Showing 33001 words to 36000 words out of 88612 words
Chapter 12 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
"To Baba Allah kiyaye !".
Sukayi maganar kusan atare, Aynu ta mik'e tsaye tana mai duban fuskar Ya sayyadi, sai dai
yau d'aya sai taji bata son ganin fuskar tasa ma, d'auke kai tayi gefe tare da fad'in.
"Ina yini?".
"Lafiya k'alau Aynu, kwana biyu kinjini shiru ko?".
"Ehh".
Ya Sayyadi yayi d'an guntun murmushi.
"Zuwa nayi har gida inji amsa ta".
"Amsar mefa?".
"Ohh kina nufin kin manta Aynu?".
Aynu tayi k'ok'arin nemo murmushi saman fuskarta.
"Wannan mai sauk'ine tunda gashi har Baba ya amince da kai".
"Kina nufin kema kin amince kenan?".
Murmushi tayi tare da gyad'a kai, alamun ehh.
"Alhamdulillahi...Aynu nagode sosai Allah ya tabbatarmin da mafarkina akan ki".
Mai-makon ta amsa da amin sai cewa tayi.
"Zan shiga gida sai zuwa anjima nagaji wallahi".
"Babu komai Aynu kina buk'atar hutu dama, a gaishemin da Umma".
"Za taji".
Ta fad'a tana mai shigewa cikin gida ta barshi nan tsaye.
Kafin shima ya kama hanya yabar wajen.
***
" Ya kamata indai da gaske kana sona Iyayena su sanka ko?".
"Kamarya kenan !, wani abu ya faru ne?".
"Ehh jiya naji Babana yana bawa Ya Sayyadinmu umarnin ya cigaba da zuwa wajena, kuma
baki d'aya su Umma shi suka sani basu sanka ba".
Ajiyar zuciya Yarima ya d'anyi, yana mai duban fuskar Aynu dake k'asa sosai yake nazarinta
kafin ya bud'e baki ya fara magana.
"Ke yarinyace Aynu !, nasan cewa ina sonki sosai Aynu amma kamata yanda nake d'innan
har saina k'ask'antar da kai zan samu abu?".
"Ban gane ba?".
Aynu tayi tambayar tana mai duban fuskarsa.
Dafa kafad'arta yayi da hannunsa guda d'aya, d'ayan hannun kuma cofin juice ne yana sha.
"Nifa d'an Sarki ne !, muna da kud'i da mulki aganinki ko da mahaifinki ya bayar dake idan naje
zai hanani auren ki?, idan ma zai hana ai ga kud'i !".
Aynu tabishi da kallo kawai tana nazarin maganarsa amma ta kasa fahimtar abin da yake nufi,
shima kuma dama bawai buk'atar fahimtarta yake ba.
" Karki damu Yarima naki ne har abada !, Mubar wannan maganar kinji ?".
Yayi maganar yana mai zama a gabanta suna fuskantar juna, aransa yasan gaskiya ta fad'a
amma girman kai da Izzar mulki bazasu bari yakai kansa gaban iyayen taba domin shi akomai
nasa yanayin ammafani da mulki da kud'i ne, yasan kuma indai akwai kud'i tamkar ya samu
Aynu ne, domin yasan iyayenta gajiyayyu ne ba tunyanzuba sabida bai je k'ofar gidansu ba sai
da ya fara sanin wacece Aynu?.
Murmushi Aynu kawai tayi tare da dubansa duk da cewar zuciyarta bata aminta da zancen da
yayi ba, shima kuma ya karanci hakan, amma yasan duk iya tunaninta bazai tab'a kawo kan
abin da yake nufi ba.
Gimbiya Safiyya ce ta shigo fuskarta cike da murmushi, amma yanayin data gansu ya sanya
fuskarta canjawa daga murmushi zuwa b'acin rai, Aynu tayi k'ok'arin mik'ewa da sauri ta tsaya,
shi kuwa gogan ko a jikinsa wai antsikari kakkausa, saima cigaba da shan juice d'insa da yayi
bai ko kalli inda take ba bare ya nuna mata cewa yasan ta shigo.
Sosai Safiyya taso danne zuciyarta sai dai shaid'an yaci galaba akanta ta hanyar hura wutar
kishi sosai a cikin ranta.
A hankali ta taka zuwa inda Aynu take sai jin sautin k'arar mari kawai Yarima yayi akunnenta ya
d'ago da sauri dan ganin wa aka mara ?, ganin Aynu yayi rik'e da kunci tana bin Safiyya da
kallo, Safiyya ta watsa mata wani mugun kallo tare da fad'in.
"Banza kawai KARUWAR CIKIN GIDA....!".
Kafin ta kai ga rufe bakinta Yarima Fudhal shima yad'auke ta da wani gigitaccen mari, ba
Gimbiya Safiyya ba hatta Aynu ta girgiza da marin da Yarima ya yiwa Safiyya, cike da b'acin rai
yake fad'in.
"Zaki iya sanya hannu ki mare ni in kyaleki, amma tunaninki zaki mari Aynu natsaya ina
kallonki ne!, idan kin kirata da karuwar cikin gida ke kuma a kira ki da me?, akwaima mace mara
aji da rashin kamun kai data wuce matar da zata biyo saurayinta har cikin gidansu ta zauna
kuma kullum k'afarta na hanyar d'akinsa wai da sunan soyayya?".
Shiru ya gauraye d'akin sai aikin kallon-kallo da sukeyiwa junansu, Yarima Fudhal ya katse
shirun da fad'in.
"Akwai banbanci mai yawa tsakanin Mace me kyau Mara aji da mummuna mai aji !, da yawan
'yan mata kuna daukar aji da ake fada abun wasa ne toh aji Yana nufin wadda take tamkar
MAR'ATUSSALIHA irin macen da akai kwatan ce da ita a ilmance wallahi dana auri mai kyau
ballagaza mara kamun Kai kwara mummuna mai aji da sanin hak'k'ina !, har yanzu bangama
aminta da tarbiyarki ba, taya zan auri macen da tarbiyarta bata wadace taba bare ta baiwa
'ya'yan da zata haifa zuwa gaba ?, kiyi tunani da kyau sosai Safiyya ni Yarima Fudhal ko kusa
ban dace da ke ba sabida ni ba ajin ballagazar mace bane !".
"Sannan ina mai baki kyakykyawan albishir ki gayawa kowa AYNUL-HAYAT nakeso wato 'yar
aikina kuma Baiwata !, ko da kinmatsa na aure ki to kisani babu d'igon sonki a cikin raina !,
domin nasan ke baki da aikin da yawuce kai k'arata to bismillah...!".
Ita dai Aynu tana gefe tana aikin zubar hawaye k'asan zuciyarta kuwa Innalillahi wa'inna ilaihi
raji'un kawai take ambato domin tasan Allah kad'ai yasan yau iya yawan ruwan da Yarima
yab'allo mata.
Shi kuwa a ganinsa hakan da yayi ne dai-dai domin shi bayason takura a cikin rayuwarsa, yayi
hakan ne domin ya share tunaninta naganin cewa yana sonta kawai sharewa yake, a gefe guda
kuma hakan yake ganin mafita wajen warwarewar alak'ar aurensu da akeson k'ullawa.
Zuwa yayi gaban Aynu ya kama hannunta ya jata zuwa cikin bedroom d'insa ya bar Gimbiya
Safiyya nan tsaye kamar anjona mata lantarki, tayi mutuwar tsaye hawayan dake zuba kan
fuskarta ne kawai zai iya tabbatar maka kasan cewa da ranta ba mutuwa tayi ba tsabar kad'uwa
da tayi da maganganun Yarima Fudhal.
Toilet ya kai Aynu tare da fad'in.
"Wanke fuskarki, kada ki fita da hawaye".
Shi kuma ya dawo cikin d'akin gefan katifarsa ya zauna tare da dafe kansa yana tariyo
abubuwan da suka faru.
"Mai Martaba...!".
Ya furta hakan afili yana mai d'ago kansa da sauri cike da kad'uwa hankalinsa ya tashi sosai.
Ko meye dalilin hakan ?, Oho.
Gimbiya Safiyya kuwa da k'yar ta iya d'aga k'afafuwanta tabar cikin falon ta koma b'angaren
Fulani Sokoto tana tafe tamkar zata fad'i, duk inda tawuce sai anbita da kallo tare da
tambayarta lafiya?, amma bata iya furta komai sai hawayen takaici dake bin fuskarta.
Tana shiga falon Fulani ta zube k'asa tare da fad'in.
"Wayyo Allah Momy ki taimake ni wai baya sona!".
Fulani Sokoto da Jalila sukayi ca akanta kowa na tambayarta.
"Lafiya !, mai ya faru ?".
Safiyya ta fad'a kan cinyar Fulani ta kifa kanta, tana mai cigaba da rera kukanta, d'ago da
kanta Fulani tayi tare da fad'in.
"Kalle ni Safiyya share hawayenki ki bani bayanin abin da yafaru, domin insan abinyi insan irin
lallashin da ya kamata inyi miki, amma kinzo kin sani gaba kina kuka ban san me ya faru ba
taya zan lallashe ki?".
Gimbiya Safiyya ta share hawayenta ta fara bawa Fulani labarin dukkan abin da ya faru bata
rage ko d'aya ba illa k'arin masu sugar da tayi cikin bayanin nata domin Fulani Sokoto ta zuciya
sosai.
Ai kuwa idan ran Fulani ya kai duba ayau yab'aci, amma da yake mata ce irin 'yan duniya da
suka goge a iya bariki murmushi tayi tana fad'in.
"Wannan ne zai tada hankalinki?, har kizo kina ihu akan wani banzan kwaro Fudhal !, kwantar
da hankali ai anzo inda nake so azo WACECE AYNUL-HAYAT kuma ?, hmmmm karki damu
yanzu za'a fara wasan indai ni naci sunan nawa da ake kirana dashi Fulani Sokoto zanga
tayanda za'ayi Fudhal ya samu dukkan cikar burinsa a duniya !, bare kuma har ya auri wacce
yake ikirarin ita yake so !, kuma ko yak'i ko yaso sai kin aure shi indai ina raye.... !".
Jalila dake zaune gefe tana jin batun da mahaifiyar tasu takeyi tayi wani guntun murmushi tace.
"Ai dama Momy ke kika k'yale komai haka sakaka wallahi, ya kamata ki tashi tsaye tun da
wuri!".
***
Zainab ce zaune falonsu tasa kwanun abinci a gaba tana ci gefe guda kuma Maman tace
zaune tana yankan farce, Zainab ta d'an dubi Mamanta tace.
"Wai kuwa Mama idan saurayi yace bazai zo gidanku yaga iyayenki ba susan juna, kawai dai
yasan ko bayan anba dake zai zo da kud'ine yasan kuma dole a bashi ke me hakan ke nufi?".
Baba Ta Sallah tabar yankan farcen tana duban Zainab tare da tambayar .
"Waye wannan shi kuwa?".
"Wani ne ya gayawa Aynu wallahi".
Baba Ta Sallah tayi ajiyar zuciya kafin tace.
"A iya sanina da tunanina da kuma duk wanda yaji wannan zancen, abin da zai d'auka koma
ince yanda gaskiyar al'amarin yake, shi wannan saurayin kwata-kwata baisan muhimmanci
iyayenta ba, asalima ko da auren akai taya zai daraja iyayenta domin a ganinsa iyayen banza
ne sun bada 'yarsu shi kuma yazo ya nuna kud'i anbashi ita !, wannan mutumin baya daga cikin
irin mazajen da ya kamata mace ta aura".
Zainab tayi shiru tan duban Baba Tasallah kafin tace.
"Mama Yarima Fudhal shiya fad'awa Aynu haka, ni abin ya bani mamaki fa, yanzu ace duk irin
son da yake nunawa da fad'a yanayi mata kenan ya tashi abanza tunda bai d'auki iyayenta
bakin komai ba?".
"Sosai ma kuwa ni dama tunda kika bani labarin yana son Aynu nasan za'ayi haka, ku a
tunaninku gidan Sarkin nan da danginsu baki d'aya sund'auki talakan mutum a bakin komai
ne?".
"Ban gane ba Mama?".
"Ku yara ne yanzu kukazo duniya, amma abin da baki sani ba shine Sarki Ubaiyd bai d'auki
talaka abakin komai ba illa ya zama bawansa, kuma a hakan ya tarbiyartar da iyalinsa".
"Amma kunsan hakan kuka bari muke aiki a gidan?".
"Dole ce ta sanyamu Zainab da muna da yanda zamuyi da ko k'ofar gidan ba zamu je ba".
Zainab shiru tayi tana duban Mamanta cike da tambayoyi kala-kala amma ayanda ta karanci
yanayin Maman bazata iya sanar da ita komai ba.
KO MEYE DALILI?.
Nima kaina ina buk'atar sanin wannan amsar, amma nasan koma mene akwai wani boyayyan
al'amari.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdaucee Jeebour.
21
DARE
9:00PM
Falon Mai Martaba cike yake da mutanan gidan sabida meeting d'in gaggawa da Mai
Martaba ya shirya a daran nan.
Gefe guda Mai martaba Sarki Ubaiyd ne kishingid'e bisa kusun, daga wajen kansa Fulani
Bingel ce tare da 'ya'yanta Aunty Sadiya da Aunty Sa'ida mazajensu suka kawosu, sai Yarima
Fudhal daga wajen k'afarsa kuma Fulani Sokoto ce tare da 'ya'yanta ita ma a kusa da ita,
Yarima Jaleel da Jalila sai Gimbiya Safiyya .
Mai Martaba ya shafe tsayin lokaci yana bin iyalinnasa da kallo, kafin yayi gyaran murya tare
da jero addu'o'i sannan yayi sallama suka amsa ya fara fad'in.
"Ba komai ne yasa ni shirya wannan taron na gaggawa ba sai dalilin faruwar bijirowar wata
b'araka daga cikin danginmu, da kuma shirya rushewar martabar danginmu da mutuncin
sarautarmu!".
"Fudhal...!".
Mai martaba ya kira sunan da kakkausar murya.
Kowa sai da ya dubi Mai Martaba domin yau karo na farko da sukaji ya kira Yarima Fudhal da
sunansa sab'anin Magaji da akafi ji yana kiransa da shi tsayin shekaru.
Mai martaba ya cigaba da maganarsa.
"Fudhal kai ne ke shirin ruguza mana komai !, mene haka ka ke shirin aikatawa ?, k'asar wajen
da na kai ka tsayin shekaru kayi karatu abin da suka koya maka kenan soyayya da Baiwarka?".
Yarima Fudhal yayi shiru kansa a k'asa ya kasa iya d'aga kansa bare har ya iya bada amsar
tambayar da ake yi masa, mai martaba ya cigaba da fad'in.
"Karka manta kaifa magaji ne a bayana, shin kanason bijirewa umarni nane kome?, ko kuwa
ban isa da kai bane?, kar kamance ni Ubaiyd bana magana biyu auren ka da Safiyya tamkar
anyi angama ne !".
Sai lokacin Yarima Fudhal ya d'ago kai ya kalli Mai Martaba kafin ya sake yin k'asa da kansa
ya fara magana.
"Bazan gajiya wajen neman afuwarka ba, sai dai ina rok'o agareka Abba ka taimaka kabani
zab'in raina nasan hakan tamkar tozarcin Family namu ne amma babu yanda na iya ne tabbas
inason Aynu amma da ace ina da damar da zan iya cire soyayyar da na cire ta domin samun
yardarku da cika umarninku...!".
Yayi shiru nad'an wani lokaci yana jira yaji ko Mai martaba zai ce wani abu jin da yayi bai ce
komai ba yasa yacigaba da magana.
"Kayi hak'uri Abba !, ni banyi haka domin na bak'anta ranku ba burina kullum bai wuce ganin
farin cikin iyayena ba ko da zan rasa raina !, amma Abba ina son yarinyar ne badan komai ba
sai domin ta can-canci a so ta, sabida tarbiyarta da kamalarta....sannan!".
"Kaga ya isa Magaji !, ban kira ka dan intambayeka can-cantar taba ko tarbiyarta na kira ka ne
domin in tabbatar maka kome za kayi aure kai da Safiyya da Saima babu fashi sai dai idan sune
sukace basa so !, kuma babu kai babu auren wannan Baiwar KO BAYAN RAINA !".
Yarima Fudhal ya rintse ido sabida yanda yaji zuciyarsa na zafi sosai, har jiyake kamar ransa
zai iya barin gan-gan jikinsa a lokacin.
Fulani Bingel ta dubi d'an nata tare da duban Mai Martaba, ta so yin magana amma tasan
bazai saurareta ba, tana tausayawa Yarima Fudhal domin tasan halinsa ko kad'an bai iya
sanyawa ransa damuwa ba.
Mai Martaba ya sake duban kowa kafin yace.
"Sannan ita kuma yarinyar daga yau tabar aiki a gidan nan, kowa ya tashi ya tafi ".
Wannan hukuncin bak'aramin dad'i yayiwa Fulani Sokoto da Yarima Jaleel ba, musamman
uwar gayyar Gimbiya Safiyya gefe guda kuma ga Aunty Sa'ida domin itama tak'i jinin ace
Yarima Fudhal yarasa wadda zai lak'ewa sai Baiwarsa tir da wannan al'amarin.
Kowa ya mik'e ya fice ban da Fulani Bingel da Yarima Fudhal ya ya kasa mik'ewa, domin
yasan indai yamik'e a wannan lokacin to tabbas sai dai su d'au keshi hakan yasa yayi zamansa
yana karanto addu'o'i cikin ransa, Mai Martaba ya dube shi duba na musamman yana fad'in.
"Ka kwantar da hankalinka Magaji kai fa magajina ne, akan wane dalilin zaka bari ka lalata
rayuwarka a banza?, ina so ka cire duk wata damuwa dake cikin ranka kayi ayyukan dake
gabanka, an kammala ginin Asibitin dana shirya gina maka, na gayyato gwararrun likitocin da
zasuyi aiki a cikinsa tare da kai, zuwa nan da sati guda sai ayi bikin bud'eshi ko?".
"Ehh duk yanda kace Abba, Allah yasaka da alkhairi ya k'ara girma da arzik'i ".
"Amin".
Fulani Bingel ta amsa tare da cigaba da fad'in .
"Ka k'ara hak'uri kaji ?, komai mai wucewa ne a rayuwa !".
"Insha Allah".
Yarima Fudhal ya mik'e yana mai jan k'afafuwansa da sukai masa nauyi tare da bin bango
yabar d'akin kai tsaye d'akinsa ya nufa ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan shower mai
sanyi domin wai yaji sanyi cikin ransa.
Fulani Bingel ta dubi Mai Martaba bayan fitar Yarima Fudhal tace.
"Da anbi komai a sannu Mai Martaba !, wannan hukuncin kamar yayi tsauri domin ban da
Allah babu wanda yasan matar mutum, domin shi al'amarin aure sai anbi a sannu...!".
"Ki na so ki goyi bayan d'anki ne?".
"A'a ko kusa kaima ai d'an kane".
"To bana buk'atar jin wani k'orafi cikin maganar da nayi !".
"Allah ya huci zuciyarka !".
***