Showing 18001 words to 21000 words out of 88612 words

Chapter 7 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8294

ta baya ta d'ago da sauri dan ganin waye?.

Zainab ce ta zagayo ta zauna tana fad'in.

"Subhanallahi !, Aynu mai ya faru kike kuka ya akayi kika k'one ke da ba a kitchen kike aiki
ba?".


"Yarima ne Zainab, Yarima ne !".

Aynu ta sake fashewa da kuka tana mai d'ora kanta kan cinyar Zainab, Zainab ta d'an bubbuga
bayanta alamun rarrashi tana fad'in.

"Mai kikayi masa?".

"Wai akan Yarima Jalil...".

Nan dai ta kwashe dukkan abin da yafaru ta sanar mata, Zainab tayi ajiyar zuciya tana fad'in.


"Kece bakyaji ai na gaya miki waye Jalil kin k'i yarda, amma abin tambaya kenan Yarima
Fudhal yana kishin ganinki da Yarima Jalil?, Idan har kishi yake kenan sonki yake ko?".

"Oho nima nasani jeki tambayeshi".

Zainab dariya tayi domin wasu lokutan tasan Aynu 'yar rigimace ta k'arshe, a fili kuwa cewa tayi.

"A'a mai da wuk'ar bani nakar zomon ba ratayarma ban d'auka ba".

Aynu tad'an kaiwa Zainab dukan wasa, tana fad'in.

"Ni ko sona yake Allah bazan soshi ba mugune wallahi na k'arshe".

Zainab tayi murmushi tana fad'in.

"Ki godewa Allah Aynu samun irin su Yarima Fudhal wuya garesu a yanzu, wallahi nayi miki
murna sosai Allah tabbatar mana da alkhairi, ni yanayin soyayyar tashi ne ma ta fara burgeni !".

Wani kallo Aynu ta jefi Zainab da shi mai dauke da harara.

"Wai ke waya gaya miki sona yake ?, nifa bai fad'amin ba".

"Daga jin yanda labarin ya fara kowa kika sanarwa Allah yasan al'amarin so ne yaja hakan,
domin idan ba so ba mata nawa ne suke harka da Yarima Jalil a gidan nan amma bai da muba
sai a kanki, nasan wata rana zai fad'a miki yana sonki".

"Tab..Allah ma ya kiyaye, dubi fa hannu na wanda yayi maka haka kuma yazo yace yana
sonka?".

Cewar Aynu kenan tana mai k'arewa hannunta kallo cike da takaici, ba tayi aune ba sai ji tayi
ruwan hawaye na bin fuskarta.

Nan sai suka Zauna Zainab na k'ok'arin ganar da ita amma ita tana faman botsewa da haka har
k'arfe biyu tayi basu sani ba, a gurguje suka had'a inasu inasu sukayi gida, dan Aynu ko part
d'in Yarima k'in komawa tayi dan kada wani abun ya sake faruwa.


Yarima na dawowa sallah yahau nemanta amma sama ko k'asa ya rasa ta sai Jakadiyya ke
sanar dashi sun tafi gida, kwafa yayi yana duban maganinta da aka bata yana tunanin yanda
za'ai ta sha domin kada k'unar ta tashi kafin gobe, hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, sai
dabara tazo masa ya baiwa Jakadiyya ta kai mata domin yaga ta san ta, ba musu Jakadiyya ta
karb'a ta nufi gidan su Aynu domin kai mata maganin lokacin kuwa daf da maghriba ne.


***

Ko da Aynu ta koma gida k'in sanarwa Ummanta abin da ya faru tayi, duk da cewar Umman
taji muryarta ta canja tayi tambayar duniya akan meya sata kuka?, Aynu tace .

"Babu komai Umma kawai tari na d'anyi".

Nan dai ta k'ok'arta tayi dukkan abin da zata iya ta nufi Islamiyya dawo warta kenan ta shiga
d'aki ta cire hijab taji sallama, ta fito domin ganin waye sai taga ashe Jakadiyya ce har Umma ta
bata gurin zama.

Aynu ta fito suka gaisa tamik'awa Umma ledar maganin tana fad'in.

"Gashi Aynu maganin naki, Yarima duk ya tashi hankalinsa yace kisha kafin ki kwanta, Allah
ya k'ara sauk'i ni zan koma".

"To mungode Allah saka da alkhairi ki gaida gida a yiwa Yarima godiya sosai abisa d'awainiya".

Cewar Umma kenan dake zaune gefen tabarmar da Jakadiyya ta zauna.

Jakadiyya tayi musu sallama ta tafi, Aynu dai mutuwar tsaye tayi tana jira taji mai Umman zata
ce da ita.

"Zo nan Aynu".

Taji muryar Ummanta Aynu ta k'arasa kusa da ita ta zauna tana fad'in .

"Gani Umma".

"Fad'amin gaskiya mai ya faru?".


"Dama....dama fa...dama Umma ruwan zafi ne ya zubomin a hannu".

"Amma shine zaki min k'arya kice ba komai tari ki kai".

"A'a Umma kawai banaso hankalinki ya tashi ne ".

Murmushi Umman tayi tana fad'in.

"Aynu kenan, bani hannun inyi miki tofi".

Aynu ta mik'a mata hannun, Ummanta ta kama tayi mata addu'a kafin ta saki hannun tana
fad'in.

"Da ace kina k'onewa ansamu gasarar koko anzuba akai ba zata tashi ba, domin k'una sanyi
take so, da zarar ansanya gasarar iska na kad'awa har ta bushe shikenan ba zata tashi ba".

"Umma ai yanzuma bata tashi ba kawai dai ja hannun nawa yayi".

"To Allah sauwak'e ya kiyaye gaba ki dinga lura da kyau dai".

"To ummata".
[22/07, 20:22] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)


SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



12

Washe gari wayar gari akai Mai Babban d'aki wato Mahaifiyyar Mai martaba babu lafiya, baki
d'aya hankalin kowa ya tashi da ka shiga gidan zaka san babu lafiya musamman Yarima Fudhal
da Mai Martaba sunfi kowa shiga damuwa da ciwon Mai Baban d'aki.

Ciwo anwayi gari da shi rana d'aya amma kai kace tayi shekara tana yi, tuni aka d'ebeta sai
asibiti likitoci uku ne akanta amma sun kasa gano musabbabin ciwon nata bare har asan abin
da za'ayi akai.

Ni dai tun da muka doshi gidan ni da Zainab mukasan babu lafiya agidan, muna shiga kuwa
muka samu bayanin Babar Mai martaba ce ba lafiya tana asibiti, Yarima ma nacan hospital d'in
Zainab ce ta tayani gyara b'angaren Yarima sabida k'unar dake hannuna muna gamawa na nufi
gida kuwa domin Saima ma da tazo ta tadda abin da yake faruwa bata zauna ba ta koma gida
abinta.


***

Daf da maghriba kuwa Hajiyar Mai Martaba tace ga garin kunan, ba Sarkin ba duk wanda
yaji mutuwar baiwar Allahn nan dole yayi kuka mace kamila mai hak'uri da dattako mai son
addini da son iyalinta ga uwa uba barkwanci da faram-faram.

Gaskiya bak'aramin rashi su Yarima sukayi ba gari ya d'auka kaf da rasuwar baiwar Allahn
nan, ni dai ina zaune a gida najiyo a babban masallacin unguwarmu ana sanarwa cewa za'ayi

jana'izar ta da safe idan Allah ya tashemu da rai da lafiya, ba wani shak'uwa mukai da ita ba
amma naji mutuwarta sosai babu abin da yafara fad'omin arai irin so da shak'uwa dake
tsakaninta da Yarima fudhal koya zaiji aransa oho?

"Allah sarki Yarima Allah baku hak'uri da dangana !".

Abin da nace kenan ina yankewa Ummata farce ta amsa min da.

"amin Aynu mutuwa ai dole ce sai dai in lokaci baiyi ba duk kuwa irin so da shak'uwar da kukai
da mutum dole wataran zaka barshi".

Jikina yayi sanyi da kalaman Ummata sai naji hawaye nabin gefan fuskata har dai da na tuna
Ummata da Baba na su kad'aine duniyata sune farin cikina su kad'ai na sani sune nake kalla inji
dad'i, yanzu dole watara zan barsu ko su barni, duniya kenan babu matabbata Ubangiji Allah
kasa mu dace ka kashemu da imaninmu amin.

***

Ka sancewar rasuwar da akai nasan kuma cin koso da jama'a yanzu sun cike gidan hakan ya
saka nak'i zuwa washe garin da akai rasuwar, nayi zamana agida amma wunin ranar nayi shine
cike da tunanin gidan.

washe gari kuma ranar biyu da rasuwar nayi niyar zuwa kodan inyi gaisuwa sai dai na tashi da
wani irin matsanancin ciwon kai, Zainab data biyomin mu tafi har da ita asa bakin inyi zama duk
da cewar naso zuwa amma Umma da Zainab suka kafe kan in zauna har zuwa gobe inga
yanda jikin nawa zaiyi.
"Haba Fudhal kayi hak'uri kad'au dan gana abisa rashin Hajiya da mukayu mutuwa kasan
dole ce amma sai da hak'uri, muma da muke mata munyi hak'uri bare kai namiji ?".

Cewar Yayarsu Aunty Sadiya kenan data iske Yarima d'akinsa shi kad'ai kwance kamar wani
mara lafiya.

Falonsa abokansa ne cike amma shi ya wuce bedroom ya kwanta kamar mai bacci amma
azahiri ba baccin yake ba domin duk abin da ake yana ji.

Ta gaji da magana amma ko d'ago kai baiyi ya kalleta ba, ta tashi ta fice daga d'akin ta koma
wajen mahaifiyyarsu Fulani Bingel tana sanar mata.

Fulani tasan Yarima ya shak'u da Hajiya sosai amma tasan akwai wani abu daban da yake
damunsa domin tasan waye Yarima tasan halayyarsa sarai, hakan yasa tayi murmushi kawai ta
dubi Aunty Sadiya tana fad'in.

"Rabu dashi kawai akwai abin da dai yake damunsa, kar ki damu".

"Kamar ya ! Wanne abune yake damunsa haka?".

"Zanyi miki bayani wani lokacin".

Fulani Bingel ta wuce ta koma falo inda tabar jama'arta ke jiranta, ta bar Aunty Sadiya nan
d'akin tana tunanin me yake damun d'an k'anin nata?.


Yarima kuwa gani yayi kwanciyar babu abin da zata haifa masa illa tarin damuwa mai yawa,
hakan yasa shi mik'ewa ya fito harabar gidan yana dube-dube kome yake nema oho?.

Duk inda ya wuce sai gai dashi ake wani ya amsa wani ya wuce kawai da haka ya isa har filin
shamaki inda bayi da ma'aikatan gidan ke zaune, suka durk'usa baki d'aya suna gai dashi ya
amsa tare da k'urawa Zainab ido, yana tunanin indai bai mance ba tare yafi ganinsu da Aynu
may be zata iya sanin wani information akanta.
"Ke zo nan".

Yayi nuni da Zainab ta mik'e da sauri tabi bayansa domin har ya bada baya ya tafi.

Wani guri yaja ya tsaya inda babu mutane yayi shiru kansa a k'asa bai ce da ita komai ba, har
Zainab ta gaji da tsaiwa taji kaman zata fad'i, amma babu daman zama can ya d'anyi ajiyar
zuciya ba tare daya d'ago kai ba yake fad'in.


"Ke kinsan Aynul-hayat ko?".

"Ehh Yallab'ai?".

"Ok mai yasa 2days bata zoba, ko gaisuwa ma tak'i zuwa ?".

"Ba tajin dad'i ne".

Yarima Fudhal ya d'ago kai da sauri yana dubanta, jin maganar da ta doki kunnensa.

"Me yake damunta?".

"Tace dai ciwon kai ne".

A jiyar zuciya ya saki mai k'arfi wadda har sai da Zainab ta dubeshi, ya cigaba da fad'in.

"Bani address d'inta".

Nan da nan Zainab ta bashi bayanin gidansu Aynu, tana gamawa ya juya ya tafi ya barta nan
tsaye babu ko godiya Zainab tabi bayansa da kallo aranta tana fad'in.

"Ikon Allah maganar minti biyar amma ashafe awa guda da wani abu anayi, lallai Yarima na
musam-manne Matarsa na da aiki kuwa".

Ta juya abinta itama tabar wajen ta koma inda ta taso.


•••

Aynu dai bata samu ciwon kan ya lafa mata ba sai dare wajen k'arfe takwas bayan sallar isha'i
kenan, ta tashi tayo alwala ta hau gabatar da sallolin da bata samu ta iyayi ba, ta idar kenan
tana addu'o'in data saba ko yaushe sukaji sallamar Yaro a tsakar gidansu.

Umma dake zaune gefe daga inda Aynu take sallah ta amsawa Yaron Sallama, ya gaishe da
Umma yana fad'in.

"Wai ana kiran Aynu a waje".

"Aynu kuma da daren nan?".

"Ehh haka yace min Aynu yake nema".

Aynu ta sallame addu'ar tana fad'in.

"Kace ina zuwa".

Yaron ya fice Aynu ta dubi Ummanta tace.

"Yanzu haka Ya Sayyadi ne dan yaga yau banje Islamiyya ba".


"Ehh nima nayi tunanin hakan !, tashi kije kada ki jima dan kinga dare yayi".

"To Umma ni dama bana jin dad'i, tsayuwarma bazan iya ba muna gaisawa zan dawo".


Aynu tasa takalminta ta fice.

Dake dare ne kuma unguwar duhu basu da wadatar nepa, hakan yasa bata iya shaida
kowane ba, yana tsaye jikin darbejiyar k'ofar gidan cikin k'ananun kaya daya tabbatarwa da
Aynu ba ya sayyadi bane domin ta sanshi gwanine wajen shigar jallabiyya yau kuwa taga
sab'anin haka, ta waiga bata ga kowa ba illa dai wanda ke tsaye jikin bishiyar.
Dake wa tayi tare da k'arawasa sai dai tun kan takai da isa wajen zuciyarta tahau bugun
uku-uku ga kuma k'amshin turarensa daya doki hancinta wanda bata iya manceshi ko a wane
yanayi taji shi zata gane nasa ne.

Shi kuwa tun fitowarta ya kafeta da idanuwa yayin da wani sanyin dad'i ya mamaye zuciyarsa,
har yanaji aransa kamar yaje ya d'aukota don hutar da ita daga tafiyar da take.

Ta k'arasa wajen da sallam cikin siririyar muryarta ya masa mata ta d'an rissina ta gaisheshi
tare da fad'in.

"Kayi hak'uri ban d'auka kai bane...".

Sai kuma tayi shiru, shima baice komai ba yayi shiru tare da nad'e hannunsa bisa k'irjinsa, a
hankali ta d'ago kai duk da a duhu ne amma ta fahimci kallonta yake.

"Ya k'arin hak'uri kuma?, Allah yaji k'anta ya gafarta mata".

"Amin nagode sosai".

"Mai ya hanaki zuwa kwana biyu?".

Aynu ta gyara tsayuwarta sosai tana wasa da yatsun hannunta, ta bud'e baki ta bashi amsa.

"Banajin dad'ine".

"Shine dalilin da yasa kika k'i zuwa?".

"Ehh".

"Ko dai kinajin haushi nane akan k'onakin da nayi".

"A'a wallahi bani da lafiya sosai musamman yau yanzune ma nad'anji sauk'i".

"Ok".

Ya fad'a yana mai mik'o mata ledar dake ajiye gefansa Aynu ma ko lura da ita batayi ba.

Batayi magana ba haka kuma bata karb'a ba, shima kuma baice komai ba illa kafeta da
idanuwa da yayi.

"Dole fa ki dinga karb'an kome na baki banason gaddama kamar yanda banaso inyi kyauta
adawomin da ita".

Aynu tasa hannu ta karb'a tare da fad'in.

"Nagode sosai Allah k'ara girma da arzik'i yaji k'an hajiya".

Murmushi ne ya kufce masa wanda yasa fararen hak'oransa baiyana waje sosai yaji dad'in
addu'ar Aynu agareshi, kamar yanda yake jin dad'in sautin muryarta akunnensa yana kuma jin
dad'in kasan cewarta atare da shi ko da ba zaice da ita komai ba yanaso ya dinga kallon beauty
face d'inta any time.
Aynu tsayuwar tafara isarta har k'afafunta na kakkarwa, amma ta gaza iya furta masa zata
shiga gida.

"Kije gida sai da safe".

Taji muryarsa ta doki kunnenta, domin batayi tsammanin zai sallame ta ba a yanzu.

"To nagode sosai, a gaida su Hajiyarku".

Ta juya ta tafi domin tasan ba lallai ya amsa ba, shi kuwa bin bayanta da kallo yayi har ta shige
cikin gidan nasu ya jima anan tsaye kafin ya nufi wajen da yayi parking motarsa ya shige ciki ya
zauna yana tunanin da baisan kona mene ba haka kawai yaji zuciyarsa tab'aci duk da baya
raba d'ayan biyun tafiyar Aynu ce taja masa hakan.


Aynu nashiga gida samun guri tayi kusa da Ummanta ta zauna tana fad'in.

"Ashe Yarima ne ba Ya Sayyadi ba".

"Yarima kuma Allah sa lafiya dai?".

"Lafiya k'alau Umma wai yazone yaji lafiya ko k'unarce take damuna banjeba kwana biyu".

"Allah sarki yaron na da kirki kuwa".

Aynu ita dai ajiyar zuciya tayi ranta tana fad'in.

"Dan bakisan waye shi bane kikace haka Umma".

A fili kuwa cewa tayi.

"Kin ga harda kaya yazomin da shi kona mene oho, bari in duba ingani".

Ta fad'a tana mai jawo ledar ta bud'e magunguna tana gani aciki sai kayan snack a ciki da juice
gefe guda kuma taga wata guntuwar ta kadda ta bud'e aranta tana fad'in.

"Ko mene a ciki?".

"Kisha kowanne da k'aidarsa maganin ciwon kannaki ne".

Aynu tayi shiru tana sake karanta takaddar tare da tunanin inda yasan kanta na ciwao sai kace
aljani?.

Ta fad'a aranta.

"Umma magani ne ashe tare dasu snack !".

"Allah sarki sai kisha maganin to, kyasamu sauk'in ciwon angode masa sosai Allah saka masa
da alkhairi".

*YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®


SADAUKARA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.


Ina kike ne? Miemie Bashir (Queen) matso kusa wannan page d'in naki ne domin jin dad'inki
kawai.



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login