Showing 9001 words to 12000 words out of 88612 words
Chapter 4 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
ya fice daga d'akin, ajiyar zuciya na
saki kafin in mik'e da sauri nima na fice daga d'akin har ina tun-tub'e.
A hanyata ta zuwa inda sauran ma'aikatan gidan ke zama insungama aiki naci karo da
Zainab taa ganni duk a wani tsorace, jana tayi wani b'angare na gidan da ban tab'a sanin da
shiba domin Zainab tasan ko ina a cikin gidan kuma kowa ya san ta.
Muka zauna ta rik'o hannunta tana tambayata.
"Lafiya Aynu?".
Nayi shiru nad'an lokaci ina kallon wani gefe na wajen, kafin na dawo da kallona kanta na fara
bata labarin abin da yafaru.
Zainab ta zaro ido waje tana fad'in.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, sai kinyi taka tsan-tsan da Yarima Jalil sosai wallahi".
"Kamar yaya?".
"Nasan baki san waye Yarima Jalil bako Aynu?".
Tad'an rage muryarta k'asa-k'asa.
"To Yarima Jalil ya wuce dukkan tunaninki, ya ksance mashayin giya kuma manemin mata a
cikin gidan nan duk wacce aka kawo aiki indai ta burgeshi to wallahi duk hanyar da zai bi sai
yabi domin ta zama yarinyarsa, ma aikata uku aka zubarwa cikinsa, kuma aka kulle bakinsu da
kud'i kada su fad'a babu wanda yasan haka sai mahaifiyarsa sai kuma Jakadiyya, domin ita ce
ma take sanarwa Babah Tasallah lokacin dana fara aiki a gidan nan, ko Mai Martaba kansa bai
san muna nan halin Yarima Jalil ba".
Gumi ne ya ketomin ta gefan fuskata jin wannan bayani na Zainab nayi maza na goge ina
fad'in.
"Ina hakan ma ba zata tab'a faruwa ba, babu dole sai in hak'ura da aikin".
Dariya Zainab tayi kafin tace.
"Kina hauka kenan?, ai barin aikin ki bai ta soba domin ko kinbar aikin sai ya binciko inda kike
kuma sai ya biki".
"Wayyo Allah na to yanzu ya zanyi?".
Nace da Zainab cike da tsoro, domin kunsan halina akwai tsoro kamar farar kura.
Zainab tayi shiru kafin tace.
"Ki kwantar da hankalinki ko Ummanki kada ki fad'awa, tun da Allah yasa ba aikin dare kike ba,
ko kad'an kada ki bashi fuska iya kaci gaisuwa bazai tab'a saki wani aiki ba tunda yasan ba
b'angarensu ki kewa aiki ba kawai dai ki iya takun ki a gidan nan".
Shiru nayi ina duban Zainab kafin ince.
"Au dama akwai masu aikin dare ne?".
"Ehh akwai koni da farkon zuwana aikin dare na farayi sai da Jakadiyya tayi magana na dawo
safe".
Aynu tayi ajiyar zuciya domin kalaman Zainab ya kwantar mata da hankali ya kuma bata kwarin
gwiwa, har dai da taji batun bazai tab'a umartatta da wani aiki ba tunda ba'a b'angarensu take
aiki ba taji dad'i sosai.
Nan sukayi ta hirarsu har Zainabu take sanarwa Aynu taji Yarima Fudhal yana fad'in zai fita
shida abokansa sun shirya masa party na murnar kammala karatunsa lafiya.
Aynu tace "kaji illar wasu masu kud'inba, idan har murnar za'ayi da gaske mai zai hana ayi
saukar al'qur'ani da walima".
"Kema dai kya fad'a kinsan bakowa yake son abin da za'a fad'i abin da Allah da Manzonsa
suka ce ba, al'amuran yahudawa yafi rinjaye a zukatan yawancin mutanen mu nayanzu, duk da
cewa ba duka aka taru aka zama d'aya ba".
"Haka ne, Allah dai yasa mu dace".
"Amin ya Allah".
Suka amsa baki d'ayansu da haka har lokacin ta shinsu yayi kowacce taje ta d'auki abincinta
suka tafi gida.
*** ***
Filin wajen cike yake mak'il da jama'a maza da mata kowanne yana ji da kansa, domin kowa
ka kalla a wajen za kasan kud'i ya zauna sabida daga d'an Alhaji da Hajiya sai d'an menister
wane 'yayan 'yan kasuwanni da 'yan siyasa sune suka cika wajen bakajin komai sai tashin
kid'an turawa kala-kala da wannan ya katse sa kaji wannan ya d'ora, dare ne amma tamkar
rana haka wajen yake sabida hasken daya haske wajen wanda shine ya basu kwarin gwiwar yin
harkokinsu hankalinsu kwance.
Filin wajen kansa abin mamaki ne banda irin cikar da yayi, jerin motoci goma ne sukai layi a
harabar wajen duka bak'ak'e ta tsakiya ce kawai fara, jikin lambar motar kowacce anrubuta
Emirs 1 har zuwa 10.
Baki d'aya gurin yarud'e da ihun kiran sunan YARIMA FUDHAL.
Cikin takun k'asaita yafito kamar bazai iya taka k'asa ba yana wani shan k'amshi yayi shiga
irin tasu ta sarauta kowa ya ganshi yasan Yarima ne wanda akeji da shi a gida da kuma waje,
sauran abokansa suka take masa baya.
Waje na musamman aka ware masa shi da abokansa, hankalin 'yan matan gurin nan kaf yayi
kansa kowacce burinta tasamu shiga wajensa.
Bayan kowa ya natsa kuma aka buk'aci Yarima Fudhal yayanka cake, yamik'e fuskarsa cike da
murmushi ya d'auki wuk'ar zai yanka, aka fara irga.
"One....two.....thr..".
K'arar motar dake shirin yin parking a wajence ta katse kowa, dukkan hankulan jama'ar gurin ya
koma kan motar.
Domin mota ce da duk wajen babu wand ya halarci gurin da ita mota ce k'irar Perrari mota mafi
kyau da tsada.
Kowa burinsa a wajen yaga waye ma mallakin wannan motar?.
A hankali ta ziro shantaleliyar k'afarta da tasha dogon takalmi mai tsini yana da igiyoye wanda
sune suka taimaka wajen rik'e k'afa fuwanta, shigar dake jikinta kuwa guwn ce pink da tabi
dukkan jikinta ta d'ame, daga gaban rigar har zuwa k'asa yasha adon stone blue dark tayi
rolling da mayafi k'arami shima blue.
Wayar dake hannunta ta d'orata bisa cinyarta X ce itama kalar takalminta blue, duk wannan
bayanin da akefa bata fito da dukkan jikinta ba bare har mukai da ganin duskarta.
Ta shafe mintuna kusan biyar a haka kafin ta fito zuwa waje, anan ne fa dukkan nin mumfashin
mutanen dake wajen ya kusa d'aukewa sabida kyakykyawar halittar da idanuwansu yayi tozali
da ita, duk da bak'im glass d'in dake fuskarta daya rufe kusan rabin fuskarta, amma hakan bai
hana ganin tsan-tsan kyawun halittar dake tattare da ita ba.
Cike da murmushi ta doso inda Yarima yake tana wani taku tare da rangaji kamar bishiyar da
iska ke kad'awa.
Nidai tunani na banyi zaton zata iya taku da takalmin dake k'afar taba, amma sai naga tana
tafiya kamar wadda tasanya silifas .
Bata tsaya ba sai da taje dai-dai inda Yarima Fudhal yake tsaye rik'e da wuk'ar yanka cake
sannan ta tsaya jikinsu har yana gogar juna ta juyo tana k'arewa sauran mutanan wajen kallo
kafin ta saka hannu ta cire glass d'in da yayiwa kusan rabin fuskarta k'awajen.
A fili na furta "SAIMA!".
[10/07, 20:09] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*
NWA®
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN)
07
A fili na furta "Saima !".
Amma Yarima Fudhal kuwa tsaya wa yayi yana dubanta cike da mamaki tare da tunanin inda ya
tab'a ganin fuskarta.
A hankali ta dawo da kallonta kan fuskar Yarima da ya tsare ta da shanyayyun idanuwansa
yana nazari a kanta sosai, tunaninsa ya tsaya adai-dai lokacin daya tuna yatab'a ganin mai
kama da ita awani guri.
Idan zai iya tunawa lokacin daya ba da umarinin a kira wo masa Jakadiyya ranar da ba'ashare
falo ba, a lokacin bai zaci da mutum zaune ba yad'auka dukansu suka fita yana ta
danne-dannan wayarsa ya d'ago kai bai zata ba suka had'a ido tayi saurin sauke kanta k'asa
shine ganin da zaice yayiwa mai kama da ita.
"Wacece ke!".
Bai san sanda ya samu kansa da jefa mata tambayar ba, bata bashi amsaba illa rik'o hannunsa
dake rik'e da wuk'ar yan kan cake d'in da tayi ta fara irga, sai kawai gani yayi ta yanko cake ta
nufi bakinsa da shi kau da kansa yayi gefe yana mai komawa inda yake a zaune ya zauna.
A dai-dai lokacin da aka k'ara sakin kid'a ana ciye-ciye da shaye-shaye, Saima ta koma kusa
da shi ta zauna tana dubansa tare da zuk'ar lemon da ke rik'e hannunta, ta d'an basar kamar
yanda taga yayi mata amma ta kasa jure shirun nasa ta gyara zama tana fad'in.
"Suna na Saima 'yar gidan Alhaji Buba 'yarsa tilo guda d'aya da akeji da ita tamkar kwai, nice
first kuma nice last a gidanmu, bawai nazo wajen nan dan wani abu ba, nazone intayaka
murnar dawowarka k'asarka lafiya sanna in sanar maka irin son da nake maka, sauran bayani
zan baka numberta sai muyi magana a waya".
Duk zubar datake ko kallon inda take bai yi ba, shidai burinsa kawai ya fita daga kokwanton da
zuciyarsa takeyi masa, aransa yana fad'in.
"To idan wannan 'yar gidan Alhaji Buban dana sani ce waccan kuma da take min aiki
wacece?".
Babu amsa domin maganar aransa yake yinta bai ko yi k'ok'arin tambayarta ba, sai ji yayi ta
zare wayarsa dake rik'e a hannunsa binta kawai yayi da kallo kafin ya mai da kansa kan
al'ummar wajen, sai da ta sanya numberta a wayarsa ta d'auki tasa a tata wayar sannan ta ajiye
masa wayar a gabansa ta mik'e ta shiga filin rawa.
'Yam matan dake wajen baki d'aya sun raina kansu, da had'uwa da kud'i irin na Saima, samari
kuwa tuni sukayi ca a kanta kowa yana zuba mata kud'i, domin su sami shiga a wajen ta duk da
sun saddak'ar ita d'in ta Yarima Fudhal ce.
Shidai Yarima bai ko taka inda ake rawar ba, har suka gama aka hau d'auke d'auken hotuna
kuma.
11:30pm
Sai sha d'aya na dare aka tashi kowa ya nufi hanyar gidansu, Yarima ya dawo a gajiye wanka
kawai yayi da sallah ya nemi makwancinsa ya kwanta, yana Allah Allah gari ya waye ya
warwarewa zuciyarsa wasi-wasin da take ciki.
*** ** ***
7:30am.
Muryar Aynu ita ce tayi sanadiyyar ta shinsa daga dad-da d'an baccin da yake, domin da k'yar
dama ya samu yayi sallar asuba ya koma, domin shi mutum ne da baya wasa da sallah ko
kad'an, mik'a yayi tare da salati ya mik'e ya nufi toilet ba tare daya kula da gaishe shin da take
ba, domin inda sabo yaci ace ta saba da halin Yarima.
Nan d nan sai gashi yafito falo Aynu ta cika da mamakin shirya warsa da wuri haka yau,
lokacin Saima na zaune ta gama jere masa abincin, zama yayi yana mai k'urawa Saima ido, sai
dai wani abu daya rud'ar da shi akan Saiman jiya da wadda take masa aiki shine.
Wan nan bak'ace waccen kuwa farace sol kamar a tab'a fatarta jini ya zubo duk da manyan
idanuwansu yazo d'aya, sannan kuma ta jiya tana da hip sab'anin wannan siririya.
"Ke ! mik'e tsaye".
Sukaji saukar muryarsa akunnu wansu da sauri suka mik'e duka, sai kuma ya tuna ai ta jiya ta
sanya dogon takalmi ne bazai iya tan-tance tsayunsu ba.
"Mene sunanki?".
"Ay....".
Aynu tabud'e baki zatayi magana yakatseta da fad'in.
"Ba ke ba ".
Ba tare daya dubeta ba, domin idonsa na kafe kan Saima kawai.
Tayi shiru abinta tana kallon ikon Allah yau.
"Saima ".
Ta bashi amsa, sai yaji muryar Saiman jiya tafi siririya akan ta wannan, kai ya girgiza yana fad'in
"Sunan ne yazo d'aya tare da kama kenan?".
A fili yayi maganar yayin da Saima da Aynu suka dubi juna, Saima ta jefawa Aynu wata
muguwar harara, Aynu kuwa ta mayar mata da murmushi.
Mik'ewa yayi ya fice ba tare daya bi takan abincin nasa bama.
Kai tsaye shashin mahaifiyarsa ya nufa, ya sameta tana bada umarnin wasu abubuwa a gidan
neman guri yayi ya zauna yana mai gaishe da mahaifiyyar tasa yayin da ma aikanta suka
gaishe da shi, bai amsa ba suka mik'e duk suka fice.
Sai yayi shiru kuma yana jujjuya wayarsa a hannunsa, kallonsa Fulani Bingel ta tsayayi tana
karantar yanayinsa.
"Lafiya Magaji?".
A jiyar zuciya yayi kafin ya fara magana.
"Hajiya dama a kwai mutanen da zakiga basu san junaba basu had'a wani relation ba amma
kuma kiga suna kama sosai?".
Fulani Bingel tad'anyi dariya tana fad'in.
"Magaji kenan ! to ai ko wanne mutum da kagani akwai copy d'insa bakwai a duniya, wani
abune ya faru kake wan nan tambayar?".
"A'a babu komai".
Abin da yace kenan bai sake magana ba, yamik'e ya shiga b'an garen Kakarsa Mai Babban
d'aki, anan yayi breakfast d'insa bai bar wajen taba sai k'arfe biyu da aka kira sallar azahar ya
fito ya tafi masallaci, kafin ya dawo su Aynu tuni sun gama aikinsu sun nufi gida, ya shige
d'akinsa ya kwanta abinsa.
***
BAYAN SATI GUDA !.
Sati guda kenan da had'uwar Saima da Yarima Fudhal kullum tana zuba ido taga kiransa a
wayarta, amma girman kai da jiji da kai ya hana ta nemeshi ita, yayin da shi kuma yama mance
da al'amuranta domin shi mutum ne da baya son sanya abu aransa domim yan zunnan sai abin
ya nemi ya zame masa matsala tunda ya samu Mahaifiyarsa tayi masa bayanin ana samun
copy d'in mutum bakwai aduniya shikenan domin dama kokwan tonsa ko ta zo aiki gidanne
sabida wani nufi nata amma yanzu zuciyarsa ta bashi waccen Saiman daban wadda ke masa
aiki daban.
B'angare guda kuma kwana uku kenan Aynu batazo aiki ba sabida Ummanta dake kwance
babu lafiya, sai dai ta fad'awa Zainab ta sanar a gidan sarki kada aga bata zuwa, Jakadiyya
tace babu komai taje ta sanarwa Yarima shima cewa yayi ba damuwa sannan ya ciro dubu
biyar yace a bata su sai magani Jakadiyy da kanta ta kai musu gida domin macace mai kirki da
rik'on gaskiya da amana.
A rana ta biyar ne Aynu taga jikin Mahaifiyar tata yayi sauk'i ta shirya tace zata koma aiki ta
yima Ummanta sallama da Babanta ta tafi.
7:30am.
Bakwai da rabi na safe kamar yanda ta saba ta isa gidan, bayan taje ta gaishe da Jakadiyya ta
gaida Fulani Bingel kai tsaye kuma b'angarensu Yarima ta nufa.
Tana shiga taga Naja ta fito daga d'akin Yarima Jalil da alamun rashin gaskiya a fuskarta,
Aynu tayi kaman bata ganta ba ta wuce d'akin Yarima.
Kamar yanda ta saba batayi tunanin komai ba tasa kai cikin d'akin, yanda ta ganshi ne ya sata
zubewa bisa gwiyoyinta ta runtse idonta k'am jikinta na faman b'ari kamar mazari.
Ta mudubi ya ga shigowarta a fili ya furta.
"Ohhh my God !".
Yana mai dafe goshinsa.
[17/07, 16:25] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
SADAUKARWA:- Namesy ta Pheerdauceey Jeebour.
Amma wannan page naki ne SAFIYYA GALADANCHI Allah yabar zumunci.
08
"Ohhh my God !".
Ya fad'a yana mai dafe goshinsa.
Aynu kuwa tuni hawaye ya fara zarya a kan kuncinta harta saddak'ar yau aikinta yak'are a
gidan.
"Wanne kuskure tayi da har ta shigo ta taddashi a wannan yanayin?".
Tayi tambayar cikin ranta.
"Sallama !, Ita ce kuskuren da nayi da a ce nayi sallama da ban shigo na same shi a haka ba,
da yayi k'ok'arin kintsawa kafin shigo wata, ko ya da katar dani harya suturce jikinsa".
"Wayyo Allah na !".
Ta fad'a a fili kuma da k'arfi wanda har sai da Yarima Fudhal dake k'ok'arin suturce jikinsa ya
juyo yana dubanta, wannan shine karo na farko da Yarima ya tab'a duban fuskar Aynu tun
zuwanta gidan aiki, gabansa ya buga dammm, yayi saurin d'auke kai yana mai ci gaba da
sanya rigarsa tare da tunanin yanda a kaima tazo ta taddashi a haka, aransa ya furta.
"Kuskure na ne !".
MINTUNA TALATIN DA SUKA WUCE
Kasancewar Aynu ta daina zuwa aiki kwana biyu sabida jinyar Ummanta, sai aikin wankin
toilet da shara ya koma hannun Saima duka.
Yau ya tashi yajishi a gajiye ga kuma gumi da yaji yanayi duk da sanyin AC da ke d'akin amma
hakan bai hana shi jin zafi ba, ha kan ne yasa ya nufi toilet domin watsa ruwa.
Sai dai Yarima nada wata al'ada guda d'aya, kasan cewarsa mai tsafta da kuma kyankyami
shiyasa ko kad'an baya iya barin abu jik'ak'k'ema ajikinsa yana fitowa daga toilet yake wurgi da
towel d'insa sannan ya nemi wani ya d'aura ko ya bari ya gama shafa mai da koma kafin ya
suturce jikinsa, sabida ya san babu mai shigo masa d'aki sai da izininsa hakan ya kuma zame
masa jiki sosai, to yauma a hakan ne Aynu ta shigo ta tadda shi.
Yana gama sanya rigar ya sake dawo da dubansa kan Aynu da jikinta ke ta tsuma tana jiran
saukar duka ko wani