Showing 30001 words to 33000 words out of 88612 words
Chapter 11 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
kusa da ita cikin kuka ta hau fad'in.
"Momy Yarima Fudhal ne !".
Tsaki Momyn tayi tana fad'in.
"Me kuma yayi miki yanzu?".
"Yace duka mu biyun wai baya sonmu !, Momy ji nake kamar zan iya mutuwa wallahi indai har
na rasa Fudhal arayuwata !".
A jiyar zuciya Momyn tayi tana mai d'ago da 'yar tata zaune, ta kalli fuskarta sosai.
"Haba Saima kamar ba 'ya mace ba, kamarki ki zauna kinayi namiji kuka !, ni anawa ganin tun
da har ya furta baya sonku ki hak'ura da auren sa kawai, ki danne zuciyarki akan Yarima ki
barshi bari na har abada !".
"Momy taya hakan zai yiyu?, ina son Yarima sosai wallahi Momy ki taimake ni dan Allah !".
"Bani da wani taimako da zan iya yi miki wanda ya wuce addu'a, sannan zan sanar dake wani
abu da baki saniba arayuwa, Saima..! akan ki auri namijin da baya sonki ke kike sonshi, gara ki
auri wanda yake sonki ko da bakya sonsa, domin shi zai iya jure dukkan abin da zakiyi masa na
b'acin rai, sab'anin wanda kike so, kuma ba lallai auren yaje ko inaba kuskure kad'an zaki zai
iya rabuwa dake rabuwa ta har aba da !".
Saima zaune tayi tana sauraren Momynta kawai, lokaci-lokaci tana share hawayen fuskarta,
wayarta dake kusa da Momyn tayi ringin Momy ta d'auka ta kara a kunnensa sabida ganin
number da tayi babu suna, daga can b'arin aka hau fad'in.
"Please Saima gani nan tsaye cikin gidanku !, dan Allah yau dai kifito ko gaisawa muyi kada ki
shanyani kamar ko yaushe".
Momy ta kashe wayar tana mai kallon Saima tare da mik'a mata wayar tana tambayarta.
"Waye wannan?".
Saima ta b'ata rai kafin ta bata amsa.
"Momy wanine wallahi duk yabi ya takuramin".
"Har tsawon wane lokaci ya d'auka yana zuwa gidan nan?".
"Inajin dai zuwansa uku".
"Amma shine kike wulak'anta mutum Saima !, duk wanda yace yana sonka arayuwa ya gama
maka komai fa !, tashi ki fita".
"Momy nidai ki rabu da shi dan Allah".
Tayi maganar cikin shagwab'a har ragowan hawayen fuskarta na fitowa.
"Ki tashi kije nace !, tum kafin ranki ya b'aci, bana son musu kin sani ".
Saima ta mik'e cike da k'uk'uni ta shige toilet ta wanko fuskarta ta fito, dama doguwar rigace a
jikinta ta janyo wani yalolon mayafi ta yafa akanta ta fice.
Momy ta bita da kallo tana fad'in.
"Saura kuma inji kin wulak'antashi ".
Yana tsaye jikin motarsa cikin wata sky blue d'in shadda wanda tasha d'inki d'an ubansu, hular
kansa da takalminsa duk iri d'ayane farare, kansa na kan wayarsa dake hannunsa yana daddan
nawa, iya had'uwa ya had'u son kowa k'in wadda ta rasa lol.
Saima tun da ta fito take binsa da kallo aranta taji ya burgeta sosai, yanayin tsayuwarsa da
sajen fuskarta tamkar na Yarima, ba da ban zuciyarta ta tsumu da soyayyar Yarima ba da babu
abin da zai hanata aminta da wannan gayen, abin da ta aiyana aranta kenan.
Da sallama ta isa wajen ya d'ago kai cike da murmushi yana amsa mata tare da fad'in.
"Yau wace rana ce?, rana mafi sa'a agareni...ranar da bazan mance da ita ba....domin nayi to
zali da mafi haske a cikin mata.....yau ta amsa sallamar d'an talikin da baya da zuciya akanta ko
yaushe !".
Saima bata san sanda murmushi ya sub'ucewa fuskarta ba, dubansa tayi akaro na biyu kamar
zatayi magana sai kuma ta kau da kai gefe.
"Yi hak'uri Madam kada dai incikaki da surutu, sunana ANWAR SALISU MAI KUD'I, nasan zaki
iya sanin mahaifina ko kiji sunansa?".
Kai Saima ta gyad'a tana fad'in.
"Ehh na sanshi kace kai na gida ne ma, ai mahaifinka abokin Abbana ne".
Murmushi Anwar yayi yace.
"Nima nasan da hakan !, na d'auka ke baki san hakan bane?".
"Na sani ! ".
Ta bashi amsa a tak'ai ce, shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da fad'in.
"Saima a gaskiya bazan b'oye miki, gaskiya tun sanda na ganki a wajen birthday d'in Yarima
kika kwantamin arai, sai dai naso dannewa sabida tsoron irin tarbar da zan samu daga gareki,
amma zuciyata ta gaza samun nutsuwa da hak'urin da nake bata ako da yaushe".
Sosai k'irjin Saima ya buga jin ya ambaci sunan Yarima, sai dai tayi k'ok'arin danne zuciyarta,
tare da k'ak'alo murmushin dole, ya cigaba da fad'in.
"Ina fatan zaki karb'i k'ok'on bara na Saima?".
"Kar ka damu zanyi shawara akan hakan".
"Ok sai dai ina neman wata alfarma?".
"Alfarmar me kuma?, fad'i ina jinka".
"Kimin alk'awarin zaki dinga d'aukan kirana dan Allah".
Saima tayi shiru na d'an wani lokaci kafin ta ce .
"To babu damuwa Allah ya bani ikon cikawa !".
"Amin".
"Ni zan koma, sai yaushe zan dawo kenan?".
Sosai Saima ta farajin hiran na gundurarta cikin sauri ta bashi amsa.
"Ko yaushe ma".
"Nagode sosai, sai kinjini a waya".
"To".
Ta juya kawai tabar wajen, ba tare datayi tunanin komai ba, domin ta kasa daurewa zuciyarta da
tsayuwar da takeyi da shi.
Anwar yabi bayanta da kallo yana dariya cikin ransa.
***
Ta sowarsu kenan daga islamiyya suna tafe suna hira jefi-jefi Zainab ce ma ginshik'in hiran,
can tayi shiru ta dubi Aynu da fad'in.
"Kamar fa kina cikin damuwa Aynu?".
Aynu tayi yak'e tare da duban Zainab tace.
"Wallahi abubuwa ne sunk'ullemin kai sosai, kinsan Yarima Fudhal yana sona to gefe guda
kuma Yarima Jalil shima yace yana sona har yana fad'in inrabu da Yarima Fudhal indawo
wajensa, ta d'aya gefan kuma Ya sayyaadi Umar".
"Dama na sani ai !, inkaga kare na shin-shinar takalmi to d'auka zaiyi, nidai kinsan daman na
gaya miki na fisonn ki da Yarima Fudhal wallahi Aynu?".
"Ni kuma kinga Ya sayyadi yafi kwantamin arai domin shine dai-dai ni, shi yafi dacewa dani da
rayuwata".
Zainab taja dogon tsaki.
"Ke kam bakya fahimta wallahi !, yauwa ni kuwa mai ya had'aku da Yarima Fudhal ne?".
"Mai kika gani?".
"Babu komai, naga dai kamar bakwa shiri kamar da".
"Ehh to gaskiyar daya b'oyemin akansa ne ta fito fili".
"Kamar ta me fa?".
Nan Aynu ta kwashe dukkan abin da yafaru tsakaninta da Yarima Jalil ta sanarwa Zainab.
"Ni na yanke shawaran barin Yarima Fudhal kawai?".
Cike da fushi Zainab ta hau fad'in.
"Zancen banza !, wai ke haryanzu baki san waye Yarima Jalil ba ko?, lallai da sauran ki Aynu to
Jalil ya wuce dukkan tunaninki da har zaki d'auki maganarsa gaskiya wallahi zai kai ki yabaroki
ne kawai".
"Nifa gani nayi gaskiya ya fa'amin ai".
"Gaskiyarsa d'in banza !, baki d'auki shawaran da nabaki ba ko?, shikenan kinga tafiyata ni".
Zainab ta wuce tabar Aynu nan tsaye tana ta kwala mata kira amma tayi banza da ita.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARYA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jibour.
19
Yarima Fudhal na shirin fitowa faga falonsa shima Yarima Jalil na fitowa tare da wata 'yar
aikin gidan, yarinyar ta rissina ta gaishe da Yarima Fudhal tabar wajen da sauri, wani mugun
kallo Yarima Fudhal ya watsawa Jalil yana fad'in.
"Wai kai yaushe ne zaka san abin da yake maka ciwo ne?, idan aure kake so ka sanar ayi
maka mana da wannan muguwar rayuwar da kake?".
Yarima Jalil ya sosa k'eyar kansa yana fad'in.
"Broda bafa laifina bane 'yan matan ke bibiyata fa !".
"Ehh naga alama !, kenan Aynu ma bibiyarka takeyi ko?".
Yarima Jalil ya d'an fiddo ido waje alamun tsoro k'arara bisa fuskarsa kafin ya wayence ya
nemowa fuskarsa murmushin dole tare da fad'in.
"Haba dai..!, kawai mutuncin Yarinyar nake gani amma...?".
"Daga yau ina so ka daina ganin mutuncin nata !, bana shiga harkar rayuwarka kasani ko?,
kasan nafi kowa sanin waye kai Jalil?, kayi tunani idan na sanarwa duniya ko kai waye mai zai
faru?, to inaso ka fita cikin tawa rayuwar kafin zuwan lokacin da zaka fara fuskantar fushi na !,
fatan ka fahimce ni ?".
Yayi kwafa tare da barin wajen yabar Yarima Jalil tsaye yana binsa da kallo har sai da yaga ya
b'acewa ganinsa sannan yayi dariya yana fad'in.
"Ina....bazai yiyu inzuba ido a cikin gidan nan ana neman mai damu bayi ba !, mumafa 'yayane
da har zai kasance komai sai kai !, yanda aka raba ni da Gimbiya Safiyya to kaima dole ka
hak'ura da Aynu..!".
Ya juya ya koma cikin falonsa cike da dariya ciki-ciki.
Aynu da ke shara falon Yarima Fudhal duk tanajin abin da ya faru, babu abin da yafi d'aure
mata kai sai maganar Yarima Jalil ta k'arshe har sake mai-maita maganar tayi cikin ranta.
"Yanda aka rabani da Gimbiya Safiyya to kaima dole ka hak'ura da Aynu....".
"Ke nan Yarima Jalil yayi hakane domin yarabamu?, kenan son da yake fad'a yanaimin duk
k'aryace?, ashe gaskiya Zainab take gayamin na kasa fahimta?".
Aynu ta zauna d'abas ak'asan carpet tana tunani kala-kala, tsoro ya kamata sosai har dai da ta
tuna irin wulak'ancin da tayiwa Yarima Fudhal, take ta yanke aranta zata bashi hak'ura.
"Zai hak'ura kuwa?".
Wani b'angare na zuciyarta ya jefa mata tambayar, tayi ajiyar zuciya tare da addu'ar Allah yasa
ya hak'ura, domin itama cikin kwanakin nan Allah kad'ai yasan halin da tashiga sabida
k'auracewa Yarima Fudhal da tayi sauk'in tama tana ganinsa kullum duk da cewa bata kulashi
hakan na d'an rage mata damuwar dake k'unshe k'asan zuciyarta.
Yarima Fudhal kuwa yana barin wajen neman Zainab yaje yi, a can b'angaren mahaifiyarsa
suka keb'e waje guda babu wanda yake iya jin dukkan abin da suke tattaunawa akai, amma da
ka kalli fuskar Yarima Fudhal zaka san ransa a b'ace yake sosai.
Sun shafe tsayin lokaci kafin yabar wajen ya koma b'angarensa, zaune ya tadda ita tayi zurfi
cikin tunani bai kulata ba illa neman guri da yayi ya zauna yana fuskantarta ya k'ura mata ido na
wani lokaci kafin yayi gyaran murya mai k'arfi daya sanyata d'ago kai da sauri tana kallonsa.
Aynu ta sauke kanta da sauri ba tare da tace komai ba.
"Tunanin me kike?".
Ya jefa mata tambaya shiru tayi na d'an lokaci tana wasa da yatsun hannunta tana son yin
magana amma kuma ta kasa, shima bai kuma cewa da ita komai ba illa kafeta da idanuwa da
yayi shi komai Aynu takeyi ba k'aramin burgeshi take ba, da k'yar dai ta iya furta.
"Kayi hak'ura abisa abin da nayi maka !".
Ta fad'a ba tare da tayi tunanin bashi amsar tambayarsa ba.
"Babu komai, amma kinsan wani abu kuwa?".
Kai ta girgiza alamun a'a, ya cigaba da fad'in.
"Mai yasa kika k'i sanarmin dukkan abin da ya faru tsakaninki da Jalil?, ke nan har yanzu baki
rabu da shi ba?".
"A'a, babu yanda zanyi ne akan had'uwata da shi".
"Ok..amma mai yada kika d'au maganarsa serious ba tare da bincike ba?".
"Kawai na kasa tausar zuciyata ne".
"Aynu !, har yanzu baki yarda da son da nake maki bane?, ko nine baki yarda dani ba?".
"A'a na yarda mana".
Ajiyar zuciya Yarima Fudhal yayi yana mai cigaba da kallonta tare da nazarin yanayinta, kafin
yace.
"Kada ki yaudari zuciyarki kamar akwai abin da kike kokwanto a kaina haryanzu, zanyi
k'ok'arin kau da kokwantanki nan da lokaci k'ank'ani zaki fahimci waye ni Fudhal?".
"Amma kafin nan kisani ina k'aunarki sosai wallahi Aynu sai dai bazan iya tsayawa inyi miki
bayanin son da nake miki ba amma zaki iya karantar hakan a cikin idona, sannan ni aganina
tsayawa infad'awa mace irin son da nake mata k'auyanci ne kiyi hak'uri dani Aynu a duk yanda
kika ganni, kiyi hak'uri da halayyata".
Murmushin jindad'i Aynu tayi domin sosai takejin dad'in kalamansa a cikin zuciyarta, ta fahimci
Yarima Fudhal sosai yana sonta sai dai girman kai da izzar mulki bazai bashi damar nuna mata
ba, duk da wani lokacin tasan zuciyarsa na rinjaye akan girman kansa indai akanta ne.
"Ba kice komai ba sai murmushi da kike?".
Aynu ta sanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta wai ita a dole kunyarsa takeji, murmushi yayi
mai sauti yace.
"Kunyarki na burgeni Aynu, ina son mace mai alkunya sosai".
Ita dai Aynu ta gaza cewa komai, ya cigaba da fad'in.
"Wannan malamin naku naga kaman yana neman wuce gona da iri fa !, domin Zee ta fad'amin
cewa shima sonki yake?".
Ya k'arashe maganar tare da guntun tsaki, Aynu ta d'anyi murmushi kawai.
"Ina magana kinyi shiru?".
"Ni mai zance to".
"Komai ma kice, ina buk'atar jin muryar taki".
"Kinsan wani abu ?".
"Bari inje fada yanzu, anjima kad'an zan dawo ka da kitafi gida ki jira ni ".
Ya k'arashe maganar yana mik'ewa tsaye tare da sakarwa Aynu wani tsadaddan murmushi da
bata tab'a ganinsa saman fuskar Yarima Fudhal ba sai yau, Aynu ta mayar masa da martanin
murmushinsa tana fad'in.
"Angama Ranka ya dad'e !".
Yasa yatsan hannunsa d'aya ya lakuci karan hancinta yace.
"Kema ranki ya dad'e Gimbiya".
Ya fice yabarta zaune falon, yana fita tamik'e ta k'arashe sharar falon zuciyarta fari k'al, har wani
sanyin dad'i takeji yana ratsa dukkan wasu k'ofofin gashin dake jikinta.
A gag-gauce ta kammala ta fice zuwa wajen Zainab domin taji dalilin da yasa ta sanarwa
Yarima Fudhal komai.
Zainab tace "aini fushi nake da ke Aynu tunda har zaki yarda da maganar Yarima Jalil".
"To ya kikeso nayi ne Zainab kishi ne duk yajamin hakan"
Dariya suka d'anyi kad'an Zainab na fad'in.
"Kaga masoya !, Aynu ta Yarima Fudhal d'inmu".
"Ke banson iskanci fa !, me yasa kika sanar mishi abin da na fad'amiki?".
"Me zai hana bazan sanar masaba d'an bawan Allah na neman zaucewa akanki, wallahi Aynu
Yarima Fudhal yana sonki sosai bazan daina fad'amiki ba".
"Nima na sani Zainab, to amma ai naga mata biyu zai aurafa, kenan ni zai aura ta uku kome?,
ko kuwa matsayim k'warkwara zai aure ni?".
"Wannan ne bansani ba gaskiya".
Aynu tayi ajiyar zuciya tana fad'in
"Nasan inason Yarima Fudhal nima, amma bazan iya kishi da Gimbiya Safiiya ba".
"Nima inna tuna haka abin nad'an tsorata ni, kawai dai muyita addu'a shima abin da ya gayamin
kenan".
" Yauwa wai kuwa kinsan abin da naji Yarima Jalil na fad'a d'azu?".
"Sai kin fad'a ina jinki bani labari".
"Na fasa fad'a domin nasan sai kin gayawa Yarima Fudhal, in kina son ji sai kinyi alk'awarin
bazaki fad'a masa ba".
Zainab tayi shiru tana duban Aynu taga tabbas da gaske take hakan yasa tace.
"To na amince fad'amin".
Aynu ta kwashe komai ta fad'awa Zainab, Zainab zaro ido waje tayi tana fad'in.
"Kin ji ko?, ai nagaya miki dama kiyi hankali da Yarima Jalil ya wuce dukkan tunaninki wallahi".
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdaucee Jeebour.
20
(Kuyi hkr dani abisa rashin jina da kukayi kwana biyu, amma yanzu komai nml insha Allah zaku
dunga jina kullum, ngd sosai sosai masoyana da masu call zuwa message).
"Ya bawa da kyakykywar halaiyarka tasa na aminta da kai !, na baka dama ka cigaba da
zuwa wajen Aynu, kafin zuwan lokacin da zamu san abinyi, duk da cewa sai kayi hak'uri da ita
sosai domin Aynu yarinyace haryanzu batasan me rayuwa take ciki ba...".
Aynu da keshirin shiga gida taji Babanta yana yiwa Ya sayyadi Umar maganar, sosai k'irjinta
ya buga har sai da tad'an dafe wajen da hannunta.
"Gata nan ma ta dawo ai".
Babanta ya fad'a fuskarsa cike da fara'a, Aynu ta durk'usa ta gaisheshi ya amsa yana mai
cigaba da fad'in.
"Ga Malaminku nan, anan na sameshi yana zaman jiranki, ni bari ink'arasa bakin kasuwa ".