Showing 84001 words to 87000 words out of 88612 words

Chapter 29 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

16 Aug 2025

8301

ita ya ɗorata bisa ƙafarsa yahau shafa mata
man sai da ya gama sannan ya shiga kici-kici zare mata rigar zai sanya mata mai ɗan kauri ta
rintse idonta sosai dai-dai sanda taji ya janye rigar daga jikinta.

Sai da yagama sannan ya dubeta da murmushi yace.

"Buɗe idon sarkin tsoro, kinci abinci kuwa?".


Kai ta girgiza alamun a'a kwantar da ita ya sake yi ya fice daga ɗakin da sauri.


Mintuna kaɗan ya dawo hannunsa ɗauke da jug cike da kunun gyaɗa da soyayyar wainar kwai
a plat ya ajiye gefe ya zauna sosai kan gadon ya ɗagota yana mai bata kunun akan dole taci
badan ranta naso ba, sai da taƙoshi sosai sannan ya bata magani ya mai da ita ya kwantar ya

faɗa toilet domin yin wanka.


***


Saima zaune bisaaya daga cikin kujerun falonta daya sha kayan alatu kala-kala tana kallonta
cikin nishaɗi dajin daɗi Anwar yayi sallama ta amsa cike da fara'a tana faɗin.


"Sannu da zuwa" taanyi hug nasa ya nemi guri ya zauna ita kuma ta fara gabatar masa da
kayan abinci kala-kala tana faɗin.


"Na dai san cikinka ɗauke yake da yunwa".


"Kamar kin sani wallahi yau munsha yawo sosai da Fudhal danma na matsa dole abincin
matata zan ci, sukayi dariya baki ɗayansu.






Tun randa aka kai Jalilah atsayin matar Ya Sayyadi Umar yayi amanna da irin halaccin da
iyayenta sukayi masa ya karɓi Jalilah matsayin mata a gareshi hannu bibbiyu, sun fahimci juna
sosai a daren duk da cewa Jalilan bata magana.


Ya Sayyadi Umar kuma yaci alwashin insha Allah zai nema mata Maganii duk a inda yake,
domin tashi ɗaya yaji sonta fiye da yanda yaso Aynu domin Jalilah ma ba bayaba wajen ladabi
da biyayya da sanin ya kamata ga uwa uba kyau domin zai iya cewa tafi Aynu kyau sabida
jikinta a goge yake kuma ita fara ce.

(Tofa..! Masoyan Aynu shin kunyarda da batun Ya Sayyadi Jalilah tafi Aynu kyau kuwa?, kodai
ya faɗa ne kawai domin ya rasata?).




*******

Aynu ce keta faman shige da fice domin haɗa musu kayan kalacin safe, Yarima Fudhal na
zaune kan carpet da system a gabansa amma baki ɗaya hankalinsa nakan Aynu can dai ya
kasa daurewa tana zuwa zata wuce domin shiga bedroom ɗinsu zata ɗauko wani abi yayi
saurin janyota ta faɗo jikinsa Aynu ta rufe idonta da sauri domin bala'in kunyarsa take ji sosai.

"Buɗe idonki ki kalle ni".


Sake rintse idon tayi Fudhal yayi murmushi ya cikata daga riƙon da yayi mata yana faɗin.

"Wai har yaushe ne zaki daina jin kunya ta ne?".


Aynu ta miƙe da sauri tana murguɗa masa baki ta shige bedroom ɗin da gudu ya biyo ta yana
faɗin.


"Idan na kamaki zakiyi bayani".


Basu tsaya ko ina ba sai kan gado, Fudhal ya hau yi mata wasa mai matuƙar rikitarwa kullum
shi aikinsa kenan sai dai yayi wasa da ita son ransa ya rabu da ita , ita abin nasa har ya fara
bata tsoro har Zee na faɗin ko ba shi da lafiya ne?.





BAYAN WATA ƊAYA...!.


°°°°

Yauma kamar yanda ya saba ya shafe tsayin lokuta yana wasa da ita kafin ya sauko daga kan
gadon yana faɗin.


"Zoki gani Aynu".

Ta matso da sauri domin ta tsorata ta ɗauka wani abin ne.


Wani ɗan akwati taga ya miƙo mata yana buɗewa zobe ne ya baiyana a ciki sai walwali yake
dan kyau.

Murmushi tayi tasa hannu ta karɓa cike da murna.


Yarima Fudhal shima murmushin yayi ya cire zoben daga cikin akwatin ya kamo hannunta ya
sanya mata tare da yin kiss ɗin hannun yana faɗin.


"Mai yasa kike gayawa Zee har yanzu babu abin da ya shiga tsakanin mu?".


Aynu ta rufe idonta cike da kunya yasa hannunsa ya janye hannuwan nata suna duban juna
yace.


"Nayi hakanne kawai ba dan rashin lafiya ba, kawai inason tabbatar miki da irin son da nake
miki, wallahi Aynu zan iya ƙare tsayin rayuwa a tare dake ba tare da wani abu ya shiga
tsakanimu ba sabida soyayya ta dake gaskiya ce amma...!".


Aynu ce tasanya tattausan hannunta ta to she masa baki kanta na ƙasa take faɗin.

"Na yarda wallahi Yarima, na yarda da son da kake min ba sai ka rantse ba duniyama ta
shaida ba ni ba, ina Sonka kuma zan cigaba da sonka har ƙarshen rayuwa..!".




Kaiii...nima fa gaskiya aradu na antaya kogin soyayyar YARIMA FUDHAL kodai sakin Aynu
zansa ayi ni a antaya ni lolll.






Wannan page ɗin nakine SHAFA'ATU UMAR inayinki nima irin sosai ɗinnan wallahi.

[12/12, 12:04 PM] NANAH FIRDAUSI❤❤: *YARIMA FUDHAL*




NA
QURRATUL-AYN.




NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®.





SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.





48.




BAYAN WATA UKU.


Kwance yake bisa doguwar kujera dake cikin falonnasu lokaci-lokaci yana ɗan riƙe cikinsa
dakeyi masa ciwo, Safiyya na zaune can gefe hankalinta na kan TV ko kaɗan bata lura ba sai
kawai ganin sa tayi ya faɗo kan carpet da sauri ta miƙe ta ƙarasa wajen sa tana faɗin.


"Lafiya Jaleel mai yake damunka?".


Shi dai ya riƙe ƙam faɗi yake a hankali.

"Cikina.! Wayyo ciki na..!".


Safiyya ta miƙe da gudu ta nufi wajen Fulani Sokoto a ruɗe ta shiga falon tana faɗa mata halin
da Jaleel yake ciki da sauri sukayo waje zuwa ɓangaren su Safiyyan.


Shi kuwa sai faman malelekuwa yake yana ihun cikinsa suka ƙarasa kansa tuni Safiyya ta fara
kuka Larai ce dake biye dasu ta sake ficewa a guje zuwa wajen Sarkin gida ta faɗa masa halin
da ake ciki tuni ya nufi fada domin sanarwa sarki Ubaiyd.


Sarki Ubaiyd yace a fito dashi a kai shi asibiti, Magaji Saif dake zaune yamiƙe da sauri suka
nufi cikin gidan tun zuwansa har yanzu bai koma ba Sokoto ba Sarki Ubaiyd yaƙi bari ya tafi.


Sarkin gida ne ya tallafoshi tare da Magaji Saif Safiyya ta biyosu tana kuka aka ce ta zauna
Fulani Sokoto da Magaji Saif sune suka tafi kai shi asibitin.


Tuni ciwon Jaleel ya baza cikin gidan.


Yarima Fudhal kuwa basu san wainar da ake toyawa ba domin ko buɗe falonsu ba suyi ba
ranar duk da cewa suna zaune falon.


Aynu na bisa cinyar Fudhal akwance shi kuwa ya dage wai tsifar kai yake mata Zee zata zo
tayi mata kitso, suna hirarsu jefi-jefi cikin so da ƙauna abin dai abin sha'awa, bugun ƙofar falon
da aka hau yine yasa Fudhal miƙewa yana faɗin.


"Waye?".


"Jakadiya ce".

Ta bashi amsa ya buɗe yana faɗin.


"Yadai lafiya kuwa?".

"Babu lafiya ranka ya daɗe, Fulani ce tace a gaya maka ka shirya zaka kaita asibiti yanzu aka
tafi kai Jaleel".


"Jaleel kuma..! Mai ya sameshi?".


"Ciwon cikinsa ne ya tashi".


Yarima Fudhal yaɗan dafe kai kafin yace.


"Ina zuwa bari in shirya".

Jakadiyya ta koma shi kuma ya juya cikin falon yace da Aynu.


"Bari inyi wanka asibiti zamu".


Dake Aynu taji komai to kawai tace ya shige cikin bedroom dinsu ya barta nan falon tana cigaba
da tsifarta.


Mintuna kaɗan sai gashi ya fito cikin sauri harya shirya yayi mata sallama ya fice zuwa part ɗin
Hajiyartasu.


Ko da yaje ta shirya shikaɗai kawai take jira, yana shiga suka fito suka nufi inda motar take
suka shige Fudhal yaja suka tafi.



Suna isa asibitin suka tadda Fulani Sokoto zaune gefe tayi jugum Magaji Saif na tsaye sai
faman zarya yake, Hajiya ta nemi guri ta zauna Fudhal ya karasa inda Magaji Saif yake tsaye
yana faɗin.


"Ina Jaleel ɗin?".


"Yana emergency".

"OK".

Abin da Fudhal yace kenan ya nufi ɗakin shima, domin asibitinsa ne kuma shine babban Doctor.


Bayan shigarsa sun shafe tsayin a wanni kafin su Fudhal su fito wujuga-wujuga dasu ya kalli
Magaji Saif yace.


"Yana buƙatar akawo masa Safiyya".

"Me yasa wani abu ya sameshi ne".


"Aa adai kawotan tukunna".


Magaji Saif ya dubi driver yace.


"Yi maza kaje ka ɗauko Safiyya".


Driver ya miƙe da sauri ya fice domin cika umarnin Magaji Saif.


Yarima Fudhal ya koma cikin ɗakin da Jaleel yake ya zauna kawai yayi tagumi yana kallon halin
da dan'uwannasa yake ciki.



Lokaci-lokaci yana duba agogon hannunsa yana jira yaga zuwansu Safiyya.


Magaji Saif ya buga ƙofar ɗakin Yarima Fudhal ya share kwallar dake kawo masa ya miƙe ya
fita zuwa wajen har da Aynu ya gani tsaye ta biyo Safiyya.


Fudhal yace.

"Zaku iya shiga dukkan ku".

Ai kuwa tuni suka ɗure cikin ɗakin zuwa inda Jaleel ke kwance bisa gado abin tausayi.

Ya riƙe cikin sosai Safiyya tariƙo hannunsa tana faɗin .


"Sannu Allah ƙara sauƙi".


Jaleel ya juya yana kallonta hawaye nabin kuncinsa ya buɗe baki a hankali yace.


"Kiyi haƙuri Safiyya, ki kulamin da abin da yake cikin ki, ni bana da tabbacin zanga abin da
zaki haifomin amma inaso ki kulamin da tarbiyarsa a hannunki, bana so ɗana ya taso hannun
Mahaifiyarmu domin ina jin tsoron kada ta bashi irin tarbiyar data bamu ni da ƙanwata...!".


Yakai maganar yana mai kallon idon Fulani Sokoto dake tsaye gefe kunya duk ta cikata da
maganar da Jaleel yake.


"Momy kece duk silar halin da nake ciki a yanzu kuma kece silar rasa bakin Jalilah duk nasan
wannan, na tabbatar bada ban mugun nufinki nason halaka Fudhal da son a dole ni ne zanyi
sarauta ba da duk hakan bata faruwa ba".


"Yanzu gashi tsananin son kanki mai yaja mana Momy?".


Magaji Saif ne ya ƙarasa wajen sa ya rufe bakinsa yana faɗin.


"Aa Jaleel mahaifiyarkuce fa kada kace haka ka yafe mata dukkan abin da tayimaka kaji domin
nasan tayine cikin kuskure ka yafe mata na roƙeka wannan alfarmar".


Kai ya gyaɗa alamun to, yana duban Magaji Saif ya buɗe baki a hankali yace.

"Na yafe mata".


Yakai maganar da murmushi akan fuskarsa, ya sake ɗaga harshe yana salati sai gani sukayi

idonsa ya kafe akan Mahaifiyartasa har lokacin murmushin bai ɗauke daga kan fuskarsa ba.

Yarima Fudhal dake tsaye bakin ƙofa yana kallonsa sai yayi maza ya juya masa baya yana
share kwalla, bai aune ba saijin mutum yayi a jikinsa yana shash-sheƙar kuka ya buɗe ido yaga
ashe Aynu ce ƙara rungumeta yayi sosai yana share mata hawayen.


"Jaleel...!".


Kowa ya ɗago kai ya mai da dubansa inda sukaji ankira sunan Jaleel Magaji Saif dake rufe
idanunsa tare da Jan mayafin dake kan gadon ya karasa lullbeshi yana duban wacce ke
magana.


Jalilah ce tsaye bakin ƙofa tayi maganar kowa ya bita da kallo itama sai take kallon kan nata
domin jin maganar tayi kamar ba daga bakinta take fita ba.


Ƙarasawa tayi da gudu ta buɗe mayafin da aka lulluɓe Jaleel dashi ganin da tayi baya numfashi
hakan ya ƙara tabbatar mata da cewar ya mutu kenan?.


Da baya ta koma ta zube ƙasa tana rusar kuka Hajiyarsu Fudhal ta dafata tana faɗin.

"Kuyi hakuri Jalilah ba kuka zakuyi masa ba addu'a zakiyi masa kinji".


Jalilah ta share hawayenta tana yiwa Mahaifiyarsu Fulani Sokoto wani irin kallon tsana.

Fulani sokoto dake tsaye ƙame gefe ta kasa ɗaga harshenta tayi magana idonta ya bushe ƙam
babu ko kwalla kukan zuci kawai take.


Jalilah ta ƙarasa wajenta tana kuka take faɗin.


"Kin gani ko Momy?, kin gani kinyi silar rasa ɗan'uwa na da munanan halayenki akan duniya
kin zaɓi Jaleel ya mutu...!".


"Ba Jaleel aka zaɓa ba..! Ke aka zaba ki mutu..! kuma tabbas zaki mutu domin burin
mahaifiyarku shine, ta raba auren ki da Umar ta raba Jaleel Safiyya ta raba Aynu da Fudhal

inyaso Fudhal ya auri Safiyya Jaleel kuma zai zama Magaji a bayan Mahaifinku".


Larai na kaiwa nan ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya tana mai cigaba da faɗin.


"Boka yace dole akai ruhin Jalilah indai kina so Jaleel yayi sarauta inda dama ma sai a kashe
Fudhal ko Hajiya haka kikace ai yanzu zanje infaɗa masa".


Saita kama rawa a wajen kowa jikinsa sai yayi sanyi aka mai da hankali wajen bin Fulani
Sokoto da kallo Jalilah kuwa tuni ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, Fudhal yazo ya ɗauke ta aka kaita
can wani ɗaki domin taimakon gaggawa, ita kuma Larai yasa akayi waje da ita.


Domin tone-tone take tayi na irin abubuwan da suka dinga shiryawa Yarima Fudhal amma sai
abin ya dinga komawa kan Yarima Jaleel.


Safiyya zaman daɓaro tayi tana risgar kukar rashin mijinta ga kuma wanna mugun jin da
kunnuwanta suka jiye mata akan Momynsu Jaleel.


"Yanzu da tuni nine acikin wannan halin?, da tuni nike neman mata da shaye-shaye, Allah
yajikanka Jaleel yanzu ga abin da shaye-shayen yaja maka ya illata kayan cikin ka har yayi
sanadiyyar rasa ranka".


Yarima Fudhal keta wannan zancen aransa domin babu wanda yasan abin da yayi sanadiyyar
mutuwar Jaleel da gashi dai sauran likitocin da sukayi masa aiki, kuma Fudhal ne ya gargaɗesu
akan kasa su faɗa, sabida gujewa halin da zai shiga idan yaji tare da ƴan uwansa sai kuma
gashi mai aukuwa ta auku.
ALLAH KENAN..! AISHI BA AZZALUMIN BAYINSA BANE, SUN MANTA DA CEWA YANA
GANINSU,KUMA YANA JINSU, SUN MANTA DA CEWAR IDAN BABU DUNIYA AKWAI
LAHIRA, ALLAH KASA MU DACE KASA MUFI ƘARFIN ZUCIYARMU AMIN.
[12/12, 12:28 PM] NANAH FIRDAUSI❤❤: *YARIMA FUDHAL*




NA
QURRATUL-AYN.

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®.



SADAUKARWA:-NANESY FIRDAUSI JEBOR.





49.


Nan dai aka fice da gawar Jaleel aka tafi kai shi gida domin ayi masa wanka akaishi
makwancinsa.


Gimbiya Safiyya tayi kuka iya kuka domin iya kacin kwanakinta da Jaleel sun shaƙu fiye da
tunanin duk inda tunanin mutum zai kai.


Magaji Saif kuwa hankalina gaza kwanciya yayi daga abin da Larai ta faɗa hakan yasa yana
fita daga asibiti bai wuce gida ba sai wajen wani malami da yasani masanin fiƙihu sosai ya
zaiyane masa dukkan abin da ake ciki, malamin yace idan da dama suje yaga Jalilah .



Babu musu Magaji Saif ya ɗauki Malam har cikin ɗakin da Jalilah ke kwance asibitin suna shiga
malamin ya ƙare mata kallo yace.

"Tabbas gaskiya suka faɗa, amma ka kwantar da hankalinki insha Allahu babu abin da zai faru
daga gareta".


Malamin ya nemi guri ya zauna ya buɗe alqur'ani ya fara karantawa Magaji Saif ya nemi guri ya
zauna, malamin ya shafe kusan awa guda yana karatun kafin ya rufe Qur'an ɗin ya buɗe
jakarsa ya ɗauko wani ruwan rubutu ya nufi inda Jalilah take kwance ya zuwa rubutun a
hannunsa ya yarfa mata sau uku saiga wani Koran hayaƙi na fita daga jikinta yana gama fita ya
kuma watsa mata tayi wata irin atishawa tare da ajiyar zuciya.

Malamin ya dubi Magaji Saif yace.


"Insha Allah babu abin da zai faru, sai dai a gaya mata ta dage da azkar da tsayuwar dare tare
da yawaita salati ga Annabi Muhammad (S. A.W)".


"Domin da yawanmu mu mutane muna shagala da duniya sosai mu manta abin da Allah da
Manzonsa sukace, waɗannan abubuwa dana lissafa ba karamar kariya bace garemu, ga kuma
dumbin lada da zamu samu bayan wannan ta dalilin yinsu sai ka ka samu aljana Allah dai yasa
mu dace".

"Amin ya Allah".

"Mungode sosai malam muje in ajiyeka gida zan wuce jana'izar Yayanta ne anata jirana".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login