Showing 15001 words to 18000 words out of 88612 words

Chapter 6 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8308

Sayyadi aikin dana samu ne sai a hankali, ban cika da wowa gida da wuri ba".

"To ikon Allah adinga dai daurewa ana zuwa".

"Insha Allahu kuwa".

Zuwan Babanta dake shirin shiga gidan ya ka tsesu daga tattau nawar da suke, Ya Sayyadi ya
durk'usa ya gaishe da Babanta cikin girmamawa, shima ya amsa fuskarsa fal farin ciki ya wuce
ya barsu nan, yana shiga gida Ya Sayyadi yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta koma cikin
gidan.

Tana shiga taji Ummanta da Baban nata suna tattaunawa akan Ya Sayyadin ita dai bata tsaya
taji mai suke fad'iba ta cigaba da aikinta ganin babu wanda ya sakota a zancen.


*** *** ***

Yaune ta kama ranar da za'a fara biyan su Aynu albashi, tun asuba ta tashi zuciyarta fes cike
da nishad'i, nan da nan ta kammala komai nata na gidan kafin k'arfe bakwai da yake Zainab ta
bata wani k'aramin agogo da shi take amfani, bakwai nayi taci abinci tayi komai ta kama hanyar
zuwa gidansu Zainab domin su tafi tare.
Tana isa ta tadda itama ta gama shiryawa suka kama hanya.

Yau dai ta tadda Yarima Fudhal ya war-ware tsaf har ya tashi yayi wanka ya shirya yana
zaune gefan katifarsa ta taddashi, ta durk'usa ta gaishe da shi ya amsa fuskarsa cike da fara'a,
ta mik'e ta nufi toilet ta kama aikinta.

Tana fitowa ta cigaba da sauran gyare-gyarenta k'arfe takwas akai kiransu za'a bawa kowa
kud'insa na aiki.

Su nasu b'an garen har k'ari suka samu daga dubu goma sha biyar zuwa a shirin ba k'aramin
dad'ine ya rufe Aynu ba sosai tana tafe tana lissafin abubuwan da zasu siya sai ji tayi taci karo
da mutum taja baya da sauri tare da d'ago kai sai taga ashe Yarima Fudhal ne, ya kuwa had'e
fuska kamar bashi ne ta ganshi d'azu cikin fara'a ba.
"Bani kud'in !".

Yayi maganar babu alamun sassauci, jiki na b'ari ta mik'a masa yasake kallonta yana fad'in.

"Jeki kawomin breakfast".

Ba musu ta juya ta nufi kitchent domin cika umarninsa.


Haka tayi ta zaryar shirya masa breakfast sai da ta gama ta had'a mai komai ta mik'a masa
sannan ta koma gefe tana jira ya gama, komai baya wuce cokali d'aya zuwa biyu yake ci ya
gama ta kwashe kwanukan ta mayar ta dawo ta zauna kenan yace taje ta kawo masa fruit, haka
ta sake mik'ewa taje ta kawo, ta kuma zauna a gefansa yana daga kishingid'e tana yankawa
tana mik'a masa yana sha, musamman apple ta fahimci yana cinsa sosai.

Sai da ya gama ta kwashe ta mayar ta dawo ta zauna ta jira taji yace ga kud'inta ta tafi, amma
taji shiru gashi tana jin nauyin tambayarsa sai dai ta dubeshi kaman zatai magana sai taji ta
kasa.


Sun jima a haka kafin yamik'e ya shige cikin d'akinsa, ya barta nan zaune tana tufka da
war-wara.

"Aynul-hayat !".

Taji ya kira sunanta ta amsa a hankali tana mai nufar d'akin nasa da sallamarta ta sanya kai
d'akin.

"Zo nan".

Ya kuma kiranta ta k'arasa inda yake a zaune gefan katifa ta durk'usa tana kallon ikon Allah.

Kud'ine dank'am a gabansa tun daga dollar zuwa dubu-dubu d'ari biyar-biyar 'yan d'ari biyu har
zuwa kan naira biyar kowanne bandir-bandir.

"D'ebi duk yanda ki keso".

Aynu ta saki baki tana dubansa, sai take ganin abin kamarma wasa yake mata.

"D'ebi mana".

Ta kai hannu kan 'yan goma ta d'auka, dariya ya d'anyi yana fad'in.

"Sarkin tsoro".

Karb'a yayi ya d'auki bandir d'in 'yan dubu ya mik'a mata, girgiza kai tayi alamu a'a, shiru yayi
Yarima yana dubanta cike da mamaki fal cikin ransa.

"Kyauta tace a gareki karb'i".

"A'a nidai ka bani kad'an, sunmin yawa wad'annan".

Jujjuya kud'in yayi tayi na wani lokaci kafin yayi murmushi yace.

"To idan na k'ara miki goma akan naki zaki karb'a?".

Shiru tayi ba tare da ta ce dashi komai ba, ya irgo dubu talatin ya mik'a mata ta k'i karb'a.

"Idan baki karb'i wannan ba sai dai ki rasa kud'in naki duka".

Aynu ta dube shi da sauri ya gyad'a kai alamun da gaske yake, hannu biyu ta sanya ta karb'a
tana yi masa godiya, yace baya buk'atar godiya nan da nan taja bakinta ta tsuke.


***

Aynu ce zaune gaban Ummanta tana faman lissafin abin da ya kamata su saya, Ummanta ta
murmushi tayi tana fad'in.

"Aynu kenan !, to ai duk lissafin da kike kud'in ba zasu kai ba sai dai asayi abin da ya samu
kawai".

"To Umma amma dai ya kamata musayi atamfa ko ta dubu d'aya da d'ari biyu ce, sai a
asiyawa Baba yadi shi kuma ya d'inka, sauran sai mu sayi takalma da ta barma ko?".


"Uhmmm yanzu dai d'auki dubu biyu ki kaiwa mai shagon da muke karb'o sabulu, ki bashi
dubu kud'insa ne da yake binmu, dubu d'ayan kuma ki siyo silifas ki sayo mana sabulun wanka
da wanki tare da makilin".

"To Ummata".

Ta fad'a tana mai mik'ewa tare da d'aukan kud'in ta fice.

A hanya ta gamu da Ya Sayyadi suka gaisa yana fad'in.

"Ina zaki haka da rana tsaka?".

"Ummata ce ta aikeni".

"To masha Allahu muje in taka maki".

Haka suka tafi suna hira jefi-jefi har zuwa shagon tayo siyayyar suka dawo tare har k'ofar gida
ya rakota sukai sallama ya tafi.

A ranar dai aka siyawa Aynu sabon hijab da atamfa Daviva guda biyu suka sayi sabuwar
tabarma da 'yan kwanuka da cofuna domin nasun duk sun lalace.

Aynu sai jinta take kamar sun shiga wata sabuwar rayuwa, jinta take kamar ba ita ba yau ita
ce da sabon d'inki abin da sai dai abata kwance yau kuwa gashi ta d'inka da guminta.

"Alhamdulillahi, Alhamdulillahi ala kulli halin !".

Abin da take ta faman mai-mai tawa kenan cikin ranta cike da nishad'i da jin dad'i.



7:40am

Yau dai Saima ta rigata zuwa gidan, sabida yau ta makara sosai ko da ta gaishe da Yarika k'in
amsawa yayi bata damu ba domin tasan halin sa, tayi dukkan abin da ta saba ta gama ta nemi
guri ta zauna, har lokacin ko kallonta bai yiba gefe guda kuma ga Saima sai faman wani ciccika
take tana batsewa da zaran sun had'a ido da Aynu ta jefe ta da harara.
"Zaku iya tafiya".


Suka ji muryarsa yana basu umarni, ko wacce tamik'e ta fice daga d'akin a hanyane Aynu ta
dubi Saima tana fad'in.

"Kwana biyu bakya zuwa har anyi albashi....".

Bata k'arasa maganar ba Saima ta katseta da fad'in.


"Ke kud'in ya dama".

Ta wuce ta barta nan tsaye tana searching d'in maganar Saima.

"Me take nufi da ni kud'i ya dama?".

Kafin ta kai da bai wa kanta amsa sai ganin Yarima Jalil tayi a gabanta fuskarsa fal murmushi
yake fad'in.

"Beauty kin b'uya !? ko da yake naga Yayan namu baya buk'atar ganinmu tare".

Aynu ta tsaya tana nubanshi dan ko kad'an bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba.

"Zauna nan magana za muyi da ke".

Yayi mata nuni bisa d'an da kalin dake kusa da su, Aynu ta zauna shima ya zauna gefe da ita
kad'an.

"Kin san wani abu?".

"A'a sai ka fad'a".

"Wai me yasa Yarima baya son gani na da ke ne?".

"Nima ban sani ba gaskiya".

"Ok".

Shiru ne ya biyo baya na d'an wani lokaci, kafin yasake dubanta yana fad'in.

"D'an juyo nan".

Aynu ta zuyo tana dubansa, ya kai hannu gefan fuskarta yana fad'in.

"Wani abu ya b'ata beauty face d'inki bari in goge miki".


"Jalil.....!".

Suka ji muryar Yarima Fudhal akansu, Yarima Jalil ya sauke hannunsa yana fad'in.


"Sannu da fitowa Broda".

Bai ko dubeshi ba, illa kafe idanuwansa da suka fara rinewa daga fari zuwa ja akan Aynu da
yayi, a hankali ya furta.

"Jeki k'arasa aikin ki".

Sum-sum Aynu ta wuce zuwa falon Yarima ita dai tasan ta gama aikin ta, may be wani aikin zai
saka ta abin da ta raya aranta kenan.

Mintuna kad'an da zamanta ya shigo fuskarnan babu annuri neman guri yayi ya zauna yana
fad'in.

"Had'amin tea".

Da rawar jiki ta mik'e ta zuba masa tea d'in tafa shashshe sosai, yace ka da ta sanya komai illa
sugar nan da nan ta had'a ta mik'a masa yasa hannu ya karb'a, tana shirin mik'ewa taji ya jawo
hannunta kafin ta ankara sai jin rad'ad'i da azabar zafin ruwan tea d'in tayi bisa hannunta wanda
ya ratsa har cikin kwakwalwar kanta. [20/07, 14:40] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*




Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA :-Namesy Pheerdauceey Jeebour.



(RAZ) ku matso kusa wannan page d'in nakune AMRAH, ZAHRA, RABI'ATU....Allah yabar
manaku ya k'ara donk'on zumunci da k'aunar juna Inayin ku irin sosai d'innan (Raz).

11



Har cikin kwakwalwar kanta ta jiyo rad'ad'i da zafi na ruwan tea d'in, ta kafe Yarima da
idanuwa cike da kallon mamaki mai d'auke da tambayar me nayi maka?.

Shima Yarim ita ya kafe da idanuwa yana karantar yanayinta can ya kau da fuska gefe yana
mai naushin hannunsa na hagu da hannun da mansa game da furzar da iska daga bakinsa mai
zafi.

Aynu kuwa ta kasa magana illa hawaye dake zarya bisa kuncinta kawai tarik'e hannun da
d'ayan da babu k'unar.

Yarima yayi k'asa da kansa ya dafe da hannu na d'an wani lokaci, kafin ya d'ago ya sake
kafeta da ido a karo na biyu, tsaki ya d'anja kad'an yana mai sanya hannunsa ya kamo nata
daya k'ona ya dubi hannun tare da duban fuskarta.

"Am so sorry...nayi hakanne domin ki fahimci irin k'unar da na keji a duk lokacin dana ganki da
Jalil, why me yasa kika kasa fahimta har na kai da yi miki wannan hukuncin?".

Ita dai Aynu kallonsa kawai take domin ko kad'an bama ta fahimtar me yake fad'i, azaba ta
isheta hawaye kawai take fitarwa domin kuka mai sauti ma k'in fita yayi daga bakin ta a wannan
lokaci.

Kai hannu yayi kan fuskarta da niyan share mata hawayen sai kuma ya fasa, ya dubeta yana
fad'in.

"Da zafi sosai ne?".

Kai ta kyad'a masa alamun ehh.

"Sannu yi hak'uri !".

Abin da yace da ita kenan yaja hannunta suka fito zuwa waje, haka yayi ta janta har suka isa
b'angaren Fulani Bingel duk inda suka wuce sai a bisu da kallo amma kasancewar Yarima
Fudhal ne kowa yasan babu wasa da sun had'a ido da mutum zaiyi k'asa da kansa yana gaishe
shi.
Shi kuwa Yarima bai cika niba har sai da muka isa cikin falon mahaifiyarsa, Fulani Bingel na
ganinmu ta mik'e tsaye tare da fad'in.

"Lafiya Magaji?".

"Hajiya kira doctor d'inki ".

Fulani Bingel ta bishi da kallon mamaki cike da tambaya.

"Mai ya faru da ita?".

Yarima neman guri yayi ya zauna ya dubi sauran masu aikin dake d'akin.

"Ku bamu waje".

Sum-sum ko wacce ta fice ya rage daga ni sai Yarima da Hajiyarsu.

Fulani dai ta kafeshi da idanuwa tana jiran amsar sa.

Yarima yad'an yatsina fuska kafin ya bata amsa da fad'in.

"K'onata nayi".

"Subhanallah ! garin yaya?".

Cewar Fulani kenan tana mai k'arasowa wajena, taga hannuna yayi jawur ta mai da dubanta
kan Yarima.

"Akan me ka aikata wannan d'an yan aikin?".

"Hajiya ita ta jama kanta fa !, na gaya mata bana son ganinta da Jalil ba ta ji ne yarinyar !".

"To dan baka son ganin ta da Jalil sai kayi mata wannan mugun hukuncin ?, mai yasa bazaka
fad'amin ba ko kayi mata hukunci dai-dai misali".

"Abin da nake ji araina ne !, shine na gwada mata taji yanda nakeji ko tafi fahimta".

Fulani Bingel sakar baki tayi tana duban sa cike da mamaki ko mamakin me take yi oho?, sai
dai ta kalleni ta kalleshi.

Ajiyar zuciya tayi tana fad'in.

"Mai zai hana ka kira likitanka?".

"Haba dai Hajiya Namiji ne fa?".

"Dan namiji ne bazai duba taba".

"Ina ! A'a gaskiya ki taimake ni dai ki kira likitarki dan Allah Hajiya kinji?".


Ya k'arashe maganar kamar zaiyi kuka, ni dai ina zaune ina jin ikon Allah tun da nake da
Yarima yaune karo na farko da yayi doguwar magana kuma duk a kaina, ga shi kuma babu ko
kunya ko nauyi ko shakka bare jin tsoro yana sanarwa mahaifiyarsa da kansa ya k'ona ni !, nidai
sai na nemi hawaye na rasa tsabar mamaki da al'amarin Yarima Fudhal.
Hajiyarsa girgiza kai kawai tayi tana dubana ta d'auki waya bugu d'aya tayiwa likitan bayanin
abin da yake faruwa, muna ji likitan ta amsa da cewar ga tanan zuwa da yake wayar a free ta
sanya ta.

Hajiya ta ajiye wayar tana kallon Yarima da yayi ta gumi yana kallonta, ta jima tana nazarin
Yarima Fudhal ba tare da tace komai ba, haka shima bai kuma fad'in komai ba, baka jin k'arar
komai a d'akin sai k'arar A.C da ajiyar zuciyata jefi-jefi sabida kukan da nayi.

Muna haka har Doctor Hafsat ta shigo ta tadda mu, ta gaishe da Hajiya da Yarima Hajiya tayi
mata bayanin nice na k'one da ruwan zafi, nan da nan tayimin allura tare da bani magani domin
k'unar bata tashi ba bare ace za'a wanke, tayiwa Hajiya sallama ta tafi domin tana bakin aiki ne
ta tawo.
Tana fita Hajiya tace.

"Ka da ka sake mai-maita hakan kana jina?".

"Insha Allah".

Abin da yace da ita kenan, yana mai kwanciya kan kusun, Hajiya tace.

"Mai yake shirin faruwa tsakaninka da yarinyar nan?".

Yarima ya mik'e ya zauna tare da dubana yana fad'in.

"D'an bamu waje".

Na mik'e na fice abina dama duk a takure nake jina.

"Ka da dai kacemin sonta ka ke?".

Murmushi Yarima yayi yana sosa k'eyar kansa jin tambayar da Hajiyan tasa take yi masa.

Fulani Bingel tayi ajiyar zuciya domin ta fahimci komai tun farkon tattauna warsu.

"Ka da kamance 'yar aikin kace, 'yar aiki kuwa a gidan nan tamkar bayi ne ko ka mance ne?".

"A'a".

"Kasan ko Mai Martaba bazai tab'a yarda ba idan ni na amince !".

Dammm gaban Yarima ya buga amma ya dake ba tare da yace komai ba, Fulani ta cigaba da
fad'in.

"Duk bama wannan ba, kasan cewa ana nema maka auren Gimbiya Safiyya kuwa?".

A firgice Yarima ya dubi Fulani.

"Safiyya kuma ni nace ina sonta ne har da za'a nema min aurenta?".

"A'a zab'in mahaifinka ne, to ita wannan d'in tasan kana son tane?".

"A'a amma ai zan fad'a mata lokaci nake jira, amma Hajiya da gaske kike akan maganar
Safiyya?".

"Na tab'a yi maka wasa ne ?".


Yarima ya girgiza kai alamun a'a, yayin da kuma zuciyarsa ke ta aikin bugawa da sauri da sauri
hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, har sai da Fulani Bingel ta fahimci haka ta dafa kafad'arsa
tana fad'in.

"Kada ka d'aga hankalinka Magaji ka nemi zab'in Allah kawai, domin kafi kowa sanin waye Mai
Martaba".

"Amma Hajiya ki fahimtar dashi mana nifa gaskiya bana sonta".

"Kai mai zai hana ka sanar dashi, zaifi fahintar maganarka akan tawa ma".

Yarima ya dubi Mahaifiyartasa kafin ya kau da kai gefe zuciyarsa na cigaba da k'una, gefe
guda kuma yana tunanin mafita akan wannan batun.



***


Aynu kuwa na fita inda ta saba zama taje ta zauna ta had'a kai da gwiwa tana kuka, ji tayi an
dafa kafad'arta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login