Showing 36001 words to 39000 words out of 88612 words

Chapter 13 - YARIMA FUDHAL Book Complete By Fiddausi S.A.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

8388


Ko da Aynu ta koma gida wunin ranar tayi shine sukuku, har zuwa sanda ta dawo daga
Islamiyya ta zauna gaban Ummanta tare da d'aukan littafin Hisnul-muslum tana dubawa,
Umman ta d'an kalli gefen da Aynu take zaune tace.

"Meye alak'arki da Yarima Fudhal kuma?".

Aynu ta d'ago da sauri fuskarta cike da murmushin jindad'i domin ansosa mata inda yake mata
k'yaik'ayi.

"Umma ba wani abu bane bafa, kawai dai cewa dai yayi wai yana....!".

Sai kuma tayi shiru domin jin nauyin mahaifiyarta akan maganar da zata fad'a mata.

Umma tayi 'yar dariya tare da k'arasa mata maganar da take son yi.

"Yana sonki ko?".

"Ehh".



"Aynu kenan...!, amma kinsan abin da zan fad'a miki kuwa?".

"A'a umma".

"Duk da cewa ba ganinki nake da ido ba, amma ina kallonki ta zuciyata, nasan kina son Yarima
Fudhal amma kada ki bari soyayyarsa tayi tasiri aranki da yawa domin mudai iyayanki zab'inmu

shine Ya Sayyadi Umar, duk da ba musan yanda Allah zaiyi nasa hukuncin bisa wannan
al'amari ba, amma inaso kiyi tunani Yarima yafi k'arfinmu mu iyayenki bare ke Aynu ki tsaya a
matsayinki kada ki kai kanki inda Allah bai kai kiba kinji ko?".


"Ehh Umma insha Allah zan kiyaye !".

Aynu takai maganar tana mai goge hawayen da ke bin kan fuskarta, tasan tana son Yarima
Fudhal amma kuma bazata iya jayayya da umarnin mahaifiyarta ba.


***

Misalin 6:25 na yamma.


Aynu ta dubi Ummanta tana fad'in.

"Umma bari inje wajen Zainab yau duk bamu had'uba sabida banje aiki ba, kuma ina son karb'o
wani littafi ne".

"To amma kinga yamma tayi ankusa sallar maghriba ki dawo da wuri kada Babanki yazo ya
tarar bakya nan".

"To Umma dama ba jinawa zanyi ba, ina karb'owa zan tawo".

Ta kai maganar tana mai ficewa, ko da ta isa gidansu Zainab Mamanta bata nan sai Zainab d'in
zaune tana yankan farce, Aynu tayi sallama ta shiga ta nemi guri kusa da Zainab d'in ta zauna
suka fara hira.


"Kinsan kuwa amsar da Mama ta bani dana tambayeta akan maganar nan?".

Cewar Zainab kenan tana mai duban Aynu, Aynu tace.

"A'a sai kin fad'a".

Nan Zainab ta kwashe duk yanda sumai ta sanar mata, sosai kayan cikin Aynu suka juya har
sai da ta nufi toilet ta fito ta nemi guri ta zauna tayi ta gumi tana fad'in.


"Ko kinsan d'azun nan Umma kemin maganar wai inyi baya-baya da Yarima su zab'insu
Yasayyadi Unar ne?".

Zainab taja ajiyar zuciya tana fad'in.

"Karki damu Aynu muyita addu'a dai koma waye mijinki Allah ne masani kuma shine zai zab'a
miki mijin da ya dace da ke, sannan akwai wata magana ma da zan fad'a miki".

"Ina jinki".

Aynu ta fad'a ba tare data dubi Zainab ba.


"D'azu Jakadiyya tazo tace a fad'a miki kinbar zuwa aiki sabida Mai Martaba ya bada umarnin
kada ki sake zuwa !".


A firgice Aynu ta d'ago kai ta dubi Zainab.

"Me kika ce?, to mai nayi masa ?".


"Baki masa komai ba, akan d'ansa Yarima Fudhal yace kibar aiki gidan sabida ya raba ku".

Aynu tayi ajiyar zuciya tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un !, shikenan ta faru ta k'are".

*YARIMA FUDHAL*


Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®



SADAUKARWA:-Namesy:-Phirdauceey Jeebour.




22

WASHE GARI



"Aynu lafiya kuwa !, yau ba zaki je aikin ba ne?".

Aynu da ke kwance bisa tabarma ta d'ago kai ta dubi Ummanta ta bud'e baki a hankali zatayi
magana suka jiyo ana sallama Umma ta amsa da fad'in.

"Amin wa'alaikissalam Ta Sallah shigo mana?".

Maman Zainab ta shiga d'akin, Aynu ta mik'e daga kwancen da take ta matsa waje guda
domin bawa Maman zee waje ta zauna, Aynu ta gaishe da ita, ta amsa cike da fara'a kafin ta
mai da kanta kan Umma tana fad'in.


"Umman Aynu !, Sai mukaji mummunan labari kuma ?".


"Labarin me fa?".

Umman Aynu ta jefawa Maman Zee tambaya mai makon amsar daya kamata ta ba ta.

Duban Aynu Maman Zee tayi tare da fad'in.

"A'a kardai kice Aynu bata fad'a miki ba?".

"Ni Aynu bata gayamin komai ba".

"Ai Mai Martaba Sarki Ubaiyd yace kada ta kuma zuwa aiki".

"Subhanallahi !, wani abun tayi musu ne?".

"A'a kan dai maganar yaronsa Yarima Fudhal da nayi miki magana jiya ne, to Jakadiyya tazo
har gidana ta ba da sak'on nima bana gida lokacin Zainab ta samu, amma da Aynu taje gidan
Zainab tace ta gaya mata.

Shiru d'akin yayi babu wanda ya sake furta ko kallama d'aya, sai can Umma tabud'e baki tace.


"To Allah ya kyauta daman inata kwab'ar Aynu dayi mata fad'a kancewa ta tsaya iya matsayin

da Allah ya ajiye ta, shikenan haka Allah yak'addara babu komai!".

Aynu dake zaune gefe sai tausayin mahaifiyarta ya kamata domin tasan abin da yake damun
Ummanta bai wuce toshewar hanyar samun abincinsu ba yanzu.

"Umma kiyi hak'uri dan Allah...!".

"A'a Aynu ko kad'an bikimin laifi ba, sai dai ni yakamata inbaki hak'uri, ki cigaba da hak'uri tare
da addu'a kan halin matsi da talaucin rayuwar da Allah ya d'ora mana kinji".

"Hakane komai ai mai wucewa ne Umman Aynu, wannan al'amarin dama sai addu'a".

Cewar Maman Zee kenan tana mai mik'ewa tsaye ta cigaba da fad'in.

"Ni zan koma, kuyi hak'uri dan Allah".

"Babu komai fa Ta Sallah karki damu".

Cewar Umma kenan, Aynu tabi ta da fad'in.

"A gaishemin da Zainab".

"To zataji insha Allah".


Maman Zee na fita Baban Aynu yayi sallama cikin d'akin nasu ya nemi guri ya zauna yana
fad'in.

"Wacce magana naji kunayi kuma?".

"Wallahi wai Aynu ce suka kora daga aiki kan wannan yaron".

"Wanne Yaro kuma?".

"D'an Sarkin da yace yana sonta mana".

"Wai Fudhal ko Jaleel".

"Fudhal d'inne ko Aynu?".

Umman ta fad'a tana tambayar Aynu, Aynu tayi shiru tare da sauke kanta k'asa, Baba yayi
ajiyar zuciya tare da kallon Aynun bai kuma cewa komai ba kan maganar sai tambayar da yayi
kan abinci.

"Kuna da abin da zaku dafa yau ne?".

"Ehh a kwai Baba shinkafar da akayi mana rabonta a gidan Sarki ai bama muci ta ba".

"To yayi bari infita sai in tawo da kayan miya".

"To Allah ya kiyaye".

Suka bishi da addu'a dukansu.

"Umma wai me yasa Baba baya son maganar gidan Sarki ne !, kuma naga bai damu da barin
aikin da nayi ba?".

"Karki soma tambaya akan wannan al'amari ke dai kiyi ta addu'a sosai kinji?, domin dama da
k'yar ya amince kike aiki agidan shiyasa yanzu bai damu ba akan barin aikin".


Aynu ajiyar zuciya tayi kawai tana mai bin Ummanta da kallo kafin ta mik'e ta fita zuwa tsakar
gida domin d'ora musu sanwar abinci.


***


"Komai ya rushe Anwar !, wai ya Abba yake so inyi da rayuwata ne?".

Yarima Fudhal yakai maganar yana mai goge kwallar data fiddo saman idonsa, Anwar ya dafa
kafad'arsa yana fad'in.

"Hak'uri tare da addu'a sune abin da ya kamata kayi Yarima".

"Nasan da wannan amma zuciyata bazata iya d'aukan hukuncin Abba ba!".

"Na fahimci damuwarka sosai Yarima, dole zuciyarka ta damu sosai akan rabuwa da wacce
take muradi, first love bak'aramin abu bane nasan zafin hakan, amma ka kwantar da hankalinka
mu nemi mafita mana?".

Yarima Fudhal yayi ajiyar zuciyar tare da kora sas-sanyan juice d'in dake gabansa ya lumshe
ido tare da kwantar da kai kan kujerar da yake kai, yakai kusan mintuna biyar a haka, kafin ya
d'ago kai ya dubi Anwar dake zaune har lokacin yana dubansa.

"Mene mafita Anwar?".

Anwar yayi shiru nad'an lokaci yana juya cofin glass d'in dake gabansa, kafin yad'an d'aga
kafad'arsa sama yana mai fad'awa kan kujera ya zauna ya fara magana.

"Mafita d'ayace zuwa biyu, yarinyar itama ai tana sonka sosai ko?".

"Fad'ema ai b'ata baki ne".

"Ok mafita kawai ka nemi yardar iyayenta, bayan komai ya kammala sai ka nemi aurenta ba
tare da sanin Mai Martaba ba, sannan kada ka bijirewa dukkan nin umarninsa kayi dukkan abin
da yace akan auren da yake son yi maka".


"Kana nufin in durk'usar da kaina gaban Iyayen Aynu !, daga baya intura iyayen k'arya in aureta
kake nufi kome?".

"Yes ! durk'usawa wada ai ba gajiyawa bane, dole fa wannan karon ka ajiye duk kan wani
girman kai da izzar mulki da kake tak'ama da shi ! ".

"Taya hakan zai kasance".

"Ok ka gane ko?, idan har ka samu soyayyar iyayenta suka amince da kai daga baya zamu
san yanda zamuyi su yarda su aura maka ita ba tare da sanin mai Martaba ba, bayan lokaci duk
ta hanyar da mai martaba ya dace asanar masa sai mu sanar, nasan lokacin dole yayi hak'uri
ya karb'i Aynu natsayin surukarsa".
Yarima Fudhal yayi shiru yana gyad'a kai, kafin yace.

"Babu wata mafitar sai wannan?".


"A kwai mana dama nace maka hanya biyu ce ai, idan hakan bai yi maka ba, mai zai hana kasa
iyayenta su aminta da kai sosai inyaso sai ka sanar dasu matsalarka ka mayar da Aynu
makaranta har zuwa nan da wani lokaci sai ka samu sannu a hankali ka shawo kan mai
martaba, ba dai talaka ce ba'aso ka aura ba kan lokacin ka mai dasu masu kud'i mana nasan
kana da arzik'in da zaka iya hakan nima zan taimaka maka tunda Mai martaba bai tab'a ganinta
ba kaga baka da matsala akai".

Yarima yamik'awa Anwar hannu suka tafa yana fad'in.

" Woww mutumina !, Kai amma shawaran tayi wallahi amma ta biyum zamu d'auka ita ce zata
fi tafiya dai-dai ina ganin daga baya ma kawai incanja musu gari ko?".

"Ehh mana ai duk hakan na cikin tsarin amma kayi komai cikin iya taku fa...?".

" K'arar fad'uwar abu sukaji daga dai-dai window tare da ganin giftawar inuwar mutum daga
jikin labulan da sauri sukayo waje domin ganin waye?, sai dai basu ga kowa ba kasancewar
dare ne duk da hasken fitulun farfajiyar wajen hakan bai sa sunga kowa ba.


"Ashe ba kowa ma yanzu haka k'arar wani abu ne daga wani wajen".

Yarima Fudhal ya girgiza kai yana fad'in.

"A'a tabbas mutum ne, anyi mana lab'e !, to amma waye?".

"Kada ka zurfafawa kanka tunani Yarima, yanzu haka gizon wani abu muka gani".

"Mutum ne Anwar ka yarda kawai !".

"To shikenan koma waye ma tara wata rana".

Yarima Fudhal ya koma kan kujera ya zauna, Anwar ya dubeshi yana fad'in.


"Ni zan wuce gida sai gobe ma had'u ko?".

"Ok ".

Abin da yace dashi kenan sukai musabiha ya tafi.


***

Fulani Sokoto ce kushingid'e ta tayar da kai da kusum sai cika take tana batsewa, Baiwarta
mai suna Larai tana durk'ushe gefe tana jiran unarninta.

"Kamar dai yanda aka saba Larai ga kud'innan dubu d'ari ki kaiwa Malam sai kuma dubu goma
naki kiyi kud'in mota sauran ki rik'e".

Larai ta washe baki tana mai d'aukan ledar da kud'in yake tare da fad'in.

"Uwar Magajin gobe Allah ya nuna mana cikar wannan burin namu !".

"Amin, ki kula da kyaufa Larai ban da shirme kinji ko?".

"Insha Allah komai zai tafi kamar yanda aka tsara".

Jalila dake zaune gefe sai wani faman yatsine take tana fizgarwa, ta dubi Larai a wulak'ance.

"Sai ki tashi kije ko?".

Larai ta mik'e da sauri jiki na b'ari, Jakadiyya dake shirin shiga falon jin maganar da suke ya
sanya ta tsayawa tana sauraron maganarsu duk da cewa ba yau ne karo na farko data sabajin
haka ba, amma yau hankalinta ya tashi sosai domin ba ta san me suke k'ullawa ba, jin da tayi
Larai na shirin fitowa yasa ta sanya kai cikin falon tare da sallama har suna d'an bangazar juna
da Larai.

Jakadiyya ta durk'usa tana fad'in.

"Gani ranki ya dad'e".

Kallom wulak'anci Fulani Sokoto ta watsa mata tare da fad'in.

"Yarima Jaleel yana buk'atar sababbin 'yan aiki !".

"Amma ranki ya dad'e wata uku kenan da kawo masa wasu".

"Yace sun tsufa sabbi yake buk'ata !, ko bazai samu ba ne?".

Fulani tayi maganar cike da tsawa da b'acin rai, Jakadiyya ta durk'usa tana fad'in.


"Aimin afuwa ranki ya dad'e !, angama gobe insha Allah za'a kawosu".


Fulani Sokoto ta d'an murmusa kad'an .

"Tashi kije".

Jakadiyya tamik'e ta fice daga falon.


"Bintu...! Bintu...!!".

Fulani Bingel tahau kiran wata Baiwarta dake cikin d'aki tana gyarawa, sai gata da sauri ta fad'i
agabanta tana fad'in.

"Gani ranki ya dad'e na amsa kiran ki !".

"Je ki kiramin Uwar Soro ".

"Angama ranki ya dad'e".

Ta mik'e ta fice.


Mintuna kad'an sai gasu a tare sun shigo, Fulani Sokoto ta dubi Bintu tace.

"Je ki waje zan neme ki".

Ta mik'e ta fice.

"Bamu waje Jalila".

Jalila tamik'e tana tura baki gaba ta shige d'akinta .

Falon ya rage daga Fulani Sokoto sai Uwar Soro.


"Ya dai Uwar Soro !, kwana biyu babu labari ne?".

"Fulani kenan kedai kawai fad'i abin da ki ke buk'atar fad'i".

Fulani Sokoto tayi wani guntun murmushi kafin ta mik'e zaune daga kwancen da take.


"Ina buk'atar takun k'afar Yarima Fudhal !".





Tofa wata sabuwa !, ya kuke ganin abubuwan zasu kasance ne?.


Mafitar dasu Yarima suka nemawa kansu zatai aiki kuwa?.



Me Fulani Sokoto kuma za tayi da takun k'afar Yarima Fudhal?".

Wanne abu Fulani Sokoto take shiri aikatawa haka?".



Sai naji comment naku masoyana


Team
AYNU-FUDHAL

Team
AYNU-JALEEL

Team
AYNU-YA SAYYADI UMAR

Da wanne kuke ganin Aynu ta dace?".

Ina jiran amsarku

ASHA KARATU LAFIYA.

*YARIMA FUDHAL*

Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®

SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.


23


Page d'in naki ne Munayshart tare da 'yan group naki, Allah yabar so da k'auna, ana tare har
bada.


Cikin lokaci k'ank'ani Anwar da Saima sun fara sabawa da juna, duk da cewar a b'angaren
Saima wani lokacin idan ta tuna da Yarima takanji kamar ta yaudari kanta ne, idan har ta sake

ta karb'i soyayyar Anwar ta mance da Yarima, hakan yasa wani lokacin take kakkauce masa,
amma sai dai Anwar ya wuce dukkan tunaninta duk yanda taso ta kauce masa bata iyawa
sabida salo da iya taku akan tafiyar da al'amarin soyayya na Anwar, shi kanshi yana tak'ama da
hakan, shiyasa Yarima bai bawa kowa wannan aikin ba sai shi domin yasan shine kad'ai zai iya.
YAMMANCIN RANAR ALHAMIS.


Yarima ne tsaye k'ofar gidansu Aynu lokaci-lokaci yana duban k'ofar gidan tare da kallon
agogon da ke sanye bisa tsintsiyar hannunsa.

Dai dai lokacin da ya sake d'ago kai ya kai dubansa k'ofar gidan ita kuma tana sanyo kai zata
fito, wani sanyin dad'i ya ziyarci zuciyar Yarima har yana ji kamar yaje ya rungumeta sai dai yayi
ta maza ya dake har ta k'araso zuwa gareshi fuskarta babu yabo babu fallasa sab'aninshi da
yake ta faman doka murmushi har fararen hak'oransa na bayyana waje.
Sallama tayi tare da gaishe da shi, ya amsa cike da fara'a kafin shiru ya biyo baya.

Can dai ya katse shirun da fad'in.

"Kiyi hak'uri kinji?, abisa abin da ya faru !".

"Babu komai".

Ta bashi amsa, tana d'an basarwa.

"Kina son ki koma karatu?".

Da sauri Aynu ta d'ago kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login