Showing 81001 words to 84000 words out of 88612 words
Chapter 28 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
ai ka bari kaɗan ƙara murmurewa
ko?".
Fudhal murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya mai da kansa kan TV yana kalla,
amma a zahiri ba kallon yake ba baki ɗaya tunaninsa ya tafi akan neman mafita wajen ganin
Aynu.
Can dai ya motsa ya dubi Hajiyar wadda itama shi take kallo domin tun shigowarsa taga alamun
akwai abin da yake son faɗi amma kuma ya kasa furtawa.
Hajiya tace.
"Yadai Magaji akwai wata matsala ne?".
Yarima Fudhal ya gyara zama yace.
"Ammmm..dama..dama".
"Kayi magana mana inajinka".
Yarima Fudhal ya ɗan dubi Hajiya yau baki ɗaya wata irin kunyarta yake ji haɗe da jin nauyinta
amma haka ya daure ya sake buɗe bakin yace.
"Kan maganar Aynu ce Hajiya, naje gidan Aunty Sadiya tace wai...!".
Sai kuma yayi shiru ba tare daya iya ƙarasawa ba, Hajiya tayi murmushinsu na manya tace.
"E nasan abin da kake son cewa, kayi haƙuri har zuwa sanda aka yanke kaji?".
Yarima Fudhal ya gyaɗa kai kawai ba tare daya iya cewa komai ba, domin bai zaci wannan
amsar daga bakin Hajiyartasa ba.
Haka yayi mata sallama ya koma part ɗinsu ranar ko kaɗan kasa cin abinci yayi sabida shi gani
yake tamkar gidan Aunty Sadiya babu tsaro za'a iya zuwa a ɗauke masa Aynu.
***
RANA BATA ƘARYA...!.
Cikin satin nan kullum sai Fudhal yaje gidan Aunty Sadiya amma Allah bai sanya idanuwansa
sunga Aynu ba ko da sau ɗaya, gani yakema kamar kawai faɗa akayi Aynu bata gidan.
Rana ɗayane suka kusan haɗuwa.
Ana ijibi ɗaurin auren su jaleel ranar ta shiga kitchen ɗin Aunty Sadiya domin ta ɗora ruwan
wanka sun ɗauke nepa tana ɗorawa shi kuma ya shigo kitchen ɗin neman cofi.
Inda Allah ya taimake ta tayi saurin tsugunawa dake irin kitchen ɗin nan ne mai kanta a tsakiya,
kuma bai wani tsaya dube-dube ba yana ɗauka ya fice.
Ranar kusan awanta uku a kitchen tana jira ya tafi har sai da Allah ya taimaketa akayi masa
waya ya tashi ya fice daga falon aikuwa da gudu ta ɗauko ruwan zafin ta shige ɗaki domin
itama bala'in nauyinsa takeji gani take ba zata iya haɗa ido da shi ba.
RANAR JUMA'A DA MISALIN 2:00.
Bayan saukowa daga masallaci aka d'aura auren.
JALEEL DA GIMBIYA SAFIYYA
ANWAR DA SAIMA.
Ɗaurin auren yayi jama'a sosai, Fudhal tamkar shine aka ɗaurawa auren a lokacin, shigarsu iri
ɗaya sukayi dukansu su ukun bluen yadi wanda yasha aiki irin na sarauta.
Daka kallesu dole su birgeka hardai Fudhal da Jaleel dasu ke matuƙar kama tamkar ƴan biyu
ga kayan ya amshesu sosai duk da shima Anwar ɗin ba baya ba wajen kyau da haiba.
Da dare aka fara hayaniyar kai amare gidajensu, Jaleel da Fudhal dama tuni an gyare musu
part ɗinsu nanne za'a kawo musu amaren, Anwar shi kuwa gida ya gina guda acan ƙasan layin
gidansu gidane mai kyau da tsari.
Sai da aka ɗauko amaryar Anwar aka kaita gidanta sannan aka wuce ɗaukan nasu Fudhal
mutane kaso uku aka rabu wasu suka tafi ɗaukan amaryar Fudhal wasu kuma ɗauko ta Jaleel
domin ta baro sokoto tana nan gidan Yayan Babanta, sai kuma wasu suka tafi kai amarya
Jalilah wadda tasha kwalliya da alkyabba sai buga kamshi take.
Gidan da Magaji Saif ya danƙawa Mallam Umar nanne aka kai Jalilah gidan sosai ya haɗu
dai-dai zaman mutum ɗaya.
Fulani Sokoto ranar tayi kuka mutane sun ɗauka kodan rabuwa da ɗiyarta ta ne, amma a zahiri
ba hakan ba ne baƙin ciki ne kawai ace wai ƴarta kamar Jalilah itace yau za'a kai gidan wani
baƙirin mutum kuma malamin islamiyya da bai aje komai ba bare ya bayar.
Babu yanda ba tayi da Jalilah ba akan tace bata so amma ƙememe Jalilah ta to she
kunnuwanta akan taji ta gani zatayi biyayya ga mahaifanta domin ita yanzu ba zata ce bata son
mahaifitarta ba sai dai baki ɗaya halayenta sun cire mata arai, gashi bata da bakin maganar da
zata iya yi mata maganar da dazata fahimta.
Sai dai kullum tazo ta ƙaraci bambamin faɗanta ta fita, amma Jalilah bata taɓa zuwa tayiwa Mai
Martaba zancen Mallam Umar ba tun ranar da suka kirata suka sanar da ita anɗaura mata aure
ko kan bata ji wani ciwon a ranta ba, addu'ama ta dingayi Allah yasa mijin ya sota itama ta soshi
suyi zaman lafiya da amana sosai Mai martaba da Magaji Saif sunji daɗin biyayyar Jalilah
akansu musamman Magaji Saif da kokaɗan baiyi tunanin hakan ba.
To taya kuma yanzu tashi ɗaya zataje tace musu bata so?, bayan sun bata dukkan nin yardarsu
da amincewarta.
DARE
9:30.
Misalin ƙarfe tara da rabi na dare aka kawo amaren gidan Sarki Ubaiyd, Gimbiya Safiyya da
Aynu tuni gidan ya rincaɓe da guɗar ƴan kawo amare sai kusan 11 dai-dai sannan kowa ya
watse aka bar Amare da ƙawayensu kawai.
A dai-dai lokacin ne angwaye sukayi sallama abokan Yarima Fudhal suka rakashi part ɗin sa
na Jaleel ma sukayi part ɗin Jaleel.
Zee na idar da sallah sukayi sallama tayi maza ta naɗe shinfiɗar tana tsokanar wani Mukhtar
abokin Fudhal dake ta san shi sosai.
Shi kuwa gogan naka sai faman kwaɗa murmushi yake idanuwansa kafe kan Aynu dake
zaune tsakiyar gado kanta lulluɓe da mayafi.
Nan dai akayi siyan baki cikin raha da nishaɗi tare da yi musu nasiha angwaye sukayi musu
sallama suka tafi tare da ƙawaye amarya Aynu tariƙe hannun Zee ƙam wai a dole ba zata tafi ta
barta ba da ƙyar ta lallaɓeta ta fizge hannun suka tafi.
Haka suma sauran angwaye anyi siyan baki lafiya kowannensu angwayen sunyi musu nasiha
sosai mai ratsa jiki kafin kowa ya watse dakin ya rage sai amarya da ango kawai.
Suna fita Yarima Fudhal ya matso inda Aynu ke zaune suna fuskantar juna yasa hannu ya
janye mayafin dake kanta fuskarta ta baiyana a fili sai yaga Aynun kamar ba wadda ya sani ba.
Sosai yau kyawunta ya fito fiye da koyaushe duk da ruwan hawaye dake kan kuncinta sai yaga
hakan ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba ga kuma uwa uba kamshin turarenta daketa dokar masa
hanci.
Tattausan hannunsa yasan ya ya ɗago fuskarta suna kallon juna Aynu ce tayi saurin sauke kai
ƙasa yayin da hawaye ya cigaba da bin kuncinta.
Hannu yasa ya sake ɗago fuskarta akaro na biyu yana mai share mata hawayen yace.
"Mene na kuka kuma, ko bakya farin ciki da wannan ranar ne?".
Aynu shiru tayi kawai ganin bata da niyar bashi amsa yasa shi faɗin.
"Kina da alwala?".
Kai ta gyaɗa alamun E amma acan ƙasan zuciyarta fargaba ce fal ciki.
Yarima Fudhal ya miƙe tare da cire babbar rigar dake jikinsa ya shige toilet mintuna kaɗan sai
gashi ya dawo jikinsa duk ruwa da alamun alwala yayi.
Ya buɗe wardrobe ya ɗauko abin sallah ya shimfiɗa sanann ya sake buɗe wani murfin jikin
wardrobe ɗin ya ɗauko mata hijab ya miƙa mata Aynu ta karɓa cike da mamakin hijab ɗin waye
ya bata?.
Shi yayi musu limanci suna idarwa Yarima Fudhal ya shafe tsayin lokaci yana addu'a kafin yayi
sallama ya kama kanta yayi mata addu'a sosai sannan ya dubeta ya fara yi mata tambayoyi
akan addininta kamar yanda yazo a koyarwar addinin musulunci, tana bashi amsa dai-dai da
abin da ta sani.
Sosai Yarima yaji daɗin yanda Aynu tasan addini domin shi a rayuwarsa yana son mutum
wanda ya san addininsa bare kuma matarsa uwar ƴaƴansa.
Suna gamawa yajawo ledar dake gabansa ya buɗe da ƙwalan kajini kwala-kwala guda biyu
aciki sai Freeshyo manya-manya suma guda biyu gefe guda kuma kilishi ne sai tashin kamshi
yake.
Yarima Fudhal ya miƙe ya fito zuwa falo kai tsaye kitchen ya nufa ya ɗauko musu plat da kofuna
ya dawo, da kanshi ya zuba musu freesh ɗin ya juye kilushin a plat tare da kazar.
Ya yago yakai mata bakinta takau da kai, sai da taga ya ɓata rai sannan takarɓa tana ci a
hankali sosai yanda take cin kazar ya tafi da imaninsa ya shagala a kallonta, sai da ya tabbatar
ta ƙoshi sannan shima yaci yana gamawa ya kwashe komai ya kai kichen.
Yanda ya barta haka ya tadda ita murmushi yayi kawai ya nufi wardrobe ya ɗauko wata
sleepingdress ya miƙa mata ya juya yahau cire kayansa Aynu ta ɗauke kanta da sauri yayi
murmushi domin yana kallonta.
Toilet ya faɗa da dukkan nin alamu wanka zaiyi Aynu najin ya shiga tayi maza ta cire kayanta ta
ɗauki rigar zaya saka taganta guntuwa iya gwiwa gata shara-shara tsaki tayi aranta tana faɗin
bazata iya sawa ba.
Ajiyeta tayi gefe ta mai da kayanta ta koma can ƙarshen gado ta kwanta tare da lullubɓe jikinta
da bargo.
Ko da yafito yaga rigar a gefe kallonta ya tsayayi kawai sai kuma yaga ashe tayi bacci dariya ya
ɗanyi mai sauti ya ƙarasa jikin mirrow ya shafa mai tare da feshe jikinsa da tuararuwa sannan
shima ya ɗauki wani boxer nasa ya saka yahaye gefan gadon ya kwanta tare da janyo Aynu.
Firgigit ta farka Jin antaɓata yanda ta farka ya bashi dariya sosai amma ya kanne yana faɗin.
"Ki rage kayan jikin ki zakifi jindadin baccin zafi ake fa".
Aynu ta takura waje ɗaya kawai tana sauraronsa murmushi ya sakeyi tare da matsawa inda
take ya dafa kafaɗarta da hannu biyu yace.
"Duk wannan tsoron na meye?, ki kwantar da hankalinki babu abin da zanyi miki wallahi kin
yarda da ni?".
Aynu ta gyaɗa kai alamun E.
"OK idan Kin yarda dani da gaske jeki canja kayan naki, idan kuma rigar batayi miki ba ki duba
cikin wardrobe ki ɗauki wata duk kayanki ne cike kinji?".
"To"
Abin da tace kenan tana mai saukowa daga kan gadon Yarima Fudhal yabita da kallo, shi yanda
take nuna jin tsoransa ma dariya yake bashi sosai.
*YARIMA FUDHAL*
NA
QURRATUL-AYN.
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION®.
SADAUKARWA:-NAMESY FIRDAUSY JEEBOR.
47
Wardrobe ɗin ta buɗe ta dubo wata riga mai ɗan dama-dama ta shige toilet ta saka sai kuma
ta kasa fitowa hakan yasa ta ɗaura zaninta akai tare da yafo mayafinta ta fito a hankali ta koma
gadon ta kwanta dan tunaninta yayi bacci domin ta ɓata tsayin lokaci a toilet ɗin kafin ta fito.
Shi kuwa yana jinta yana kuma kallonta duk da duhun dake ɗakin dariyarsa kawai yake
ciki-ciki.
7:00am
Bata tashi farkawa ba sai ƙarfe bakwai dai-dai da a gogon ɗakin ya buga ta buɗe ido taga
haske garin miƙa tayi tare da salati ta ganta lulluɓe da bargo daga ita sai rigar baccin data saka
kanta ko ɗan kwali babu bare kuma zanin data san ta ɗaura akan rigar da mayafin data naɗe
kanta dashi damm gabanta ya faɗi ta dafe kai tare da salati.
Miƙewa tayi da sauri ta ziro ƙafafuwansa ƙasa ta zauna bakin gadon tana sauraron taji ko yana
toilet, jin shirun da taji yayi yawa ya sata miƙewa ta nufi bakin toilet ɗin da niyar bugawa sai
kuma taga ƙofar ta buɗe ta leƙa taga babu kowa ajiyar zuciya tayi tana mai cigaba da tunanin
abin da ya faru jiya amma ta gaza tuna komai tun daga kwanciyarta kan gado bacci ya ɗauketa
bata tuna komai bayan nan.
Ganin tana ɓata lokaci da yawa ya sata shigewa toilet ɗin domin yin wanka tare da alwala.
Ko da ta fito sai gani tayi an yaye zanin gadon an bar shimfiɗar haka ta taka zuwa bakin gadon
cike da mamaki jin hayaniyar da tayi a bakin ƙofar dakin ya sanyawata juyawa da sauri.
Su Larai ta gani su uku tsaye bakin ƙofar suna wani cika da batsewa batayi aune ba sai ji tayi
sunja hannunta sunyi waje da ita tana turjewa tana komai, bata tashi ganinta ako ina ba sai filin
tsakar gidan tana ɗaga idonta ta ganta tsakiyar mutanen gidan kowa na kallonta tayi saurin
takure jikinta sabida daga ita sai rigar baccin dake jikinsa kawai aka fito da ita.
"Me kike wani jin kunya bayan kin riga kin gama zubar da mutunci tun a waje, Gimbiya Safiyya
dai ta ciri tuta domin ta kawo budurcinta gidan mijinta, sai dai ba muyi zaton Yarima fanko zai
aura ba?".
Cewar Larai kenan, Fulani Sokoto dake tsaye gefe tayi dariya tare da ƙarewa Aynu kallo.
"Waya san ma ina aka shiga aka fita?, domin ni dama tunda Fudhal ya nace nasan ba lafiya
ba da walakin goro a miya".
Tuni sauran bayin gidan suka hau salati da sallallami, zuwan Fulani Bingel wajen ya sanyasu
da katawa suna duban ta domin jin mai zata ce.
"Meye haka kukeyi kuma?".
"Babu komai surukarki dai ta zubar da mutunci da ƙimarta Larai nuna mata".
Larai ta buɗe farin bedsheet ɗin tana nunawa Fulani Bingel, Fulani Bingel ta dafe kai cike da
takaici ta girgiza kai tana faɗin.
"Wai har yaushe ne za'a bar wannan mummunar al'adar ne?".
"Babu rana kam".
Cewar Fulani Sokoto kenan tana wani cika da batsewa, Larai ta buɗe bedsheet ɗin ɗakin
Gimbiya Safiyya tuni aka hau ihu da murna gurin ya kacame kowa na tofa albarkacin bakinsa a
kan Aynu ita kuwa tuni fuskarta ta jiƙe da ruwan hawaye sai shash-sheƙar kuka take.
Tsawar fudhal da sukaji ne ya sanyasu yin shiru tsaye gefansa kuma Anwar ne kallo ɗaya
zakayi masa kasan ransa a ɓace yake sosai, takawa yayi har zuwa inda Aynu ke tsaye a takure
tana shash-sheƙar kuka sai ji tayi kawai anyi sama da ita ta buɗe ido da sauri sai ganinta tayi
ɗauke a hannun Fudhal tayi maza ta sake runtse idonta yayin da hawayen ya cigaba da bin
kuncinta.
Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gado ya kwantar da ita tare da janyo bargo ya rufa mata sabida
ganin da yayi tana kakkarwa, yasa hannu ya share mata hawayen har alokacin bata buɗe idon
ba.
Su kuwa suna ganin ya ɗauke ta tuni kowa ya kama gabansa Fulani Bingel tayi murmushi
kawai itama ta bar wajen.
Fudhal na fita bai zame ko ina ba sai ɓangaren Fulani Sokoto ya sameta ita dasu Larai anata
mai da zance da dariya tsawa ya daka musu yana duban Larai tare da faɗin.
"Ka da in sake ganin ki cikin gidan nan, ki tattara ki fice kafin in dawo".
Bai jira mai zasu ce ba ya fice daga falon Fulani Sokoto ta bishi da kallo kawai Larai kuwa tuni
ta fara tsima tare da hawaye tace.
"Kin gani ko?, Hajiya abin da nayi gudu kenan".
"Kefa sokuwa ce wallahi Larai shi ai ba shi da iko kan bayina kamar yanda bani da iko akan
nasu kwantar da hankalinki babu inda zaki je".
Yarima Fudhal ya wuce part ɗin Hajiyarsu ya sameta tare da su Anwar zama yayi tare da
gaisheta bai kuma faɗin komai ba yayi shiru kowai can dai ya buɗe baki yace.
"Wai Hajiya ba zakuyi magana adaina wannan mummunar al'adar ba?".
"Taya za'a daina Magaji?, abu ya samo asali tun kaka da kakanni mu da muka zo yanzu meye
namu a ciki?".
Yarima Fudhal yaja guntun tsaki cikin ransa yana mai mid ba tare da yace komai ba suka fito
tare da Anwar.
A hanya Anwar ke faɗin.
"Ai duk abin da ya faru laifinka ne fa Fudhal kasan al'adar gidan nan taya zakayi sake har
hakan ta faru?".
Yarima Fudhal yaja dogon tsaki yana duban Anwar.
"Kai nifa ba wannan ne a gabana ba, akwai dalilin da yasa ni yin hakan kawai".
"Kamar ya..! Mene dalilin kuma?".
Yarima Fudhal ya tsaya daga tafiyar da yake yana duban Anwar tare da faɗin.
"Ina so in tabbatar wa da Aynu irin son da nake mata, ni zan iya zama da ita har a bada ba
tare da wani abu ya shiga tsakaninmu ba".
Anwar ya bi Yarima da kallon takaici yama rasa mai zaice masa can dai yace.
"Hmmm ayi dai mu gani?".
"Zaku gani kuwa".
Fudhal ya bashi amsa suka ci gaba da tafiya suna zuwa kofar part ɗin su Fudhal sukayi sallama
Anwar ya tafi gida shi kuma ya shige wajen sa.
Inda ya barta nan ya sameta sai faman takurewa take ya taka inda take kwance da sauri ya
taɓa goshinta da wuyanta zafi sosai alamu fever ya kamata.
Yaye bargon yayi tare da miƙewa zuwa gaban mirrow ya dauko man shafawa ya ajiye gefan
gadon sannan ya koma jikin wardrobe ya buɗe ya ɗauko mata doguwar riga yellow mai ratsin
baƙi ya ajiye gefe, Aynu na kallonsa ya ɗago da