Showing 75001 words to 78000 words out of 88612 words

Chapter 26 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8275

sanya abin da yafi so a cikin idanunsa, amma idan aka samu
akasin hakan ba zan iya cewa wani abu ba domin rayuwa da mutuwa duk na Allah ne amma

mudai fatanmu ya samu lafiya".

"Haka ne Doctor insha Allahu komai yazo ƙarshe ai, zai samu abin da yake so da yardar
Allah".

Faɗin Sarki Ubaiyd kenan yana mai miƙewa domin fita daga office ɗin, sukayi musabiha suka
fito kai tsaye ɗakin da Fudhal yake suka nufa domin ƙara dubo yanayin jikin nasa.

***

WASHE GARI

Baban Aynu na zaune ƙofar gida tare da muƙar-rabansa sai ga samari nata shigowa layin
ɗauke da kayan abinci suna ajiyewa ƙofar gidan nasu Aynu.

Baban Aynu ya cika da mamaki sosai ya miƙe ya tari ɗaya daga cikin samarin.

"Yaro anya nan akace ku kawo kayan nan?".

"E nan ne Baba".

"To amma waye ya aiko ku?".

"Mai Martaba ne yace mu kawo nan ai muna tare da abokin Yarima Fudhal shine ya nuna mana
gidan ma".

Daga nan Baban Aynu bai kuma cewa komai ba ya zuba ido kawai yana kallon yanda ake jere
kayan abinci ƙofar gidansa Wanda har bayan biki sai sun shafe tsayin watanni shida basu nemi
abinci ba.

Suna gama kawo wa Anwar ya ƙaraso zuwa inda Baban Aynu da mutanansa ke tsaye
cirko-cirko ya durƙusa ya gaishe su, suka amsa .

"Amma Anwar irin wannan hidima haka?".

"Baba babu komai ai daga Mai Martaba ne wannan aiken yace a gaisheka".

"Ina amsawa Anwar kayimin godiya sosai, sai nazo da kaina".

"Babu komai Baba".

Ya kai maganar tare da zaro rafar yan ɗari biyar ya miƙawa Baban Aynu yana faɗin.

"Ga wannan yace kuɗin cefane ne".

"Bayan wadan nan kayan kuma?".

"E Baba ".

"To angode Allah ya saka da alkhairi".

Baki ɗaya ƴan gurin suka amsa da "Amin".

Su Aynu nacan gidan lalle da gyaran jiki anata fama wanda duk wannan abubuwan ƙoƙarin
Zainab ne dan dai ta Aynu da babu abin da zatayi sabida abin da yake damunta kaɗai yasa baki
ɗaya bata sha'awar komai ba kuma tajin farin ciki da wannan auren ko kaɗan ji take acikin ranta
tamkar wannana auren yayiwa rayuwarta karan tsaye.
Damuwa da faɗuwar gaba sun tsananta agareta cikin kwanakin nan, hakan ne yasa baki ɗaya
ta rame ta zama kamar wata mai ciwo, mutane sai cewa suke fargabar biki ce sai dai ita kai
tasan abin da yake damunta.

A ranar da yammaci akayi walima kamar yanda suka tsara amarya tayi kyau sosai cikin wata
doguwar riga pink data sha stone fari mai ratsin blue tayi rolling kanta da mayafin doguwar riga
Wanda shima pink ne, ƙawar amarya kuma aminiya doguwar riga blue ta saka mai ratsin stone
pink yayin da sauran al'umma sukayi shigar after dress baƙa maza kuma jallabiya abin gwanin
ban sha'awa ankira malamai mata sunyi wa'azi sosai akan aure da zamantakewar rayuwa tayau
da kullum, anci ansha a walimar abin da al'umma basu taɓa zata za'ayi ba a taron walimar
shine ya faru.

Duk yanda Aynu taso su haɗu da angonta Ya Sayyadi Umar ƙi yayi sai taga kamar ma gudunta
yake yi abin da ya ƙara dagula mata lissafi kenan ba ita bama hatta Zainab abin yaɗaure mata
kai sai dai kawai tana ƙoƙarin kwantarwa da Aynun hankali ne amma a can ƙasan zuciyarta
damuwace ita ma a cunkuce.
RANAR JUMA'A...!.

Bahaushe yace "Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya".

A ranar juma'a ƙarfe goma da rabi na safe za'a ɗaura auren.

Mai Martaba da Magaji Saif tare da muƙar-rabansu tun ƙarfe goma da ƴan mintuna suka
halacci wajen ɗaurin auren kar kuso kuga gayyar jama'ar dake tare dasu wai danma auren yazo
a ƙurarren lokaci.

Tuni unguwar ta kaure da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe yara maza da mata sai gudu suke zuwa

cikin gidansu Aynu suna bada bayanin ɗaurin auren Aynu har dasu Sarkin garin Umman Aynu
dake tasan komai sai dai kawai tayi murmushi sauran jama'a kuwa faɗi suke.
"Ohh auren Aynu da farin jini yake harda sarki yazo da kansa.

Su Aynu na can gidansu Zainab anata shirye-shirye ita kuwa ta shige cikin ɗaki ta kwanta
kawai ita kanta ba zata iya cewa ga abin da yake damunta ba, Zainab ce ta dage mata har dai
ta tashi ta hau shiri itama.



10:30Am

Goma da rabi dai-dai Baban Aynu ya fito cikin wata da kak-kiyar farar shadda hula da takalmin
ƙafarsa ma duk farare ne wanda duk aikin magaji saif ne, aka ɗunguma baki ɗaya zuwa
masallacin da za'a ɗaura auren.

Magaji Saif shine ya miƙa kuɗin sadakin Aynu dana jalilah Naira dubu hamsin hamsin tare da
kuɗin aure shima dubu hamsin nan take aka ɗaura auren.

FUDHAL UBAIYD SALMAN

Da

AYNUL-HAYAT ABDALLAH

Da

UMAR FARUK KHALEEL

Tare da

JALILAH UBAIYD SALMAN

Kan sadaki dubu hamsin hamsin wanda duka Magaji Saif ne ya biya.

Abin da masu shela suka hau faɗi kenan take gurin ya kaure da kaɗe-kaɗe.

Mai Martaba dai Allah-Allah yake ayi agama komai sabida a yaune ake saran farkawar Fudhal
yana gudun faruwar wani abun.

Mutanan da sukaje ɗaurin auren baki ɗaya saranda sukayi jin da wanda aka ɗaura auren sai
sukaji tamkar kunnuwansu bai jiye musu dai-dai bane, sai da suka sake ji masu shela nata
mai-maitawa nan fa kawunan kowa ya kulle masu farin ciki nayi akasin haka nayi.

Kanwar Zainab ce mai suna Jamila ta shiga gidan da gudu tana faɗin.

"Aunty kinsan da wa aka ɗaura auren Aunty Aynu?".

Zainab ta dubeta a gaggauce tana shirya Aynu.

"Dawa za'a ɗaura banda Ya Sayyadin mu".

Jamila tayi dariya.

"To baki canka ba Aynu dai da Yarima Fudhal aka ɗaura aurenta".

Zee tayi tsaki tana faɗin.

"Aikin banza aike kin shiga uku da ƙarya".

Jamila tayi kwafa taji haushin maganar Zee hakan yasa ta shiga ɗakin Baba ta Sallah ta ɗauko
redio ɗinta ta kunna musu.

Jin abin da ake sanarwa a radio yasanya duk yan matan dake gidan kasa kunne domin tabbatar
da a abin da suka fara ji da farko.

Ai ana sake mai-maitawa Zee ta rungume Aynu tana faɗin.

"Alhamdulillahi Aynu yau addu'armu ta karɓu kin zamto mata ga Fudhal mai yafi wannan daɗi?".

Aynu kuwa ta kasa furta komai illa ruwan hawaye dake bin fuskarta kona Mene oho?.

"Amma ya akayi abubuwa suka canja haka?".

Cewar Zee kenan harara Aynu ta jefa mata.

"Ta ina zan sani nima ".

Sukayi dariya tare da tafawa.

"Yanzu Ya Sayyadinmu ya zama angon Jalilah ƴa ga Sarki Ubaiyd, Fudhal ya auri Aynu? abin
mamaki Allah mai yin yanda yaso".

Abin da sauran ƴan matan dake gidan suke faɗi kenan.

Zee tayi dariyar jin daɗi tana mai ƙarewa ƙawarta kuma aminiyarta kallo sosai taji daɗin

wannan al'amari kuma tana matuƙar taya Aynu murna da farin ciki.

Mai Martaba kasa jurewa yayi har sai da yaja Baban Aynu gefe ya sanar dashi buƙatarsa da
kuma abin da Doctor yace.

Baban Aynu shima ya amince domin yana ganin yanzu sune suke da iko da Aynu ba shi ba.

Mai Martaba yayi murna sosai da amincewar Baban Aynu.

Magaji Saif kuwa na can ya sanya samari sai jido akwatuna suke suna shiga dasu gidansu
Aynu akwati goma sha biyu haka aka jeresu a filin tsakar gidansu Aynu, Umman Aynu da Baba
ta Sallah ta sanar mata kayan da aka kawo tsabar farin ciki saita fashe da kuka abin da bata
zataba abin da ko a mafarki bata taɓa kawowa ba wai Aynu ce yau ta zamto mata ga ɗan sarki
jikan Sarki Allah mai yanda yaso da bayinsa.

Baban Aynu ya sanya aka kira masa su Aynu mintuna kaɗan sai gata tare da Zainab.

Ya sata cikin ɗakinsa ya sanar da ita komai sannan yace zata bi su Mai Martaba yanzu asibiti
inyaso idan komai ya dai-daita zata dawo.

Aynu tace babu komai domin yasan dama ba zata taɓayi masa musu ba ya sanar da itane
dama domin ya fidda ita daga cikin duhu ne.

Anwar shine yake driving yayin da Magaji Saif yake zaune kusa dashi a baya kuma Mai
Martaba tare da wazirinsa.

Sai motarsu Aynu driver ne kawai yake ja sai Aynu da ita da Zainab kawai a motar domin ance
babu wanda zai bisu sabida asibiti zasuje itama Zainab ɗin dan dai kawai kada a bar Aynu ita
kaɗai ne ba zataji daɗi ba.


Tun da suka tafi basuyi parking ko ina ba sai cikin harabar asibitin a parking space.

Kai tsaye ɗakin da Fudhal yake jinya suka shiga Fulani Bingel da Aunty Sadiya suka taso cike
da farin cikin ganin Aynu ita kuwa sai ta sanya kanta cikin mayafi sabida wata irin kunya da taji
ta lulluɓeta.

Ta gaishesu tare da samun guri ta zauna ta takure waje ɗaya Zainab ma ta nemi guri kusa da
ita ta zauna kowa ya amsa gaisuwarsu amma ban da Sa'ida dake ta cika tana batsewa.

Sai dai kuma babu wanda ya lura da hakan illa su Aynu.

*YARIMA FUDHAL*

NA
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.






44


Babban ɗan yatsan ƙafarsa ne ya fara motsawa sai kuma leɓansa da yake buɗe shi a hankali
alamun yana ƙoƙarin furta wani abu ne.


Anwar shine ya fara lura da hakan da sauri ya miƙe daga inda yake zaune ya nufi bakin gadon
yana faɗin.


"Abba kamar ya farka fa?".

Da sauri dukansu suka mime suka ƙarasa bakin gadon a dai-dai sanda yake ta ƙoƙarin buɗe
idanuwansa dishi-dishi ya fara ganinsu baya iya shaida ko suwaye hakan ne yasa shi mai da
idonsa ya rufe kafin ya sake buɗewa yana ƙoƙarin ɗago ƙafafuwansa da yake ji sun zame masa
tamkar dutse a jikinsa.
Da sauri Anwar ya fice daga ɗakin domin kirawo Doctor.

Yana fita Yarima Fudhal yana buɗe bakinsa sosai yana salati ya sake buɗe idanunsa akaro na
biyu yana duban dukkan waɗanda ke tsaye jikin gadon domin jiran farfaɗowarsa.

Idonsa na gama wayewa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya alamun yanason tuna wani
abu.

A dai-dai lokacin Anwar da Doctor suka shigo ɗakin, Doctor da Anwar suka miƙar da shi zaune
tare da karashi jikin pillow.

Doctor ya lura da matso leɓansa da yake lokaci zuwa lokaci hakan ya sanya shi kara kunnensa
dai-dai bakin sa.


"Ina AYNU?".

Kalmar da yaji ya furta kenan.

Doctor ya juyo yana duban su mai martaba dake ta sharar kwallar farin ciki.

"Tambaya yake ina Aynu".

Dukkansu suka juyar da kallonsu inda Aynu ke zaune kanta na ƙasa tana ta wasa da zoben
hannunta.

Aunty Sadiya ta ƙarasa da sauri ta riko hannunta har zuwa jikin gadon ta tsai da ita tana mai
kallon fuskar Fudhal.


Aynu dai kanta na ƙasa hannunta na rike da gefan karfan gadon tana murzawa ko kaɗan ta
kasa ɗago kanta bare har ta iya kallon Fudhal.

Shi kuwa Fudhal ƙura mata ido kawai yayi babu ko kiftawa yana son gasgata abin da
idanuwansa ke nuna mana ne, domin gani yake tamkar irin mafarkin daya saba yi ne a kullum.

Doctor yaɗan dafa kafaɗarsa yana faɗin.

"Ga Aynun taka nan".

Sannan ya juyo kansu Fulani Bingel yace.

"Kuɗan bashi ko da tea ne idan ya buƙaci wani abu bayan wannan zaku iya bashi".

Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin ya barsu.

Sarki Ubaiyd ya ƙarasa gefan gadon da Fudhal yake ya zauna tare da kallon ɗan nasa yana
faɗin.

"Sannu ya jikin naka?".

Fudhal dai bai amsa ba illa kawai kallon Baban nasa da yake.

Sarki Ubaiyd ya ci gaba da faɗin.


"Ga Aynu nan yanzu ta zama taka halak malak, domin a yau ɗin nan aka ɗaura aureta da kai,
tare da Amince wata da ta iyayenta".


Yarima Fudhal bai san sanda wani murmushi ya suɓuce masa ba sai a lokacin ya buɗe bakinsa
da ƙyar yace.


"Amma Abba Umar ɗin ya yarda?".

"E mana shine yace ma ya barmaka ka aura, yanzu Umar surikinka ne domin Babanku Magaji
Saif ya bashi auren Jalilah".

Yarima Fudhal yayi murmushi har sai da fararen haƙoransa suka baiyana, sai kuma yayi shiru
tsayin lokaci yana nazarin maganar tare da kafe Aynu da ido.

"Abba tace ai bata so na".

Jin Kalmar da ya furta ya sanya Aynu ɗago kai da sauri ta dube shi tuni idanuwansu suka sarke
da juna wani irin abu ya ziryaci Aynu tun daga babban ya tsan ƙafarta har kwakwalwarta da
sauri ta sauke kanta ƙasa domin ba zata iya jure kallonsa ba.

Yarima Fudhal yayi wani irin murmushi dana kasa gane fassarar sa kafin ya mai da kallonsa
kan Anwar yana faɗin.


"Zanyi brush".


Magaji Saif dake gefe ya taso da sauri ya kamashi kallon kallo aka hauyi tsakanin Fudhal da
Magaji Saif Fudhal ya ƙarasa saukowa ya taka kafafuwansa bisa kasa, amma can ƙasan
zuciyarsa cike take da tambayar.

"Waye wannan mai matukar kama da Abbansu sai dai kawai yafi Abbabsu girma".

Magaji Saif kamar yasan mai FUDHAL yake tunani, murmushi ya ɗanyi kaɗan yace.


"Ni ne Magaji Saif da kaji Abbanku ya faɗa wato Yaya ga mahaifinku".

Yarima Fudhal yaɗanyi murmushi kaɗan tare da guam kai alamun gamsuwa da maganar Magaji
Saif, Magaji Saif ya kamashi har toilet ya raka shi ya dawo.


Yarima Fudhal yayi brush ya fito ya zauna bakin gado, Aunty Sa'ida ta miƙo masa cofin tea ya
karɓa yahau sha, yana sha yana duban Aynu dake zaune bisa tabarma ita da Zainab suna hira
jefi-jefi murmushin da takeyi kaɗan-kaɗan shine abin da yafi komai Jan hankalinsa sosai .


Abba dake zaune gefansa yana lura da yanayinsa shi kanshi sai yanzu ya ƙara tabbatarwa da
irin ƙaunar da ɗansa kewa Aynu.


Gyaran murya ya ɗanyi kafin yace.


"Hajiya ku shirya ke dasu Sadiya muje gida a ɗauko masa abin da yake ɓukata sai driver ya
dawo daku sabida ni yau muna da meeting".

Magaji Saif yayi caraf yace.

"Sai mu tafi tare dama zanje wani waje nima, Anwar da su Aynu sai su zauna kafin su Hajiyar
su dawo sai Anwar ɗin sai ya mai dasu gida".


Haɗa kayansu Aunty Sa'ida tahauyi Yarima Fudhal na zaune gefan gadon baice dasu komai
ba, domin tun da kowa dama yasan halinsa da rashin son yin magana bare kuma yanzu.


Suna gama haɗawa sukayi masa sallama tare da fatan Allah yakara masa lafiya suka fice suka
tafi.


Suna fita Anwar ya koma inda Mai martaba ya tashi ya dubi Fudhal cike da murmushi yana
faɗin.

"Mutumina yaufa buri ya cika gaka ga Aynunka ya kamata mu Baku waje ku gaisa domin naga
alamun kuna buƙatar hakan".

Yarima Fudhal murmushi kawai yayi ba tare daya bashi amsa ba.

Anwar ya dubi Zainab.

"Muɗan basu waje Zainab su gaisa ko".


Aynu tayi saurin faɗin.

"Aa ku zauna wallahi a hakanma zamu gaisa".

Tayi maganar ba tare data ɗago kanta ba.


Anwar ya dubi Yarima Fudhal daya Kafe Aynu da ido kawai, yayi murmushi yana mai bata
amsar.

"Idan ke bakya buƙata mijinki na buƙatar hakan, tashi mu fita Zainab".


Zainab babu musu ta miƙe tana dariya suka fice daga ɗakin, suka bar Yarima Fudhal da Aynu.


Tsayin lokaci ɗakin yayi shiru tamkar babu mutane a cikin ɗakin, sai can Fudhal yayi ƙarfin
halin faɗin.


"Zo nan Aynu".

Ba musu ta miƙe ta tako har zuwa inda yake zaune gefan gado ta tsaya a gefansa ba tare data
dube shi ba.

"Babu gaisuwa bare tambayar ya jikin nawa ko haryanzu kina jin haushi nane?".


"A a, ya jikin naka?, Allah kara sauki".

Takai maganar cikin siririyar muryarta.

Yarima Fudhal yayi murmushi yace.

"Bana buƙata sai da na roka?".

"Aa kafinnayi ne ka rigani tambay...!".


Kafin takai ƙarshen maganar sai ji tayi ya kamo hannunta ya haɗa da nata, da sauri ta ɗago kai
suka hada ido ya sakar mata wani irin tsadaddan murmushi wanda itama bata san sanda ta
mayar masa da Martani ba tare da yin ƙasa da kanta.


Yarima Fudhal ya jawo ta zuwa dai-dai inda yake zaune gefan gado suna fuskantar juna ita na
tsaye.

"Na tambaye ki mana Aynu.!".

"Har yanzu kina sona kuwa?".


Aynu ta ɗago kai da niyar bashi amsa sai dai kuma taji nauyinsa game da kunyarsa sun
lulluɓeta ta sakeyin ƙasa da kanta.


Tattausan hannunsa ya sanya ya ɗago haɓarta tare da kafeta da idanuwansa mai sanya wanda
yake kallonsa jin kasala.

Aynu kasa juran kallon nasa tayi ta rintse idonta gam, Yarima Fudhal yayi ƴar dariya kaɗan.

"Wai duk kunyata kike ji haka?".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login