Showing 63001 words to 66000 words out of 88612 words
Chapter 22 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
karashan maganarba kai tsaye ya fice daga ɗakin Jakadiyya
ta biyo bayansa da sauri.
Tunda yasa kafa falonsa yake cin karo da kwalaban giya da karan sigari dakin inbanda wari
babu abin da yake yi, Yarima Jaleel na kwance sharkaf tsakar ɗakin sai amai ne ke fita daga
bakinsa mai warin tsiya.
Juyowa yayi yana duban Jakadiyya yace.
"Asamu a gyarashi akaishi a sibiti".
Yana faɗin hakan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗinsa.
"Wacce irin ƙaddara ce wannan?, mene ya jamin hakan?".
Mai Martaba ya faɗa cikin ransa tare da cigaba da zaga falon, kafin ya shige bedroom ɗinsa
domin shiryawa.
Ana isa da Yarima Jaleel asibiti shima kai tsaye emergency aka nufa dashi.
Suna zaune sai ganin faɗowarsa cikin ɗakin kawai sukayi, binsu yayi da kallo ɗaya bayan ɗaya
kafin ya sauke idonsa kan Yarima Fudhal dake can kwance, karasawa yayi jikin win windown
yana kare masa kallo sosai tausayin ɗan nasa ya kamashi take yaji zuciyarsa ta karye jiyayi ba
zai iya jurar rasa ƴayansa maza har biyu ba waɗanɗa sune magada a bayansa.
Duban Anwar yayi dake zaune kan wata farar kujera.
"Ka same ni a waje".
Ya Sakai ya fice Anwar yabi bayansa da sauri.
A office ɗin Doctor ya taddashi anayi masa bayani kan batun Yarima Jaleel.
Bayan ya gaishe dasu Mai Martaba yace ya zauna suka cigaba da maganarsu.
"Yanzu wanne halin yake ciki to?".
"E to yanzu dai munyi masa allurar bacci sai idan ya samu relief ya farka zamu San abinyi
domin ya bugu ne sosai har kwayoyin da yake sha sunfara barazanar taba masa kwakwalwa".
Mai Martaba yayi shiru tsayin wasu lokuta kafin ya buɗe baki yana mai cigaba da faɗin.
"Ya batun Magaji kuma?, yaushe ne zai farfaɗo?".
"Jikinsa alhamdulillahi ana samun nasara sosai, zai iya farkawa nan da kwana hudu ko biyar
idan zuciyar tasa taɗan samu relief sai dai abu guda ɗaya, duk yanda za'ayi dole ne idan ya
farka ya fara sanya ido akan abin da yafi so idan ba hakaba za'a iya samun matsala domin
ciwon zuciyar tasa ya taka matakin ƙarshe na rayuwa ko mutuwa?".
"Karka damu insha Allah zamu San abinyi".
Doctor ya mike ya fice daga office ɗin domin zuwa duba wasu patients nasa ya barsu nan suna
tattaunawa da Anwar.
Mai Martaba ya gyara zama yana mai duban Anwar tare da cewa.
"Anwar...!, Ina so ka bani labari akan yarinyar da Magaji yake so bana so ka ɓoyemin komai dan
Allah".
Fudhal ya gyaɗa kai alamun ya fahimta nan ya kwashe komai tun daga farko har ƙarshe bai
ɓoye masa komai ba ya sanarmasa.
Mai Martaba ya da ɗe tsayin wani lokaci yana gyaɗa kai tare da jinjinawa al'amarin jikinsa yayi
sanyi ainun.
"Haƙƙina nane innemawa Magaji auren yarinyar da yake so...!".
Anwar duban Mai Martaba yahauyi baki galala cike da murna da farin ciki amma daya tuna
ankusa bikinta sai jikinsa yayi sanyi da ƙyar ya iya ɗaga harshensa ya furta.
"Abba ankusa bikinta fa !, Inajin baifi nan da sati guda ba".
"Kada ka damu zansan abinyi insha Allah Magaji ne mijinta".
Anwar yaɗanyi yaƙe kawai tare da sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi yinƙurin sake cewa komai
ba.
*7:2pm*
Bayan sallar maghriba misalin ƙarfe bakwai da mintuna biyu Umman Aynu da Babanta suna
zaune tsakar gidansu suna hira tare da tattauna yanda zasu tafi da al'amuran bikin ɗiyarta tasu
tilo.
Aynu na cikin ɗaki kwance kan tabarma kanta na bisa pillow tayi ruf da ciki kai kace bacci
take, amma azahirin gaskiya idonta biyu ba zaka tabbatar da hakan bama sai ka lura da kai
hannunta da take kan fuskarta tana share kwallar dake taruwa cikin idonta lokaci zuwa lokaci.
Har cikin ranta bata jin son auren nan nata da za'ayi a cikin ranta ba tajin zata iya rayuwa da
kowa idan ba Yarima Fudhal ba.
Sallama suka jiyo ƙofar gida Baban Aynu ya sanya takalmansa ya fita domin ganin mai
sallamar.
Dogarawan Sarki Ubaiyd ya gani tsaye bakin ƙofar gidan suka gaisa tare da faɗin.
"Sarki Ubayd na da buƙatar ganinka a dai-dai wannan lokaci".
"To...! Lafiya dai ko?".
"Koma dai menene idan kaje za kaji".
Ɗaya daga cikin su ya bashi amsa, Baban Aynu ya gyaɗa kai tare da faɗin.
"Bari inshiga ciki insanarwa iyalina".
Yana shiga ciki bai ƙarasa inda Umman take zaune ba yahau faɗin.
"Zanje gidan Sarki yana nemana yanzu zan dawo".
Tsaye Umma ta miƙe tana faɗin.
"Allah yasa dai lafiya?".
"Amin bari inje inji".
Ya fice ya barta nan tsaye, Aynu ta fito da sauri domin jin me yake faruwa?.
Suna tafiya basu tsaya ko ina ba sai ƙofar falon Mai Martaba sukayi sallama ya basu izini su
shiga.
Suna sanya ƙafa Baban Aynu sakar baki yayi yana kallon falon tare da aiyana irin dukiyar da
aka kashe a ciki, suka sunkuya tare da kwasar gaisuwa Mai martaba dake zaune bisa ɗaya
daga cikin kujerun dake falon ya amsa tare da basu umarnin su basu guri, ba musu kowa ya
fice falon ya rage daga Baban Aynu sai Mai Martaba kawai.
Gyaran murya Mai Martaba yayi tare da gyara zama kafin ya bude baki ya fara magana.
"Nasan zakaji mamaki sosai da kiranka da nayi a dai-dai wannan lokaci, hakan ta faru ne
sabida kafiya da naci irin na yaran zamani".
Yaɗanyi shiru na wani lokaci kafin ya cigaba da magana.
"Ni Sarki Ubaiyd ɗana yaga iri a gidanka yana so, ina fatan zan samu ?, domin aurar da 'ya a
babban gida irin wannan wane zai ƙi?".
"Ni zanƙi...!".
Baban Aynu ya bashi amsa bai jira mai zaice ba ya cigaba da faɗin.
"Iri na anriga anshuka harya fidda kai nan da ranar juma'a mai zuwa za'ayi girbinsa zuwa gidan
daya dace da ita damu iyayenta".
A fusace Mai Martaba ya dubeshi.
"Har ni kamata na nemi alfarma a wajeka ka iya buɗe baki kace a'a...! Da matsayina da mulki
na waye kai?, mai kataka?".
"Ni talaka ne kuma miskini, ban taki komai ba sai alkhairi, kayi hakuri amma bazanyi magana
biyu inzamo karamin mutum ba ƴata dai aurenta za'ayi ina roƙawa ɗanka samun wacce ta tawa
a wajen Allah na barka lafiya".
Baban Aynu ya miƙe ya fita daga ɗakin cike da ɓacin rai da takaici, shi kuwa Mai Martaba kasa
ko motsi yayi sabida ƙuncin da yake ji a cikin ransa, yau rana ta farko a rayuwarsa ya but buƙaci
abu bai samu ba, abin da ko da kuɗi zai siya dukiyarsa bazata taba girgiza ba, amma yau talaka
ya shigo gidansa har falonsa ya iya kallon tsabar idonsa ya gaya masa magana.
"Mene ya jawo hakan?".
"Fudhal Kaine sila...!".
Yayi maganar a fili tare da miƙewa tsaye ya na faman safa da marwa a cikin falon.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdausy Jeebour.
38
Faram-faram Baban Aynu ya shigo gida fuskarsa babu yabo babu fallasa, amma duk wanda
ya sanshi ya kuma san yanayinsa yana ganinsa zai san yana tare da bacin rai.
Umma da Aynu suna zaune inda yabarsu cike da fargaba sai ganinsa sukayi ya faɗo cikin gidan
da sauri suka miƙe Umma na tambayar.
"Lafiya Baban Aynu?".
Neman guri yayi ya zauna suma suka zauna tun da yayi tagumi ya shafe tsayin lokuta kafin ya
iya motsa harshensa ya bawa Umma amsar tambayar da tayi masa.
"Akan ƴata har akeson nunamin iko da kudi da mulki, na godewa Allah da yasa bikin kwanaki
ƙalilan ya rage da bansan abin da zasu zomin da shi ba".
Nan dai ya kwashe dukkan abin da ya faru tsakaninsa da Sarki ya sanarmusu, Umma shiru
tayi ba tare da ta iya furta komai ba, Aynu kuwa fashewa tayi da kuka tamiƙe da gudu ta shige
ɗaki.
***
"Assalamu alaikum barkanku da yamma".
Anwar ya faɗa a dai-dai lokacin da yayi parking motarsa gefan wani shagon da wasu samari
uku suke zaune kan benci.
"Yauwa barka dai".
Samarin suka amsa cikin haɗa baki.
Anwar ya sake dubansu tare da jefa musu tambaya.
"Dan Allah tambaya nake, gidansu wani ana ce masa Ya Sayyadi Umar a nan layin aka cemin
gidansu yake".
Ɗaya daga cikin samarin dake zaune bakin shagon yaɗan jinjina kai yana mai-maita.
"Ya Sayyadi Umar..! Ko wanda aka bashi wata yarinya Aynu bikin saura sati guda ko?".
"E shi nake nufi".
Anwar ya basu amsa.
"To ai gida a can ƙasan layin nan yake zaka ganshi flat mai bluen ƙofa".
"OK nagode sosai sai anjima".
Anwar yaja motarsa ya wuce su zuwa inda sukayi masa kwatancen.
Yana parking motar kofar gidan ya fito tare da jingina jikin motar yana waigen neman yaron da
zai aika.
Can sai ga wani yaro da bai wuce shekaru bakwai ba ya taho yana gara taya da niyar shiga
gidan, Anwar ya tsai da shi yana faɗin.
"Zonan dan Allah".
Yaron babu musu ya tako zuwa inda Anwar yake tsaye yana faɗin.
"Gani".
Anwar ya dafa kafaɗar yaron kafin yace.
"Dan Allah idan ka shiga kace ana sallama da Ya Sayyadi Umar".
Yaron ya amsa da "To".
Ya juya ya shige cikin gidan.
Ya shafe tsayin mintuna goma kafin yaron ya fito ya bashi amsar.
"Wai yace yana zuwa".
Anwar yace.
"To nagode zoka karɓa".
Ya laluba aljihunsa babu chanji sai ɗari biyu ita ya miƙawa yaron fuskarsa cike da murmushina
yana faɗin.
"Ga wannan kasayi sweet ko".
"Nagode sosai".
Yaron ya faɗa yana mai cigaba da gara tayarsa ya fice daga layin.
Kafin fitowar Ya Sayyadi sai da Anwar ya kuma bata tsayin mintuna goma, can sai gashi ya leƙo
yana dube-duben ganin waye ke sallama da shi domin ko kaɗan bai kawo Anwar bane a ransa,
dan zai iya cewa ya mance da fuskarsa, sai dai yana tunanin kamar ya taɓa ganinsa.
Ganin haka ne ya sanya Anwar ƙarasawa wajensa da sauri cikin sallama, Ya Sayyadi ya amsa
tare da mika masa hannu sukayi musabiha.
Anwar ya buɗe baki a hankali ya fara magana.
"Ni sunana Anwar nasan baka shaida ni ba, amma ni nakasance abokine kuma amini ga Yarima
Fudhal".
Ya Sayyadi ya faɗa ɗa murmushinsa tare da sake bashi hannu suka gaisa yace.
"To mu shiga daga ciki mana?".
Anwar babu musu yabi bayansa har zuwa cikin ɗakinsa dake soro(zaure), ya bashi guri ya
zauna tare da kawo masa ruwa mai sanyi yasha.
"Ya Fudhal ɗin yana lafiya ƙalau ko?".
"E to lafiya ba lafiya ba, domin yanzuma sanadin halin da yake ciki ne ya kawo ni wajenka".
Ya Sayyadi ya gyara zama yana faɗin.
"To Allah yasa muji alkhairi ina sauraronka".
"E to gaskiya bazan iya furta komai ba a halin yanzu alfarma ɗaya zannema a wajenka dan
Allah dan Annabi inaso ka bini yanzu zuwa asibiti".
"Amma mai zamuyi a asibiti kuma?".
"Babu komai kawai ina sone kaje kaga halin da dan uwanka musulmi yake ciki wato Fudhal".
"Ban fahimci maganarka ba, wai meke faruwa ne?".
"Koma mene ka kwantar da hankalinka insha Allah idan mukaje zaka fahimta".
Ya Sayyadi Umar yayi shiru na wani lokaci yana kallon Anwar kafin yace.
"Shikenan tashi muje".
Anwar ya miƙe suka fito Ya Sayyadi ya rufo ƙofar ɗakinnasa, ya shiga cikin gidan sukayi
sallama da mutanan gidan ya fito zuwa waje, Anwar ya kunna motar suka shiga yaja suka fice
daga layin.
Bai yi parking motar a ko ina ba sai cikin harabar asibin a parking space ya kashe motar suka
fito, Ya Sayyadi kawai bin Anwar yake a baya tare da 'yan kalle-kallensa har suka isa wani ɗaki
Anwar yasa hannu ya murda murfin ƙofar tare da turawa suka sanya kai zuwa cikin ɗakin.
Durƙusawa sukayi suna gaishe dasu Hajiya da Aunty Sadiya dake zaune cikin ɗakin suka amsa
fuskarsu babu yabo babu fallasa tare da bin Ya Sayyadi da kallo domin basu San waye ba sun
ɗauka ko abokin Anwar ɗinne.
A tare suka miƙe suka ƙarasa bakin gadon da Yarima Fudhal yake kwance domin yanzu anfito
da shi mai makon da, da ake ganinsa ta window.
Ya Sayyadi ya jima yana jero masa addu'o'in samun lafiya kamar yanda Manzo Annabi
Muhammad (S.A.W) ya koyar damu cewa.
(Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai
yace masa;
َال َس
ْأ
َب ٌروُهَط ْنِإ َءاَش ُهللا .
La ba'asa tahoorun in sha'al-lah.
Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.
ُل
َأْس
َأ
َهللا ،ُميِظَعْلا َّبَر ِشْرَعْلا
ِ
ميِظَعْلا ْن
َأ
َكيِفْشَي عبسE. Fتارم
Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7).
Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa Musulmi da zai
ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya faɗi wannan (addu'a) sau bakwai
face ya sami lafiya)".
(Allahu akbar ya Allah kasa mu dace kasa mukasance masu koyi da koyarwar Annabi ka
kara mana sonsa da ƙaunarsa Amin).
Ya sayyadi yayi musu sallama ya fito daga ɗakin Anwar ya biyo bayansa.
A zaune ya taddashi kan wani benci a wajen asibitin shima Anwar ya nemi gurin ya zauna.
"Amma har tsawon wanne lokaci ya ɗauka bashi da lafiya ne?".
Anwar yaɗan dubeshi kaɗan kafin ya bashi amsa.
"Kwana huɗu kenan".
"Kwana huɗu?, amma kamar yayi shekara akwance, me yake damunsa ne?".
Ya Sayyadi ya sake jefawa Anwar tambaya.
"Ciwon SO ne"?.
"So kuma?".
"E mana kana mamaki ne?".
"A a kawai dai nake ganin kamar akwai ciwon da yaja masa hakan bayan Soyayyar".
"E yana fama da ciwon zuciya gaskiya Wanda ya takama matakin ƙarshe na rayuwa ko
mutuwa".
"Subhanallahi to a bashi abin da yake so mana".
Anwar yayi murmushi kaɗan kafin yace.
"Wannan kuma aikin kane, Kaine kake da haƙƙin yin hakan domin abin da ya mutu akan sonsa
yana wajenka".
"Kana nufin Aynu yake so?".
"E nasan kasan da hakan ai".
Ya Sayyadi shiru yayi yana kallon Anwar ba tare da ya kuma cewa komai ba, can ya nisa yace.
"Zaka iya mai da ni gida, ko in tafi".
"A a mai zai hana?, ni na ɗauko ka ai, tashi muje in mai da kai".
Ya Sayyadi ya miƙe suka taka har zuwa Inda sukai parking motar suka buɗe suka shiga Anwar
yaja suka fita daga cikin harabar asibitin.
Suna tafiya akan titi shiru babu mai cewa da wani komai, Anwar ne yaɗan dubi Ya Sayyadi ta
gefan ido kafin ya buɗe baki ya fara faɗin.
"Zan roƙi alfarma a gareka nazo na ɗauke kane badon komai ba illa kaga abin da zan faɗa
maka da idanunka domin ganin ya kori ji inji bahaushe, yanzu wuƙa da nama suna hannunka
nasan cewa Allah ke rayawa kuma shi yake matarwa idan lokacin mutuwar mutum yayi babu
Wanda ya isa ya ƙara masa ko second ɗaya, kamar yanda Idan lokacin mutuwar mutum bai
yiba babu Wanda ya isa ya kashe shi, amma kasan cewa komai yana da dalilinsa da kuma sila
Fudhal baki ɗaya ya ta'allaka rayuwarsa akan Aynu ne rasa Aynu a cikin rayuwarsa kamar
Fudhal ya rasa rayuwarsa ne, wallahi Allah shine shaida da kuma ni Fudhal nason Aynu fiye da
rayuwarsa a iya sanina da ganina ban tana ganin mutumin dake son abin da yake so kamar
Yarima Fudhal ba...!".
Ya katse maganar dai-dai sanda yayi parking kofar gidannasu, Anwar ya sake duban Ya
Sayyadin yana mai cigaba da faɗin.
"Ka taimaki Fudhal dan Allah ka ceto rayuwarsa nasan ka fahimci abin da nake nufi".
"Zanyi tunanin akan hakan, nagode sosai ka gaida gida Allah ya ƙara masa lafiya".
Abin da yace kenan ya fice daga motar, Anwar ya amsa da
"Amin" yana mai bin bayansa da kallo, aransa yana addu'ar Allah yasa abin da yake ƙoƙarin yi
ya tabbata yasa kuma ya fahimci abin da yake so ya fahimta.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®