Showing 42001 words to 45000 words out of 88612 words
Chapter 15 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
Ummanta d'an bubbuga bayanta tayi tana fad'in.
"Kiyi hak'uri Aynu ka da kisa abun aranki kinji?, komai zai wuce da yardar Allah".
Aynu ta d'ago ja jayen idanuwanta ta dubi Ummanta tana fad'in.
"Amma Umma mai ya sa Baba ya yanke hukuncin tauyemin hak'k'ina?, ina son inyi karatu
sosai Umma ki fahimtar da Baba mana!".
"Aynu ki sani ni bani da abin cewa cikin wannan al'amarin ban da addu'a kaman yanda
mahaifinki ya fad'a, yanzu babu abin da zai fahimta kome zan fad'a masa, sai dai ina mamakin
canjawar Malam lokaci d'aya haka ban sanshi da rik'o ba !, amma koma dai mene nasan akwai
wani babban dalilin da ya sanya mahaifinki yanke wannan tsats-tsauran hukuncin kamar yan da
ya fad'a?".
"Amma Umma wanne abu ne ya faru tsayin shekaru haka da yake shirin zamowa silar
wargajewar farin ciki na?, ki sanar dani Umma!".
"Babu abin da zan fad'a miki Aynu !, amma ki sani kada ki k'ullaci Mahaifinki domin shine yayi
silar zuwanki duniya yana da ikon da zai yanke ko wanne irin hukunci akan ki...!".
"Amma Umma.....!".
"A'a Aynu kada ki sake furta komai akan wannan maganar kinji, kibi umarnin mahaifinki!".
Umma takatse Aynu daga maganar da take son yi.
Aynu ta mai da kanta kan cinyar Ummanta tana mai goge kwallar dake zuba bisa fuskarta
lokaci-lokaci.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
25
Cikin lokaci k'ank'ani Aynu ta fita haiyacinta sosai ta rame ba ta da walwala ko kad'an, ita
kanta bata san tana son Yarima Fudhal sosai haka ba sai da yayi mata nisa, dan ma Zainab a
kullum tana k'ok'arin ganin ta d'ebe mata kewa, Babanta kuwa yanzu bai fiye shiga harkarta ba
sosai shiyasa abun ya had'u yayi mata yawa, b'angaren Ummanta kuwa kullum lallashi ne nata
tana tausayawa rayuwar 'yarta sosai to amma bata da abin da zatayi da ya wuce add'a.
To shima Yarima Fudhal a nasa b'an garen haka abin ya ke, shi zama a iyacewa abin nasa ya
zarce na Aynu domin cikin kwana biyu da faruwar al'amarin sabida sanya damuwa da yayi da
yawa a ransa abin har ya kai shi da kwanciya.
Anwar ne zaune gefan katifar da Yarima Fudhal ke kwance yata lallashinsa akan ya daure ya
sha ko da ruwan tea ne amma ya yi banza da shi domin ji yake baya sha'awar komai anan cikin
duniyar nan.
Turo k'ofa akayi tare da sallama Fulani Bingel ce ta shigo tare da ma'aikatanta su biyu na biye
da ita, daga gefe guda kuma Aunty Sadiya ce da tsohon cikinta sai Aunty Sa'ida kuma da ta
keta cika tana batsewa.
Suka zauna kusa da shi Anwar ya gaishe da su ya mik'e ya koma falo domin ya basu waje,
Fulani ta dafa goshin Yarima tana fad'in.
"Haba Magaji !, jibi yanda duk ka lalace kaman ba kai ba?, ya kake so ka sanya rayuwarka
cikin tsaka mai wuya ne?".
Yarima ya dubi Mahaifiyartasu hawaye nabin gefen idonsa bai damu daya share ba haka kuma
bai iya cewa da ita komai ba, tasa hannu ta goge masa tana mai cigaba da fad'in.
"Kayi k'ok'arin cire wa kanka damuwa da yawa haka kaji?, kada ka jawa kanka wani ciwo na
daban".
Sai lokacin Yarima ya saki wani guntun murmushi ta gefan fuskarsa, amma har lokacin bai furta
komai ba kamar yanda hawayen bai bar zuba bisa pillown da yake kai ba.
Aunty Sadiya ta nisa tare da fad'in.
"Hajiya al'amarin Magaji sai addu'a wallahi !, amma ka daure dan Allah karage yawan
damuwar da kake sanyawa kanka, addu'a ita ce mafita wata rana sai labari!".
"Mtsww kema dai Aunty Sadiya !, wallahi dan yaga kawai ana lallab'ashi ne, amma kaman
Magaji ace sai angaya masa abin da ya dace da wanda ba dace ba, Doctor ne shi fa yafimu
sanin abin da damuwar zataje ta jawo masa!".
Cewar Aunty Sa'ida kenan, tayi maganar cike da fushi da b'acin rai, Yarima ya jawo hannunsa
ahankali yana mai kama hannunta yarik'e gam, fuskarsa har lokacin da murmushi samanta, sai
kuma jikinta yayi sanyi k'alau ta janye hannun tamik'e ta fice daga d'akin tana goge kwallar data
kawo mata domin ya bata tausayi sosai a wannan lokacin.
"Kayi hak'uri Allah ya baka lafiya, zamu cigaba da tausar Mai Martaba insha Allahu komai zai
dai-dai ta kaji?".
Yarima ya gyad'a kai, Fulani ta d'auki kofin tea d'in ta mik'a masa, ya mik'e ya zauna yana mai
karb'an kofin ya fara shan tea d'in a hankali.
"Ni zan koma Magaji ka cigaba da hak'uri kaji?".
"To nagode sosai".
Ya furta yana mai kallonta, itama shid'in take kallo kafin ta mik'e da k'yar tana takawa tabar
d'akin.
Fulani ta bita da kallo kafin ta dawo da kallonta kan Yarima tana fad'in.
"Allah Sarki Sadiya Allah dai ya sauke ta lafiya, cikin nan yana d'an bata wahala sosai, amma
sabida k'arfin hali tun da akace mata kana kwance ta tada hankalinta sai tazo ta ganka".
Yarima yayi murmushi har cikin ransa yana son Yayar tasa, domin itama tana k'aunarsa sosai
gata da sanyin rai da hak'uri, kusan ince baki d'aya ita ta d'auko halin Fulani Bingel.
Ajiye kofin yayi ya koma ya kwanta abinsa, Fulani ta lullub'e shi da bargo tana fad'in.
"Ka kwanta ka huta, zuwa anjima zan dawo kaji?".
Ya gyad'a mata kai ta fice daga d'akin, afalo ta samu Anwar tana fad'in.
"Sannunka da k'ok'ari Anwar mungode sosai Allah yabar zumunci".
"Amin Hajiya babu komai".
Ta juya tabar d'akin, shi kuma ya mik'e ya koma wajen Yarima, ya nemi guri ya zauna, Yarima
ya mik'e zaune shima yana duban Anwar ba tare da yace komai ba, amma da dukkan alamu so
yake yayi magana.
Da k'yar dai ya bud'e baki yana fad'in.
"Kana ta tambayata kan abin da ya had'ani da mahaifin Aynu ko?, zan sanar dakai yanzu insha
Allahu!".
***
Baban Aynu ne zaune bisa tabarma a tsakar gida, gefe guda kuma Umman Aynun ce zaune
suna hira, yayin da Aynu keta shige da fice tana aikace-aikacen data saba duk da cewa bata
wal-wala amma hakan bai hanata yin abin da ta saba ba acikin gidan.
Baba ya dubi 'yar tasa ta ba shi tausayi sosai, kiran sunanta yayi tare da fad'in.
"Zo nan Aynu".
Aynu tazo ta durk'usa tana fad'in.
"Gani Baba".
"Kin sa kanki a damuwa sosai Aynu !, kada ki d'auki fushi ki d'ora kan mahaifinki Aynu, ban so
ki san wannan labari ba amma yau yazama dole infad'a miki, domin ki yanke hukunci da kanki
akan barin soyayyar Yarima ko cigaba da son sa!".
Baban ya d'anyi shiru na wani lokaci kafin ya cigaba da fadin.
SHEKARU GOMA SHA SHIDA DA SUKA WUCE....!
"Ni na kasance haifaf-fan k'asar senegal ne, na taso cikin dangi da abokai tsayin shekaru nayi
karatu na duk a can senegal d'in, sanadiyyar barin k'asata kuwa wata annoba ce ta addabi garin
da muke ciki, an rasa rayuka sosai a lokacin ciki har da iyayena da 'yan uwana, kuma lokacin
anrasa maganin wannan annoba data saukar mana, hakan ya saka gwannati ta bada jirgi
domin d'ebo raguwar mutanan da suka rage a cikin garin zuwa duk k'asar da muke so, domin
tsiarar da rayuwarmu, ni dai alokacin na zab'i Nigeria domin nakanji Mahafina yana yawan bada
labari akan k'asar wajen kasuwanci saboda yasha zuwa yana komawa domin kasuwancinsa".
"Nazo Nigeri bani da kowa haka kuma bansan kowa ba, na sauka a gurin dagacin wata
unguwa wanda shine mahaifi ga Ummanki ya rik'e ni da amana da gaskiya har dai dana basu
labarina da abin da ya kawo ni k'asar nan, kasancewar nayi karatu shine ya samamin aikin
koyarwa a makarantar MAI TASA PRIMARY SCHOOL".
"Cikin ikon Allah suka d'auke ni, da albashin da nake d'auka nake temaka mana muna ci da
kanmu kasancewar na samesu suma bawani hali garesu ba sai dai rufin asirin Allah, shima
kamar ni yake bashi da kowa sai Ummanki ita kad'aice 'yarsu, bayan wani lokaci mai tsayi suka
yanke hukuncin aura mun ita, bayan aure da shekara guda sukayi gobara da dare duk suka
k'one a cikin dak'i, munyi kuka sosai domin munrasa wanda suke uwa da uba a garemu
bayansu ba mu da kowa a duniyar nan".
"Haka mukayi hak'uri muka dan gana, ki sani Aynu ba ke kad'aice 'yarmu ba, kafin ki akawai
Yayanki mai suna Muhammad Shadad !".
Aynu ta share kwallar dake idonta tana murmushi farin ciki fal ranta taji ance tana da yaya, cike
da d'oki ta fara fad'in.
"Ina da Yaya Baba!, Ina yake to?".
Baba yayi shiru na wani lokaci cike da tausayaa Aynu kafin ya cigaba da fad'in.
"Bayan rasuwar su Malam ashe Ummanki na da ciki, bayan wasu watanni ta haifi d'a namiji,
mun raineshi cikin so da k'auna, har zuwa samuwar cikin ki bayan shekaru uku, Shadad na da
shekaru uku a duniya aka haifeki, yaron na sonki sosai kamar yanda muke sonku dukanku,
domin ku kad'aine kuka zamto duniyarmu".
"Har lokacin dai ina aikin koyarwa lokacin na sanya Shadad a makarantar primary d'in, tare
muke tafiya da shi idan antaso mu dawo tare, har Yayanki ya kai kimanin shekaru biyar a duniya
yayin da kike da shekaru biyu ke kuma".
WATA RANA
"Rana ce da ta zamto silar rugujewar dukkan wani farin cikinmu !, rana ce da ta zamto
sanadiyyar zamowarmu haka ayanzu, ranace da ba zamu tab'a mancewa da wanzuwarta a
garemu ba har abada !, a ranar antaso daga makaranta kenan ina janye da hannun Shadad a
wannan lokaci domin tsallaka titi, a wanna lokacin wata mota ta kawo kai kan titi mu kuma mun
riga da mun kai tsakiyar titin kafin inyi wani yunk'uri motar tayi gaba da mu, na fad'i k'asa tayar
motar tabi takan k'afata yayin da Shadad akan idona yayi sama ya fad'o k'asa a wannan lokacin
ko shurawa baiyi ba yace ga garenku nan!".
Aynu ido ta fiddo waje cike da hawaye tana fad'in.
"Ya mutu kenan Umma?".
Umma ta gyad'a mata kai tana mai share kwallar da ke zuba bisa fuskarta itama.
"Naga dai yaron da ke tuk'a motar amma alokacin bansan waye shi ba?, kuma bansan ko d'an
gidan waye ba?, jama'ar gurin ne suka d'aukeni zuwa asibiti, yayin da wasu suka nufi gidana
domin sanarwa Umman ki, a lokacin wani mutum ya raka Ummanki gidan yaron da yake tuk'a
motar ba kowa bane ashe Fudhal ne lokacin baifi shekara goma sha biyar ba a duniya !".
"Mutumin da ya yiwa Ummanki rakiya zuwa fada kuwa mahaifin Zainab k'awar ki ne !, da
zuwansu sun ba da bayanin dukkan abin da ya faru amma kuma sai me ya biyo baya?".
"Sarki Ubaiyd ya rufe ido yace shi sam d'anshi bai aikata ba yaushema ya iya mota har da zai
tuk'a?, yaje yayi wannan d'anyan aiki wai basu dai gani da kyau ba".
"Ummman ki tayi kuka alokacin ta rok'eshi ko da ba zai yar da d'ansa bane to ya taimaka sai
cewa yayi da dai a ce neman taimakon suka zo kai tsaye zai taimaka, amma tunda sun fara
neman d'ansa da sharri babu abin da zai yi musu".
"Haka suka taso suka tawo, ni kuma ina kwance a asibiti ana jiran a kawo kud'in aiki kimanin
dubu d'ari domin amin aiki, sai dai a ina zamu samu wannan kud'in ?, mu da bamu ajiye ba
bamu bada ajiya ba?".
"Sai da na kwana uku a kwance ahaka da k'afa a karye tun tana zub da jini ta daina ta kumbura
likitoci sunce ba zasu tab'a ni ba sai anbada kud'i, bayan kwana uku kuma a kace ai k'afar ta
rub'e sai dai ayanke, haka Ummanki ta sai da gidan mahafinta dubu ashirin, Baban Zainab ya
taimaka da dubu goma da ya sai da ragunansa guda biyu ya bayar ta cika takai kud'i dubu
talatin aka yanke min k'afata, wannan shine asalin rasa k'afata guda d'aya, kuma shine dalilin
rasa aikina da nayi, domin sunce taya mai k'afa d'aya zai iya aikin koyarwa?, tun da aka koreni
ban kuma samun wani aiki da zanyi ba duk inda naje sai ace baza'a d'auki wanda ya nakasa
ba!".
"Bayan wannan abu da ya samemu kuma Ummanki ba ta da aiki kullum sai kuka sabida duk
sana'ar data kama sai ta lalace, muka shiga k'angin rayuwa gidansu Zainab ne kawai suke
temaka mana da abinci kullum har sai da muka shekara biyu a haka, sabida yawan damuwa da
Ummanki ta sanyawa ranta ya haifa mata da hawan jini shine yayi sanadiyar rasa idonta sabida
rashin mgani da kuma samun abinci mai kyau, lokacin kina da shekaru uku da rabi, nine na
dinga kula da ke a wannna lokaci sabida Umman ki bata da idon da zata iya kula dake har zuwa
sanda ki ka kai shekaru hud'u na sanya ki makarantar primary har zuwa sanda ki ka kai shekaru
goma a duniya cikin rufin a sirin Allah, a lokacin kuma aka tsananta karatun domin duk team
ana buk'atar a biya d'ari takwas mu kuwa bamu da ita bare dalilinta, domin fafutukar abin da
zamu cima ta ishemu, wannan shine silar barin karatun ki, ki ka dawo zaman gida sai islamiyya,
kulawarki ta koma hannuki kafin ki kai shekaru goma sha biyar kin iya komai har sai aikin gidan
da komai ya koma hannunki har zuwa yanzu".
"Wannan shine ta k'ai taccen abin da ya faru ga rayuwarmu baki d'aya, yanzu hukunci ya rage
naki na gaya miki ne domin ki daina ganin laifina cikin wannan al'amari".
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour
26
Shiru ne ya biyo baya illa shash-shek'ar kukan Aynu da ke ta shi, Ummanta keta aikin
lallashinta kafin Baban yace.
"Kuma ni duk ba wannan ne abin da yasa na yanke wa Fudhal wannan hukuncin ba, kafin
yace zai zo gidan nan da kwana biyu wani saurayi yaje ya same ni a zaune a bakin kasuwa ya
kira ni bayan mun gaisa yake fad'amin cewa....!".
"Ya zo ne wajena da muhimmin abu, abin kuwa shi ne ya kunnamin a cikin wayarsa muryar
Yarima ce sosai da abokin nan nasa suna tattaunawa ne a bisa yanda za suyi su shawo kanmu
ta hanyar yaudara".
"Babu abin da yafi d'auremin kai, sai shawaran da suka yanke na cewar zasu sanya Aynu
makaranta, sannan zai nemi soyayyarmu daga baya kuma zasu mai da mu masu kud'i...!, wato
Ummun Aynu ki fahimci wani abu guda d'aya, da yawan al'ummarmu na yanzu muna mancewa
da Allah a cikin dukkan al'amarinmu, shin su Yarima sun mance cewa babu wani mai azurtawa
sai Allah?, kuma babu mai talautawa sai Allah!, abin ya d'auremin kai sosai wannan dalilin ya
sanya na yankewa Yarima wannan hukuncin amma ba wai dan BURIN FANSA ba..!"
Aynu ta mik'e ta shige d'aki da gudu ta durk'ushe a k'asa tana rusar kuka, kafin ta share
hawayenta daga baya tana ganin meye amfanin zub da hawaye akan wanda bai cancanta ba?,
a yau ta yanke duk wata damuwa da hawaye indai akan Yarima ne.....!.
SHIN HAKAN ZAI YIYU KUWA?.
***
Yarima ya dubi Anwar yana mai cigaba da fad'in.
"Ko kad'an bani da laifi akan duk kan abubuwan da suka faru Anwar!, tabbas nasan na d'auki
mota na fita a wannan rana sai dai ban san yanda akai hakan ta faru ba duk iya k'ok'arin da
nayi domin take burki a lokacin gagara yayi ashe burkin ya samu matsala ne?, ban sani ba
Allah ne kai ya kai ni gida a lokacin cikin ta shin hankali da tsoro....".
"Tabbas babu wani bawa da zai iya kaucewa k'addararsa komai k'ank'antarta domin ita
k'addarar mutum a rubuce take tun gabanin zuwansa duniya, Anwar Mahaifina shine
ummul-aba isin haddasa dukkan a bubuwan daya faru, a ranar da abin ya faru nazo gida cikin
rud'u da tsoro fuskantar hakan da Mai Martaba yayi ne kuma yaji dukkan abin da ya faru sabida
son da yakemin sai yak'i yarda da abin da aka ce na aikata !, a lokacin nayi k'ok'arin zuwa fada
domin in tabbatar da abin da ya faru alokacin da iyayen Aynu suka zo, sai dai Mai Martaba ya
sanya aka tsare ni aka hanani zuwa ko ina, a washe garin ranar ya nema min visa da komai
domin barin k'asata