzu alhmdlh
insha Allahu indai ba wani uzuri mai k'arfi ba kullum zaku dinga samun post nawa da yardar
Allah har Allah ya nunamin inkammala muku ngd sosai masu call & message kuma raina iya
wuya ana tare.

Bissalam

*YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


SADAUKARWA:-Namesy Phirdausi Jeebour.



35



5:00AM


Har aka kira sallar asuba Yarima Fudhal yana ji amma ya gagara tashi wayarsa dake can kan

katifa sai faman ringing take yi har tagaji ta katse.


Fulani Bingel na shirin shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login