Showing 87001 words to 88612 words out of 88612 words
Chapter 30 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf
"Aa muje tare mana, inyaso na koma ni kaɗai".
Ko da suka isa anyi masa wanka da komai, su kawai ake jira suna zuwa aka sallaceshi aka
ɗaukeshi zuwa gidansa na gaskiya gidan da dukkan wani mai rai dole ne sai ya shige shi.
Su Zee dasu Baba ta Sallah Umman Aynu da Babanta duk tawowa sukayi gidan domin zaman
makoki, Aynu tayi kuka sosai da mutuwar Jaleel, Fudhal kuwa zan iya cewa yafi kowa damuwa
musamman inya tuna ata dalilin ƙiyayyarsa da Fulani Sokoto keyi masa ya rasa ransa yakanji
duniyar tayi masa zafi sosai danma ana tausarsa sabida shima Gawa taƙi rami ne.
Har Jaleel ya cika kwana uku amma Fulani Sokoto bata umm bata um-um, Jalilah ta warke
garas abinta sai dai baki ɗaya ta bar part ɗin Mahaifiyarta ta koma wajen Hajiyarsu Fudhal,
Hajiya tayita yi mata faɗa akan ta daina fushi da mahaifiyarta sai dai kawai tace.
"Ni ba fushi nake da ita ba kawai banajin daɗin ganin halin da take ciki ne".
Har akayi sadakar bakwai kowa ya watse ranar Magaji Saif ya shirya meeting da dare baki ɗaya
mutanan gidan kafin masu aure su tafi gida.
Magaji Saif yayi musu masiha sosai nasiha mai ratsa zuciya babu Wanda bai yi kuka ba a
wajen musamman ma Jalilah wanda duk nasihar akanta ne sabida fushin da take ga
mahaifiyarta take aka sanya ta ta nemi gafarta duk da cewa Fulanin bata magana.
Taro ya watse cikin jin daɗi sosai duk da cewar mutuwar Jaleel ta zame musu wani babban giɓi
a garesu amma nasihar Magaji Saif yasanya zuciyoyinsu samun nutsuwa da hakuri tare da
salama.
***
BAYAN WASU WATANNI.
Gimbiya Safiyya ta haifi ɗanta namiji an sanya masa sunan Yarima Jaleel, ba'ayi wani taron
suna ba sabida yanda haihuwar yaron da sunan da aka saka yake tunawa da dukkan ƴan gidan
rasuwar Jaleel, shiyasa Mai Martaba yace babu taron da za'ayi azo a zauna ana faman
koke-koke, yasa aka ɗauki Safiyya aka kai gida domin tayi wanka a gida.
Al'amarin Fulani Sokoto sai abin da yaƙaru yanzu bata magana ko kaɗan sai dai kawai ido,
ɓangarenta ya ɓaɓe yanzu duk taron jama'ar nan babu sai ƴan ragowar masuyi mata shara da
ɗan goge-goge, idan ka ganta yanzu a bar tausayi tayi wani irin baƙi da rama kwalliyarnan duk
babu, danma Jalilah na zuwa lokaci-lokaci dubata.
Yanzu kuma gashi cikin Jalilah ya tsufa sai dai Aynu ita ke zuwa kullum tayi mata dukkan abin
da take buƙata ta dawo part ɗinta.
Yanzu tsakanin Saima da Aynu wani zumunci ake mai ƙarfi Saima ta ƙara tabbatarwa Yarima
Fudhal na Aynu ne dole dukkan mata su haƙura duk da irin ƙaunar da suke masa kuwa, domin
shi babu wata mace dake gabansa wacce ta wuce Aynu.
Ansanya bikin Zee wata huɗu masu zuwa tare da wani malamin makarantar primary dake can
ƙasan unguwarsu, murna agun Aynu ba zata faɗu ba domin dama ita burinta ayanzu bai wuce
taga auren Zee ba.
Magaji Saif wani danƙareren gida ya bawa iyayen Aynu suka koma ya buɗewa Babanta ƙaton
shago cike da kayan masarufi yana siyarwa.
Ashe a rasuwar Yarima Jalil Magaji Saif yaga Babarsu Zee yaji tayi masa zai iya aurenta
kasancewar Mahaifinsu Zee ya daɗe da rasuwa tun suna yara kuma ba ta sakeyin wani auren
ba sai yanzu da Magaji Saif ya ganta ya koma nace aurenta zaiyi.
Nan da nan aka sanya aure sati biyu masu zuwa tare da taimakon shawarwarin Umman Aynu
domin da Baba ta Sallah ƙin amincewa tayi sai da Umman Aynu tayi ta mata nasiha sannan
tace ta amince ya turo.
Anyi bikin girma da karamci Baba ta Sallah ta tare a cikin gidansu Magaji Saif wato gidan
sarauta Aynu ba ƙaramin daɗi hakan yayi mata ba yanzu gata ga nata a kusa ai dole tafi kowa
jin daɗi, gashi bikin Zee ma anan za'ayi sabida baki ɗaya suka dawo gidan ko yaushe Aynu na
tare da Zee suna bawa juna shawarwari a tattare da su.
Yarima Fudhal ya mai da hankali sosai kan aikinsa, idan ya dawo kuma yakan zaunar da Aynu
yana koya mata abubuwan da bata sani ba na addini da na boko ganin tayi zurfi sosai shi kuma
aiki ya sakoshi gaba yanzu ya yanke hukuncin samo mata mai yi mata lesson kafin ya sanyata
School, domin so yake kafin ta shiga tasan komai data shiga akaita SS 2 ko 3 sabida tayi exam
nan da nan ta wuce university.
Hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba kullum ta zauna labarin kenan makaranta Zee tace.
"Nifa labarin skull ɗin nan ya fara isa ta mudai kawai muji labarin 'yan takwaye".
Aynu tayi dariya yana faɗin.
"Ba yanzu ba sai mum morewa amarcinmu".
Suka sanya dariya baki ɗayansu, Yarima Fudhal dake tsaye bakin ƙofa yayi sallam tafi nawa
basu ji shi ba suna hira shima dariyar yayi.
Dariyar tasa sukaji suka juya Zee tace.
"Au ashe kana tsaye?".
"E mana duk inajin hiran taku ai".
Sukayi dariya dukansu Zee tayi musu sallama ta fice, Yarima Fudhal ya riƙo Aynu tare da
rungumeta yace.
"Nima fa inason yaran nan da zaki ce ba yanzu ba so nakema tashin farko ki haifamin ƴan uku".
Aynu ta zaro ido waje.
"Haba dai uku ƙaramata dani ina laifin ɗayan ma".
"Ohh kinaso kema kenan?".
Aynu ta sanya kanta cikin ƙirjinta alamun kunya.
Dariya yayi yana mai kai bakinsa cikin kunnenta yace.
"Zo muje in baki yau tunda kin shirya".
Aynu sai ji tayi ya ɗauke ta cak sai other room
ALHAMDULILLAHI....!.
Nan muka kawo ƙarshen wannan book mai suna YARIMA FUDHAL.
Abin da muka faɗa dai-dai Allah yasa ya amfani al'umma, wanda mukayi kuskure kuma Allah ya
gafarta mana amin.
GODIYATA A GAREKU.
Mungode sosai sosai abisa ƙoƙarinku agaremu na ganin ci gaban kungiyarmu Allah ya saka da
alkhairi ya biya Ku amin.
MaryamulAbdul Kwaiseh
Adda Benaxer
Hauwa m. Jebo.
Aunty lubie mai tafsir.
Firdausi sodangi.
WANNAN BOOK SADAUKARWANE AGAREKI DUKA.
NAMESY :-FIRDAUSY JEEBOR
ALLAH YA BAR ƘAUNA.
MASOYANA.
A ko ina kuke ina miƙo gaisuwata tare da ɗumbin ƙaunarku nima kamar yanda kuke nunamin.
Zaku ji cigaban book ɗin YARIMA FUDHAL cikin BOOK mai zuwa muku nan da wani lokaci mai
suna ZUCIYA DA HAWAYE wanda Document zai zo muku basai kun jira post ba.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na
www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake
yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta
don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin
littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta
whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda
ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura
maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi
amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga
dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including
your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not
charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free,
any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending
novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our
site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or
TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
NAGODE BYEEE.