Showing 69001 words to 72000 words out of 88612 words

Chapter 24 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

8403

bi
hankalinsa kwance kai kace babu abin da yake damunsa a duniya, sai dai ƙasan zuciyarta
cunkuce take da tarin damuwa da tunanin abin da zaije ya tarad duk da cewa yana yiwa kansa
fatan alkhairi tare da saran samun nasara domin yasan aikin alkhairi yake shirin aikatawa bare
kuma al'amari na zumunci Allah zai bashi nasara.

Ko da ya isa cikin Sokoto birnin shehu ya shafe tsayin a wanni hudu yana fafutuwar neman
Magaji Saif kafin Allah ya haɗashi da wani al'amajiri mai wanki da guga shine yace ya sanshi ai
shi yake bawa wanki da guga duk sati, gidansa a can (kalan baina) yake yazo suje ya rakashi.

Haka suka tafi yaron na nunawa Anwar hanya shi kuma yana bi har zuwa bakin gate ɗin wani
tamfatse-tsen gida sukayi hon gateman ya buɗe ƙofar wangagememan gate din gidan suka
sanya kai.

Almajirin yace wa Mai gadi ya sanarwa Alhaji yayi baƙo, ba musu Mai gadin ya wuce cikin gidan
da sauri domin sanarwa ahaji dake yasan almajirin sosai, mintuna kaɗan sai gashi ya dawo
tare da amsar su shiga yana jiransu.

Su Anwar suka sanya kai zuwa cikin gidan, shi dai Anwar kallon gidan kawai yake domin yasan
ko a turai da yayi karatu bai taɓa ganin gida mai girma da haɗuwa kamar wannan gidan ba,
faɗin haduwar gidanma ƙauyanci ne sai dai masu karatu ku ƙiyassata a cikin ranku.

Yana zaune falo kan wata luntsumemiyar kujera 'yar ubansu shaddar dake sanye jikinsa ita
kanta kukan kuɗi take bare kuma azo batun takalmi da hula zuwa uwa uba agogon hannunsa,
yana zaune a hannunsa kuma news paper ce yake karanta sukayi sallama ya ɗago kai cike da
fara'a yana mai amsa musu.
Tsan-tsan kamar Sarki Ubaiyd da Anwar yagani a tare da fuskar Magaji Saif shine abin da ya
daure masa kai ainun ya kuma tabbatar tabbas wannan shine Magaji Saif yayan Sarki Ubaiyd.

Suka gaisa Anwar yayiwa almajirin godiya tare da alkhairi mai yawa ya tashi ya tafi.

Yana fita Magaji Saif yabi Anwar da kallo yana faɗin.

"Sai dai ban shaida fuskarka ba, ko zaka iya yimin bayanin waye kai?, mene kuma ya kawoka
gidan nan?".

Anwar yayi murmushi kafin yace.

"Abu mai sauƙi dama hakance ta kawo ni".

Nan take Anwar ya fara bashi amsar tambayarsa dalla-dalla tare da faɗin abin da ya kawoshi da
kuma dalilin zuwansa.

Magaji Saif ya haɗe girar sama data ƙasa tamkar bashi ne yake murmushi ba yanzu sai kace an
aiko masa da saƙon mutuwarsa haka ya miƙe tsaye yana mai mid zuwa wajen Anwar tuni
hantar cikin Anwar tahau kaɗawa tsoro ya ziyarceshi take ya fara karanto addu'a cikin ransa
domin ya gama hasko irin cin mutunci da tozarcin da zai fuskanta yau a hannun Magaji Saif.

KOMA DAI MENENE KU BIYO NI........! Smile kuna raina fa.

Nagode sosai da sosai da ɗunbin tarin addu'arku a agare ni Allah ya biyaku amin.

*YARIMA FUDHAL*





Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITWRS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-NAMESY PHURDAUSY JEEBOUR.




40







Ganin yanda Magaji Saif yake nufoshi, shine yayi sanadiyyar miƙewarsa tsaye a kasalance
suna duban juna ido da ido amma duk da hakan Anwar baiyi ƙasa a gwiwa wajen cigaba da
karonta addu'o'i ba a cikin ransa.


Har sai da Magaji Saif yazo daf da Anwar suka shafe tsayin lokuta suna kallon juna ko
wannensu da abin da yake saƙawa cikin a cikin ransa.


Sai dai abin da Anwar yaga Magaji Saif ya aikata ne yayi sanadiyyar tsayawar wayoyen jikinsa
da dena aiki take lantarkin dake sarrafasu ta ɗauke, murza ido ya hauyi domin tabbatarwa

gaske ne ko a mafarki ne?, Magaji Saif ya rungume shi har yana ɗan bubbuga bayansa...!.


Maganar Magaji Saif ita tayi sanadiyyar dai-daituwar kwakwalwarsa.


"Tabbas munyi kuskure a rayuwa nayi nadama bayan wani lokaci, ka sani yau tsayin shekaru
ina zaman jirar ranar da zanga wani ya zo nemana, sai gashi Allah ya amsa roƙona a yau lallai
dole inyi farin ciki tare da godewa Allah a yau ɗinnan".


Anwar dai sosoko yayi yana sauraransa, Magaji Saif ya janye jikinsa daga na Anwar fuskarsa
cike da murmushi haɗe da hawayen farin ciki, ya cigaba da kallon fuskar Anwar.


Anwar yaɗanyi gyaran murya tare da buɗe baki ya fara magana.


"Amma mai yasa baka je ka nemi ahalinka ba tare da neman gafararsu tasayin wannan lokaci
ka zauna sai dai a zo a nemeka, ko kasan cewar Mahaifiyarku ta rasu?".


"Na sani...!"


Jin amsar daya bayar ya sanya Anwar sakar baki yana dubansa, Magaji Saif yayi murmushi
tare da kama hannun Anwar ya zaunar da shi kan kujera shima ya koma Inda yake da ya zauna
tsayin da ƙiƙu yana ƙarewa Anwar kallo kafin ya ci gaba da magana.



"Ina gudun wulakanci da tozarci ne shine yasa naƙi baiyana kaina a wajen ƙanina amma batun
jana'idar Hajiyarmu tare dani akai hatta zaman makoki nayi dukkan wani motsi na gidan babu
Wanda ban sani ba, sai dai abubuwa da yawa suna ɗauremin kai akan Ubaiyd".


Yaɗan ja numfashi kaɗan.

"Yaushe ne Ubaiyd yazama azzalumin sarki?, taya akai ya zama mai girman kai da izgili?
tarbiyar iyayenmu babu wulakantar da ɗan adam, amma ina mamakin yanda akai Ubaiyd ya
koyi wasu irin munanan halaye ya sanyawa kansa alhali nasan a da ba haka yake ba, ko kuma
Sarautace ta koyamai hakan?".

Duk wannan tambayoyin da yake jerewa Anwar kawai kallonsa yake yana kuma sauraronsa.


"A sanda nabar gida na tafi ne tare da burin komai daren daɗewa sai na gaji mahaifinmu nayi
sarauta, amma akan Ubaiyd naji na tsani sarauta indai haka sarauta take mai da mutum mai
munanan halaye bazan taɓa addu'ar Allah ya sake bawa wani jinina ba kai ko barema domin
wannan halayen sune matsayin kuɗin siyan wutar jahannama sune za suyi sanadiyyar sayar
mana fushin Allah da Manzonsa...! UBAIYD.! UBAIYD..! UBAIYD...! Me yasa haka?, me yasa?".


Ya kai maganar cike da ƙaraji yana huci harda bugun centre table ɗin dake gabansa.


"Kayi hakuri Abba, amma nake ganin babu abin da yake sayawa ɗan Adam munanan halaye
sai dai idan dama can halinsa ne dake ɓoye cikin ransa to idan mutum ya samu wata dama ko
wani muƙami sai hakan ya dinga bashi ƙarfin gwiwar aikatawa tunda yana tunanin babu Wanda
ya isa ya hanashi bare a taka masa burki".

Magaji Saif kai ya gyaɗa yana faɗin.


"Haka ne maganarka kayi gaskiya Anwar, yanzu ya jikin Fudhal?".

"Alhamdulillahi Abba".


"Masha Allah sai ka kwana anan zuwa gobe da safe idan Allah ya kaimu zan nemi hutu a in da
nake aiki sai mu tafi can ɗin".


"OK Allah ya kaimu".

Anwar ya faɗa yana mai ƙarewa falon kallo duk hotunan Magaji Saif ne cike a falon ya baza ido
iya bazawa baiga hoton ɗa ba bare na wata mace.


"Abba nace Yaran gidan sunyi tafiya ne?".

Anwar yayi tambayar dai-dai sanda Magaji Saif ya isa wajen freezer domin kawo wa Anwar ɗan
lemo.

Magaji Saif yayi murmushi kawai ya ɗauko juice na kwali da cofi ya kawo gaban Anwar ya a jiye
yana maganar.


"Babu kowa a gidan nan babu mace taya za'a samu yara?, daga ni sai kukuna sai mai gadi
mukenan a gidan".


"Matarka mutuwa tayi ne Abba?".


Magaji Saif ya girgiza kai yana duban fuskar Anwar har lokacin murmushin dake kan fuskarsa
bai ɗauke ba.


"Ban taɓa aure ba Anwar amma a kullum ina son yi, yanzu ga ɗaki can ka shiga kayi wanka ka
huta anjima ka fito daining ni zan shiga ciki".


Ya miƙe yahau saman bene yabar Anwar nan zaune yana jujjuya maganar Magaji Saif.

"Ban taɓa aure ba Anwar amma a kullum ina son yi..!".


Ya sake mai-maita maganar.


"To amma mai yahanashi yi?, duk da gashi bai rasa komai ba a duniya, ko da yake aure nufi ne
na Allah".


Yayi tambayarsa ya bawa kansa amsa.


Juice ɗin ya buɗe ya zuba a cofin yaɗan sha kaɗan kafin ya miƙe ya nufi ɗakin da Magaji Saif
ya nuna masa.


Ɗakin komai akwai ciki hakan ba ƙaramin daɗi da mamaki yayiwa Anwar ba, kayansa ya cire ya
faɗa toilet domin yin wanka.

Yana fitowa dama yayo alwala da yake lokacin sallar maghriba yayi ya sanya jallabiya yayi
sallah yana idarwa ya jawo wayarsa yahau neman number Hajiyarsu Fudhal.


Kira ɗaya ta aga tare da sallama, Anwar ya amsa yana faɗin.


"Na samu gidansa Hajiya goben nan zamu taho tare da shi".

"Kana nufin kace ka sanar dashi komai amma ya yarda zai biyoka cikin sauƙi haka?".


"Hajiya kenan kin manta da ƙarfin fauwalawa Allah komai da addu'a kuma?".


"Hakane Allah ya kaimu goben lafiya muna zaman jiranku Allah ya kawo ku lafiya".

"Amin Hajiya ya jikin Fudhal fa?".


"Da sauƙi Anwar yau dai ansamu ya iya motsa yatsun hannunsa dana kafa amma bai buɗe ido
ba".


"Kai..Amma naji daɗi wallahi idon ma da yardar Allah zai buɗe Allah ya ƙara lafiya".


"Amin ya Allah sai da safe".


Suka kashe wayar a tare yana ajiye wayar akayi knocking ya amsa a shigo.

Wani saurayi ya leƙo yana faɗin.

"Komai ready Yallaɓai na jiranka a daining".

"OK ganinan".

Saurayin na juyawa Anwar ya biyo bayansa.


Daining cike taf da abinci kala-kala haka suka ci suka ƙoshi sunayi suna hira jefi-jefi duka hiran
akan Yarima Fudhal ne.

Magaji Saif yayi murmushi yana faɗin.


"Shi kuma sai da yaje ya ɗebo wannan zafin ran na banza ko?".

Anwar shima murmushin yayi ba tare da yace komai ba, suna gamawa Magaji Saif yayiwa
Anwar sai da safe ya hau sama, shima Anwar ɗin bai wani zauna ba ya koma aki ya ɗan huta
domin ya gaji.



*WASHE GARIN RANAR DA SAFE*


Hayaniyar ce tayi sanadiyyar ta shinsa daga baccin, yana buɗe ido yaga ashe gari ya waye
time ɗin 8:20, dafe kai yayi tare da miƙewa daga kan gadon ya zuro ƙafarsa ya sauko ya nufi
bakin windown ɗakin dan ganin hayaniyar tame ce take tashi haka?.


Jama'a ya gani cikin harabar gidan damƙam, Magaji Saif na zaune kan kujera gefansa kuma
buhu ne na kuɗi sai kayan abinci katan-katan na taliya da makaroni indomie da couscous ga
kuma manyan buhunan shinkafa nan ajiye yana ta rabawa mutanan Anwar abin ya ƙara ɗaure
masa kai ya shafe tsayin lokuta yana kallo kafin ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya
fita daining ya tadda komai is ready yayi breakfast.
ya koma ɗaki ya duba ta window yaga babu kowa kamar anyi shara maganar da yaji ne ta
bayansa yasa shi juyawa da sauri murmushi sukayi a tare Anwar ya durƙusa ya gaishe shi ya
amsa tare da shafa kansa yana faɗin.


"Harka tashi ka shirya?".

"E nagama komai, Amma Abba zakka kayi ne?".

"A a alƙawari na cika".

"Alƙawari kuma na me fa?".

"Duk ranar da Allah ya kawo wani nawa na alƙawaranta cewa zanyi sadaka ta musamman
domin nuna godiya ga Allah".

Anwar yayi murmushi tare da jin daɗin kyawawan halayen Magaji Saif har yana rayawa a cikin
ransa dama ace shine ya haifi Yarima Fudhal.



Helloooo...!


Kuyi hkr da wannan sai gobe idan Allah yakaimu da rai da lafiya zaku jini insha Allah.



Byeee

*YARIMA FUDHAL*




Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


SADAUKARWA:-NAMESY PHIRDAUSY JEEBOUR.







41



11:42am

Suka yi parking motarsu a parking space dake cikin harabar asibin.

Kai tsaye Anwar ya yi musu jagowa har zuwa cikin ɗakin da aka kwantar da Yarima Fudhal.

Lokacin Sarki Ubaiyd na zaune kan ɗaya daga cikin fararan kujerun dake ɗakin kansa na ƙasa
Wanda hakanne zai tabbatar maka da cewar ya faɗa cikin wani zurfaffan tunani ne.

Gefe guda kuma Fulani Bingel ce tare dasu Aunty Sadiya sai ƴan biyunta dake kwance kan
carpet ɗin ɗakin sunata haura-hauransu sunyi ɓulɓul abinsu gwanin ban sha'awa.

Anwar ne ya fara turo ƙofar ya shigo cike da sallama sannan Magaji Saif ya biyo bayansa.

Ba Fulani Bingel ba hatta Sarki Ubaiyd bai San sanda ya mƙe tsaye ba sabida jin muryar
mutumin da ko a mafarki bai taɓa tunanin zai sake jin ta ba.


Sai kuma gashi yau har suna ido biyu da juna kallon kallo aka hauyi tsakanin Magaji Saif da
Sarki Ubaiyd .

Abin da basu taɓa zata da tunani ba shine ya faru wato hawaye a cikin idanun Sarki Ubaiyd
amma kuma sun kasa tan-tance shin na farin ciki ne kona me?.


Sarki Ubaiyd ya taka ƙafafuwansa cike da sassarfa har zuwa inda Magaji Saif yake tsaye baiyi
wata-wata ba kawai ya rungume shi yana faɗin.


"Kaine Yaya?, a she zan sake ganinka?, a she da rabon zamu sake ganawa a duniya?, kayi
haƙuri ka gafarce ni nasan nayi kuskure a rayuwata...".


"Aa kabar faɗin haka.!".

Magaji Saif ya katse shi yana mai ci gaba da faɗin.

"Ni ne mai laifi kuma tuni nayi nadama na yafe maka fatana Allah ya yafemu baki ɗayanmu".

Ya kai maganar yana mai ɗan bub-buga bayan Sarki Ubaiyd.

Baki ɗayansu suka amsa da "Amin" kowanne daga cikin su yana matse kwallar data taru gefan
idonsa.


Sarki Ubaiyd ya bawa Magaji Saif kujerar da yake zaune shi kuma ya nemi guri a ƙasan carpet
ya zauna, Magaji Saif yayi nacin ya koma kan ɗaya daga cikin kujerun ya zauna amma yaƙi.

Nan aka gaggaisa Magaji Saif yana tambayar masu jiki kafin ya dawo da kallonsa kansu
Fulani Bingel.

"Kudan bamu waje".

Ba musu dukansu suka fice suka bar Magaji Saif da Sarki Ubaiyd sai Yarima Fudhal Mara lafiya
da yake can kan gado kwance.

Suna fita Magaji Saif ya dubi Sarki Ubaiyd ya fara magana cikin tattausan harshe ya kira
sunansa.


"Ubaiyd..!".

Sarki Ubaiyd ya amsa.

"Na'am Yaya".


Magaji Saif ya ci gaba da maganarsa.


"Naji komai a bakin Anwar sai dai ka bani mamaki sosai Ubaiyd a ce kamarka kana aikata irin
wannan abin da girmanka da komai da tunanika haba Ubaiyd ya kake nema giyar mulki tayi
rinjaye akanka har kana neman salwantar da rayuwar jininka har guda biyu".

"Idan ka manta ni zan tuna maka, da talaka da mai kuɗi basu da wani banbanci a gurin Allah sai
Wanda yafi tsoron Allah ya inganta lahirarsa, bazan tsaya dogon surutu akanka ba domin
kuskure ne anriga an aikata sai dai a kiyayi gaba".

"Sannan abin da ya kawo ni idan har na isa da kai kuma haryanzu ina nan a matsayin Yaya a
gareka inaso a yau ɗin nan dani da kai zamuje gidansu yarinyar da Fudhal yake so ayi magana,
kuma batun auren mata biyu ka a jiyeshi gefe shi kuma Jaleel shima a bashi wadda yake a
zauna lafiya".
"Amma Yaya...!".

"A a Ubaiyd wannan Umarni ne ba shawara ba idan har kaji ka yarda to, idan kuma baka yarda
ba zaka nunamin ban isa ba ga hanya nan yanzun nan zan tashi inkoma Inda na fito".

Sarki Ubaiyd yayi shiru tsayin wasu lokuta baice komai ba, haka shima Magaji Saif bai sake
furta wata kalma ba ɗakin inbanda karar fanka dake tashi kaɗan-kɗan bakajin komai.


Ganin shirun yayi yawa ya sanya Magaji Saif miƙewa ya nufi bakin ƙofa zai fita ya murɗa
hannun kofar zai buɗe Sarki Ubaiyd ya riƙo hannunsa cikin zafin nama yana faɗin.


"Kada ka tafi naji na amince zanyi dukkan abin da kace wallahi, ƴaƴana ai naka ne kana da
ikon zartar da kowanne irin hukuncin a kansu".


Magaji Saif yayi murmushin jin daɗi har ƙasan ransa ya koma ya zauna har a lokacin
murmushin bai bar saman fuskarsa ba.

Ya cigaba da faɗin.


"Ka amince zamuje neman auren yarinyar yanzu?".


Sarki Ubaiyd ya gyaɗa kai ba tare da yace komai ba.


"Idan ta kama da ba da hakuri dole haka zaka bayar, duk wani girman kai da taƙamar mulki ka
ajiye shi tun anan".


Nanma Sarki Ubaiyd kai ya gyaɗa alamun ya a mince.


"To alhamdulillahi tashi muje".


Magaji Saif ya faɗa yana mai wucewa gaba domin fita daga ɗakin, Sarki Ubaiyd ya biyo
bayansa.


A tare suka fito Inda su Anwar ke zaune zaman jiransu, Magaji Saif yace.

"Ku koma ciki Sadiya, kai kuma Anwar biyomu zuwa parking space.

Ba musu Anwar ya biyo bayansu har zuwa bakin motarsa ya kunna Magaji Saif da Sarki Ubaiyd

suka shiga baya suka zauna Anwar ya shige wajen driven yaja motar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login