Showing 6001 words to 9000 words out of 88612 words

Chapter 3 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8312

muka fara neman yafiya.


Bai ce komai ba ya shige cikin d'akinsa kawai ya barmu nan zaune.

Cike da tsoro namik'e nahau tsince kayan marmarin, Jakadiyya tace insameta b'angaren
Shamaki, suka fice ita dasu Saima suka barni, nan da nan na share wajen na gyare tsaf,
sannan natafi filin shamaki.

Nan na iske sauran ma aikatan gidan wasu na aiki wasu na hirarsu ciki har da Jakadiyya, naje
inda take na durk'usa ta dubeni kafin ta fara magana.

"Mai kika yiwa Yarima?".

Nan na bud'e baki na bata bayanin dukkan abin da yafaru, shiru tayi nad'an wani lokaci kafin ta
cigaba da fad'in.


"Idan aka kai kayan marmari yayyan kawa ake a ajiye a gefen su, wani lokacin kuma a
hannunki zaki rik'e kina yankowa kina mik'a masa yana ci, idan abinci ne zubawa zaki ki ajiye
masa ki zauna gefe har saiya gama ci wannan aikin su Naja ne, sannan dole ki dinga zuwa da
wuri kamar k'arfe bakwai na safe ki gyare ko ina na d'akinsa ki share, ki wanke toilet tsaf ki saka
turare, idan ya shiga wanka kafin ya fito ki gyare gado da d'akin ki kunna turaren wuta, amma
ke aikin ki uku ne wanke toilet d'innan da share cikin d'akin, sannan ki kai masa dukkan abin da
yake da buk'ata ina fatan kin fahimce ni".


Kai kawai na gyad'a mata domin nakasa magana, ta mik'omin wata leda viva tana fad'in.

"Ingo naki abinci kije gida, gobe kizo da wuri".

"To nagode".


Nafad'a ina mai mik'ewa na baro shamaki na nufi d'akin da muka canja kaya na d'auko kayan
dana cire tare da set gudan na unifoam d'inmu.


Zan fito daga gidan kenan muka gamu da Zainab zata tafi gida ita ma da murnarta ta tarye ni
muka fito tana fad'in.

"Ashe baki tafi ba?, naga farkon zuwa ana tafiya da wuri?".

"Uhmm ke dai bari ! ai Allah ne ya tarfawa garina nono dan da tuni ankore ni".

"Subhnallah ! garin yaya?".

Zainab ta fad'a tana mai zaro ido waje.

Nan dai na bata labarin abin da ya faru, ta d'anyi shiru kafin tace.

"Sai kiyi hankali sosai da taka tsan-tsan, mancewa nayi wallahi inyi maki bayanin ayyukan
gidan, amma yan zuma bari infad'a miki tun da Allah yarufa mana asiri ba'a kore kiba".

Muna tafe tana yimin bayani har muka iso dai-dai layin mu mukayi sallama na shige gida ita
kuma ta wuce zuwa gidan su.


Ina shiga Ummata ta tarbe ni cike da murna nan na zauna inata zuba mata labarin gidan
sarki, ita kuma ta nata gargad'ina inkula sosai inyi abinda ya kaini ka wai ban da sha shanci, har
dai da taji batun b'angaren Yarima zan dinga yin aiki, taji kuma irin tsarin aikin nawa, nan dai
tayi tamin nasiha ban sanar mata abin da ya faru ba ko kad'an nayi shiru da bakina a ganina ba
abin da zan sanar mata bane.


Na dauko kwanuka na juye abincin dake cikin ledar sai naga dukkan abincin da muka kaiwa
Yarima ne, nan muka baje muka kwashi gara cike da farin ciki har na mance rabon da tsokar
nama ta shiga baki na, Baba na dawowa na kai masa nashi abinci yakarb'a yaci yana ta samin
albarka. [07/07, 16:16] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©



05



*WASHE GARI*


Washe gari ma tun da na tashi da asuba ban koma ba, nan da nan nayi dukkan abin da na
sabayi kullum sannan na d'umama mana ragowan abincin da nazo da shi jiya, naci na barwa su
Ummata sauran.


6:30am

K'arfe shida da rabi agidansu Zainabu tamin, ko da nazo ta gama shiryawa itama tana jira na
muka yiwa Babah Tasallah sallama muka tafi.

Muna isa gidan da Jakadiyya muka ci karo tana ta zirga-zirga, muka gaisheta ta amsa tana
k'ara gargad'ina akan inkiyaye sosai nace.


"To insha Allah".

Muka wuce Zainabu tayi b'angaren Fulani Bingel ni kuma nayi b'an garensu Yarima da yake
b'angaren Yarima Fudhal dana Jalil a had'e suke daga ciki ne aka rabasu amma k'ofar falon ko
wanne d'aki tana kallon d'ayar.


Da sallamata na shiga falon babu kowa ciki sai k'arar fanka da Tv kawai ke tashi.

Na nemi guri na zauna ina kallon k'ofar cikin d'akin nasa zuciyata na bugu, innayi kamar in
tashi in shiga sai inji na kasa, ahaka na shafe kusan mintuna talatin a zaune, da k'yar dai nayi
k'arfin hali na mik'e na sanya kai cikin d'akin muryata k'asa-k'asa nayi sallama.


Wani sanyi da k'amshi ya doki hancina, na d'aga kai ina kallon d'akin naga d'akin nasa kamar
ba a nigeria ba, kayan cikin d'akin nidai tun da nake ban tab'a ganin irin suba, ga wata uwar
katifa gado guda yana kwance abinsa abin mamaaki sai naga idonsa biyu yana dai sana'ar tasa
danna waya.
Na k'arasa na zube na gaishe da shi bai amsa min ba kamar yanda bai ko kalli inda nake ba, na
mik'e da sauri na shege toilet na fara wanke shi domin ina tsoron insake yin wani laifin.

Na wanke tas na sanya turarukan toilet sannan nafito domim insanar dashi cewa na gama, bai
kalle niba illa zubo dogwayen k'afa fuwansa da yayi bisa lallausan carpet d'in dake shimfid'e
tsakar d'akin, daga shi sai boxer abinsa, ya sanya takalmin da nagani gefan katifar yashige
toilet.
Abin ya bani mamaki sosai ta kalmi a kusa da katifa, nan dai na mik'e a gaggauce na gyara
katifar tasa na share ko ina na goge, akan mudubin sama nasha mamaki sai kace wani mace,
kayan shafe-shafe kala-kala duk ciki babu wanda na tab'ani haka nagama k'are masu kallo
danni ba wani iya karatun kirki nayi ba bare in karanta.
Naso yin karatun boko arayuwata amma Allah bai yarjemin ba, iya kacina primari 5 na daina
zuwa sabida halin rayuwa na talauci daya sanyamu agaba, islamiyya ce dai nake zuwa har
yanzu sabida ita sun d'aukemin biyan ko wanne kud'i dan sun san halin da muke ciki suna
tausayawa rayuwata ainun, gashi itama ina ina neman dai na zuwa sabida wannan aikin.
"Tab ! bazai yuyuba yau kam dole inje islamiyya, domin bazanyi biyu babu ba".

Na fad'a a fili ciki-ciki ina mai cigaba da gyara d'akin.


Ashe ma har yafito bansani ba ina can ina zancen zuci, sai da naji ana tab'a kwalaben kan
mudubi sannan na lura da yafito, ban ko kalli inda yake ba na fice falo abina.

Saima na gani a falon tana shirya masa abin kari, muna had'a ido da ita ta jefeni da wata uwar
harara, ni kuwa nad'auke kai na kamar ban san tana yiba, nayi zamana abina ina jiran umarnin
Yarima.

Sai dai kuma naga ba'a gyara falon ba amma tajere masa abin kari.

"Meye zai dame ni ma tunda ba aikina bane?".

Nayi maganar cikin rai na, sai da muka shafe awa guda zaune sannan mukaji takun fitowar
Yarima, muka mik'e tsaye kanmu a k'asa ya tako cikin takun k'asaitar nasa k'amshinsa mai
sanyi ya cika falon, ya nemi guri ya zauna ba tare daya ko dubi inda muke ba bare abincin da
aka jere masa.

"Ohh ikon Allah ! ni dai tun da nake arayuwata ban tab'a ganin miskilin mutum irin Yarima ba, ko
d'an yana tak'ama da mulki da kud'i ne oho".

A cikin raina nake ta zancen ni kad'ai, Saima naga ta matsa tahau jere masa abin kari kala-kala
ni wani girkinma ko ganin irinsa ban tab'ayiba bare ince na ci.

Da katar da ita yayi da hannu ba tare da yayi magana ba.

Ina ganin haka 'ya'yan hanjina suka kad'a tsoro ya kamani ko wani laifin muka sakeyi.

"Kira Jakadiyya".

Abin da kawai ya furta kenan ya cigaba da aikin sa ko ince sana'ar tasa.

Da rawar jiki na fice na tafi neman Jakadiyya, wata mata Ladidi na tambaya tasanar min tana
b'an garen Fulani Sokoto ai kuwa can d'in na nufa.


Ina shiga na zube na kwashi gaisuwa wajen Fulani Sokoto, wani kallo ta watsomin kafin tace
da Jadiyya.

"Wannan kuma fa?".

"D'aya ce daga cikin ma aikatan Yarima".


"Cikinsu har da yarinya irin wannan ?".

"Ehh Yarinyarce suna fama da gararin talauci ne, tazo aikine domin su dunga samun abin da
zasu ci".

Sai naga Fulani Sokoto tayi murmushin da bansan ko na mene neba, araina ina tunanin meye
yasa zatayi wannan maganar akaina?.

"Meke tafe dake?".

Maganar Jakadiyya ta katse n i daga tunanin da nake, na bata amsa da fad'in.

"Yarima keson ganinki da gaggawa".

Ta mik'e tana yiwa Fulani Sokoto sallama nima nabiyo bayanta, a hanyarmu ta zuwa
b'angarensu Yarima ta dube ni tana fad'in.

"Ki iya takunki da kowa a gidan nan, ki kame kanki kada ki soma shiga abin da ba ruwanki,
sannan kiyi taka tsan-tsan da al'amuran b'angaren Fulani Sokoto".

Ni dai har tagama bayaninta ban fahimci komai ba, sabida tunani na yagama bani yau korata
z'ayi kawai tuni na fara matsar kwalla.

Muna shiga ta zube a gabansa nima haka, Saima kuwa dama tana inda nabarta illa gani da
nayi ta zubawa Yarima ido kamar zata cinyeshi


Bai ko kalli inda mukeba ya fara magana.

"Gaskiya wa 'yannan basu san aikin su ba, in da dama acanja wasu".

Jakadiyya ta russuna tana fad'in.


"Sunyi laifi ne ranka dad'e?".


Ya tsuna fuska yayi kafin ya bud'e baki a hankali yana magana.

"Ya za'a ajiyemin breakfast ba tare da anshare ba?".

"Ayi afuwa Magajin gobe, Kai kace a cire mutum d'aya, to laifi nawane aga farceni ban sanarwa
Aynu gyaren falo ya dawo gare ta ba na mance ne wallahi".

Kai kawai ya gyad'a alamun ya gamsu, yamik'e ya fice daga d'akin ya barmu nan zaune,
Jakadiyya ta dubeni.

"Aikin kine Aynu share falon nan ki goge sosai kisa turare domin Yarima ma'abocin son k'amshi
ne, ki kiyaye da kyau".

"To ba damuwa".

Haka kawai nace, domin ko bata gayamin ba na fahimci irin so da k'aunar da yakewa dangin
turare, ta mik'e ta fice daga d'akin ta barmu ni da Saima, ita ma Saiman bayan ta gama kwashe
kwanukan abincin tafice abinta tana fad'in.

"Idan kin gama zaki iya zuwa ki juye abincin nan nakine, domin kece kalar yunwa".

Ta fice abinta nabi bayanta da kallo araina ina mai-maita kalmar.


"Kalar yunw? Kalar yunw?, Ehh gaskiya ni kalar yunwace kowa ya ganni zai san haka, to amma
mai yasa zatacemin haka?, na d'auka duk wanda yazo aiki yazone domin nemana abin da zai ci
ne ko?, ko kuma akwai masu zuwa aiki ne domin ra'ayi kawai?".

Ganin bani da amsa dukkan tambayoyi na, kuma babu mai amsamin yasa na hak'ura nahau yin
aikin dake gabana, duk k'ok'arina yau in koma gida da wuri domin inje islamiyya.


"Mama kina nufin Yarima Fudhal zaki nema wa auren Gimbiya Safiyya?".

Cewar Jalil kenan dake zaune gefan mahaifiyyar tasa, murmushi tayi kafin ta bashi amsa.

"Ehh mana haka nake ganin shine mafita, bayan auren zan sanar maka shiri na na gaba".

"Amma fa ni nake son tafa kin sani Mama!".

"Kai fa sha-shane wallahi mutumin da ake nema masa hanyar sarauta mai zai yi da wata
soyayya?".

"Nasani Mama amma gaskiya banjin zan iya hak'uri da sonta".

Murmushi tayi akaro na biyu kafin ta dube shi da takaici.

"Na zaci ko sanin kana sonta Gimbiya batayi ba?".

"Ehh amma aike nake nufi ki gayawa Mai Martaba anema min aurenta".

Fulani Sokoto dariya tayi mai sauti awan nan lokacin tana mai yiwa d'an nata kallon soko baka
san abin da kake yi ba, amma a fili kuma cewa tayi.


"Amma kai dai baka da tunani ko kad'an Jalil taya Mai Martaba zaiyi maka aure ga yayan ka bai
ko kawo maganar auren ba !, ka dai sake tunani amma ni maganata na gama".

Jalil yayi shiru yana duban Mahaifiyar tasa batare daya sake furta ko mai ba itama haka.

Yarima Jalil suna matuk'ar kama da Yarima Fudhal ban-ban cinsu kawai shekaru da kuma
k'asumbar fuska, Yarima Jalil shekararsa ashirin da bakwai kuma shi baya tara k'asumba a
fuskarsa illa siririn sajen da yayuwa fuskarsa k'awanya, yayin da Yarima Fudhal ke da shekaru
talatin aduniya ma'abocin tara suma ne ta kai da kuma fuska da suke shan gyara ko yaushe
wanda hakan bak'aramin kyau yake k'ara masa ba.

Mik'ewa yayi zai fice bata dubeshi ba take fad'in.

"Ka kiramin Ladidi".

"To".

Kawai yace ya fice daga d'akin, a hanyarsa ta zuwa b'angaren sane ya gamu da Ladidin ya
bata umarnin taje mahaifiyarsa na kiranta, shi kuma ya shige b'angarensu.

Fitowa ta kenan daga falon Yarima na gama gyarawa zan tafi mukayi karo da shi yana shirin
shiga d'akinsa, durk'usawa nayi na gaishe shi bai amsaba sai k'uramin ido da yayi yana bina da
kallo, na mik'e na wuce abina domin tunanina shima miskilin ne irin Yarima Fudhal.

Har sai da nak'ule ya daina ganina sannan ya shige d'akin nasa yana sosa k'ewa fuskarsa cike
da murmushi kona menene ? oho.

Yau ban jira Zainab ba sabida saurin da nake, naje na juye abincin da Yarima ya bari acikin Viva
nayiwa Jakadiyya sallama na tafi gida.
[09/07, 00:23] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)©


06




Yauma kamar kullum haka na tadda shi kwance bisa katifarsa mai kama da gado ya lullub'e
jikinsa da bargo mai taushi, hannunsa dake rik'e da waya kawai sune a waje yana
danne-dannansa.

Naje na gaishe shi duk da baya amsawa amma hakan bai sa na dai na gaidashi ba sabida
gudun yin laifi, na mik'e na wanke toilet na fito na sanar masa na gama.

Ya ziro k'afafuwansa ya saka takalmimsa yashige toilet batare daya kalli inda nake ba, ni kuwa
na mik'e na kad'e ko ina na share na goge , na kalli agogo naga kusan awa guda kenan, araina
nace.

"Wannan wane irin wanka ne?, mutum yayi awa guda a toilet kamar mai canja fata?".

A fili kuwa na furta.

"Ko da yake komai na masu sarauta da ban ne".

Jin motsin fitowarsa da nayi ne yasa na d'ebi tsin tsiya da abin mooping nayi falo, na cigaba da
gyaran falon, na kusa gamawa sannan sai ga Saima ta shigo hannunta rik'e da tire bata ko kalli
inda nake ba ta wuce inda Yarima ke cin abinci ta fara jere masa, ni kuwa na gaggauta tsaftace
falon sabida kada ya fito yaga ban gamaba.
Allah kuwa ya taimakeni bai fito ba sai da na gama na d'auke komai sannan ya fito, shigar coat
yayi fara har zuwa wando da agogon hannunsa da takalmi duk farare ne na fahimci dai baya
son manyan kaya domin tun dawowarsa banga ya saka kayan nan k'asar ba.

Yaje ya zauna yana wani shan k'amshi, Saima ta jere masa dukkan nin abin da tasan zai
buk'ata ta koma gefe ta zauna tana kallonsa, ni dai kaina ak'asa yake addu'a nake Allah ya
rabamu dashi lafiya yau.

Cokali d'aya yayi na ruwan tea wayarsa dake hannunta tahau ringing ya d'aga yana mai sata

free, domin duk muna jin abin da ake cewa a waya r sai dai bana fahimtar abin da suke fad'i
domin yaren turanci naji sunayi ni kuwa kun dai san banko k'arasa primari ba bare ince zan ji
turanci, Saima ce dai naga tana ta murmushi kamar tana fahimtar wani abu da yake fad'a a
wayar.
Yana kashe wayar yamik'e ya fice, Saima ta tattara kayan da sauri ta fice da su tabarni zaune a
falon nayi ta gumi ina wani tunani na da ban, sai kawai ji nayi andafa ni ta baya firgigit na juya
domin ganin waye?, domin tunanina ya bani Zainab ce.

Ina juyawa sai naga sab'anin tunani na a she Yarima Jalil ne, na durk'usa da sauri na gaishe shi
duk da fad'uwar gaban da nake fuskanta awannan lokaci.

Amsawa yayi yana mai cigaba da kallo na, ni kuwa kaina na k'asa cike da tsoro na furta .

"Ko kana buk'atar wani abu ne?".

Kai kawai ya girgiza alamun a'a yana mai neman guri ya zauna yana fad'in.

"Ku nawa kuke yiwa Yarima aiki?".

"Mu biyu".

Na bashi amsa a gag-gauce, yad'an tab'e baki a hankali kafin yace.

"Kina jin dad'in aiki anan kuwa?".

"Ehh".

Na kuma bashi amsa.

Shiru ya gauraye d'akin na wani lokaci, nidai kaina yana k'asa Allah Allah nake insamu in fice
daga d'akin, dan haka kawai nidai hankalina bai kwanta da al'amarin Yarima Jalil ba, ina cikin
tunanin yanda zansamu in fice daga d'akin sai kawo jin hucin numfashinsa nayi a fuskata naja
baya da sauri, bina yayi da kallo kafin yayi murmushi kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login